Feenart Hausa Novel Page 11 | Novels Elite

Feenart Hausa Novel Page 11 | Novels Elite

Feenart Hausa Novel Page 11 | Novels Elite

✨    *FEENEAT✨


 *PROFICIENT WRITTER'S*          *ASSOCIATION*  *Wattpad nusaiba* *alkamawa* 


🅿️  1️⃣1️⃣

_Cikin sa'a kuwa na daga kiran NAce mata fateema ya akayi ?

Amman inahhh Fatima takasa magana saiii siyahma siyahma take cewa ,daram haka naji akirijina, meyasa mu siyahman? Kasa min magana tayi, sai na katse wayar,aikuwa babu shiri nakoma gida.

_,INA Shiga gidan nayi tajin sheshshekar kuka. 

"nufar dakin nayi da saurina , nan nahango Fatima rungume da siyahma, da saurina na isa gurinsu xuciyata tana bugawa, dago siyahman nayi INA tambayar Fatima meya same ta? Amman Fatima ba abinda take sai kuka.,,,,, kiran sunanta nake siyahma seeyahma Amman naji siyahma shuru kara kuramata idanu nayi nan nagama batada raiii!

Sai asannan naga jini ahannuna,nace Fatima kada kicemin masoyiya ta rasu ,,,siyahma Dan Allah kitashi kada ki mutu kibarmu ,,,kitashi ki cika burikanki ,kince fa xaki Gina mana gidan kato kikaimu makka da madina ,plx kitashi yafada cike da kuka ,yadagata yayi hanyar fita. 

"Fatima ma tuni tamike ta biyomu a daddafe,,muna fita mukaci karo da wani makwabcinmu xaifita. 

,,magana yake mana Amman bama cikin hayyacinmu  fitowa yayi daga cikin motar yakamoni yashigar dani Fatima ma tashiga.

"tuni ya nufo damu asibiti SBD yagane inda xamuje yayi tunanin siyahmace ta suma ,,muna isa likitoci suka ki karbarta waii sai antaho da da sanda,,,Allah ya taimake mu wannan makwabcin naku Dan sanda ne,, nan yanuna musu id card aikuwa suka shiga da ita sukayi bincinke suka fito ,,,mukuwa muna tsaye munkasa xama. 

"doctor yafito yana mana bayani waiii fyade akayi mata kuma har mutane uku ,,,,,kuma Allah yakarbi abinsa ta rasu. 

Innalillahi ! 

"Abin nan ya matukar gigitani idanuna yayi ja, kukan ma na nemeshi narasa ,,da xanyi kuka alokacin to da sai nafi samun sauki,babu abinda ,xuciyata take sai tafasa. 

"Xahra kuwa yanke jiki tayi tafadi asume. 

"makwabcinmu ne ma yakula da faduwar fatiman.

"domin ni hankali ma kamar ba ajikina yake ba 'shafa mata ruwa yayi ta farfado tare da sakin kuka abin tausayi tana cewa itafa yar uwarta bata mutu ba. 

Akaita wajan masoyiya ta . 

Haka aka sallame mu bayan anyi komaiii bisaga taimakon makwabcinmu. 

"Haka muka nufi gida 

Aka faffadawa jama'a akayi mata wanka da sallah !

"Tofahhh !!wajan fita da gawar siyahma ne Fatima tace batasan xancen ba. 

inda takama makarar tace baxa abinne mata yar uwar taba ita  bata mutu ba.

"sai dakyar aka rurruketa tukunna aka samu aka fita da gawar. 

aka kaita gidanta na gaskiya . 

Siyahma kam tasamu jama'a 

Saidai muce Allah yajikan raiii. 

_________Haka rayuwa ta cigaba da tafiya ,muna cikin bakin ciki bama iyacin abinci.

"duk mun rame, bana iya xuwa gurin aiki sakamakon ko naje bana iyayin komai saii tunanin siyahma,kuma haka ma idan INA gida sai naga kamar xanganta. 

 gixo gidan yake mana 

"shiyasa ma nasiyar da gidan muka koma wata unguwar ,,,,,haka muka shirya nida Fatima muka nufi gidan alhaji usman domin musanar da iyayensu abinda dansu yayi. 

"budar bakinsu sai su kace su dansu bashine yayi ba kuma karsu kara kawo musu karar dansu,kuma koshi ne yayi to yayi daidai tunda mu talakawa ba abinda muka saka agaba sai kwadayi da son abun duniya. 

" Nace musu sai nakai kararsu,sukace kona kai karar mune xa musha wahala domin baxa a iya jadasu ba. 

"Dan suna da abinda xai kare su wato (kudi )

"Haka muka tafi Amman ni axuciyata ban hakura ba saina dauki fansa komin daran dadewa. 

_haka nagama karatu naxama cikakken lawyer nasamu aiki awani babban court ,inda saurayin Fatima Wanda xata aura yasamar min 

"harda xankai karan su walid. 

"Amman saurayin Fatima yahana ni,yace nabari bayanxu ba saimun samu hujjoji.

"kuma saina Tara dukiya domin karawa da babban maii kudi kamarsu ba karamin abu baneba. 

"haka nabi shawararshi. 

Sai yanxu xamu kara dasu yakarashe maganar yana me kallon Fenart wacce idanunta fal da hawaye .

"shima share nashi hawayen yayi. 

 Feenat tace  gaskiya habibi kashiga cikin wani hali wannan shine naku kaddarar ,Allah yajikan  mama da Abba da siyahma yasada su da manxon rahma. 

 amin ya amsamin ,,nace gaskiya tunda nake ban tabajin labarin da yagigita ni kamar wannan ba inaso kuma adaukaka kara ,kuma insha Allah asirinsa saiya tonu "yace insha Allah habibty. 

"yacemin xai tafi gida  haka na rakashi har gurin motarsa tukkunna na koma dakina cike da tausayin muhd. 

 *Haka rayuwarmu da* muhd ya cigaba da tafiya cike da kaunar juna. 

ga wata shakuwa dake kara shiga tsakaninmu kowane second ,yanxu ma haka INA xaune muna chart dashi yake fadamin xa ayi xaman court gobe idan Allah yakaimu, nayimasa addua Allah yabada nasara 

 *Abangaren mahaifin* walid 

Kuwa masifa yake akan wai harsu xa akai kara ,,,to shi xai nuna musu bambamcin su dashi,haka yadauko wani babban lawyer yabashi kudi sosai ,,,,yace shi akan son shima ayi watsi da karar . 

"  Haka dai aka kammala sharia inda su muhd said sukaci nasara sakamakon kwarewarshi da kuma tarin hujjojin da yabayar.

"gaskiya tayi halinta ,,,inda aka yanke wa ,su masga da goma da walid hukuncin kisa! 

 Mahaifin Walid yasha kuka naganin irin hukuncin da aka yankewa dansa tilo daya. 

Mahaifiyarshi kuwa a take anan tafadi ranga -ranga aka kaita asibiti ,raiiii yayi halinsa ,tashin hankali biyu alhaji usman yayi kukan rashin dansa da matarsa yayi bakin ciki Mara musaltuwa. 

" Abu  yataru yayi masa yawa yadawo kamar ya xauce yarasa Abu muhimmai guda biyu ,,aikuwa hakan bai sa ya nutsuba Dan haka yace saiya dauki fansa ! 

     Tofa, yanxu aka soma wasan. 

Ba karamin dadi mukaji ba sai asannan muka samu sukuni, 

Amman haryanxu munajin kewar siyama . 

 *Haka* aka saka ranar auranmu , 

Yau saura kwana hudu bikin mu,,inda nake cikin annushuwa ,,,,,gawata irin kiba da nayi na kwanciyar hankali ga kyau Dana kara, gyara kuwa inasha ,,,,fatata saii daukar idanu take duk inda naxauna saina bar kamshi . 

Ringtone din wayata naji aikuwa da dan guduna natafi daki domin nagane Wanda yake kirana SBD ringtone din shi da banne .

"dagawa nayi cikin shauki nace hello my habibi amsamin yayi yace amaryata fatan kina lpy ?eh nace kaifa ???INA lpy .

"OK good ,,kinci abinci ??eh naci kaifa ?nima haka   ,murmushi nayi najin dadin cin abincinsa domin bayawani ci sosai ,yace habibty inajin wani iri kamar  wani Abu xai sameni,,,,gaba daya xuciyata bugawa take ,subanallah Allah katsaremu insha Allah ba wani abun DA  xaifaru dakai sai alkhairi ,da yardar  Allah ,yace Allah yasa nace amin ,,nan nadauke maganar da hirar da nake masa naban dariya ,,,SBD yasashi cikin nishadi. 

"aikuwa "yasashi haka muka gama wayar cikin farin ciki . 

*Biki biki*

Biki yayi biki 

Inda yau muka tafi *meena  event* ,munyi kyau bakinmu yaki rufuwa SBD tsantsar farin ciki. 

Photo na kuwa munsha su babu adadi ,,,,anci ansha anyi rabo kamarsu calendar memo jotters  sai kayan makulashe daidai sauransu . 

Haka aka kammala taron cikin kwanciyar hankali inda akayi event har biyar Fatima ma tahada mana har biyu dayake tayi aure ta Auri wani me kudi . 

Dayake kawai daura aure akayi mata ta tare agidanta. 

______Washe gari wajan karfe shadaya aka daura mana aure ,,,,,,idan kaganni kaganshi xakasan muna cikin farin ciki ,,da daddare aka kaini gidan miji,,nikuwa ko Dan kukan nan da amare sukeyi banyiba har wata kanwar momynmu take tsokanata . 

Bayan anyi siyan baki haka suka tafi suka barni 

Har abokansa suntafi sai ga wani babban abokinsa yaxo da yake bai da wuri ba sbd daga kasar waje yadawo jirginsu ya sauka,nandai yayimana nasiha tukunna yatashi xaitafi ,,muhd yace yagaida gida ,,aikuwa abokin yamatsa akan lalle -lalle saiya karashi hanya haka kuwa akayi inda muhd yarakashi 

Shiru shiru baidawo ba 

Tun bana damuwa harna dawo inayi. 

 Nabuga masa Amman wayar na ringing baiyi picking ba saida nayi masa five missed called amman shuru

  🤔

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post