Feenart Hausa Novel Page 12 | Novels Elite

Feenart Hausa Novel Page 12 | Novels Elite

Feenart Hausa Novel Page 12 | Novels Elite

 *FEENART* 

 *BY NUSAIBA ALKAMAWA

 *PROFICIENT WRITERS* *ASSOCIATION* 

🅿️1️⃣2️⃣


____ringtone din wayata naji cikin sauri na kara wayar a kunne na,INA dagawa naji wata murya da ba ta sahibina ba,yace!  baiwar Allah kuna da alaka da me wayar nan ,barrister muhd  saed 

???

"eh matarshi ceni"OK to Allah yayi masa rasuwa yanxu muka tsinci gawar sa anan"innalillahi wainnailahi rajiun .

"anya kuwa muhd dinane yan xufa ya fita kaiii bashi bane ba, " yace baiwar Allah to ya kamata kuxo dai kudu ba, nace masa to ina xuwa ,na katse wayar .

"nan nakira Fatima nace mata taxo yanxu da akwai matsala,aikuwa  babu shiri suka taho da mijinta. 

Nan nake kora musu bayani aikuwa mijin NATA yakarbi wayata yakara kira abinda akace min ,shi aka kara ce masa nan ya kwatanta musu gidan sukace gasunan  xuwa. 

_____Ba adade ba saiga su ,da saurinmu mukaje gurin gawar muna  addua Allah yasa bashi bane ba  taya ma xa'ace muhd dina ne da yanxu muka rabu dashi.

_____muna budewa idanunmu yayimana bakin gani aikuwa atake anan na suma 

Xahra ma faduwar tayi babu raiii sakamakon xuciyarta da tabuga. 

Bayan na farfado INA ta sunbatu INA kuka gwanin bantausayi ,,,inata fisge fisge,da kalamai kala_ kala,,haka su momy ma sukaxo suka sameni acikin wannan halin, cike da fargabar kar na xauce sukaita  rarrashina. 

____Haka akayi musu wanka aka tafi dasu gidanmu na gaskiya ,sunsamu jama a ba kadan ba,ga kuma falalar ranar juma'a gari yadauka da rasuwar barrister muhd tare da kanwarshi , yan gari sunji rasuwar su sbd mutum ne mai taimako ga kirki da son talakawa. 

Jita _jita nafara ji Maganar da naji ana fada akaina waiii kilama ni nakashe mijina domin na mallake masa dukiya. 

Amman tayaya xa ace daga aure bawan Allah ya rasu  wai da alamar tambaya akaina.

 "wasu kuma suce ai idan dukiyar ne muma muna da shi kuma bisaga wane dalilin xa ace nakashe mijina duba da soyayyar da mukewa junanmu.

*Haka  rayuwa*ta cigaban min da tafiya cikin_ bakin ciki da damuwa. 

Duk dasu momy da dady suna  iya bakin kokarinsu wajan, kawarmin da damuwata, amman duk da haka damuwar nan tananan baxa tataba fita ba acikin xuciya ta ba. 

Adalilin hakan ne ma nakamu da wannan cutar 😭

 Babu shiri ya Naseeb dawowa domin baya kasar ma. 

Yaya Ansar yana us. 

 Tunda ya bugomin sau daya yayi ta'axiya baisake kirana ba .

"hakan yana damuna, amman ba yacce na'iya dashi, tunda dama haka yake baya damuwa da damuwar wani, yanxu ma dawowa xaiyi ya kammala karatunshi.

shikuwa yaya Naseeb  xaitafi karasa karatun shi, araina banji dadin tafiyar yaya Naseeb ba sbd shine hasken gidan namu , kuma idan yaganni cikin damuwa yana kokarin kawarmin da damuwarta wa, ni sainaji dama Yaya Ansar yaxauna a us din shikuma yaya Naseeb muxauna dashi anan. 

Yanxu haka yaya Ansar yadawo shikuma bro Naseeb yatafi, da yadawo ma ,doguwar magana bata hadamu, daga gaisuwa sai kuma idan baiga su momy ba, yake tambaya ta su. 

 Wata rana muna xaune a parlour yaya ansar yace! Momy bani labarin muhd tun daga farko har xuwa rasuwar shi, nan momy tabashi labarin kaff babu abinda ta rage. 

Nikuwa acikin raina nace kome xaiyi da labarin muhd din oho? 

Bayan momy tagama bashi labarin, ya tabe dan karamin bakin shi yace Allah yajikanshi! Amen momy tace, nikuwa antabo min inda yake min kaikayi sai mutuwar tasake xamo min sabuwa fil. 

Hawaye sai sharara yake a idona. 

 Kallona yayi yace ita wannan lpy? To meye na kukan, yafada yana me gallamin harara, ga wani bakin ciki dayaji. 

Nikuwa tashi nayi ina shishshekar kuka, nanufi dakina, abu biyu yahade min ga rasuwar muhd dina, ga kuma bakin cikin yaya Ansar , sai momy ce tashigo dakina tana rarrashina har Allah yasa nayi shuru. 


BACK TO STORY . 

  kuyah kuri da rashin post da banyi ba two days rasuwa akayimin ne, ina barar adduar ku, Allah yajikan kakata da rahmar sa, ameen 

  Masu bibiyata suji ko lpy na rashin posting da banyi ba, to ngd sosai Allah  yabarmu tare amin🥰

Daga taku har kullum wato Nusaiba  Alkamawa

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post