Wata Sakayya (Sai a Lahira) page 3 - Novels Elite

Wata Sakayya (Sai a Lahira) page 3 - Novels Elite

Wata Sakayya (Sai a Lahira) page 3 - Novels Elite

👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽😭😭😭😭😭😭😭     WATA SAKAYYAR....*

            (Sai a Lahira)

👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽😭😭😭😭


By                                       

 *Nusaiba Alkamawa 


No 09030567767

                  PAID BOOK

free page

••••{3}

_____Sai wajen misalin ƙarfe goma sha daya kafin Abdullahi ya shigo cikin gidan,har sannan Hafsat tana jinsa batace komai ba,tayi guru alamar tayi bacci,amma itama tasan ta gangan take,a yanda takejin zuciyarta tana bugawa,bata san lokacin dazata lafa ba har ta samu bacci mai nutsuwa da kwanciyar hankali.

Gyaran muryar da yayine bayan ya shigo ɗakin ya sake arzamata fiyeda da yanda take a da.

Haska fitilar wayarsa yayi akan fuskarta tare da sakin murmushi,ganin yanda idon sukayi firi firi kaman an jijjiga bera a buta.

"Idan har a wajena ma bazaki samu nutsuwa ba,to a ina zaki samu kenan,karki kiji tsorona kinji,bazan taba cutar dake ba,bazan bar wani abu ma ya cutar dake ba Hafsat ,ina sonki sosai,burina a kawo farinciki cikin rayuwarki bana kawo tsoro da fargaba ba.

Zuwa nayi kawai mukwanta saboda ki samu kwanciyar hankali kinji?"

Ɗaga kai tayi a hankali,yayinda bayaninsa yake ratsata sosai.

Kwanciya yayi a bayanta tareda jawota ya ɗora kanta akan kirjinsa,kana ya kashe fitilar ɗakin,ajiyar zuciya ya sake tareda raɗa mata saida a safe a cikin kunnenta.

Da farko rayuwar jin dadi Hala ta fara a gidan mijinnata,na kimanin sati guda kafin Abdullahi ya koma bakin aikinsa,saboda ko yaushe yana gidan a kusada ita,yanzu tasake dashi sosai,musamman da abinda take tsoron ya riga ya faru,dan haka yanxu ta sake kaman ba itaba.

_______Ga wata soyayya da mai gidannata yake nuna mata zallah,hakan yasa ta manta da cikin suwa aka kawota kwata kwata.

A ranar da Abdullahi yatafi wajen aiki,ta rakashi sunyi sallama a bakin ƙofarta,ta dawo domin tattare kayan da suka bata akan dainnig,dan tun zuwanta gidan babu wanda ya bata abinci domin baƙunta,daya ga haka sai ya kawomusu kayan abincinsu ishashshu sukeyi.

Sallama akayi,tun kafin tagama amsawa mai sallamar ya shigo cikin falon,ɗaga ido tayi suka haɗa ido da wata budurwa,amma kuma daga gani tafita a haife sosai.

Wani yauƙi takeyi tareda jujjuyawa tana ƙarewa wajen kallon.

"Wow haka sashennasa yake,amma yayi kyau sosai,kuma fah duk wannann kayan babu na ubanki ko ɗaya a ciki koh,duk mijine yasaka,abin kunya da Allah wadai"

 Hawayen da yake ƙoƙarin zubowa a fuskarta tayi saurin mayarwa tareda ƙaƙalo murmushi.

"Mahaifina yayimin kaya daidai ƙarfinsa,gidannkune dai sukace bai musu ba,ko yanxu aka bada dama zan saka nawan kuma na zauna dasu,hakan ba abin damuwa bane"

Ƙara cune fuska rabiatu tayi ganin Hala bata mayar mata martanin da take so ba sosai,sai kawai ta basar da wannan zancen tareda cigaba da yi mata tujara iri _iri.


Ko kallonta batayi ba ta bar wajen domin tana da aikin yi. 

Ganin duk naiman fadan da tazo dashi Hala taki kulata sai aikinta takeyi, tayi kamar bama tasan akwai wata halitta a wajan ba, goge gogenta kawai takeyi, hakan ya sake tunzura Rabi'atu, "kee dan ubanki ba dake nake magana ba" duk da Hala taji zafin zagin amma haka ta dake ba tare data kulata ba, a fusace ta fito daga falon tayi bangaran mahaifiyar Abdullahi, Hajiya inna na zaune akan kujera ta dora kafa daya akan daya taji an banko kofar falon babu ko sallama, a harzuke ta mike saboda taga wane dayin wannan kuskuran, ta dauka ko masu mata aiki ne, amma sai taga Rabi'atu ta shigo tana kuka, a firgice Hajiya inna ta rikota, "kee! lafiya kika shigo kinawa mutane kuka" cikin rashin tarbiya ta fara magana, "kinga kiyiwa matar danchan naki magana, kawai dan naje mu gaisa shine ta fara zagina, wai harda cewa in fitar mata daga gida tunda gidan bana ubana bane, kuma tace na gaya miki kemah dai dai take dake, tana nan dawowa kanki" ta karasa maganar tana matso kwalla, "kan uban chan, harni yar matsiyatan chan zata gayawa haka" tana gama fadin hakan taja hannun Rabi'atu sukayi bangaran Abdullahi.

_________Suna shiga sukaga bata falo, suna kokarin shiga bedroom suka jiyo karar kwanuka a kitchen, suna shiga suka tarar ta juya baya tana shirya kwanuka, fisgota Hajiya inna tayi, tare da kifa mata mari, "yar iska yar gidan matsiyata  harni zakice kina dai dai dani, na rasa ma mai Abdullahi ya gani a jikin wannan kwailar har daya birgesa","ai wllh Hajiya asiri sukayi masa, bakiga yadda ya susuce ba a kanta" tunda su Hajiya inna suka fara mgn Hala take kuka, ita bama marin  da aka yi mata bane ya dameta ganin yadda ake ci mata mutunci akan abinda batasan ma mai tayi ba, "ki dai bini a hankali in ba haka ba in sanya dana ya sake ki, ki koma gidan ku, a cigaba da cin tuwo da miyar kuka" tana gama fadin haka tayo waje, hankadata Rabi'atu tayi, "dole kibar gidan nan, nice dai dai da Abdullahi ba ke ba" tana gama fadin haka ta ficewa itama, kara Hala ta saki saboda kanta daya bugu da drowar kitchen din, sunji karar data saki amma ko juyowa basuyi ba suka fita daga part din.

Kusan awarta daya da rabi tana durkushe a wajan rike da kanta da yake matukar sara mata kamar zai tsage gida biyu, a daddafe ta tashi ta koma daki, kan gado tahau taci gaba da kukan ta, yanzu haka zata cigaba da rayuwa a cikin wannan gida, ta tambayi kanta amma babu mai bata amsa, a haka har bacci barawo yayi awon gaba da ita, kana kallon fuskarta kasan tasha kuka abinka da farin mutum, ga hawaye nan duk ya bushe a fuskarta ta.

"Yanzu hajiya haka zamu zuba ido muna kallo wannan yar iskar ta cigaba da raina mana wayo" ki barta dani zanyi maganin ta, gobe zamuje wajan boka nakan tsauni nida mamanki dan haka ki kwantar da hankalin ki, kamar kin zama matar Abdullahi ne" cike da jin dadin kalaman Hajiya inna ta samu kujera ta zauna tana kallon Hassana, matar yayan Abdullahi, "Hassana yaushe kika zo?","wllhi hajiya yanxu, nazo inata sallama naji shiru" hmm ki bari kawai ina chan wajan yar iskar matar Abdullahi","wllh nima hajiya na tsani yarinyar chan, kar ku damu duk ku barni da ita zanyi maganin ta" haka dai sukai ta tattauna yadda zasu bullowa Hala.

Ba ita ta tashi daga bacci ba sai bayan sallar la'asar, a gurguje ta shiga bathroom tayi wanka ta dauro alwalla, tana fitowa ta zura doguwar jallabiya ta tada salla, koda ta idar da sallar ta dade tana kaiwa Allah kukanta.


No 09030567767

Plx Share and comment.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post