Wata Sakayya (Sai a Lahira) page 4 - Novels Elite

Wata Sakayya (Sai a Lahira) page 4 - Novels Elite

Wata Sakayya (Sai a Lahira) page 4 - Novels Elite

👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽  

😭😭😭😭😭😭 


 *WATA SAKAYYAR*

        (Sai a Lahira)


👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽


By

            Nusaiba Alkamawa


 PROFICIENT WRITER's ASSOCIATION

                  


 page 4

Tana zaune akan sallayar taji ana kwala mata kira, "ina kike ko bazaki fito ba, saina shigo na fito dake da kaina" gabanta ne yayi mugun faduwa dan yanzo batasan da wacce sukazo ba, a hankali ta mike ta fito, tsaye ta tarar da Rabi'atu sai faman girgiza jiki takeyi, watsa mata pant da bireziyar hannunta tayi a fuska, wani karni ne ya doki hancin hala, "gashi nan ki wanke min su fes, badai kince sai kin zauna da Abdullahi ba, to mu zuba mu gani, banza yar gidan matsiyata" tana gama fadin haka ta fito daga falon zuciyarta fal bakin ciki, saboda ta ko,ina Hala ta fita kyau, ga diri daga saman har kasan, ga kyaun fuska, itako a tsaye take kamar   sanda.

Cikin kuka ta duka ta debi kayan, gaba daya pant din jini ne a jikinsu, shin ita wannan wace irin kazama ce, bathroom ta shiga ta fara wanke kayan tana kuka, wannan wace irin rayuwa ce ace kayan al'adar wata zatana wanke wa, kuma da suke zaginta yar matsiyata mene lefinsu a ciki, suma da Allah ya basu arzikin bawai dan ya fi son su bane, da wannan tunanin ta karasa wankin har lokacin bata daina kukan ba, shanya kayan tayi sannan ta wanke bandakin, wanka tayi saboda wankin kayan jinin nan da tayi gaba daya kenkemin jikinta takeyi, tana fitowa ta shafa lotion da humra mai kamshin gaske, drower ta bude ta dauko wani les mai kyaun gaske ta saka, zanso kuga yadda tayi kyau gashi sai zuba kamshi takeyi duk inda ta gilma.

Fitowa tayi ta fada kitchen, yau tun girkin safe bata karayin wani girkin ba, saboda wannan abin da ya faru,ita ko yunwar ma bataji, abu mai sauki ta dora saboda tasan lokacin dawowar sa ya kusa,taliya da miya ta dafa dataji kayan lambu sai kamshi takeyi, a kula ta zuba abincin ta jera akan dining,jin an fara kiran sallar magariba yasata mikewa danta sauke farali,ko minti biyu batayi da shiga daki ba Rabi'atu ta shigo tazo karbar kayanta,tun daga bakin kofar falon taji kamshi yayi mata sallama, idonta ne ya sauka akan kulolin da suke kan dining,a hankali taje ta bude ko wanne, spoon ta dauka ta tsamo nama takai bakinta, lumshe ido tayi jin dadin daya ratsa kan harshanta, "yar iskar ashe ta iya girki, aiko bazaku ci abincin nan ba" cikin hanzari ta fada kitchen sugar ta naima amma bata gani ba, idonta ne ya sauka akan robar yaji, da hanzari ta dauka ta fito,kular miyar ta bude ta zuba yajin sosai sannan ta saka spoon ta motsa, da sauri ta maida robar yajin inda ta dauko ta.

Da gudu _gudu sauri_ sauri ta fito daga part din nasu,tana tafe tana waiwayen bayanta, jitai ta fada kan mutum kara narkewa tayi a jikinsa tana shakar daddadan kamshin turaran sa, ko bata dago ba tasan wane mamallakin wannan kamshin, ture ta Abdullahi yayi ganin sai shafa sa takeyi, ko kallonta baiyi ba ya shige gida, da kallo ta bisa harya shige, lashe baki tayi, "dole ne in mallake ka ko dan na dandana irin zumar ka, nasan yadda kake kakkarfan nan dole zakayi aiki mai kyau" ta fada a fili, "ke kuma dawa kike magana" Hassana ta fada tana kallon ta, "bansani ba, yar sa ido kawai" daga haka itama ta kara gaba, tun da ta fito daga bangaran Abdullahi akan idon Hassana, duk abinda ya faru ta gani kuma taji duk abinda Rabi'atun ta fada, "ni kuwa indai ina numfashi bazaki taba mallakar Abdullahi ba" itama bangaranta ta shige bakin ciki fal zuciyarta.

Da sallama ya shiga falon, da sauri ta taso ta rungumesa tana masa sannu da zuwa, kara rungumeta yayi a jikinsa saboda shima yayi missing din matar sa, a hankali ta zame jikin ta tana karbar jakar hannun sa, ajiye jakar tayi sannan taja hannunsa zuwa bathroom ta hada masa ruwan wanka, tana kokarin fitowa taji ya rike hannunta, "ki karasa ladan ki mana" ya fada a shagwabe, "nima fa ban dade dayin wankan ba" kallon bakinta yayi yadda take motsa sa a hankali, "to yanzu ma saiki sake, kinga dazun ai ke kadai kikayi yanzo kuma tare da mijin ki zakiyi" badan taso ba haka ta biye masa suka sakeyin wani wankan, saida suka share kusan awa daya kafin su fito, kamar wata jaririya haka ya nadota a tawel, mai ya shafa mata sannan ya dauko mata wasu kayan bacci wanda dasu da babu duk daya, a kunyace ta karba ta saka, shima kayan ya saka suka fito falo yana rungume da ita.

Abincin ta zuba musu, lomar farko da yayi ya dawo da abincin bakinsa, jin yajin daya ratsa masa baki, "Sweetheart lfy kuwa","Baby kinci abincin nan kuwa?" da mamaki take kallon sa, tura mata abincin yayi gabanta, a hankali ta debo abincin takai bakin ta, da sauri ta dawo dashi, "wllhi sweetheart lfy lau nayi abincin nan bansan ta ina aka samu wannan yajin ba, kuma bari na debo maka ragowar miyar kaji" tashi tayi tana hawaye ta shiga kitchen din, da kallo ya bita shi kam ya gano daga inda matsalar take, dama tunda yaga Rabi'atu ta fito sai waige waige takeyi yasan akwai abinda ta aikata amma babu komi zasu hadu ne, miyar ta aje ta sake zuba masa wani abincin, a dadare ya sake kai loma bakinsa, amma sai yaji dadi a bakinsa, hakan ya kara tabbatar masa da aikin Rabi'atu ne, abincin sukaci suna wasa suna dariya cikin farin ciki da annushiwa. 

Koda aka kira sallar isha masallaci ya tafi,ita kuma ta shiga daki donyin salla, ana idar da salla ya dawo gida,a daki ya tarar da ita tana karatun alkur'ani mai girma, zama yayi yana sauraran yadda take karatun, tana kai aya ta rufe alkur'anin saboda ganin ya dawo, inda take aje Alkur'anin takai ta aje, tare da nade sallayar, kwanciya sukayi, addu'a yayi musu sannan ya kashe fitilar dakin, ya kunna musu marar haske, niko nace asuba ta gari ina ja musu kofa.

Tunda ta shigo take zuba kunnuwa taji fadan Abdullahi amma taji shiru, safa da marwa kawai take a falon tana jira ko zai shigo amma shiru, Hajiya inna ganin tanata zagaya falon yasa ta tmby, "lfy kuwa Rabi'atu?" murmushin yake tayi, "dama Hajiya naga Abdullahi ya dawo ne, to na dauka zaizo ya gaishe ki amma na jisa shiru gashi har karfe tara" danjim Hajiya inna tayi, "tabbas in banyi da gaske ba sai yarinyar nan ta rabani da yaro na, amma karki damu gobe za'ayita ta kare ai" da wannan zanchan suma suka tafi dakunan su suka kwanta ko wannen su da abinda ya damesa.

Washe gari ana idar da sallar asuba Hajiya inna ta dauki motarta ta fita, gidan kanwarta taje ta dauke ta suka tafi wajan boka na kan dutse, tafiya kawai sukeyi sai daf da magariba suka isa wajan,    suka shiga da baya da baya, bokan na ganin su ya tuntsure da dariya, "dama an sanar min da zuwan ku, to kunzo inda za'a share muku hawaye, so kuke ya saketa ko kuwa a haukatar da ita ko kuwa a kasheta kawai?" caraf Hajiya inna ta karbe zancen "ah kashe ta kawai"aa yaya yadai saketa kawai","aa boka ka haukatar da ita kawai tabi duniya","shiknn an gama kafin ku koma gida zaku tarar da ita a haukace" kudi masu yawa suka ajiye masa suna godiya sannan suka tashi suka fito kamar yadda suka shigo,  sannan suka shiga mota suka bar wajan.

Share fisabilillah.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post