Wata Sakayya (Sai a Lahira) page 7 - Novels Elite

Wata Sakayya (Sai a Lahira) page 7 - Novels Elite

Wata Sakayya (Sai a Lahira) page 7 - Novels Elite

👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽  

😭😭😭😭😭😭 


 *WATA SAKAYYAR*

        (Sai a Lahira)


👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽


By

            Nusaiba Alkamawa


Dedicated to my bloody sister *jiddah alkamawa* 🥰

 Free page 7

Suna daf da shiga bangaran Abdullahi sukaji amenu yana kwalawa Hajiya kira, a fusace ta juyo, "kai kuma ya'akayi?","dama naje bangaranki na tarar babu kowa, to na fito shine na hango ku, ina zakuje haka naga kunata sauri?" kwafa tayi tana fadin, "wajan mutumin banzan chan zanje, harni zai wulakanta"amma Hajiya mai yayi maki dahar ya bata maki rai haka"iyayen matar sa ne sukazo shine sai wani rawar jiki yake wajan gaidasu, ga ladabin da yake musu koni dana haifesa bayamin irinsa" ta karasa maganar tana kumfar baki, "Hajiya wannan abin da kikeson yi fa ba daidai bane, ya kamata ki kyale Abdullahi da matarsa su zauna lfy" kasake tayi tana kallonsa, "ahh lallai amenu kaima sun shanye ka, to bari kaji inku sun shanye ku ni basu shanye ni ba" tana gama fadin haka ta cigaba da tafiya Rabi'atu na take mata baya, "wllhi Hajiya indai kika shiga sai naje na fadawa Alhaji Baba duk abinda yake faruwa" cak ta tsaya ta juyo tana kallonsa da mamakin jin abinda ya fada, shiko sunkuyar da kansa kasa yayi ganin irin kallon da mahaifiyar tasa takeyi masa, kamar zata tashi sama haka tazo ta wuce ta gaban sa ta koma bangaranta, sim _sim _simm Rabi'atu tazo zata wuce ta gabansa, "keee! ya daka mata tsawa, "nasan duk abinda ke faruwa a gidan nan akwai sa hannun ki a ciki, to waike tsayama na tambaye ki, tunda kanina yace bayason ki to ki rabu dashi mana yayi rayuwar sa da matarsa lfy, kuma da kikazo kika zauna mana a gida kinata haddasa mana fitina ke bakida gidan iyaye ne sai nan" shiru tayi tana zazzare ido, saboda tana tsoransa sosai, "bace ki bani waje kafin na karya miki kafa, banza marar kamun kai" da gudu ta bar wajan har tana tuntube, shima barin wajan yayi ransa na suya.

Koda Hala taji karar bude kofa saita fito tana fadin, "Baby ka fasa fita.. maganar ta makale sakamakon ganin Mamanta da tayi tare da Gaje, ai da gudu taje ta rungumesu tana fasa ihun murna, "ki bi a hankali mana saboda abinda ke jikin ki" maganar ta subucewa Abdullahi  saboda shi yama manta a gaban suwa yake ganin matarsa nason illatar da kanta, sosa keya ya farayi yana sunkuyar da kansa kasa, a kan kujera suka zazzauna aka kara gaisawa sannan Abdullahi ya fita ya basu waje don su sake, Hala gaba daya ta rasa inda zata saka kanta don murnar ganin iyayenta da tayi, cikin kankanin lokaci ta cika musu gabansu da abinci da kayan motsa baki, saida sukaci suka koshi sannan ta kaisu dakin dake kusa da nasa don suyi salla su kuma huta, bayan sunyi sallah nan suka kara dasa wata hirar, "Hala ni wai ya zaman naki da sirikan naki, ina fatan kuna zaune lfy?"lfy lau Goggo Gaje ai bakuga yadda suke riritani ba" Gaje na kokarin bawa Hala lbrn abinda Rabi'atu tayi musu umman Hala ta girgiza mata kai alamar karta fada mata, kawai saita sauya akalar zanchan ta hanyar fadin, "to Allah ya kara dawwamar daku cikin farin ciki" da Amin Hala ta amsa saboda bazata iya fadawa iyayenta irin cin kashin da ake mata a cikin gidan nan ba, tasan muddin ta fada musu to hankalin sune zai tashi.

"Inata tmby ka kayi shiru ka kyale ni, wai waya tabo min kaine?"ki bari kawai abinda Hajiya takeyiwa Abdullahi da matar sa yayi yawa, yanzo harta kai ta kawo, Hajiya ta shiga har bangaran Abdullahi taciwa matarsa mutunci, ni babban abinda nake tsoro ma, kar suyi sanadiyar da cikin jikinta zai bare, tunda Hajiya ta nuna batason cikin"jikin Hala. dince take da ciki" Hassana ta fada tana dafe kirji tare da zazzaro ido, "to mene kika wani firgita, bafa cewa nayi iyayen ki sun rasu ba, Hala nace tana da ciki"ehh nima ba firgita nayi ba, mamaki kawai nakeyi gani nayi duka _duka yaushe sukayi auran da harta samu ciki" sake da baki amenu yake kallonta, naga wasu da zarar sunyi auran suke samun ciki, ita kuwa saida sukayi wata hudu sannan ta samu cikin"nide na gaya ne karta zo masa da cikin wani ta haifa masa dan da ba nasa ba" a fusace ya mike yana nunata da yatsa, "karna kuskura na karajin wannan maganar a bakin ki, inba haka ba zakiga matakin da zan dauka akanki" yana gama fadin haka ya fito daga falon shi garama ya bar gidan karsu hassala shi, "tab wllhi yadda ban haifa ba, itama bata isa ta haifa ba saina yi sanadin cikin nan koda zanyi yawo tsurara a duniyar nan.

kwanan su maman Hala biyu suka tafi, Abdullahi ya bada mota a maidar dasu har gida, ranar wuni Hala tayi tana kuka, Abdullahi sai aikin rarrashi yakeyi, haka dai rayuwarsu taci gaba da tafi yau dadi gobe babu dadi, awajan Abdullahi kawai takejin dadi, sai wajan Yayansa amenu a nan ne kawai take samun sukuni, kwanci tashi babu wuya a wajan Allah, yanzo cikin Hala harya shiga wata biyar, Abdullahi kuwa sai kara riritata yakeyi, "maganin zubar da cikin nan Hajiya inna ta dauko, tayi kunun gyada da yasha madara da mallo gudu hudu ta zuba a ciki, saida ta tabbatar ya narke sannan ta kwalawa Rabi'atu kira, babu jimawa sai gata tazo, "anshi maza ki kaiwa Hala, nasan maganin a ciki, yau ita da abinda ke cikinta sai sun bakunci lahira" cikin farin ciki ta karba, yanajin motsin za'a fito yayi maza ya bar wajan, da sauri ya rigata isa bangaran Hala din, a zaune ya tarar da ita tana hutawa, gaishe sa tayi tana tmby yasu Aunty Hassana, aminu cikin kokarin boye bakin cikin abinda mahaifiyar sa take son aikatawa ya amsa da lfy, ya naimi daya daga cikin kujerun ya zauna, Rabi'atu ce ta shigo babu ko sallama, amma tana ganin aminu saita sha jinin jikinta, "dama Hajiya ce tace in kawo maki" da mamaki Hala ta karba tana godiya, itako juyawa tayi ta fita, budewa tayi taga kunun gyada ne sai kamshi yake, "yaya aminu ko a zuba maka"ehh zuba min kinsan inason kunun gyada"to bari na dauko kofi" tashi tayi ta shiga kitchen , fitowa tayi dauke da kofi a hannuta amma mai zata gani babu aminu babu flask din kunu, murmushi tayi tana fadin, "ouu bazai ma jira na sammasa ba shine ya dauke flask din duka" ta fada tana komawa ta zauna akan kujera ta cigaba da daddanna wayar ta, shiko yana fita yaje ya tittilar da kunun ya wanke flask din sannan ya nufi bangaran mahaifiyar sa, da mamaki Hajiya take kallonsa ganinsa dauke da flask din, "gashi Hajiya Hala ce tace na dawo maki dashi"to harta sha ne?"ehh tasha kofi daya shine ta juye sauran tace anjima zatasha, shine ta wanke flask din tace na dawo miki dashi" to shknn kaishi kitchen" ta fada murna fal cikin ta, shiko yana fitowa ya fice daga falon, su kuwa suka zauna suna zuba kunne jin abinda zai faru.

Muna son ji daga baking ku yadda wannan littafi ya burge ku ko akasin haka, ko wani gyara dangane da wannan littafin, muna jiran ra'ayoyinku a comment.

Like

Shere

Comment.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post