A Rubuce Take (K'addarata) page 19 Hausa Novel - Novels Elite

A Rubuce Take (K'addarata) page 19 Hausa Novel - Novels Elite

A Rubuce Take (K'addarata) page 19 Hausa Novel - Novels Elite

H U G U M A

A RUBUCE TAKE

      (K'addarata)

Arewabooks: Huguma

Page 19

          Kafin ya iso tuni hajiyan ta sanya an tanadar masa abincin da yafiso har kala biyu,irin abincin da tasan zaiyi wuya ya samu a gidansa,duk da qaunar da yake masa,ta kuma hada masa lemo shima kala biyu,zobo da kuma ginger drink da aka dan matsa lemon tsami kadan a ciki qamshinsa ya fito.

           Da yake tun karfe tara na safiya ya taso,ana azahar yana shiga layinsu,jakarsa kawai ya bayar aka shiga dasu shi da drivern nashi da yake usulmi ne suka wuce masallaci.

          Ana idar da sallah yace masa zai juya ya koma kaduna,yasan akwai aikin da ya baro,saboda haka bai matsashi ba,yadai karba abincin wajen hajiyar ya hadashi dashi,yace yaci a mota,ya kuma fidda kudi masu dan nauyi yayi masa ihsani,wannan yana daya daga cikin abinda yasa abbas din ke samun biyayya da qauna gami da daukaka a wajen aikinsu,duk da biyayya dole ce a tsarin aikunsu,amma suna masa soyayya ne ta har cikin ransu saboda kyawawan dabi'unsa.

           Cikin nutsuwa ya shiga gidan nasu,yana jin farincikin ganin hajiyar tasa,jtama tana falo a zaune tana ta dakon shigowarsa,ta amsa sallamarsa ya sanyo kai falon fuskokinsu dukka dauke da murmushi.

         Kamar kullum ya duqa a qabanta ya gaidata,ta amsa masa cikin kulawa addu'a gami da tambayar lafiyarsa data iyalinsa,ya tabbatar mata da komai lafiya lau,ya kuma isar mata da saqon gaisuwa daga hafsa din,wanda a zahiri bata samu hakan ba,shi ya qirqira abinsa saboda sama mata soyayya da kuma kare martabarta a idanun mahaifiyarsa.

         Da kanta tayi serving nashi,yana cin abincin suna hira,wanda kusan abubuwane da suka dan faffaru da baya nan,ciki harda ciwon da diyar babbar yayarsu tayi

"Zanyi qoqari na shiga in sha Allah"

"Ya kamata,don ka kwana biyu bakaje mata ba,tana ta min qorafi rannan"

"In sha Allah".

           Sai da aka kira la'asar sannan ya fita a falon,yace ma hajiyan zaije wajen Suraj,amma bayan magariba zai dawo

"To Allah ya tsare,akwai maganar dama da nakeson nayi dakai"

"To bari na zauna mu gama sai na wuce"

"A'ah,jeka abunka,idan ka dawo mayi maganar,Allah ya tsare".

         Tsahon lokaci suka dauka shi da suraj din,saboda kwana biyu basu hadu ba,yanayin ayyuka da canjin muqamai da abbas din ke samu a kufi a kufi,anan suraj din ya samu damar masa qorafin


"Naji mamaki sanda naji ka ajjiye appointment dinka,dama cefa da 'yan sanda da yawa suke jira" kansa ya shafo kadan yana duban suraj din

"Nafi nutsuwa da hakanne suraj"


"To kuma gashi sun biyoka da asp ba"


"Gwara wannan kam,qarin matsayi ne,a tayamu da addu'a Allah ya bamu wuyan dauka da saukewa"


"Ameen ya rahman".


         Bayan sun idar da magariba suka sake fita da suraj din a mota ya rakashi wani waje,a hanya ya tsaya qofan wani suya spot yana kashe motar


"Kadan rakani ciki na yima hajiya siyayya mana"


"Ba damuwa muje mana",tare suka jera xuwa cikin,suna tafe suna hira har suka isa,suka wuce kai tsaye inda zasu bada order din abinda sukazo siya din.


          Sun samu 'yammata biyu tsaye gaban kantar,wanna yasa abbas din ya bada taqi a tsakaninsu,ya tsaya daga baya baya suna ci gaba da magana da suraj din,irin hirar da ta shafesu.


        Tunda suka tsaya din gaba daya hankalinta ya karkata a kansa,ba qaramun daukan hankalinta abbas din yayi ba,shigar qananun kayan dake jikinsa sun taimaka wajen fidda surarshi ta qaqqarfan namiji,har suka gama biyan abinda zasu siya din,saita bude da duba wayarta tadan matsa gefe kadan tana cewa qawarta


"Ina zuwa".


         Hankalinsa nakan suraj yana saurarensa yana saka order din abinda yakeso,har yaso yayi mistake ma saida waiter din yayi masa magana,aka hada masa komai ya irga kudin cikin wallet dinsa ya aje musu,saidai garin daukan ledan bai ankara ba ya dauki tata ledar,tana sane ta barshi har sai da isa gaban motarsa sannan yaji ana fadi cikin siririyar muryarta dake nuna zallar yauqi da gwalli


"Hi.....hi,ranka ya dade" cak ya tsaya,don har ya bude murfin motar,ya waiwayo don ganin ko dashi ake.


           Da murmushi ta dinga jifansa har ta iso,cikin tausasa muryarta tace


"Yallabai ledata ka dauke" ledar hannun nasa ya daga ya kalla,sai sannan ya lura,ya sauketa gami da miqa mata yana cewa


"Sorry"


"Ba laifi ai,hakan yayimun,kaga ko babu komai leda zata qulla mana zumunci" bai amsa mata ba illa amsar tasa ledar da yayi


"Sunana rafi'ah" tayi saurin fada ganin yana shirin shigewa motarsa


"Good,thank you ko" matsowa ta sakeyi don fa fuskanci rufewa zaiyi


"Ko zan samu digits naka?"


"Am sorry to say no" ya fada yana maida murfin motar a hankali ya rufe,sannan ya tashi motar yayi reverse suka fice daga wajen.


             "Har yanxu kana lokaci mutumina,bansan me yake fusgar hankalinsu ba haka,adan bani sirrin mana" ya fuskanci sarai abinda suraj yake fada,fuskarsa kadaram kadaham ya waiwayo kadan ya dubeshi sannan ya maida kansa ga titi


"Kai har yanzu baka girma na suraj,ana ta neman na abincin da za'a kaiwa iyali kuma wa yake ta wannan" ya fada yana shafar habarsa dake zagaye da gemun daya samu wadataccen tsafta da gyara


"Banga alama ba,don duk sanda muka fito irin haka sai wata ta taya"


"To ai sai suyita yi,ta gidanma ya ka cika da ita bare ka sake daukan wata,kayita hadama kanka rigima da zafi,bazan iya daukan wannan ba"


"Fada dai kake,bari ayi katari da wadda zata sace maka zuciya" 


"Haka kake gani" abbas ya maida masa amsa,hankali da idanunsa naga titi.


        Dariya kawai Suraj yayi,bai sake cewa komai ba suka shiga wata hirar.


          Sai daya fara sauke suraj a gida bayan ya hadashi da tashi ledar sannan ya koma gidan hajiyan.


         Bayan isha'i ya zauna sukaci abinci,kusan tare da hajiyan,saidai kowa kwanonsa daban,bayan sun kammala ya dauke kwanukan da kansa ya tattare wajen sannan ya dawo ya zauna yana fuskantar hajiyan


"Hajiya kince zamuyi magana ko?" Gyara zamanta tayi sosai


"Eh tabbas"


"To ina jinki,Allah yasa ba wani laifi nayi ba" murmushi ta sake


"Laifi abbas?,a'ah ko kadan,wani alkhairi na hango maka,na kumayi karambanin zartar maka dashi ba tare dana tuntube ka ba" qaramin murmushi ya saki


"Hajiya...ai kinfi qarfin ki yiwa rayuwata karambani,kome kika ga dama ki zartar dashi kanki tsaye kawai" kai ta dan jinjina sannan tace


"Aure na nema maka,'yar uwa ko 'yar muhsin" sosai gabansa ya fadi,abinda ya jima baiji irinsa ba tsahon rayuwarsa


"Hajiya nujood?" Ya fada cikin fargaba,don ko da ya kasance itace bazai iya musawa hajiyan ba,haka zai auretan,yarinyar dake kallonsa a mazaunin ubanta


"A'ah,widad" ajiyar zuciya ya sauke,sai yaji tashin hankalin da yake ciki din ya ragu,ya samu 'yar nutsuwa,duk da fahimci wa take nufi din ba,amma dai ya fahimci wata ce daban ba nujood ba


"Inason kaje ka ganta,duk da ina zaton zuwansu gidan nan kamar ka taba ganinta,amma wannan zuwa ne na musamman,kaje ka gabatar mata da kanka" kai yadan sunkui qasa


"In sha Allah hajiya zan saka rana sai na sanarwa muhsin din sai naje" har cikin ranta ta sake qaunar abbas din,tasan dama bashi da matsala kome kuwa tace yayi,saidai ta dauka zaiyi jayayya ko ya qalubalanci wannan danyan hukuncin nata.


          Duk yadda yaso ya fidda damuwa ya zauna suyi hira sosai amma ya kasa,jiki da zuciyarsa dukka a takure suke,dole bayan qarfe tara ya yiwa hajiyan sallama ya wuce gidansa.


         A kan hanya yana tuqi amma tunani ne fal kwanyarsa,aure?,wacece widad din ma?,oho shi bai ganeta ba,amma me hajiya ta hango masa?,sai Allah,bazai iya mata wannan tambayar titsiyen ba,da wannan damuwar da kuma tunanin ya isa gida.


           Bashi da hadi da sassan hafsa,don haka sassansa ya wuce,yabude ya shiga yana tsaye tsakar falon kamar maison tuna abinda ya kamata yayi wayarsa ta dauki sassanyan busar sarewar dake a mazaunin ringtone dinsa,don bayason ringtone mai hayaniya da yawa,mafi yawan lokutta ma yafi barin wayar tasa a vibration.


          Cikin wata kasala da gajiya da maganar hajiya ta saukar masa ya zaro wayar yana duba me kiran,hafsat dince,sai ya daga kiran yana neman kujera daya cikin falon ya zauna


"Ina ka shiga ne inata kira baka daga ba" ta fada muryarta a tsaye carrr,alamun qagauta da son samun mutum,shuru yayi yana nazartar muryarta


"Lafiya?" Ya fada da nutsatsiyar muryarsa mai nauyi,wadda ta dawo da hafsat din cikin nutsuwarta kadan,ta kuma fuskanci yanayin data masa magana baiyi dai dai ba,kishi ne keta cin ranta,har idanunta suka so rufewa,gani take kamar yana tare da wata ne shi yasa yaqi daga wayarta,


"Ah....uhmm lafiya qalau,kawai hankalina ya dan tashi da naga inata kira baka daga ba"


"Oh.....am fine,kufa?"


"Lafiya qalau muke,yara gaba daya sunyi kewarka"


"That's my babies.....kefa?" Ya fada yana danne damuwarsa,murmushi ta saki wanda ya jiyo sautinsa


"To nima nayi" ta fada tana danjin nauyi,idanunsa ya lumshe yana kuma budesu,she's not romantic woman at all,ya rasa yadda zai canzata,kamar irin matan da soyayya bata damesu ba sam,dai dai da greetings cards da yake siya mata time to time,musamman idan yayi tafiya ya dawo bata wani daukar abun da muhimmanci,wani lokaci ma idan ya kawo cards din bata ko budesu bare ta karanta,karba take ta ajjiye bayan ta bishi da SANNU.


"I miss you more than you can imagine" ya fada with softness,wanda har sai data ji tsigar jikinta ta tashi,wani abu ya tsarga mata,amma sai tace


"Allah ya qara zumunci"


"Zumunci dai?" Ya maimaita a ransa,even kalmomin da zatayi appreciating nasa bata dasu,har ya fara sabawa.


          Shurun da ya gilma tayi amfani da wannan daqiqun


"Magana da zamuyi ko ince tambaya zanyi"


"Am sorry ranki ya dade,yanzun nan na shigo gida,bari na gama shiryawa saina kiraki,inaso yau ayimin hira sosai,na gaji da yawa"


"Kai da kaje hutu?,me kayi daya gaji da kai?" Ta fadi da salon tambaya,ita sam hankalinta bai kwanciya idan basa tare


"Yawo" ya amsa mata a taqaice,sai ranta ya sosu,anya ba abinda take zato bane


"Yawo kuma abban mimi?,don Allah ka daina banso wallahi"


"It's okay" ya fada fuskarsa na fidda miskilin murmushin da bai shiryawa ba,yasan meke damunta


"Ka kira da wuri,don bacci nakeji inason na kwanta"


"Okay" yace da ita yana katse wayar gami da ajjiye ta gefe


"Hafsat hafsat,ko sai yaushe zata canza?" Yayi maganar shi da zuciyarsa,sai ya miqe yana wucewa bedroom.KI KULANI miss xoxo


DAUDAR GORA Billynabdul


RUMBUN K'AYA hafsat rano


IDON NERA Mamuhghee


A RUBUCE TAKE huguma


sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so,zasu fara fita a gobe da izinin mai duka


masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin


0022419171

Maryam sani

Access bank


Saiku tura shaidar biya ga

+234 903 318 1070


Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan

09166221261


Al'ummar nijerπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ zaku tuntubi wannan number

+227 90 16 59 91Zafafa biyar kadai keda sinqin nau'ikan kalar labarun da kukafiso jimilla a lokaci gudaπŸ€πŸ˜„


Thanks for choosing usπŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post