A Rubuce Take (K'addarata) page 20 Hausa Novel - Novels Elite

A Rubuce Take (K'addarata) page 20 Hausa Novel - Novels Elite

A Rubuce Take (K'addarata) page 20 Hausa Novel - Novels Elite

H U G U M A

A RUBUCE TAKE

      (K'addarata)

Arewabooks: Huguma

Page 20

         Sai daya gama duk abinda yakeyi ya kwanta yaja bargonsa zuwa qugu bayan ya rage hasken dakin sannan ya kirata.

           Har tayi ringing ta gama bata dauka ba,ya sake kira karo na biyu sannan ta miqe daga kwanciyar da tayi,ta jawo wayar tana sakin hamma,dan qaramin tsaki taja,banda maganar da takeso suyi nada muhimmanci da bazata daga ba,batason zancan motar yayi nisa kada taje ta zama rabon wasu,abinda kawai bataso yanzun zaice saita tsaya sunyi hirar soyayya,batasan me dame zata ce masa ba,daga qarshe kuma ya tada mata feelings ko ya isheta da fitina idan ya dawo.

         Cikin qaramin sauti tayi masa sallamar wanda baccin data fara ji ya jawo hakan,saidai shi din abun ya tabashi,har ya tada masa tsigar jikinsa,ya rufe idanunsa yana amsa mata

"Am sorry,na tasheki halan?"

"Ummm,babu komai"

"Thanks" da hanzarinta ta katsi numfashinsa

"Abban mimi ina cikin maka gyara ne shekaran jiya naga key din sabuwar mota,to yau kuma mimi ta tabo wajen ta zubda kaya,da na maida kayan banga key din ba,nace Allah yasa ba wani wajen ta jefa maka ba"

"Noo,ni na tafi dashi,motar dama ta hajiya ce,so sai na baiwa samuel nace gobe ya biyoni da ita a kawo mata,kinsan motar da ake fita da ita ta samu matsala" idan tace ga irin bacin ran da taji ya saukar mata ma ta yiwa kanta qarya,abinda taketa hasashe kenan,take kuma gudu,yanzun motar ya dauka ya baiwa hajiyan bayan yasan tana da buqata,tana ta kuma gaya masa ya canza matan bai canza ba?,ta yaya zata nuna masa ma zallar bacin ranta?

"Abban mimi amma dai kasan ina da buqatar motar nan ko?,sati nawa ina maka naci ka hanani?,amma a gabana ka siya......"

"Hafsatu" ya kirata da sunan da mafi yawa jama'a ke kiranta ba tare da ya bari ta idar da maganarta ba,kiran kuwa ya ratsa mata ko ina,yana da wata murya dake da kwarjini 

"Baki gane wacce na siyawa motat bane?,hajiyata mahaifiya ta nake magana" boyayyar ajiyar zuciya ta sauke,tana kuma qoqarin sassauta harshenta

"Bance bakayi dai dai ba ai,amma nafi buqatar motar,da sai ka karba ta wajena ayi mata gyara ka bata,tunda hajiya bako yaushe ta fiya fita ba,sai ta dade a gida bata fita ba,zata iya manage da ita" 

"Hajiyan tawa za'a bawa ragowar motarki tayi manage?" Cikin zallar mamaki ya jefa mata tambayar, jikinta daga can yayi sanyi,saidai bacin ran da takeji a zuciyarta ya hanata gayawa kanta tana fadin abinda bai kamata bane

"To menene a ciki?"

"A wajena wani abunne,idan bakisan darajarta ba ni nasan darajarta,tafi qarfin cin ragowar kowa a duniya bare taki ragowar,karki kuskura ki kaini bango da banzayen maganganunki,idan ba haka ba zaki gane kuskurenki,ki adana maganganunki basu da wani amfani a wajena,kudi dai nawa ne,zan kuma wahaltawa mahaifiya ta a duk sanda naso ba tare da shawara ko yardarki ba"

"Amma dai kasan nima ina da hakki ai a kanka ko?,tunda nima matark......"

"You are very stupid" ya fada da zafi yana datse kiran,bayason yaci gaba da saurarenta kada ta tunzarashi,idan ya tunzura baisan me zai biyo baya ba,yana kallonta tanata kiransa amma yaqi dagawa,sai ma ya maida wayar silent ya maida kansa ya kwanta yana ta furzar da iska a bakinsa ko zai samu zuciyarsa ta rage zafin da take masa.

           Bayan kiran ya tsagaita da shigowa sai kuma wani haske yayi blinking,alamun shigowar tex,wayar ya jawo da niyyar kasheta gaba daya,saidai saqon ya fito saman screen din


Tunda ni bankai wani bigire na abu mai muhimmanci a tare da kai ba,nima bazan zauna ina aikin da ba'a gani ba,zan dawo garinmu inda akasan darajata


"Mtsweew,shirme kawai" ya fada qasa qasa,ya danne switch button ya kashe wayar gaba daya ya dorata saman bedside drawer,ya sake jan duvet yana rintse idanu,saidai gaba daya baccin yaqi daukarsa,muraja'a kwanyarsa ta shiga yi masa kan halaye da dabi'un hafsat,tun daga kan aurensu kawo yau,tun kafin aurensu ya fahimci wasu baqin halaye daga gareta,banbancin ra'ayi da kuma wasu abubuwa masu yawa,ya dauka idan sukayi aure zai iya canzata,ashe yayi kuskure,babu wani sauran canji,saima abubuwa da suke ta'azzara kullum.


          Gefe daya kuma tunaninsa ya cilla kan maganarsu da hajiya,sai ya sauke ajiyar zuciya yana ambaton sunan Allah ya kawo masa agaji.


****Washegari bai tashi da wuri ba,saboda ya sanyama ransa babu inda zai fita yau din,sai wajen sha daya da rabi sannan ya shiga kitchen ya dafa irin tea dinsa ya soya qwai hudu ya dauki slice of bread ya hada dashi ya dawo falonsa ya zauna yaci,bayan ya gama ya kalli labarai kadan kafin ya canza wani program da akace masa jiya anyi da senior dinsu bai samu gani ba,bayan ya gama ya buda qofa ya karbi news paper wajen yaron dake kawo masa ya karanta,sai yayi wanka ya sanya wata jallabiya mai sulbi,wadda ta karbeshi sosai,ya daura alwala ya wuce masallacin dake gaban unguwarsu wanda suke sallah qarfe daya na rana,a qa'ida idan zai hau abun hawa zuwa masallacin zai biya 30naira amma ya zabi takawa a qafa,don tafiyar qafa ba baqon abu bane a wajensu.


         Bai dawo gidan ba sai qarfe biyu da rabi na rana,don yadan tsaya da mutane,yaron dake masa aike aike ya aika ya samo masa masa me kyau ko tuwo,sai daya buda fridge yasha ruwa mai matsakaicin sanyi sannan ya samu waje ya zauna yana qoqarin kunna wayarsa.


         Saqonni ne suka soma shigowa,kamar bazai bude ba don yana tsammanin hafsa ce,kada ya karanta abinda zai bata masa rai,sai kuma ya buda din,ba ita bace,ire iren 'yammatan dake crushing a kansa ne,yana mamakin ta inda suke samun numbers dinsa,bai ma batawa kansa lokaci ya karanta din ba ya goge saqon,yana tuna sanda yake barinsu ga wayarshi,irin tashin hankalin da sukeyi da hafsa din a kansu a lokacin,shi kuma rashin muhimmancinsu da rashin damuwa da masu saqon yasa yake mantawa ma dasu cikin wayar bare ya share kada ta gani din,yayin da kishi ke sanyata taga kamar yana sane ya barsu.


           Number hajiya ya nema ya kira,suka gaisa,ya shaida mata yau bazai fito ba yana gida kada taji shuru,fatan alkhairi tayi masa sukayi sallama,kamar ya ajjiye wayar sai yaga akwai kuma wani haqqin bisa wuyansa,don haka ya nema number hafsa din ya kira.


          Tsaf ta qaraci ringing dinta ta katse ba'a daga ba,sai ya sake kira amma sai aka gaya masa a kashe take,yayita qoqarin kira ana maimaita masa a kashe take,sai ya ajjiye wayar ya haqura,dai dai lokacin yaron da ya aikata din ya dawo ya karba saqon ya sallameshi.


             Sai da yaci abinci ya nutsa sannan ya kira suraj,suka gaisa suka taba hirarsu sannan ya buqaci ganinsa


"Yau bana gari,na danyi balaguro azare,amma yau din zan dawo,zan sameka gida gobe"


"Yayi,babu damuwa,saina jika" sukayi sallama.


        Wunin ranar a gida yayita shi kadai,yanata juya maganar auren da hajiyan ta nema masa,saida yamma ne ya fita farfajiyar gidan ya motsa jikinsa,ya danyi strolling cikin layinsu zuwa baya sannan ya dawo ciki.


        A farfajiyar gidan ya sanya musu kujeru shi da suraj,sannan ya dafo musu black tea wanda yasha kayan qamshi da ganyayyaki masu dadi,ya zubo musu a wata buta me hade da wasu irin cups ya zuba ya miqawa suraj,sannan yaja kujera yana zama


"Kai....abbas badai iya dafa tea ba wallahi"


"Zaka fara ko?" Kai ya girgiza yana dariya


"Kasan Allah?,sai an tara mata da yawa basu iya dafa tea kamar haka ba" baice komai ba illa kai nasa cup din baki da yayi,saboda yasan haka dinne,koda a cikin gidansa ma,don yawancin lokutta ya gwammaci ya tashi ya dafa tea dinsa da kansa akan yasa hafsat ta dafa masa,indai kaga ya sha nata to lalura ce babu yadda zaiyi.


          Suna shan tea din suna taba hirar da bata qarewa tsakaninsu,suraj din aboki ne na tun lokacin quruciya har zuwa girma,kuma har yanzun kusan shine babban abokinsa sannan muhsin ya biyo baya.


           "Kace kana son ganina,me ya faru?" Cup din abbas ya ajjiye,yana hade yatsun hannunsa guri guda,sannan yayi crossing qafafuwansa suma yana duban suraj din,sai kuma yadan shafi goshinsa kadan sannan ya fara magana


"Bansan ta ina ma zan fara maka bayani ba suraj,hajiya ce ta nema min auren 'yar yayan muhsin"


"Ummm,kaga dan gata...kai yanzun ma auren sai an nema maka,bana fari ba ba komai ba?"


"Akwai matsala suraj" da dan mamaki saman fuskarsa yake dubansa


"Matsala ta meye?,matar ce bata yi maka ba ko kuwa?" Kai ya girgiza


"Ba wannan maganar ake ba,don ko fuskarta ban sani ba,suraj cikin gidana akwai matsala sosai,ban kuma gama solving matsalar ba ta yaya zan qara aure suraj? Da shegen kishin hafsa zanji ko kuma da sabon auren da nayi?,beside ma kwata kwata banajin ina da cikakken lokacin fuskantar matsalolin mata bayan wadda nake ciki" Murmushi suraj din yayi cikin kwanciyar hankali,ya kuma gyara zamansa da kyau,shi kam kamar hajiya ta shiga tunaninsa ne,wannan abun da tayin shawarar da ya dade yana son bawa abbas din,amma kasancewarsa ba mai magana ba,ba kuma me fadan sirrinsa ba yasa ya qyaleshi ya zuba masa idanu,duk da cewa mutumin da yake da matsayi a wajensa kamar suraj dake shiga gidansa lokaci bayan lokaci zai fuskanci akwai damuwa a gidan,daga fannin tsafta kawai zakasan akwai nakasu,tunda tsafta da qazanta basa boyuwa


"To ai kai abinda baka sani ba,wannan auren shine hanyar gyaruwar duk wata matsala taka da damuwa"


"Kamar yaya?" Ya tambayeshi yana dan yamutsa girarsa 


"Bari nayi maka gwari gwari,yawancin mata suna qoqarin ganin sun gyara tsakaninsu da mazajensu ne a sanda suka qara aure,gudun kada kishiyar data shigo taga gazawarsu,ko ta qwace musu miji ka fahimta?,to sai kaga itama ta zage damtse don kar a barta a baya,gefe guda kuma ga kulawa daga amarya kana samu,kowacce qoqari take taga itace star a wajenka" shuru abbas yayi kawai yana jin suraj,mai daki shi yasan inda yake masa yoyo,baya tunanin qarin aurensa zai zama gyara ga hafsat,amma bai san ikon Allah ba,kawai abu daya ya sani,ko ransa hajiya tace ya cire ya bayar zai iya,bare wannan buqatar da bata fi qarfin ikonsa ba,ya sauke ajiyar zuciya yana zama sosai cikin kujera manyan idanun san nan akan suraj


"Hajiya tafi qarfin komai a wajena suraj,batun rashin karba ma bai taso min ba,kawai inason jin yadda za'ayi" dariya yayi ya koma ya jingina da kujera


"Ya kuwa za'a yi,kawai ka shirya kaje kuga juna kai da ita,sai mu fara shirin biki".


*****Tunda hajjaa ta gaya mata saura kwanaki biyar ta tafi kano take murna da zumudi,kullum cikin shirya kaya take,ko ta shirya sai ta fiddasu ta sake shiryawa,kowa a gidan dariya yake mata yana tsonakarta,ranar da nujood ta tsokaneta da cewar


"Dama abba yace an fasa" fada suka kusa yi,taqi kula nujood din wunin ranar,saida hajjaa ta shiga batun ta musu sasanci.


          Saura kwanaki uku ta tafi da yamma suna kitchen suna ma hajjaa yanke yanken kayan miya,da yake tun zuwansu hajjan ke hadasu su shiga kitchen tare,ko daya widad din bata da son jiki,kuma tana sha'awar yin girkin dama,ummu ke hanata tana ganin kamar zata qone ko kuma wani abun zai sameta.


          Uncle muhsin ne ya shigo,dawowarsa kenan daga aiki,kai tsaye ya wuto kitchen din ya tsaya bakin qofa ya leqo yana tsokanarsu


"Manyan 'yammata ne ke girki yau kenan" murmushi hajjaa tayi 


"Aiko dai yau su abba za'a ci dadi"


"To Allah ya taimaka,dan zo mana minti uku"


"To abba" ta fada tana tsame hannunta daga abinda take tabi bayansa.


            Sai da suka shiga bedroom dinsa,ta tayashi ya rage kayan jikinsa sannan yace mata


"Widad fa gobe zatayi baqo,hajiya da kanta ta kirani ta gayamin gobe abbas zaizo suga juna" baki hajjaa ta kama tana murmushi


"Ikon Allah,abu kamar wasa yana shirin zama gaske,to Allah dai ya doramu akan 'yar rigimar hajiyan,tunda dai abbas ba shine na farko ba"


"Ba komai in sha Allah,idan sun gama girkin ki turon ita nayi mata magana da kaina"


"Yafi dai abba" sai yayi dariya


"Na fuskanci tsoro dai kike"


"Wallahi abba,Allah dai ya tabbatar da alkhairi,ya kauda fitina"


"Ameen ya rahman" ya amsa mata yana nufar bandaki,ita kuma ta baro dakin da zummar zuwa ta kawo masa abun sha kafin girkin ya kammala.KI KULANI miss xoxo


DAUDAR GORA Billynabdul


RUMBUN K'AYA hafsat rano


IDON NERA Mamuhghee


A RUBUCE TAKE huguma


sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so


masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin


0022419171

Maryam sani

Access bank


Saiku tura shaidar biya ga

+234 903 318 1070


Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan

09166221261


Al'ummar nijerπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ zaku tuntubi wannan number

+227 90 16 59 91Zafafa biyar kadai keda sinqin nau'ikan kalar labarun da kukafiso jimilla a lokaci gudaπŸ€πŸ˜„


Thanks for choosing usπŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post