A Rubuce Take (K'addarata) page 34 Hausa Novel - Novels Elite

A Rubuce Take (K'addarata) page 34 Hausa Novel - Novels Elite

A Rubuce Take (K'addarata) page 34 Hausa Novel - Novels Elite

H U G U M A
A RUBUCE TAKE
      (K'addarata)

Page 34


         Batulu dake zaune gefe tunda suka shigo gidan ta tabe baki,itakam ba haka taso ba,abubuwa da dama ta samesu ba a yadda take fata ba

"To da alama dai uwar gidan nan tayi sake da yawa" ta fadi can qasan ranta,babu abinda take tunawa illa zamansu da fatima kafin su samu tabar musu gidan,koda yaushe mahmud ya tashi fatima dai.....fatima ce,basu samu salama ba saida tabar gidan,ko yanzun sun san cewa bawai tanar zuciyarsa bane gaba daya,rayuwarsa dai ta bari.

         Basuci da yawa ba suka ture abincin,can bayan awa daya saiga wasu sabbin coolers din,suna shigowa hajjaa ta gane daga gidan hajiyan abbas ne

"Yanzu zakuci abinci ku ture" ta fada tana dariya sanda take bude coolers din,lafiyayyen abinci ne sosai,harda wani na daban tace na widad ne,sai ta miqawa nujood

"Kai mata daki taci" nujood ta sutumi qawatacciyar warmer din dake fidda qamshi tun kafin ta bude ta wuce dakin da suka baro widad din. Su kuma a sannan suka sake sukaci suka qoshi.

          Saman katifa ta sameta,tana ta daddanna wayarta,wadda har yanzu batasan amfaninta ba idan ba game ba,dab da zata taho dai anty madeena ta saka mata numbers din mutane,ta kuma koya mata yadda zatayi wasu abubuwan

"ga abincinki inji surukarki" nujood ta fada tana dariya,mayafin kanta tana gefe ta galla mata harara

"Wai meye haka don Allah nujood"

"Allah da gaske hajiya ce tace naki ne" ta zauna gefan widad din tana bude warmer din

"Kedai kinji dadinki,kowa sai tattalinki yakeyi,kinga gidanki widad?,kinga kitchen dinki?,mtsewww,inda abbana zai yarda nima auren nan zance ayimin" kallonta kawai widad din keyi,ita kuma ji take dama itace su,tun sanda ummu ta fara mata fadan komai yace tayi tayi ta soma jin wani abu mai kama da takura ya sauka arayuwarta,kullum zancan ummu 

"Mijinki ne,babu musu a tsakaninku,ki girmamashi kamar yadda zaki girmama babanki da alhaji dani,ya fini matsayi yafi babanki matsayi" to wai banda abun ummu ta yaya zatace ya fisu matsayi?,idan tace tayi girmamashi tayi masa biyayya ta yarda da wannan,amma banda finsu matsayi (hankalinta baikai wajen ba).

          Tare suka soma cin abincin da nujood,tana ta bata labarin kayan da aketa jera mata, murmushi kawai takeyi,ita.mamaki abun yake bata,wai duk girman abu sai ace nata ne,har nan ma wai gidanta ne?.

          Koda suka gama saita labe ta cikin labule tana ganin yadda ake shirya falon,nujood na sake zugata ta tsaya ta kalla,har sai data gaji sannan ta koma ta zauna

"Wallahi idan nice ko?, tabdi,sha'anina zansha babu takuramin" ta fada tana fadawa saman katifar,sai suka qyalqyale da dariya a tare.

         Da daddare aka sake kawo musu wani,muneer qanin abbas ya shigo da kansa bisa wakilcin abbas din,yayi musu sannu da zuwa,ya kuma tabbatar basa buqatar komai,sannan ya ajjiye musu kudi yace injishi.

        Sai wajen sha daya da rabi na dare ya shigo gidan,zuwa lokacin ya tabbatar kusan kowa yayi bacci cikin gidan,idan ma akwai wanda baiyi ba d'ai d'aiku ne,don haka kai tsaye ta wuce sashensa.

           Ya sameshi yadda yakeso,harma yayi mamaki,cike da tantama da kuma shakkar hafsa dince ta gyara ko sakawa tayi a gyara masa,bai sani ba,sai ya aje wannan tunanin,ya soma rage kayan jikinsa ya zubasu a laundry basket,ya wuce bandaki ya soma tara ruwa mai dumi sosai a bathtub,sai daya cikashi taf sannan ya fada ciki yana sauke ajiyar zuciya,bayan ya cikashi da turaren wanka mai sanyin qamshi.

       Luf yayi a ciki,idanuwansa a lumshe,yana jin hayaniyar daya wuni yana debowa tana sauka daga kanshi,sai daya kashe minti kusan talatin sannan ya wanke jikinsa daya tsumu da qamshin turaren wankan da kuma dumin ruwan daya jiqa kansa a ciki,ya zari daya daga cikin lausasan towels dinsa wanda qamshin shower gel da body mist dinsa suka kamashi da kyau,koda kuwa an wanke ya daura ya fito.

        A bakin madubi ya tsaya ya dauki wayarsa yana laluban layin hafsat,duk da bashi da hope kan zata daga,saidai cikin sa'a gab da zata katse ta dauka din

"Ka dawo ne?" Abinda ta fara tambayarsa kenan,hakan kuma sai yayi masa dadi,saboda ya jima baiji magana cikin nuna kulawa kamar haka daga bakinta ba

"Yeah,can u come to my room?" Ya fada da lallausar muryarsa da sauti can qasa

"Why not?,gani nan zuwa" ta fada tana ajjiye wayar tata,sai ta miqe kanta tsaye ta soma canza kayan jikinta zuwa night gown,sannan ta shiga kitchen ta hada masa abinci ta kulle sassan nata,don taci alwashin yau din acan zata kwana ta fito.

         Duk da dare ne,hakanan babu cikakken haske a sassan widad din sai data zubawa part din nata harara,taja wani mugun tsaki kamar zata cire harshenta

"Zakici ubanki da kyau,saboda tsaurin ido yarinya kamar wannan wai tasan soyayya?,tasan aure?,auren ma mutum kamar abbas,zaki gayawa aya zaqinta" ta sake fada tana jinjina kai tare da tabbatarwa da kanta hakan.

           Sanda ta shiga yana shafa mai ne,saita ajjiye abincin,fuskarta kadaran kadaham,ta koma gefan gado daga bayansa ta zauna,ya waiwaya kadan yana duban fuskarta,sai kuma ya dauke kai ya maida dubansa gabansa yana daukar body mist dinsa

"Kinyini lafiya?,ya yaran" sai data dan yamutsa fuska kadan bayan ta tabbatar bazai ganta ba,tayi qoqarin saita muryarta,don tana jin kamar wani abu ya mata tsaye ne a hanyar shaqar numfashinta

"Lafiya lau,yara kuma suna gida" ta cikin mudubin yadan dubeta kafin ya kawar da qwayar idanunsa

"Har yanzu?,for now ya kamata ace sun dawo gida ko?,i missed them alort" baki ta tabe,bataga alamun hakan ba,ya shiga hidimar qara aurensa abunsa zai gaya mata haka?,da daa ne da tuni ya aika da mota ko kuma ya taka da kansa ya debo yaransa,amma yanzu saboda dalilin aurensa baiyi hakan ba,sai zancan a dawo masa dasu kawai yakeyi

"Sai gobe idan Allah ya kaimu,zasu taho tare da nazeera,zata tayani hada abincin baqi" ajjiye body mist din hannunsa yayi ya waiwayo gaba daya yana kallonta,ya harde hannayensa aqirji,da gaske fa tana bashi mamaki,kamar ba hafsa na.

        Taji a jikinta sarai ita yake kallo,idanunsa ba normal idanu bane irin na kowa,zaiyi wuya ya kalleka dasu bakijisu har cikin qashinka ba,saita kauda kanta gefe,bataso su hada idanu,bare ya karanci komai ta cikin idanunta da wannan qwarewar aikin nasa da yake amfani dasu wani lokaci a kanta.

         Batasan tahowa yake ba sai da hancinta ya shaqi mayataccen qamshin nan nasa dake kashe mata jiki da zuciya,saman sofa bed ya zauna dab da ita,har gwiwarsa tana gogar tata,ya kamo hannuwanta sosai ya riqe cikin nashi,sai taji hawaye na shirin sauko mata,saboda yadda zuciyarta ta karye da tuna a yanzun abbas din sunan mijin mace biyu yake amsawa,so samu ta fusge hannunta,ta kalli idanunsa ta gaggaya masa magana,amma kuma hakan ya bata da tsarinsu,dole tayi laqwas,tana jin yadda azababben sonshi yake motsa mata.

         Da wata irin murya mai laushi yake mata magana,har yanzun bai saki hannunta ba

"Idan nace miki banjin dadin wannan karamcin da kika yimin ba nayi qarya,kinyimin abinda babu wadda zaiyimin sai ke din,kin bani nutsuwar cikawa da sauke wannan nauyin,bansan da bakin da zan miki godiya ba hafcy" sunan da ya kirata dashi,wani suna ne mai dadadden tarihi a tsakaninsu,wanda ya jima bai kirata dashi ba,kuma kusan itace silar faruwar hakan.

          Dukka wadan nan maganganun da yake gaya mata gani take kawai rainin hankali da rainin wayo ne,maganganu masu zafi takeson gaya masa amma saita buge da janye hannunta daga nashi

"Tunda dai ka samu yadda kakeso kuma ba shikenan ba?" Ta fada tana duqawa qasa ta soma serving dinsa,tasan idan ba haka tayi zata fallasa kanta ne kawai,saboda ta soma tsarguwa da irin kallon da taga yana binta dashi

"Bismillah ga abinci nan"ta fadi tana matsawa gefe

"Kiyimin alqawari zaku zauna lafiya ke da ita"

"Banyi ba" ta fada a zafafe,saboda yadda takejin ta fara kaiwa maqura,haqurinta ya fara qarewa,ya zuwa sannan takai bango.

         Ita ta fara janye idanunta daga kallon qurillar da yake mata

"Zanyi iya bakin qoqari na,zan mata yadda zanwa qanne na,amma idan ka taimakawa hakan ta hanyar nuna mata mutunci da kimata" ta qarashe zancan hawaye yana sauko mata.

         Karamin murmushi ya sake,sai ya bude mata hannayensa,with coolness yace

"C'mon,is okay".

          Yadda taso din hakance ta faru,a sassan abbas din ta kwana,ya sake tsumata da muguwar soyayyar nan tasa data sake dasa mata matsanancin kishinsa,ta kuma sake cin buri da alwashin hana kowacce diya mace lasar wannan tsadadda zuma daga gareshi.

          Tare suka kintsa sukayi alwalar asuba,abinda ya dade bai faru ba,shi ya sanya jallabiyya yadau hula da carbinsa ya wuce masallaci,ita kuma bayan ta idar ta maqale daga gefan gado,zuciyarta nata lasafta mata irin abubuwan da zasu ci gaba da biyowa baya cikin gidan bisa tsarinta da kuma yadda taso,tana jin bacci,tana kuma son komawa,amma tana son ta sake yin wani abun da zai qara wanke ta a wajensa,ya kuma share mata filin da zata aiwatar sa qudurinta hankali kwance.

          Sanda agogo ya kada shida saita miqe tana fita a sashen zuwa nata,ta kuma fada kitchen tanata qunquni da surutan hanata rawar gaban hantsi,tsahon rayuwar aurenta batajin ta tana shiga kitchen sau uku a irin wannan lokacin,koda abbas kuwa yana da fitar sassafe,saidai ya hadawa kansa komai,kafin ta tashi ma ya fice abinsa.

          Daga masallaci sai ya wuce sassan widad din don ya gaida baqi,yasan cewa dole akwai manya a cikinsu,duk da rabinsu suna masaukin da gwamnan bauchi da kansa ya bayar yace a sauki baqin.

         Yadda ya gaidasu cikin girmamawa da dattako ya qara shiga ransu inna laila,dukkan wata haiba da nutsuwa tasa gami da sanin darajar dan adam ta bayyana,widad ita da nujood da anty madeena suka kwana a dakinta,anty madeena tunda tayi sallah ta fito nan wajensu ta barsu a dakin,don haka cikin hikima inna laila tasa aka taso nujood a dakin,saura widad kawai.

         Har ya miqe zai juya inna laila tace dashi

"Tana ciki ai" sam bai kawota cikin ransa ba,to amma ya kamata ya dubata,tunda yanzun dole tana qarqashin kulawarsa,bugu da qari kosa yaushe akwai wani sashe na zuciyarsa dake sake tunasar dashi muryar hajiya cikin sautin dake gaya masa amana ce ita a wajenka,ka riqeta amana.

          Da qanqanuwar sallama a bakinsa ya tura qofar ya shiga,qamshin sabbin furniture da turarukan wutan da aka ajjiye cikin dakin saman mirror suka cakuda suka bada wani kalar qamshi suka daki hancinsa.

            Sake maimaita sallamar yayi amma ba'a amsa masa ba,ya dan sake takawa zuwa ciki kadan,sai ya hangota daga gefan gadon,kwance saman lallausar sabuwar dadduma,ta qudunduna sosai cikin hijabinta jakar daddumar,da alama dasu tayi sallah,tana kuma idarwa baccin ya dauketa a wajen.

       Takawa yaci gaba da yi har ya isa gabanta,yadda ta cure sosai kamar maijin sanyi ko jariri a cikin mamarsa yasa ya fahimci kamar sanyi takeji,saiya waiwaya inda ac din dakin yake,sun qureta ne da yawa,ta kuma hadu da sanyin asuba,ya laluba remote saman bedside drawer ya kasheta,sannan ya maida dubansa ga fuskarta da rabinta ne kawai ya bayyana.

        Idanun nasa ya dauke,yaja da baya ya nufi qofar fita,dai dai lokacin da hancinta ya cika sa qamshin wani tutare na daban,saita buda idanunta da sauri,take ta hangi bayansa sanda yake ficewa a dakin,saita miqe da sauri ta zauna tana jingina bayanta da gado tana kuma raba ido

"Me yasa ya shigo?,haka kawai tana baccinta" saita kalli jikinta 
"Allah ma dai yaso hijabine a jikina" ta fada tana sake jan hijabin tana rufe qafafuwanta,kamar ce mata akayi zai dawo.

*AREWABOOKS:HUGUMA*

KI KULANI miss xoxo

DAUDAR GORA Billynabdul

RUMBUN K'AYA hafsat rano

IDON NERA Mamuhghee

A RUBUCE TAKE huguma

_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_

_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

0022419171
Maryam sani
Access bank

Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070

*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261

*Al'ummar nijerπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63


*Thanks for choosing us*πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post