A Rubuce Take (K'addarata) page 35 Hausa Novel - Novels Elite

A Rubuce Take (K'addarata) page 35 Hausa Novel - Novels Elite

A Rubuce Take (K'addarata) page 35 Hausa Novel - Novels Elite

H U G U M A

A RUBUCE TAKE

      (K'addarata)

Page 35

       Tun gari bai kammala wayewa ba suka tashi da aikin qarasa kintsa gidan,saboda suna son wucewa a ranar,saidai hakan bata samu ba,don abbas ya sake dakatar dasu yace su sake kwana,wannan ya basu dama suka buqaci mota,ya kira samuel daga office yazo ya kawo musu tare da yi musu jagora,inna laila,batulu anty deena anty halima da hajjaa suka sada widad da gidan hajiyan abbas.


          Fadin irin dadin da hajiyan taji bata baki ne,bata zaci zuwanta ba sam,saboda taga ba kasafai ake hakan ba,tunda ba unguwa daya suke ba,yadda ta dinga nan nan dasu zai baka mamaki,farincikinta ya gaza boyuwa,ta kirayi gwaggo fanteka donta tayata karbarsu.


         Duk abinda akeyi fantakea din da kallo take binsu,saidai ta saci ido ta tabe baki,idanuwanta qir akan fuskar widad


"Ashe.....ba banza ba,ashe sadakar yalla ya kwaso,kai jama'a,kashin hafsatu ya bushe,ba abinda ba zata gani ba,idan Allah ya tsare ma bata fiddata gidan ba" wannan ta dinga maimaitawa a ranta tana binsu da kallo,musamman da taga kowanne a cikinsu daga yanayin fata zuwa halittarsu da sumar kansu batayi kama sam da hausa fulani ba.


          Duk da batasan da zuwansu ba haka ta cikasu da abinci kala kala,kasancewarta mace mai karamci,baka rasata da abubuwa  irin wadan nan.


         Tun basu bar gidan ba ta kira abbas ta shaida masa,shima yaji dadin yadda suka karrama masa mahaifiya,yasan zasu fita,tunda muhsin ya gaya masa,don hajjaa tace ya gaya masa,amma baisan can zasu kaita ba.


           Sai yamma lis suka dawo gidan,a sannan hafsa tana daga jikin window dinta tanata leqe,har yanzu batakai ga ganin fuskar widad ba,sai giftawarsu data gani kawai.


          Dan kwalinta ta cire ta jefar,ta koma ta zauna jabar saman kujera tana fidda wani hucin azababben kishi dake cinta,tunda zancan nan ya bullo har kawo yau bata sukuni ko qanqani,gaba daya a birkice take jinta,hatta da yaran tace kada a dawo dasu sai gobe ko jibi,sai kawai tasa hannunta a fuska ta fashe da kuka mai cin rai,tana tsananin son abbas tana kuma kishinsa,batasan yadda zata jurewa wannan al'amarin ba,abu mafi dagula mata hankali shine sadakar yalla da akace ya auro,tana sane da yadda suke fidda mace da yaranta daga gidan,ta yaya zata kaucewa wannan?,saita tayi cikin bedrooms dinta gudun kada wani yaji gunjin kukanta,don kukan take da buqatar yi sosai.


            Su biyu ne a dakin ita da nujood,sun nutse abinsu saman gadon da yasha shimfida da lafiyayyen zanin gadon da yake tafiyayye tun daga yemen,sai hira suke abinsu suna dariya,babu abinda ya damesu,ita sam bata wani tuna wai amaryace,nan din gidan aurenta ne,zamansu a haka dasu anty madeena yana mata dadi,hankalinta kwance,bata tuna tafiya zasuyi su barta.


             Dai dai nan anty deena data gama hada kayanta tsaf ta tura qofar dakin ta shigo,saita saki baki kawai tana kallonsu,gadon da aka gama gyarewa aka sa masa zanin gado mafi tsada suka haye tsakiyarsa abinsu?


"Qaniyarki nujood,sauko" anty deena ta fada tana mata daquwa


"Gadon amaryar zaki kama ku haye?,ke baki mata fada ba ita batayi miki ba?" Nujood din tana dariya ta sauko,sai widad tayi tsam da ranta tana kallon anty deena,itakam batason ana nuna banbamcin nan sam,yanzu meye laifi don sunyi kwanxiyarsu ita da nujood din a nan


"Ke kuma bakiji inna laila na kiranki ba tun daxu mijinki ya shigo kizo ku gaisa?" Kanta ta dauke sannan ta tura baki gaba,ita wannan miji da aketa cewa,ita an takurata fa da zancansa


"Ni banji ba"


"Bakiji ba amma na gaya miki ana kiranki a falo ko?" Nujood ta fada gudun kada tayi laifi


"Ya isa naji,jeki falo nujood" anty deena ta fada tana wucewa ciki,ba musu ta miqe ta fice,ita kuma ta isa babbar wardrobe din widad,ta bude tana duba kayan dake ciki.


          Wata lafiyayyar gown ta atamfa ta dauko mata hade da mayafinta ta ajjiye mata,kusan duka kayanta a tsume suke da wani irin turaren kaya na itace mai matuqar qamshi da daukar hankalin duk wanda ya jishi,ta duba inda suka adana mata kayan ado ta fidda mata sarqa dan kunnen da abun hannu masu matuqar kyau,sannan ta dauko mata sabbin undies,saita juyo tana kallonta ganin wata guntuwar pad


"Kin taba yin period ne?" Gaban widad ne ya fadi,saita daburce lokaci guda,saboda bada kowa take magana irin wannan ba idan ba ummunta ba,ganin ta rude sai anty deenan tayi murmushi


"Ni kikejin kunya?,to ai kowa ma yana yi,kin taba yi ne?" Kai ta gyada.mata a hankali,sai anty deena din ta sauke ajiyar zuciya,duk sanda ta daga idanu ta kalli widad din sai taji fargaba da tausayinta,babu tabbacin zata yita zama a haka ba tare da komai ya hadasu ba,tasan halin mazan yanzu sarai wajen rashin haquri,duk da cewa yana da mata,amma sometimes masu matan sunfi fitina,saboda sunsan yadda abun yake


"Sau nawa kikayi?,kuma yaushe ne yinki na qarshe?"


"Sau biyu inayi,yau sati biyu" kai ta jinjina,saita koma gefenta ta zauna,cikin dabara take mata tambaya kan jinin haila da kuma wankan tsarki,cikin ikon Allah komai ta sani,saboda ba baya bace ita din wajen zuwa islamiyya,sannan ummu ta zauna da ita ta mata bayanin komai. Sosai anty deena taji dadin hakan,saita dubeta


"Shiga bandaki ki sake wanka kizo ki shirya zaki je ki gaida mijinki,tunda mukazo baku gaisa ba,ko kun gaisa?" Bata kawo komai a ranta ba ta girgiza kai alamun a'ah,saboda dazun tana bacci ya shigo,sai fitarsa ta gani,yanzun kuma tana nan suna hira da nujood


"Amma anty deena sanda zamu gidan hajiya fa nayi"


"Wannan daban yake,duk sanda kikasan zaki wajensa ko kinyi wanka ki dinga sakewa kinji?,ki dauko kayan kwalliyar nan da aka kawo miki kiyi kwalliyarki ki saka sababbin kaya,maza tashi qanwata ta kaina" murmushi kawai tayi,ta tashin ta shiga bayi ta hada ruwa kamar yadda ta umarceta,tayi wankanta da kyau.


          Kusan ita ta shiryata,wani irin tururin qamshi na fita a jikinta


"Muje na rakaki,amma zan dawo,kya taho ke kadai" kai ta gyada mata,bata wani damu ba,kawai tana jin dadin yadda tayi kyau abinta,suka jera da anty deena din tana mata wani karatu cikin hikima widad din na jinta.


         Daga dan nesa kadan da part din nasa ta juya,ita kuma widad din ta wuce tana dosar wajen.


          A darare,cike da baqunta da kuma tsoro,kasancewar a sannan sha daya kusan na dare ta murda handle din falon,saidai a kulle ta jishi,sai ta saka hannu tadanyi knocking,tana rayawa a ranta indai ba'a bude ba tafiyarta zatayi,to amma me zata cewa anty deena?,tunda tayi mata alqawarin zuwa,kuma bata iya qarya ba bare tace taje ta dawo ne.


             Dai dai lokacin da yake zaune qasan carfet,ya bude babbar farar takarda mai girma wadda ke dauke da map na garin kaduna,system dinsa na kunne hakanan akwai wani dan madaidaicin allo dake tsaye a gefe,yayi wasu zane zane da qananun rubuce rubuce da shi kadai yasan ma'anarsu,akwai babban aikin da yake tunkara,wanda yakeson gabatar dashi a sirrance,kamar yadda ya saba,kusan nasarar aikinsa kenan,a duk sanda zai gabatar da aiki na kama masu laifi da sauransu,yakan shirya komai a boye ne,dagashi sai amintattun sa irinsu samuel,sai lokacin gabatarwa yayi sannan.


           Idanunsa daya tsurawa takardar yana karantar map din ya daga yana duban qofa,yana tunanin hafsa ce,saboda ta kirashi taji ya dawo ba jimawa,to amma kuma knocking din ba irin nata bane,sai ya miqe a hankali ya juya allon,ya kuma kifa takardar,ya matsar da butar coffee din da yaketa sha a madadin abinci ya nufi qofar.


        Tuni fuskarta ta soma narkewa da tsoro,ta sake daga hannu cikin saarewa zatayi bugun qarshe ya buda qofar,iska mai sanyi da taushi dake kadawa a gurin ta yayibo dukka qamshin dake jikinta ta jefo zuwa hancinsa,dai dai sanda ya sauke kallonsa ga baby face dinta,fararen idanuwanta tarwai a haske wajen hadi da hasken falon daya sake haske fuskarta.


         Idanu ta zuba masa kamar zata saki kuka,shima idanun ya zuba mata,sai kuma ya janye gefe yana bata hanya,tsaiwa tayi kamar ba zata wuce ba,ta wurga idanunta ta gefensa tana hango cikin falon,tanaskn tava da mutum ko su kadai ne?,hango system dinsa da tayi sai ranta ya bata bashi kadai bane,wannan ya bata sukunin rabawa ta gefansa sosai ta wuce zuwa ciki,tun daga ranar da ummu ke gargadinta da kebewa da duk wani namiji ko kusantar inda suke bata qara bari sun hada inuwa da kowa ba,nan nan kusa kuma data sake tsawatar mata fiye da baya,watanni uku baya sanda ta fara period,ta sake jadda da mata batun.


           Wata ajiyar zuciya ce ta subuce masa,yayi tsaye a wajen kamar mai jiran wani,saidai yana shaqar qamshin ne da yayi masa dirar mikiya,hannunsa ya miqa ya maida qofar ya turata,widad dake zaune a darare a qasa tadan fidda ido waje kadan,kai.....ya zai rufesu su biyu?,saita tsirashi da idanu sanda yake takowa zuwa ciki,tana masa kallon tuhuma.


        Yana shirin zama suka hada idanu,farare sol din idanuwanta suka hadu da nasa manyan idanun,sai yadan lumshe nasa kadan,ya janyo computer dinsa gabansa yana cewa


"Bakiyi bacci ba?" Kai ta gyada a maimakon ta amsa masa,sannan tace


"Ina wuni?" 


"Kin yini lafiya?" Ya amsa mata yana daddanna system din ba tare da ya sake dubanta ba


"Lafiya lau,dama anty deena ce tace nazo na gaisheka,wai bamu hadu ba dazu" yadda tayi maganar cike da quruciya da kuma sakalci shigen na yaran fari ya tilasta masa daga kai ya kalleta,suka sake hada idanu a karo na uku,qaramin murmushi ne ya subuce masa,kallonsa take kanta tsaye kamar mai masa kallon tuhuma,ya karanci me take nufi a cikin zancanta,amma yana sa yaqinin ita din bata fahimci komai ba,ta taho abinta ne gaba gadi


"Anty deena ta kyauta,kinga ta fiki kirki,sai ita tayi tunanin kizo ki gaida mijinki" ya bata amsa yana sake maida hankalinsa ga system din nasa


"Uhmmm" ta fada cikin rashin sabo da kuma baqunta.


           Coffee din gabansa ya tura mata yana sake kallonta,saita girgiza kai alamun a'ah,saboda ummu ta hanata karbar abun hannun maza,yana nan kuma daram a kanta bata manta ba,bai sake cewa komai ba sai kawai ya miqa hannunsa,ya jawo allonsa yaci gaba da aikinsa,abun da ya dauki hankalin widad kenan,ta dinga binsa da kallo


"Dama malamin makaranta ne?,amma kuma nujood tace mata har bindiga ce dashi,to amma wa yake koyawa karatu bayan shi kadai ne a dakin?,inama zai dinga koya mata,tayi missing makaranta da karatu sosai,tanason karatu" ire iren wadan nan tunanukan ta dinga yi,har sai da taga aikinsa yakeyi sosai cike da qawa zuci,ta dan fara motsawa,so take ta koma,amma kuma tasan ba zata iya fita ita kadai ba,saidai ya rakata,amma kuma ta kasa buda baki ta gaya masa.


         Marker din hannunsa ya ajjiye yana fesar da iska daga bakinsa,yayi taku biyu baya a hankali,sannan ya duqa dab da ita,idanu suka sake hadawa,sai ya kauda kai ya soma zuge jakar dake aje a gefanta,wasu tsofaffin takardu ne da yasa samuel ya kawo masa su zai duba wani abu a jiki,yasoma zarosu,sai tsanya tayi tsalle ta biyosu har guda biyu,daya ta fada gefe dayar kuma kai tsaye ta fada jikin widad.


          Gigitaccen ihu data saki ya sanyashi watsar da takardun hannun nasa,kafin ya ankara tayo kansa tana tsalle gami da kiran wayyo Allah,wayyo ummu,taso rudashi amma ya tattara hankalinsa waje guda,saidai duk yadda yakeson dawo da ita nutsuwarta widad batasan yana yi ba,mayafi tuni ta cillar dashi,dankwali ma ya zame,lafiyayyen baqin gashinta dake fitar da qamshi ya tarwatse.


             Suciyarsa tayi wani mugun bugawa sanda ta shige jikinsa tana,sassalkan gashinta ya wanzu a fuskarsa,ihu take da zazzaqar muryarta dake cike da tsoro tana fadin ya cire mata


"Calm down,ki nutsu,tsanyace fa kawai" ya fada muryarsa na dan rawa kadan,saidai ko daya bata jishi ba,tsoro ya cika kwanyarta a lokacin.


*AREWABOOKS:HUGUMA*


KI KULANI miss xoxo


DAUDAR GORA Billynabdul


RUMBUN K'AYA hafsat rano


IDON NERA Mamuhghee


A RUBUCE TAKE huguma


_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_


_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_


0022419171

Maryam sani

Access bank


Saiku tura shaidar biya ga

+234 903 318 1070


*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*

09166221261


*Al'ummar nijerπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ zaku tuntubi wannan number*

+227 96 09 67 63*Thanks for choosing us*πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post