RQ
Page 12
Hafsat Rano
***A kofar gidan ta tsaya ta zaro wayarta ta shiga wajen message ta rubutawa Hajiya Zeenat sako.
_"Na dawo, kuma ya samu sauki."_
Sai ta kashe wayar gaba daya dan bata so ta kirata kwata kwata idan suna tare da yan gidan su. Da sallamar ta, ta shiga gidan da daukin ganin su, ga mamakin ta sai ta tarar basu karaso ba.
"Wai basu karaso ba Adda?" Ta tambayi Addan tana zama a gefen ta
"Eh wallahi, bakuyi waya ba?"
"A ah bamuyi ba, bari na kira su
"Ok kira su muji."
Wayar ta kunna ta kira amma har ta gama ringing ba'a daga ba, dukkansu tabi da kira amma duk basa dagawa, hankalin ta ne ya soma tashi tunda dai babu yadda za'a yi dukkan su ace basu ga kiranta ba. Mikewa tsaye tayi cike da zulumin abinda ya faru ko yake faruwa. Ita kanta Addan jikinta yayi sanyi ganin sai cigaba da kiran Raihana take amma ba ta ma shiga daga baya. Baki daya hankalin su ya gama tashi kusan awa guda kenan da dawowar ta amma duk da haka basu karaso ba, ba kuma su kirata ba. Sam ta kasa zaune ta kasa tsaye haka ta dinga zagaye zuwa chan ta soma kuka dan gaba daya jikinta ya gama bata ba kalaou ba.
***A kofar gidan Lamido yayi parking cikin yanayin gajiya da tafiyar dukkansu suka fito Dadah da jikin ta ya gama laushi sosai saboda tsabar gajiya ta zuro kafafun ta a hankali Hydar ya cicibo intisar da take baccin wahala. Shi da Dadah da intisar din ne a baya sai Lamido da Sadeeq a gaba bayan sun chanja tukin saboda wahala. Awar su kusan biyu a cikin hold up ashe masu manyan motoci ne suke zanga-zanga akan an kashe musu dan uwa, shine suka rufe hanyar gaba daya suka hana kowa bi sai zagaye ta wasu kauyukan suka dinga yi abinda ya saka su dadewar kenan. Sun ga kiran Raihanan sun kuma san tana cike da zulumi amma sanda duk suka ga kiran nata babu service a in da suke balle su iya kiranta.
Tana tsakar gidan tsaye taji alamun tsaiwar mota, da mugun gudu ta kwasa tayo waje, bata san sanda ta rungume Lamido ba kasancewar shine a hanya cikin kuka kuka dariya dariya. Tausayi ta basu a lokaci daya duk da sun san zata aikata dama, ta bi su duk ta rungume taki daina kukan da k'yar ta kyale su ta kama hannun Dadah suka soma shiga cikin gidan.
"Raihata kukan na menene kuma?"
Dadah tace ganin still hawayen take, ita kadai tasan yanayin da zuciyar ta ta shiga dan saura kiris ta buga saboda tsabar tsoro. Kin musu magana tayi har aka shiga suka zauna a falon Adda Maimunan da ta taso ta riko mahaifiyar ta.
"Sannun ku da hanya Dadah." Tace ta taimaka mata ta zauna Raihanan ta zauna itama a kujerar ta nanuke mata
"Sannun ku Maimunatu,kun ganmu sai yanzu ko?"
"Eh wallahi, gaba daya hankalin mu ya gama tashi."
"Ku bari kawai, hanya ce tayi mana matsala wallahi, amma alhamdulillah tunda an iso lafiya."
"Alhamdulillah kam."
"Ina wuni Addah?"
Yan mazan suka hada baki wajen gaishe ta.
"Lafiya lou ya hanya?"
"Alhamdulillah."
"Menene wai?"
Hydar yace yana kallon fuskar Raihana da tayi kicin-kicin ita a dole fushi take dasu.
"Tunda dai gamu mun iso ba shikenan ba?"
Lamido yace yana dariya
"Ku kyale min kanwata, kusan ta da saka damuwa a ranta, nasan ta tsorata ne, toh gamu mun zo shikenan ko?"
Daga mishi kai tayi sai hawaye shar-shar
"Naji tsoro sosai."
Tace da muryar kuka
"Babu abinda zai faru damu kinji? Sai Abby ya fito mun yi rayuwar mu, mun aura miki best husband da zai kular mana dake"
"Kai Hammaaa." Tace tana kunshe fuskar ta a jikin Dadah.
"Kaga jaira taji maganar aure har ta murmushi."
Sai aka kwashe da dariya gaba daya.
Abinci da ruwa da lemuka aka kawo musu sannan aka kaiwa Dadah nata daki Raihana da Adda Maimuna suka bita ciki aka bar su Lamido da Muhammad din Adda Maimuna a falon suka fara sallah sannan suka ci abincin.
***Tsaki yaja a karo na ba adadi, sau biyu kenan yana kiran Kamal a waya amma yayi biris dashi. Tashi yayi bayan ya ture system din dake gaban sa ya nufi office din Kamal din da kansa.
Yana zaune yana aiki kansa ya dau zafi sosai dan ya manta ma shaf da kiran da Aryan din yayi masa sai gashi ya shigo. Fuskar sa ya kalla ya tuno da abinda yace masa, ya tuntsure da dariya yana mikewa tsaye
"Yanzu tsakani da Allah fa jiran ka fa nake."
"Bata zo ba fa Aryan, beside kai da kanka kace baka son nata, a gaban ta, kuma yau Friday bata zuwa aiki kasan."
"Call her toh mana.."
"Allah ni ba zan iya kiranta ba, ka kirata da kanka amma ai da kunya nace tazo ta dafa maka tea."
"Ba zaka kirata ba? Ni bani da number ta."
"Waye ya kirata ranar nan? Beside ma ga number ta wajena bari na baka."
"You have problem."
"Ai gaskiya ne,da kunya ai."
"Karka kira ta din."
Ya juya ya barshi yana yi masa dariya.
Dariya sosai Kamal ya dinga yi bayan fitar sa, yayi saurin karasa abinda yake ya bishi office din. Ya same shi yana ta jan tsaki fuskar sa a hade shi a lallai Kamal din ya bata masa rai.
"Bari nasa Zainab ta dafa maka, amma dai kana da bukatar ka shiga daga ciki wallahi, dan rashin yardar ka dole abubuwa da yawa ba kowa zaka yarda yayi maka ba."
"Sai ka sani dole nayi ai, dama ina ta so nayi maka magana, shine kaje kuka hada kai da Ya Nabila ko?"
"A ah hira ce tsakanin ya da kanin ta."
"Munafurci dai,kasan yanzu duk zata bi tasa abun a ranta"
"Ai gaskiya ne."
Chanja zancen yayi zuwa wani daban
"Yarinyar nan ma dole ta zabi ko zuwa duk satin ko naki signing wannan watan."
"Wacce yarinya?"
"Oho."
"Wai Raihana? A ah idan baka mata signing ba ma ni sai nayi mata, tunda dai batayi laifin komai ba, laifin ta daya da bata zo ta dafawa katon gwauro shayi ba."
Wani kallo Aryan yayi masa, be sake magana ba ya ja system dinsa ya shiga motsa mouse din dan ya lura Kamal din so yake ya kure shi, shi be ma san yadda akayi har ya biye masa haka ba
🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*_SAK'ON ZAFAFA BIYAR GA AL'UMMAR K'ASAR NIJER_*🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
_ASSALAMU ALAIKUM MASOYA MAKARANTA LITATTAFAN ZAFAFA BIYAR JAMA'AR NIJER_
_DIMBIN GAISUWA DA FATAN ALKHAIRI A GAREKU_
_MUN FIDDA TALLA MUN BADA NUMBER DA ZAKU TUNTUBA,TO AMMA WANCAN NUMBER DA ZAKU TUNTUBA BA'A SAMUNTA,A HALIN YANZU GA SABUWAR NUMBER DA ZAKU TUNTUBA DON TURA KATI KU SAMU DAMAR SHIGA GROUP NA ZAFAFANKU BIYAR_
+227 90 16 59 91
*Yan jamhuriyyarmu nigeria kuma😂🇳🇬🇳🇬,zaku ci gaba da pyment ne ta account dinmu na*
Maryam sani
0022419171
ACCESS bank
Ku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070
*Katin waya ko VTU zaku tura ta wannan number*
09166221261
Litattafan dai sune kamar haka
RUMBUN KAYA Hafsat rano
A RUBUCE TAKE Huguma
IDON NERA Mamuhghee
KI KULANI Hafsat xoxo
DAUD'AR GORA Billynabdul
*Muna godiya da zabin zafafa biyar*🤝🤝🤝🔥🔥🔥🔥