Rumbun Qaya hausa Novel Page 13

Rumbun Qaya hausa Novel Page 13

Rumbun Qaya hausa Novel Page 13

RQ


      Page 13


Hafsat Rano


   Da weekend suka shirya gaba dayan su a karo na farko suka nufi prison din. Hajiya Zeenat na kwance akan tafkeken gadon ta kira ya shigo wayarta, sai data fara kallon number kafin ta daga da dan sauri dan bata wasa da duk wani information akan sa 


"Hajiya barka da safiya."


"Barka dai Malam Salihu, ya aiki?"


"Alhamdulillah, kina da labarin zuwan iyalan Barrister kuwa?"


Wani irin wantsalawa tayi daga kwanciyar da tayi cikin yanayin tashin hankali tace


"Iyalai kamar ya? Ban gane ba."


"Toh dai gasu nan baki dayan su, mahaifiyar sa, da Yayan dukkan su."


"Kan balai! Yaushe har suka shigo garin amma bani da labari?'


"Toh gaskiya sai dai ki bincika, nima mamakin ganin su yasa ni kiran ki, bayan kuma naga baki sanar dani zuwan nasu ba."


"Ka kyauta, ka sake ajiye min account details dinka ta whatspp, ko da yake, bana harkalla da account, zan aiko driver da cash sai kasha ruwa."


"Godiya nake Hajjaju, bari na koma na bibiyar miki yadda ake ciki."


"Toh sai na jika Salihu."


Mikewa tayi tsaye ta hau safa da marwa a tsakanin dakin nata, ko da wasa bata ji zuwan nasu ba kamar yadda take bibiye da duk wani motsin su. Wayar ta, ta dauka da sauri ta yi dialing number sa. Ta cigaba da zagayen har zuwa sanda ya daga daf da katse


"Ya akayi baka fada min zuwan su ba?"


"Kano suka zo?'


"Auw baka sani ba?"


"Ban sani ba wallahi, Kaduna mukayi dasu zasu biki bansan me ya kawo su nan ba kuma, ko Raihana suka zo dubawa?"


"Itace ma." Tace tana zame dankwalin kanta, idan ta bud'e baki ta fada musu komai fa? Tabbas tana fadan sunan ta da bayanin zasu gane, shikenan komai zai koma baya kenan.


"Yanzu menene abun yi?" Yace jin tayi shiru


"Ka kira Hydar kaji yaushe ne dawowar su, a cikin satin nan nake da bukatar key din nan, idan yayi dadewar duniya sati biyu,kai ba ma zan iya jira ba."


"Shikenan, zan kira."


Kashe wayar tayi da sauri ta sake kiran Salihu, yana daga tsaye a dakin da suke zaune suna jiran fitowar Abbyn, dukkan su cike suke da zumudi musamman da suka samu wani dadadan labari da ya saka su kusan sumewa dan dadi, signal yayi wa Lamido kafin ya matsa daga wajen ya daga wayar


"Me yake faruwa Salihu?"


"Babu abinda yake faruwa Hajjaju, kamar ma ba zasu samu ganin sa ba gaskiya"


Ajiyar zuciya ta sauke da karfi hankalin ta,na dan kwanciya


"Shikenan, ka kirani duk abinda ake ciki."


"An gama hajjaju."


Komawa yayi ciki, ya sake kallon Lamido da shima shi yake kallo, yayi masa alama da hannu ya jingina masa kai kawai.


  A hankali ya zuro kafafun sa a karo na farko bayan shekaru masu yawan gaske, kansa ya d'aga kad'an ya kalli sararin samaniya sannan ya sauke a hankali yana cigaba da shak'ar iskar yanci, bayan tsawon lokacin da ya dauka a rufe.


_"babu abinda yafi yanci dadi."_ ya furta a kan labban sa


   Idanun su na kan kofar kyam ko kiftawa basayi, cikin yanayin farin ciki suke dukkannin su, hannun Raihana na sarke da na Haydar ta kasa nutsuwa ko kadan. Ita ce ta fara gano shi sanda ya fito, ta kwace a guje suka rufa mata baya, idonsa a kanta har ta karaso ta rungume shi kafin ta fashe da wani irin kukan na farin ciki.


"Abby...". Suka kira sunan sa a kusan tare cikin yanayin nuna tsantsar farin ciki, jinjina kansa kawai yake ya kasa furta kalma daya saboda tsabar farin cikin da yake ciki, da k'yar Raihana ta cikashi tana share hawayen dake kwance a fuskarta tana had'awa da dariya.


"Alhamdulillah Ya Allah."


Ya furta bayan ya rungume yan mazan daya bayan daya banda Lamido dake tsaye hannun sa zube a cikin aljihun sa, fuskar sa a sake sai dai yanayin sa be sakashi furta kowacce kalma ba sai jinjina kansa da yake kawai. Kokarin dukawa yake ya gaida Dadah tayi saurin hanashi tana rufe fuskar ta da mayafin ta. Girma sosai ya kamashi duk kuwa da askin da yayi fuskar sa tayi fayau yayi matukar ramewa. Dukkan gandurobobin suka zagaye su cike da farin ciki, shi kansa Abby be san wanne irin yanayi yake ciki ba, tun bayan da ya samu labarin fitar sa a jiya da daddare, wanda ya rasa dalili tunda babu wanda ya sanar dashi dalilin sauyin lokacin da aka samu, shi dai kawai an ce ya shirya yau zai fita daga gidan, hakan kawai ya sani shikenan babu kuma wani bayani da ya biyo baya amma tabbas yasan akwai dalili me girman gaske, da har zai saka a chanja komai cikin dan kankanin lokaci.

   Dukkan abinda ya kamata ayi an gama, haka suka rako shi har mota suna daga masa hannu, a hankali ya saka hannu ya share hawayen da ya biyo gefen kuncin sa a boye dan kar ma su gani, ya daga musu hannun suka fita daga harabar wajen. Idanun sa akan titi tunda suka fara tafiya yana mamakin sauye-sauyen da ya gani, yana tuna ganin sa na karshe sanda suka tabbatar sun tura shi prison bayan bashi da shakikai aminai sama dasu.idanun sa ya runtse ranar ta shiga dawo masa akan sa.


****KURMAWA PRISON,KANO. 


   Karar motar prison din ce ta sasu dagowa suka bi ta da kallo har zuwa sanda ta isa gate din, gandurobobin dake kula da kofar suka tashi da sauri daya daga cikin ya bud'e gate din motar ta saka kanta a ciki, a hankali gate din ya rufe ruf bayan shigar motar. Kallon ta yayi itama a lokacin ta kalle shi sukayi wa juna murmushi


"Munyi nasara!" 


Tace cikin yanayin da yake nuna tsantsar farin cikin ta

   

"Yes we won!" 


Yace yana mika mata hannu. Kallon hannu tayi kad'an sai kuma ta zuge zip din jakarta ta ciro envelop me fadi ta dora masa a saman hannun sa


"Na cika alkawari."


Gid'a kansa yayi cikin yanayin jin dadi yace


"Of course."


Sai ya tura envelope din a aljihu ya murd'a handle din motar yana kokarin fita 


"Sai yaushe Barrister?" Tace tana dan karyar da kanta


"Sai sanda kika neme ni Hajjaju, for now dai aci duniya da tsinke."


Dariya ta kwashe da ita sosai yana tayata kafin ta ware yan yatsun hannun ta, ta kada su tana girgiza kanta


"Sai ka ji ni."


"Ok..." Yace ya karasa fita daga motar.  Motar sa ya nufa da take dayan side din. Ta zuba masa ido tana kallon sa ya shiga motar  ya kunna ta, yayi horn sannan ya bar wajen. Ajiyar zuciya ta sauke sannan  ta daga waya ta kira driver ta da yake tsaye daga chan gefe tace


"Mu tafi." 


"Ok Ma."  Ya karaso da sauri ya kunna motar suka bar wajen suma.

   

Kallon daidaikun motocin dake kai kawo a tsakanin titunan garin take har suka kusa isa gida, wayar tace tayi yar kara ta ciro ta, murmushi ya subce mata, a yangace ta daga tana kara ta a kunne kafin ta dan yi baya yadda zata fi jin dadin amsa wayar


"Kin kusa karasowa?" Aka fada daga cikin wayar bayan ta yi masa bayanin nasarar su.


"Yes muna daf da shigowa, ya kayi da mutanen?"


"Nasa aje a tashe su yanzu, sai dai kin karaso zaki ji komai."


"Ok..." Tace tana zare wayar. Ba yau ne karo na farko da ta fara samun nasara a duk abinda tasa a gaba ba, haka nan take jin ta sakayau tamkar ta cire wani gagarumin abu daga birnin zuciyar ta, tayi fatali dashi, a yanzu ne zata mike kafarta sosai taci duniyar ta da tsinke! Babu wanda ya taba shiga gonar ta face ta saka kafa tayi fatali dashi daga cikin rayuwar ta, koma duniyar baki daya. Shi yafi komai sauki a wajenta. Barrister NASIR MATAWALLE! Kayi kad'an kace zaka tozartani, ta ja tsaki tayi cilli da wayar akan kujerar.


"Abby na!" 


Muryar Raihana ta dawo dashi daga tunanin bakar ranar, ranar da ya fara kwanan bakin ciki, ranar da yayi kwanan tsaye saboda kwarkwasar da ta cika dakin da aka kira shi da nasa. Ido ya zuba mata dan bata da maraba da mahaifiyar ta zamanin kuruciyar ta, hatta dimple din da take dashi irin nata ne sak. Murmushi yayi mata yana riko hannun ta yana tunawa da rikon da yayi mata na karshe a wanchan lokacin 


"Raihana."


Jinjina kai tayi dan dama tunanin da ya tafi ya sakata yi masa magana dan ta hangi damuwa shinfide a fuskar sa. Daidai lokacin suka isa asibitin Al-ihsan dake titin karkasara,tun suna hanya Babbo Sadeeq ya kira Dr Karaye a waya yace gasu nan, kafin ma su isa shi ya rigasu suna zuwa aka karbi Abby aka bashi gado domin a bashi kulawa ta musamman. 

   Da Magriba Hydar ya maida Dadah da Raihana gidan Addah Maimuna ba dan sun so ba, Raihana har da kukan ta akan ba zata tafi ba. Kayan jikinta ta rage ta shiga wanka dan zafi take ji sosai, tana fitowa Hajiya Zeenat na kiran ta, taga kiran dazu ma amma bata daga ba dan tana tare da yan gidan su kuma tsaf zasu gano ta tunda sun san ita ba wai wasu kawaye ne da ita ba. Abinda ya faru da taje ne ya fado mata,sai kunya ta sake kamata, kamar ta bud'e kasa ta shige dan gani take shikenan a marar kamun kai zai dauke ta. Sake kira tayi dan yau baki daya ba'a nutsuwar ta take ba duk da Salihu yace mata ba'a barsu ma sun gansh ba amma dai tana son duk yadda za'a yi Monday Raihana ta dauko mata key din nan daga nan kuma duk ma abinda yaran suke shiryawa da sauki tunda ta samu abinda take nema a hannun ta.


"Wai ba kiran ki ake bane Raihana?"


"Dadah wata bakuwar number ce, idan ma na daga shiru akeyi."


"Ko dai  saurayi kikayi da bakya so mu sani ba. Amma ina ji dazu ma ana ta kiran ki."


"A ah ai duk number ce fa."


"Toh ai shikenan, idan ma hakan ne ai zamu sani ko ba dade ko ba jima."


Wayar ta dauka tayi waje tana wa Dadan dariya, sai da ta zagaya bayan dakunan sannan ta bi kiran aikuwa ko ringing bata ji ba sai ji tayi an daga.


"Ina kika shiga daughter ina ta kiran ki."


"Ina tare da yan gidan mu ne Anty, ba zasu yarda ba idan suka ji muna waya hanani zasuyi."


"Akan me?"


"Ba komai, haka kawai suke ."


"Toh tunda haka ne karki bari su san muna magana kinji? Ba zan kara kiranki ba sai Monday, nagode da taimakon da kikayi min ranar gashi har Aryan ya koma bakin aikin sa, nagode miki kwarai, Allah yayi miki albarka."


"Amin." 


Tace cike da jin dadi, a duk taraiyar su da Hajiya Zeenat din babu abinda tafi jin dadi sama da albarkar da take saka mata, sai taji kamar mahaifiyar tace take shi mata albarka a duk lokacin da tayi wani abu. Sallama sukayi soyayayr matar na sake ninkuwa a ranta, dan samun kishiyar uwa me kaunar dan mijin ta kamar yadda take kaunar Aryan duk kuwa da baudadden halin sa sai an tona.




🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*_SAK'ON ZAFAFA BIYAR GA AL'UMMAR K'ASAR NIJER_*🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪


_ASSALAMU ALAIKUM MASOYA MAKARANTA LITATTAFAN ZAFAFA BIYAR JAMA'AR NIJER_


_DIMBIN GAISUWA DA FATAN ALKHAIRI A GAREKU_


_MUN FIDDA TALLA MUN BADA NUMBER DA ZAKU TUNTUBA,TO AMMA WANCAN NUMBER DA ZAKU TUNTUBA BA'A SAMUNTA,A HALIN YANZU GA SABUWAR NUMBER DA ZAKU TUNTUBA DON TURA KATI KU SAMU DAMAR SHIGA GROUP NA ZAFAFANKU BIYAR_


+227 90 16 59 91


*Yan jamhuriyyarmu nigeria kuma😂🇳🇬🇳🇬,zaku ci gaba da pyment ne ta account dinmu na*


Maryam sani

0022419171

ACCESS bank


Ku tura shaidar biya ga


+234 903 318 1070


*Katin waya ko VTU zaku tura ta wannan number*


09166221261


Litattafan dai sune kamar haka


RUMBUN KAYA Hafsat rano


A RUBUCE TAKE Huguma


IDON NERA Mamuhghee


KI KULANI Hafsat xoxo


DAUD'AR GORA Billynabdul


*Muna godiya da zabin zafafa biyar*🤝🤝🤝🔥🔥🔥🔥

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post