Rumbun Qaya hausa Novel Page 2

Rumbun Qaya hausa Novel Page 2

Rumbun Qaya hausa Novel Page 2

RUMBUN QAYA

           Free Page 2

Hafsat Rano

ZAFAFA 2023🔥🔥🔥🔥🔥

***A tsaye yake ya rike karfen jikin stairs din yana amsa waya, wayar da yake me matukar muhimmaci ce daga yadda yake magana. Idanun sa ya daga sanda yaji an bud'e kofa. Adam ne, dauke kallon sa yayi zuwa wani shashen na daban yana kokarin katse wayar


"Zan kiraka back." Yace ya katse yana juyawa da nufin hayewa saman.


"Aryan..." 


Ya kira sunan sa yana tahowa, tsayawa yayi da hawan ya juyo yana masa kallon neman karin bayani


"Ashe kana ciki baka fita ba."


"Ya akayi?" Yace a gajarce cikin yanayin rashin son maganar tasu tayi tsayi


"Nothing much, kawai dai maganar Daddy zan tuna maka, dan naga kamar ka manta ne ko kuma kana kokarin shashantar da maganar, ina jiran ka ajiye aikin ka bani wajen, dan da alama babu abinda zaka iya da irin wannan zuciyar taka."


Kallon rainin wayo yayi masa, yaja tsaki kawai ya juya da sassarfa ya haye saman, murmushi Adam yayi yana janye hannun sa ya hade su waje daya.


"Karamin dan air." Sai ya juya yana bouncing shima ya bar wajen.


   A harabar gidan suka hadu, daidai lokacin ta fito daga motar fuskar ta dauke da annuri, tsayawa yayi ta karaso ya karbi handbag dinta yana murmushi


"Mom sai yanzu? Har ina shirin fita."


"Bari kawai, yau nayi babban kamu, duk da dama da wannan plan din na fita, and it was a success gaskiya, muje ciki."


"Sai Mommy ta, mu je toh." Tayi gaba ya bita a baya yana mata hirar maganar da yayi ma Aryan yanzu, da kin amsa ma san da yayi


"For now ka bar wannan maganar, mu bi komai a sannu dan na samo bakin zaren."


"Wai kina nufin na bar masa matsayin MD din?"


"Kwarai, ka cigaba da bin sa a hakan, saura kiris ya rage."


"Oh shit! Mom yaron nan fa yana kokarin kai ni karshe ne, ni dai ayi duk yadda za'a yi na gaji da bin sa kamar wani uba na."


"Kai dai ka zuba ido, ka kyale min komai."


"Shikenan Mom, I trust you ai."


"Yawwa My boy, yanzu kaje in da zaka idan ka dawo sai muyi maganar, ka biya office din Daddyn naku kaga ko yana da bukatar wani abu."


"Shikenan, sai na dawo."


Ya ajiye mata jakar a gefen bedside ya fita. Zama tayi ta ciro wayar ta, ta shiga number Hajiya Maryam wadda itace Co-ordinator ta NYSC Kano, maganar minti uku sukayi ta fada mata bukatar ta, take tace ta tura mata NYSC number din yarinyar cikin kankanin lokaci akayi komai, ta sauya mata zuwa company su. Tashi tayi bayan ta gama ta shiga toilet tayi wanka ta fito ta sauya shigar ta zuwa wata shigar ta alfarma sannan ta fito babban falon tana kwala kiran Harira.


    ***Wanka tayi bayan sun gama jimamin abinda ya faru da ita da su Adda Maimuna da Amina, magungunan ta, tasha sannan ta haye gado ta kwanta, cikin kankanin lokaci kuwa tayi bacci har da mafarkin matar da suka hadu wadda tayi masifar shiga ranta farat daya, ta burge ta matuka yadda ta jata a jiki cike da kulawa. Wajen la'asar ta tashi shima sai da Amina ta tashe ta dan yin sallah. Kasala ce ta rufe ta bayan ta tashi, tayi sallar da k'yar ta dan ci abinci sai kuma tunanin gida ya dawo mata, tayi kewar su dukka sosai, kamar ta fasa bautar kasar ta koma wajen Dadan ta tayi zaman ta haka take ji, dan ma gidan Adda Maimunan akwai dadin zama musamman aka zauna bayan magriba ayi ta hira wani lokacin sai akai sha biyu ana hira ana ciye -ciye, shiyasa take dan jin dama-dama. Dada ta kira bayan magriba sai dai bata fada mata bige ta da motar tayi ba dan tada hankalin ta zatayi tace dole dole sai ta taho shiyasa sai tayi kum suka gama wayar cike da kewar juna.

   Kwana biyu da haduwar su da Hajiya Zeenat sai ga kiranta, tayi mamakin yadda ta samu number ta dan bata karba ba ranar amma sai bata kawo komai ba, ta duba ta sannan ta sake jaddada mata ta shigo goben ta karbi posting letter din tata kasancewar gobe sukayi dama Monday. Godiya ta sake yi mata cike da jin dadi sukayi sallama.  Washegari ta shirya cikin doguwar bakar abaya ta yafa medium veil tayi kyau sosai haka itama Amina ta shirya dan ita zata rakata suka fito titi suka samu napep suka masa kwatance kamar yadda yake a rubuce,kai tsaye yace


"Ko dai gidan Alhaji Mukaddas?"


Kallon juna sukayi ita da Amina kafin tace 


"Eh sunan dai matar da zamu gani Hajiya Zeenatu Mukaddas, gashi a jikin katin."


"Ai sanannan gida ne wannan."


"Alhaji Mukaddas wai me kudin nan da ake fadan sa?" Amina tace bayan sun shiga sun zauna


"Eh shi fa."


Me napep yace. Jinjina kai sukayi dukka suka ja bakin su sukayi shiru. Har gaban tangamemen gate din gidan ya kai su, kansa tsaye kuwa dan ba wannan ne karon farko da ya taba zuwa ba, duk azumi ana rabon kayan abinci kuma ya sha samu shi ma, dan ba wani nisa ne dasu sosai ba. Sakowa sukayi dukkan su idonsu akan gidan da ya cika da kyau da tsari, girman gate din ma kadai abun kallo ne.


"Kin tabbata nan ne Raihana?"


"Eh bari na kirata, amma dai ina kyautata zaton nan ne."


"Toh kirata muji." Tace tana cigaba da kallon gidan. Kiran wayar tayi no answer, ta sake gwadawa a karo na biyu kafin ta daga tace mata suna waje, ok tace mata sannan ta katse wayar ta kira gate din tace a shigo da ita, suna tsaye aka bud'e karamar kofar shiga gidan, wani buzu ya leko kansa a rufe yace su shigo, a sanyaye suka shiga duk jikin su ya mutu saboda mamaki, har balcony din ya rakasu sannan yace su shiga, suna dosar kofar ta bud'e da kanta suka shiga da sallama wani masifaffan sanyi me hade da wani irin feshin raba ya bige su, wani irin tsam sukayi suna wurgurga ido a tsakiyar tamfatsetsen falon dake cike da manyan kujeru na alfarma


"Raihana.." 


ta sake kiran sunan ta, tana sakkowa daga stairs din dake tsakiyar falon, murmushi ne a fuskar ta har ta karasa saukowa. Da sauri suka gaishe ta, ta amsa musu a sake tana nuna musu wajen zama. 


"Ya jikin naki?" Ta tambaye ta bayan sun gaisa tana cigaba da kallon su fuskar ta a sake sosai


"Na samu sauki." 


"Alhamdulillah, sai zuwa ganin Baba kenan."


Dariya suka sa dukka ta jawo wata drawer a jikin centre table din ta ciro envelop ta mika mata


"Ga posting letter din ki as I promised!"


Dadi ne ya kamata ta karba tana godiya sosai, ta bud'e sannan ta mikawa Amina ta karba itama ta gani, a sannan ne aka kawo musu snacks da juice da ruwa tace su ci tana zuwa. Zagewa sukayi suka ci Amina har ta daukar wani buns ta saka a tissue ta tura a jaka suka saka dariya


"Mom!"


 Ya turo kofar yana kiran ta. Riga da wando ne a jikin sa, sai takalmi sau ciki, kansa rufe da pcap ya jona airpod a kunnen sa fari. Tsayawa yayi chak yana kallon su, kafin ya karaso ciki sosai still idanun sa na kansu yazo ya zauna a daya daga cikin kujerun falon.


"Ina wuni?" Suka hada baki wajen gaishe shi


"Lafiya Lou, wajen Mom kuka zo."


"Eh suka amsa."


"Adam ka dawo?" Tace tana fitowa daga hanyar dakin ta na kasa


"Eh shigowa ta kenan, naga kin yi baki beauties dasu."


"Raihana ce da sister din ta, ni ban ma tambayi sunan ki ba Yan mata."


"Amina."


"Yawwa Aminatu ce ashe tsohuwa."


"Raihana... What a name! itace kuka bige ranar da driver?"


"Eh itace."


"Wow!" Yace yana taba gemun sa yana wani irin kallo k'asa k'asa, yana ayyana wani abu a ransa.
*RUMBUN QAYA🔥*DAUDAR GORA*🔥*IDON NERA*🔥*A RUBUCE TAKE*🔥*KI KULANI*🔥*_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊*Nasan zakuce ya da murmushi haka?**Wanda bai shigo ba bazai gane ba**Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️*KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU**KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?**KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?*Littafi daya---400


Biyu---600


Uku----800


Hudu-----1k


Biyar din duka----1200*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥0022419171


Maryam sani


Access bank*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*09166221261🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪


*Ina yan uwa 'yan nijer?*


*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*+22799643131Littafi daya---450CFA


biyu---650CFA


uku----850CFA


hudu----1050 CFA


Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*

*Thanks for choosing us*🔥

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post