Rumbun Qaya hausa Novel Page 3

Rumbun Qaya hausa Novel Page 3

Rumbun Qaya hausa Novel Page 3

RUMBUN QAYA

           Free Page 3

Hafsat Rano

ZAFAFA 2023🔥🔥🔥🔥🔥

_____________

_*MAAB LUXURY HOME!!* Sabuwar duniyar hamshakan mata da ƴaƴan gata.💞_

_*GIDAN* ƙawa da ƙawata gidajen da suka cika gida._ 

_*SABUWAR DUNIYAR* Amare da uwargidan data amsa sunanta ƴar gaban goshi._

_*MAAB LUXURY HOME* wata duniya ce ta ƙawa da ƙawata gidajenmu da kayan ƙyale-kyale na burgewa da ɗaukar hankalin duk wani mai kallo_. 

_*SUNYI FICE* Fice irin na ɗaya a cikin tsara, sune na farkon fari, a farin da za'a kira fari a kowace irin duniya._

_*A GAREMU* ba sitturu na alfarma da kawa ne kawai ke tabbatar da mu hamshakai ba. Sai mun haɗa da ƙawata gidajenmu da kayan MAAB LUXURY HOME zamu kasance cikakkun ƴan gata ababen kallo da nunawa sa'a koda a cikin dubun da sukafi dubu._

_*MAAB LUXURY HOME* sun takaita mana dukkan wahalar nema ko order a kasashen ketare ta hanyar wadatamu da galla-gallan kayayyakin adon gidajenmu_

_*MAAB LUXURY HOME.* Duniyar kayan Kitchen da decoration din gida na keta raini._ 

_*INA UWARGIDA INA AMARYA!!?* Ku ziyarci shagon mu dake No 22 Ahmadu Bello Way, Kano state. Ko kuyi order daga shafin mu na Instagram @maabluxuryhome. Ko Facebook @maabluxuryhome. Ko Ku nememu a lambar waya *08034631010*._

*_Mai azama shi za'a kira dana farkon fari😉. Bara nai sauri nawa suzo hannuna kafin a kwashe😁⛹🏼‍♀️⛹🏼‍♀️⛹🏼‍♀️._*


****Yana tsaye a jikin gate din suka fito rike da yar madaidaiciyar leda, tasowa yayi ya tare su a hanyar yana sakin fuskar sa


"Yan mata kun fito?" Yace idanun sa akan Raihana da tayi kicin-kicin da fuska dan har ga Allah yanayin kallon sa yayi mata kama da na shaidanun maza, da ka ta amsa sai Amina ce ta bud'e baki ta ce masa eh, ya jera dasu har zuwa gate din kafin yayi musu tayin motar sa, noke kafada tayi da sauri ta rike hannun Amina sannan tace


"Mun gode." Daga haka sukayi waje da dan saurin su, dage kafadarsa yayi ya saki guntun murmushi da ya tuna a wajen su zatayi aiki har na tsawon shekara daya. Juyawa yayi da shirin komawa ciki yaji horn din motar Aryan, fasa shiga yayi ya tsaya rataye da hannuwn sa har ya shigo cikin gidan ya samu gefe yayi parking sannan ya fito da dan saurin sa, mantuwa yayi dan har ya kusa zuwa office ya tuna shine dalilin dawowar sa. Sarai ya ga Adam a compound din ya kuma san ganin shigowar sa ya hana shi shiga ciki amma sai yayi kamar be ganshi ba, yayi wucewar sa da dan saurin sa, bin bayan sa yayi suka shiga a kusan tare a lokacin tana zaune bayan fitar su Raihana tana amsa waya tana dariya cikin jin dadi, ganin Aryan a lokacin yasa ta yin saurin katse wayar tana fata da addu'ar Allah yasa be hadu da su Raihana da suke fita yanzu ba, dan ta tabbata idan yasan akwai wata alaka tsakanin su ba zai taba accepting dinta ba.


"Son me ka dawo yi?" Tace tana mikewa tsaye cikin yanayin rashin gaskiya


"Akwai abinda zan yi." Yace a gajarce yana hayewa saman da dan saurin sa, kallon Adam tayi da yake tsaye daga baya tace


"Ya hadu da su Raihana ne?"


Girgiza mata kai yayi


"Basu hadu ba, dan su ta gaba suka bi shi kuwa ta baya yake shigowa."


"Ok." Tace daidai lokacin ya dawo ya sake wuce su ya fice cike da sassarfa. Tsaki taja me tsawo bayan ya fita, bata son ganin sa tamkar yadda yaki jinin ganin ta, ta sani kuma tana da yakinin da za'a bashi damar kashe mutum daya a duniyar nan toh tabbas da itace kai tsaye, sai dai be sani ba, tsanar da tayi masa har ta ninninka wadda yake mata, dan ita baki daya rayuwar ta da tsanar sa ta ginu, fiye da yadda ta tsani mahaifiyar sa, shikuwa a baya ya sota, so me tsanani har baya iya bacci ba tare da ya ganta ba, ya mata irin son da d'a yake wa mahaifiyar sa ko ma fiye da hakan.


***Washegari ta tashi cikin shirin zuwa wajen aiki, ta shirya cikin shigar doguwar rigar atamfa A shape  me gajeran hannu sannan ta dora NYSC jacket dinta a sama ta yi rolling mayafi medium akanta sannan ta dora pcap din a sama. Jakar ta, ta dauka ta tura takardar da sauran abinda zata bukata ta fito falon ta samu Adda Maimuna zaune tare da Abban su Amina, ta durkusa ta gaishe su sannan tace zata tafi, kudi ya dauko ya bata sannan ya saka mata albarka.

  Har gaban gate din me napep ya kai ta, ta sauka ta karasa wajen masu gadin dake zazzaune a kan benci ta gaishe su sannan ya fada musu abinda ya kawo ta, ciki suka ce ta shiga ta hau sama tayi godiya ta wuce ciki. A reception ta samu wata mata zaune tana shigar da abu cikin desktop, matsawa tayi ta gaishe ta sannan tace mata sabuwar corper ce ita, takardar ta karba ta duba sannan tace ta hau sama office din oga Kamal, godiya tayi ta wuce zuwa saman tana dubawa har ta kawo office din nasa, Knocking ta yi akofar kad'an ta jira aka ce ta shigo sannan ta tura kofar bakin ta dauke da sallama, yana tsaye yana duba wasu takardu tare da head supervisors na company suna magana akan sells din da kowanne gidan mai ya kawo a satin gaba daya, shigowar ta yasa su tsayawa ta karaso ta dan russuna ta gaishe su kafin ta fadi abinda ya kawo ta ya rigata cikin sigar tsokana yace


"Corper we!" 


Murmushi tayi ya nuna mata wajen zama yace ta zauna ta basu minti biyu, ta zauna suka cigaba da dubawa har suka gama, sannan ya tafi shi kuma ya zauna a kujerar sa sannan yace ta taso, ta taso tazo ta zauna ta gaishe shi ya amsa a sake da tambayar camp, ta amsa itama tana murmushi


"Ok welcome to Mukaddas and sons." Yace yana mika mata hannu ta bashi posting letter din tata 


"Thank you." Tace ta mika masa cike da girmawa ya duba ya saka hannu a wajen da ya kamata ya saka sannan yace


"Bari na bawa Oga kwata-kwata ya saka hannu anan, bani minti biyu."


Ya mike kenan aka dan yi knocking sau daya kafin ya turo kofar ya shigo kansa tsaye


"Ina stamp din office dina?" Yace yana shigowa


"Gashi nan dazu aka kawo, sai kuma Faisal ya shigo zan kawo maka kenan, dama yanzu office din ka zanzo we have a new corper."


"I don't think muna bukata, reject her."


Yace ba tare da ya kalli ko in da take ba, ya dauki stamp box din ya juya zai fice


"Wait please , we need her saboda field din da ta karanta."


"Regardless! Just reject her please wahalar corpers din nan yawa ne da ita."


Yayi ficewar sa kawai, wata kwalla ce ta ciciko a idanun Raihana, ta tsani wulakanci a rayuwar ta, sai kace wadda tazo neman aljanna zaa wulakanta ta haka. Dawowa Kamal yayi ya zauna yana girgiza kai


"What a tough guy! Sorry please don't be offended, I'm coming." 


Ya tashi ya fita da sauri, share kwallar tayi da bayan hannun ta, tana jin duk shaukin da take dashi na zama a wajen na gushewa.

   A zaune ya same shi yana latsa computer as if nothing happens, ajiye masa takardar yayi a gaban sa yace


"Please sign and stamp here, idan kuma ban kai nayi making decision anan ba sai na sani." 


Dagowa yayi ya tsaya da abinda yake ya kalle shi, sannan ya kalli takardar kad'an kafin yace


"Me yasa kake so mu dauke ta?"


"Haka kawai nake so, coz naga zatayi amfani, computer science ta karanta."


Be ce komai ba, yaja takardar gaban sa ya dauki biro yayi signing a wajen da ya kamata yayi sannan yayi stamp ya tura masa yana maida kansa ya cigaba da abinda yake yi. Dauka Kamal yayi ya fice shima be ce komai ba, bayan sa yabi da kallo ya girgiza kai karon farko da yaga me irin sunan ta


_"Raihana."_  ya furta a chan kasan makoshin sa, wani memory me matukar muhimmaci a rayuwar sa ya shiga yi masa yawo aka, ko suna wacce duniya a yanzu? Allahu a'alam. 


  ***Zuciyar ta a chunkushe ta bar office din, sam bata ji dadin abinda ogan yayi mata ba, ko ba komai mutum ba abun wulakanci bane ba. Tana tafiya a kafa ta kusa karasawa titi wayarta tayi kara, ta kalli screen din ganin me kiranta ya sakata dauka da dan sauri ta daidaita muryar ta sannan ta gaishe ta


"Ok gani nan."


Tace cike da zumudita tura wayar a jakarta sannan ta tare napep tace ya kai ta KURMAWA.  Motar ta, ta hango an yi parking dinta a chan gefe, ta sauka ta karasa ta danyi knocking, sauke glass din tayi tace ta shigo, ta zagaya dayan bangaren ta shiga, driver ya tashi motar suka nufi cikin prison din.


Jikin ta gaba daya yayi sanyi tunda taga an shigo ciki, a waje ta hangi mutane a layi masu son samun shiga ciki domin ganin yan uwan su, sai an fara baka takarda ka shigar da sunan Ka sannan ku samu shiga ciki shima sai ku zazzauna a wasu kujeru kuna jira har a zo kanku sannan ku shiga ciki bayan an baku tag kun makala a wuyan ku. Su kuwa kai tsaye suka wuce duk wannan layin har ciki sukayi parking, manyan gandurobobin ne suka fito suka tare su, suka dinga kwasar gaisuwa ita dai Raihana sai kallo take yi, ciki suka shiga kai tsaye zuwa wani office suka zauna sai gashi an kawo mata tag din an ce ta taso, cike da zumudi ta mike suka fita, ta hade hannun ta waje daya saboda yadda suke mata wani iri. Wani dan daki aka ce ta shiga ta zauna ta jira, ta na zaune akayi sallama ta juyo da sauri, bata san sanda ta fashe da kuka ba,ta tashi ta rungume shi cikin kuka


"Abby na." 


"Uwata... Kece da kanki? Ke kadai? Masha Allah Alhamdulillah." 


"Toh ya isa haka na, bar kukan ki zauna muyi magana, ya isa haka." Yace yana shafa bayan ta, shiru tayi ta zauna tana kallon sa cike da tausayawa


"Abby ina wuni?"


"Lafiya lou Raihanata, kece kika zo ganin abbinki da kanki?"


Gid'a masa kai tayi


"Basa so su zo dani kwata-kwata bansan me yasa ba."


"Basa so kiyi kuka ne, amma kullum suka zo sai sun nuna min hotonki sannan sai sun yi ta min hirarki."


"Abby yaushe zaka fito?"


"Saura kiris kinji? Ki cigaba da min addu'a, sannan ki rike min mutuncin ki a duk in da kika samu kanki, sannan duk runtsi karki ci amanar wadanda suka aminta dake, ki zama me riko da gaskiya da amana duk runtsi."


"In sha Allah Abby, zan zama me bin maganar KU."


"Allah yayi miki albarka kinji? Allah ya baki sa'a a duk abinda kika saka a gaba dake da Yan uwanki, ki musu biyayya domin su ne iyayenki a yanzu da nan gaba ma."


"In sha Allah." Tace tana cigaba da kukan da ta dan tsagaita da, sun dan dau lokaci suna hira har sai da yayi mamakin dalilin da ya saka aka barsu suka dade haka, amma be kawo tunanin komai ba, suka sha hirar su sannan tayi masa sallama cike da kewar sa, ta koma office din farkon nan jikin ta a sanyaye. Kayan provision ta gani a zube ana maganar su, ta shigo


"Yawwa Raihana, gashi nan za'a bawa Abban ki, tunda zuwan bagatatan ne baki zo masa da komai ba."


"Nagode sosai Anty, Allah ya saka da Alkhairi."


"Amin Amin, officer bari mu koma, thank you so much, sai ka jini."


"Ba komai Hajiya, dan Allah a mika mana gaisuwa wajen Alhaji, muna shan abin arziki sosai sai dai fatan Allah ya kara girma da arziki."


"Ba komai." Tace suka fito ya rako su har mota suka shiga, sai da yaga tafiyar su sannan ya koma ciki. 


   Sanda suka hau titi sosai ne Hajiya Zeenat ta riko hannun Raihana, ta saukar da kanta k'asa cikin yanayin damuwa tace


"Ina cikin damuwa Raihana, damuwa me tsanani."


"Allah ya yaye miki damuwar ki Anty." Tace cike da tausayin matar me tsananin kirki da karamci


"Kina so ki san matsalar da nake ciki Raihana?" Gid'a mata kai tayi da sauri


"Ko da yake be kamata na dora miki nauyin damuwa ta ba, ke yarinya ce, amma inaso kiyi hakuri da taka tsantsan da halin Aryan."


"Aryan?" Tace tana kallon ta


"Eh Aryan, ina kyautata zaton kin hadu dashi yau a office da kike je."


"Shine oga?" Tace da sauri


"Shine, yana da zafin rai da wani irin hali, shine kadai damuwa ta a yanzu, ina kaunar sa tamkar yadda nake kaunar raina, sai dai..."


Sai tayi shiru kamar me tunani


"Shikenan Raihana, zamuyi magana wani lokacin kinji?"


"Tam." Tace a kasalance abinda yayi mata dazu ya dawo mata, lallai yana da babbar matsala idan har zai iya saka mace kamar Hajiya Zeenat a cikin irin damuwar da ta hanga a cikin idon ta. 

  A hanya suka sauke ta, tayi godiya ta tsaya jiran abun hawa, sai ga kiran Hamman ta, da sauri ta daga tana dan matsawa baya daga titin.


"Kina ina?" Dadah tayi maganar tana jin an daga


"Daadah na, yanzu nake neman abun hawa zan tafi gida, yau ce ranar farko da na fara zuwa in da akayi posting dina."


"Shikenan, ki kula da kanki kina zuwa ki kirani kinji?"


"Tom."  tace muryar ta a sake ba tare da tayi tunanin komai ba.


*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*


*DAUDAR GORA Billyn abdul*


*KI KULANI hafsat xoxo*


*A RUBUCE TAKE Huguma*


*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*


*IDON NERA Mamuh ghee*


_LITTAFI DAYA: 400_

_LITTAFI BIYU: 600_

_LITTAFI UKU: 800_

_LITTAFI HUDU :1000_

_LITTAFI BIYAR: 1200_


_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_


_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_


_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_


_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_


_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_


_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_


ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN


MARYAM SANI

ACCESS BANK

0022419171


SAI A TURA SHAIDAR BIYAN 


09033181070


IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA


09166221261


*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*


+22799643131


Books biyar  1250CFA

Books hudu  1050CFA

Books uku  850CFA

Books biyu  650CFA

Bookk daya  450CFA


KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post