Rumbun Qaya hausa Novel Page 6

Rumbun Qaya hausa Novel Page 6

Rumbun Qaya hausa Novel Page 6

RUMBUN QAYA

           Page 6

Hafsat Rano

ZAFAFA 2023🔥🔥🔥🔥🔥


_____________


_*MAAB LUXURY HOME!!* Sabuwar duniyar hamshakan mata da ƴaƴan gata.💞_


_*GIDAN* ƙawa da ƙawata gidajen da suka cika gida._ 


_*SABUWAR DUNIYAR* Amare da uwargidan data amsa sunanta ƴar gaban goshi._


_*MAAB LUXURY HOME* wata duniya ce ta ƙawa da ƙawata gidajenmu da kayan ƙyale-kyale na burgewa da ɗaukar hankalin duk wani mai kallo_. 


_*SUNYI FICE* Fice irin na ɗaya a cikin tsara, sune na farkon fari, a farin da za'a kira fari a kowace irin duniya._


_*A GAREMU* ba sitturu na alfarma da kawa ne kawai ke tabbatar da mu hamshakai ba. Sai mun haɗa da ƙawata gidajenmu da kayan MAAB LUXURY HOME zamu kasance cikakkun ƴan gata ababen kallo da nunawa sa'a koda a cikin dubun da sukafi dubu._


_*MAAB LUXURY HOME* sun takaita mana dukkan wahalar nema ko order a kasashen ketare ta hanyar wadatamu da galla-gallan kayayyakin adon gidajenmu_


_*MAAB LUXURY HOME.* Duniyar kayan Kitchen da decoration din gida na keta raini._ 


_*INA UWARGIDA INA AMARYA!!?* Ku ziyarci shagon mu dake No 22 Ahmadu Bello Way, Kano state. Ko kuyi order daga shafin mu na Instagram @maabluxuryhome. Ko Facebook @maabluxuryhome. Ko Ku nememu a lambar waya *08034631010*._


*_Mai azama shi za'a kira dana farkon fari😉. Bara nai sauri nawa suzo hannuna kafin a kwashe😁⛹🏼‍♀️⛹🏼‍♀️⛹🏼‍♀️._*.


•••••Suna isa airport din daidai lokacin jirgin ya sauka, tun kafin ma Aryan ya samu damar fita Adam ya fice daga motar cikin yanayin bacin ran abinda Aryan din yayi masa, sai dai tunda ya nufi wajen da Daddyn yake ya saki fuskar sa kamar babu abinda ya faru, ya kuma tabbatar da idan Daddyn ya fito dashi zai fara arba kafin Aryan din ya kuma san hakan me zai kara zama a gareshi.

  Hango fitowar su yasa shi nufar su da farin cikin sa, tare Daddyn yake cikin tagawar manyan abokan kasuwancin sa. Cike da tsananin girmamawa da kankan da kai ya tare su da gaisuwa har da durkusawa chan kasa, wanda hakan yake kara Samar masa fada a zuciyar Daddy dan shi mutum ne me matukar son girmamawa da sanin ya kamata. Shiyasa a ko da yaushe suke samun matsala da Aryan dan shi duk irin wadannan abubuwan be iya su ba sam. Kamar yanzu ma sai gashiya nufo su yana tafe yana amsa waya sai dai yana cike da wani irin haiba da kwarjini da kowanne lokaci yake samun galaba akan Adam din da duk kudure-kuduren sa. Ganin sun hango shi sun ya saka shi katse wayar da suke da Ya Nabila ya nufe su cikin tafiyar sa. Idanu duk suka zuba masa har Adam din hakan ya sakashi jin ya takura sosai, ya dan rissina kad'an ya gaishe su suka amsa babu yabo babu fallasa, hakan ya dan bata ran daddy ganin irin tarbar da sukayi wa Adam ba irin ta Aryan din ya samu ba, hakan kuma baya rasa nasaba da shi yadda Adam din yazo musu fuskar sa a sake cikin iya mu'amula da mutane. 

  A wajen shiga mota Daddy suka rabu da sauran, Adam ya karbi key din driver da ya kawo su ya shiga wajen tukawa yana jaddada shine zai kai Daddy gida, dariya sukayi shi da Daddyn dan shi komai Adam din yayi yana burge shi sosai yasan duk abinda zai ya faraanta ran Daddyn, a dole ba dan Aryan yaso ba, ya shiga gaba gefen sa ya zauna shi kuma Daddy ya hakimce a baya yana cigaba da nazarin halayen Aryan din duk da ba wai yau ne karo na farko da ya fara fuskantar hakan daga gare shi ba, amma kuma a yau sai yaga ya sauya masa sosai ya nuna matukar yanayin damuwa a tattare dashi, yasan damuwar sa bata raba dayan biyu akan abinda ya kwallafa rai ne yake ganin idan be cimma ba tamkar bashi da wani amfani a duniyar ma baki daya, dalilin sa kenan na sake komawa karatu a karo na uku yayi karatun da yake da yakinin samun cikar burin sa ta wannan hanyar, sai dai katse shi da Daddyn yayi ya kuma gindaya masa sharuda masu yawan gaske ciki har da dawowa yayi aiki a karkashin company sa wanda hakan yayi matukar takure shi, sai dai a duk wani abu da Daddyn zai saka shi ko ya gindaya masa baya taba iya ketare shi, shi din me matukar biyayya ne a gareshi ko da kuwa babu wata alama da take nuna soyayyar sa ga mahaifin nasa dan har kwanan gobe yana cikin mutanen da yake zargi wajen salwantar da rayuwar mahaifiyar sa, me tsananin so da kaunar sa.      Shiyasa komai ya tsaya masa chak dan yana rayuwa ne kawai a karkashin ikon sa ba wai dan yana so ba, sai dan cika umarnin Allah da Yace lallai ya zama wajibi 'yaya su yiwa iyayen su biyayya akan duk abinda be sabawa Allah ba.

   Hirar dake wakana tsakanin Daddyn da Adam din yake sauraro cike da kulawa Daddyn yake saurare shi yana kuma amsa masa daidai kamar yana hira da abokan sa makusanta. Aryan ya kan yi mamaki idan yaga yadda Daddyn ya sake da Adam ya bashi dukkan yarda fiye da kowa a duniyar nan, yayi matukar yarda dashi har ta kai baya ganin iyawar kowa sai ta Adam din. Duk da dai shi Aryan zai iya rantsewa da wayon sa ba zai iya tuna wata hira doguwa da ta hada shi da Daddyn ba, dan baya jin akwai wani abu da zasu iya tattaunawa akai idan har ba maganar mahaifiyar sa bace ba, tun da kuma yaki zancen yace masa baya so, tun daga sannan ya bar shi, be kuma sake tada masa maganar ba ko da wasa, shiyasa duk abinda yazo masa dashi toh kawai yake cewa ya aiwatar ba tare da wani dogon nazari ba, shiyasa magana a tsananin su bata tsawo kwata-kwata.


"Muhammad." Dan waigo da kansa yayi bayan motar hade da amsawa a lokaci guda


"Na'am?"


"Akwai wata matsala ne?" 


_"matsala?"_ ya tambayi kan sa, dan ya manta rabon da yaji irin wannan tambayar daga bakin Daddyn, ai shi a kullum a cikin matsala yake sai dai babu wanda ya damu ya fuskance shi ciki kuwa hadda Ya Nabila da yake ganin kamar tafi yarda da uzurin da Daddyn ya bayar shi yasa a kullum take dakushe shi a duk yunkurin da zai yi. Duk a zuci yake wannan tunanin a cikin yan dakikun da basu gaza sha biyar ba, a fili sai ya hau girgiza kansa kafin ya ce


"Babu wata matsala."


"Ka gane kuwa abinda nake nufi? Maganar company nake yi, ina fatan daga bangaren ka babu wata matsala dan shi Adam yana bani details da duk abinda ya faru a rana which I'm very impressed."


_ohh."_ Ya raya a ransa, ashe ba tasa matsalar yake nufi ba, ta aikin da ya saka shi ce._


  Dan murmushi yayi kad'an me ciwo wanda ya tsaya iyakar leben sa sannan yace;


"Alhamdulillah,babu wata matsala."


"Good, sai ku cigaba da kulawa da komai,dan zan kwana biyu gaskiya ban shigo company ba, domin Dr. Mubarak yace ina bukatar hutu dan haka zan huta sosai."


"Allah ya kara sauki Daddy, babu wata matsala ni da Aryan zamu tsaya tsayin daka wajen ganin komai ya tafi yadda ya kamata." 


"Bana jin ka Adam, nasan zaka iya."


"Shima zai iya Daddy, duk da dai sabo ne a system din amma naga kwazon sa,gaba daya da baka nan din nan yayi dedicating dukkan energy dinsa wajen aiki."


"Ok." Daddy yace a gajarce ya daga wayar sa da take kara. 


Kallon Aryan din Adam yayi a fakaice yayi dariya kad'an, ko dagowa Aryan be ba bare ya kalli bangaren da Adam din yake tunda ya fara maganar har ya dire ta. Shi da ya riga yasan duk wani motives din Adam din babu wani abu da zai yi ko ya yabe shi har yayi masa dadi tunda ya riga yasan karya yake yi, ba kuma wai har zuciyar sa yake ba, tsabar makirci ne. Yana jin Daddyn na jinjina masa bayan ya gama wayar amma yayi kum yaki cewa komai, shi dai burin sa kawai a isa gida ya samu ya zame dan ko cikin gidan baya son shiga musamman da yasan dukkan su zasu hadu waje daya dole Hajiya Zeenat zatayi wani abun da Daddyn zai iya ganin bakin sa, shiyasa baya taba yarda zama inuwa daya ta hadasu tun bayan da yayi wayo ya kara sanin ciwon kansa, ya gano irin bakin fentin da take goga masa a duk sanda ta ganshi tare da Daddyn.

  Daga baya ya tsaya Adam ya dauki suitcase din Daddy yayi gaba, juyowa daddy yayi ganin yana tsaye yace


"Muje ciki." Babu yadda ya iya, haka yabi shi a baya har suka dangana da cikin gidan. Hajiya Zeenat na tsaye a falon cikin matukar ado ta sha kwalliya irin wadda take ciki a kowanne lokaci musamman idan Daddyn yana gari, da sauri ta karaso ta tare shi, ta jingina kad'an da jikin sa jikin farin ciki da murnar ganin sa.


"Sannu da hanya Your excellency."


"Sannun mu Hajiya, kuna lafiya?" Yace yana zama, tayi saurin zama a kubin sa ta lankwashe murya cikin kissa da kisisina ta shiga gaishe shi, hannun ta, ta kai saman kansa ta zare masa hular kansa.


"Wanka ko abinci Alhaji?"


Waigowa yayi yaga Aryan din a tsaye amma ya basu baya


"Muhammad."


"Na'am." Ya juyo suka hada ido da Hajiya Zeenat yayi saurin dauke kansa daga gallon ta, ya bawa daddy dukka attention dinsa


"Kaje kawai zan neme ka da daddare."


Da sauri yayi gaba dan dama jira yake yayi saurin hanyar fita, murmushi kawai tayi ba tare da tace komai ba, ta cigaba da shafa kan Daddyn zuwa gemun sa tana lankwasa jikinta cikin salon ta da tasan yana tafiya da Daddyn sosai.

  Shi kadai yake ta jan tsaki har ya fice daga gidan a kafa dan be dauko mota ba, kuma baya bukatar daukar motar kowa a gidan duk da ga motocin nan amma shi a komai yafi son nasa, gidan sa ya nufa wanda ya kasance mallakin mahaifiyar sa, shine asalin gidan su da suka fara zama anan ne kuma duk wani tarihin rayuwar sa yake, anan yake samun nutsuwa sannan anan ne hankalin sa ya kan tashi idan har memory din abinda ya faru a baya zai dawo masa. Babu kowa a gidan dan ko haya be yarda ya saka ba, sai Baba Me gadi da iyalinsa da suke zaune a bq suna kuma kula da gidan har yanzu sosai. Baya kwana biyu be ziyarci gidan ba, anan yake duk wani shiri da tanadin sa anan kuma yake ajiye duk wani abu me muhimmanci a wajen sa. Knocking yayi a gate din sanda me napep ya sauke shi, Baba me gadi ya leko ganin shine yayi saurin bud'e masa kofar ya shigo.


"Sannu da zuwa."


"Sannu da aiki Baba."


"Yawwa, ban tsammaci zuwan ka a wannan lokacin ba, Allah yasa ba wani abu ne ya faru ba naganka a kafa."


"A ah ba komai, motar na office zan dan huta ne anjima sai na fita, Malam Rabi'u zai kawo motar anjima kad'an idan yazo ya ajiye ta kawai inaga zan dan samu bacci."


"Ok a fito lafiya." Yace masa, gaba yayi shi kuma ya koma bakin aikin sa cike da tausayin Aryan din.


   A falon ya yada zango ya kwanta rigingine yana kallon saman pop din falon, shi kadai yasan abinda yake ji a zuciya da gangar jikin sa, da abinda yake masa yawo a cikin kwakwalwar sa, baya iya controlling fushin sa wanda yana cikin abubuwan da ke matukar takura shi, abu kad'an sai ya hau yayi ta kunci wanda yake sake kashe masa kwarin guiwar sa, sai dai a duk fushin da zai yi baya taba nadamar fushi akan cin amanar sa, baya kaunar cin amana haka kuma baya yafewa duk wanda yaci amanarsa, shiyasa har gobe ya kasa hakura da abinda sukayi masa, yake kuma kaffa kaffa da duk wanda yasan zai iya cutar dashi.


_Me Adam yake nema a wajen yarinyar nan?_ 


Abinda ya faru dazun ya fado masa, yayi tsai yana tunani ko zai iya gano wani abu,duk da yasan maitar Adam din akan mata amma kuma wannan karon yaga abu mabanbanci a tattare da kallon da Adam din yake mata. Toh amma menene nasa? Me yasa zai shiga tsakani?


_Saboda a karkashin office dinka take, shiyasa kayi hakan._ 


Zuciyar sa ta tuna masa dalilin sa 


_Toh amma kuma idan itama ta amince da Adam din fa?_


Wata zuciyar daban ta sake tunasar dashi, tsaki yaja ya mike yana wurgi da pillow da yake kan kujerar yayi hanyar bedroom, ba zai taba yarda har wata shakuwa ta shiga tsakanin ta da Adam ba, idan kuma haka ne sai dai ta koma aiki a karkashin office din Adam din dan shi ba zai iya zama da duk wanda yake zaune inuwa daya da Adam din ba. Wannan dalilin shi ya bar wa kansa, da hakan ya samu bacci ya dauke shi, wanda be farka ba sai kusan karfe uku, a kasalance ya watsa ruwa hade da alwala yazo yayi sallah sannan ya dora kansa a gefen gadon cikin yanayin rashin karfin jiki. Ya dau kusan minti talatin a haka yana jin wayar sa tana neman agaji sai da ya ji tana neman takura shi sannan ya mike ya dauke ta a gefen bedside, ya duba call log din yaga kiran Ya Nabila ne sai Kamal wanda dama yasan a cikin su ne duk kiran da ake masan, be bi kiran ba sai da ya fara zuwa kitchen ya samar wa kansa shayi ya hado a cup ya dawo dakin ya zauna sannan ya bi kiran nasu.

    Tare sukayi sallar la'asar da Baba maigadi sannan ya dawo ciki ya bud'e safe dinsa, in da yake ajiye duk wani muhimmin abun sa ya jawo takardun da ya saka a karshe ya sake duba su, suna dauke da sa hannun mutane hudu ne Wanda yake dauke da yarjejeniya da aka kulla ta cikin aminci da yarda da juna, wajen da Ammin sa ta saka hannu ya kurawa ido, a hankali kwalla ta biyo gefen idon sa, yayi saurin saka hannu ya share, sannan ya cigaba da nakaltar saka hannun da yake kusa da na Daddy. 


*_Nasir Matawalle._*  


Ya furta a chan kasan makoshin, yana nan yana jiran fitowar sa, duk da rashin bashi dama da yayi akan duk abubuwan da yaje masa da su amma ba zai taba gajiya ko karaya ba, zai jira shi har zuwa lokacin da zai gaji da nacin sa, ya bashi abinda ya dade yana jira. Sannan ya kai shi yaga mutane mafi soyuwa a gareshi idan ka cire Ammin sa da Ya Nabila.

 Ajiye komai yayi ya rufe ya maida key din inda yake, sannan ya sauya shigar sa zuwa kananan kaya, ya bar gidan zuwa wajen Kamal da yake jiran sa a shoprite tun dazu.




*RUMBUN K'AYA*🔥


*DAUDAR GORA*🔥


*IDON NERA*🔥


*A RUBUCE TAKE*🔥


*KI KULANI*🔥


*_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊


*Nasan zakuce ya da murmushi haka?*


*Wanda bai shigo ba bazai gane ba*


*Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️


*KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU*


*KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?*


*KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?*


Littafi daya---400

Biyu---600

Uku----800

Hudu-----1k

Biyar din duka----1200


*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥


0022419171

Maryam sani

Access bank. 


Shaidar biya tanan👇🏻

09033181070


*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*


09166221261


🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪

*Ina yan uwa 'yan nijer?*

*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*


+227 90 16 59 91


Littafi daya---450CFA

biyu---650CFA

uku----850CFA

hudu----1050 CFA

Biyar----1250CFA


*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*


*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*


*Thanks for choosing us*🔥

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post