Rumbun Qaya hausa Novel Page 7

Rumbun Qaya hausa Novel Page 7

Rumbun Qaya hausa Novel Page 7

RUMBUN QAYA

           Page 7

Hafsat Rano

ZAFAFA 2023🔥🔥🔥🔥🔥

____________

    Tunda ta koma gida take tunanin abinda ya faru tsakanin Adam din da Oga Aryan, bata san dalilin sa na yi mata hakan ba, sai taga rashin dacewar abinda ya aikatawa Adam din, ita a ko da yaushe a mai zafin gaske take kallon sa, dan yanayin sa baki daya ya gama nuna hakan, bata son mutum da ya cika zafi sosai a koman sa, dan ita bata ga abinda akayi da har zai yi irin wannan acting din ba. Muskutawa tayi daga kwanciyar da tayi,kamshin turaren sa na cigaba da shigar mata hanci sosai, bata san yadda akayi kamshin ya manne mata haka ba, tashi tayi ta cire kayan ta watsa su laundry basket ta zura boubou, ta koma ta sake lafewa a gadon. Gida take son komawa, tana so ta ji ta jikin Dadan ta dan ita din me masifar son jiki ce, ko zama kayi kusa da ita sai ta ra'bi jikin ka tamkar mage. Har la'asar likis tana ta juye-juye kasancewar bata sallah, ga Amina bata gidan bata dawo daga school ba balle ta rage mata zaman kadaitar. 

   Bayan la'asar ta mike da k'yar, ta shiga toilet ta chanja pad ta gyara kanta sannan ta fito, tazo ta dau wayarta a saman mirror ta zauna kiran Babbo Sadeeq, shi kadai ne basu fiya waya sosai ba saboda duk ciki ya fisu commitment saboda yanayin aikin sa da baya bashi cikakken time, dama Hamma Hydar ne best friend dinta sannan Lamido. Tana fara ringing yayi rejecting tasan dama ba zai daga ba, haka suke mata basa taba daga wayarta sai dai su kirata, kiran ne ya shigo ta d'aga da yar murnar ta


"Babbo nah." 


"Na'am, kanwata kina lafiya?"


"Lafiya Lou, sai missing dinku da nake Babbo."


"Shiyasa naji muryar ki haka?"


"A ah bana dan jin dadi ne."


"Me yake damun ki? Kinje asibiti? Kin sha magani?"


 Duk a jere yayi mata tambayar cike da kilawa


"A ah, stress ne kawai kaina ne yake dan ciwo kad'an amma nasha magani ma."


"Ciwon kan nan wai ba zai hakura bane ba ya kyale ki? Ko dai zuwa zamuyi ayi scan din?"


"A ah da sauki, kwana biyu baya damuna sosai ma, ina shan magunguna na dukka, kawai ni gida nake son dawowa."


Murmushi yayi me sauti, kafin yace


"Ke fa kika dinga murna zaki tafi ki barmu, yanzu kuma?"


"Allah na gaji, boss din wajen aikin namu bashi da kirki ko kad'an, yayi ta shan kunu."


"Duk rashin kirkin sa dai kar ya yarda ya batawa kanwata, dan wallahi ranar Kano ba zata dauke mu ba, ki fada musu yayyanki maza ne kuma ke yar gwal ce baa taba ki, ba'a bata miki rai."


"Kaiii Babbo."


"I'm serious fa, gwara su sani, ba bautar k'asa ba ko bautar duniya ce ba zamu bari wani kato chan ya bata mana ran Princess ba."


"Su ma ba zasu fara ba ai."


"Yawwa better, yanzu dai nasan maganin boredom din nan da yake damun ki, zan sa miki wani abu kije ki dan yi shopping abinda kike bukata kinji?"


"Yaayy, you are the best Babbo, nagode Allah ya kara budi, ya kawo mata ta kari."


"Amin Amin, very soon in sha Allah, bari na koma aiki, sai anjima ki kula da kanki."


"In sha Allah, bye."


Da karfin ta, ta mike dan tuni karsashin ta ya dawo, duk halin da take ciki in dai tayi magana da daya daga cikin su toh in sha Allah sai sun san yadda zasuyi su faran ta mata, bata san yawan son da suke mata ba, dan tunda tayi wayo ta gane zasu iya komai da taba kowa akanta, ko dan ita kadai ce mace? Kuma karamar su? Kuma yanayin rayuwar da suke shiga? Ta fada mahaifiyar ta da karacin shekaru amma basu taba barin ta, tayi kukan rashi ba. Dadah kakarta ce wadda ta haifi mahaifiyar ta, amma ita take mata role din uwa da kuma role din kaka a lokaci daya,tana matukar kaunar su da dukkan rayuwar ta, domin sune Raihana, sune gatan ta, sune koman ta, zata bar duk wani abun da basa so bari na har abada, zata kuma so abinda suke so ko d hakan na nufin ajalinta.

   Dawowar Amina ya kara sata warewa ta manta da komai, suka shiga hirar su irin ta daidai da shekarun su, har zuwa sanda kowa ya aje hakarkarin sa domin samun hutu daga kwarafniyar da aka sha na ranar.

   Fresh ta tashi ta shirya a tsanake bayan sun gama ayyukan gidan, ba ta zuwa aiki yau dan haka ma tana yin breakfast ta koma gado ta kwanta Amina kuma ta tafi school, sai kusan sha biyu ta tashi shima kiran wayarta akayi ya sakata tashin ba wai dan taso ba. Miss called din Hajiya ZEENAT ta gani sai wata bakuwar special number da bata san ta waye ba, rabon da sukayi magana da Hajiya Zeenat din tun ranar da taje gidan karbar posting letter. Mikewa tayi da nufin zuwa toilet ta wanko fuskarta ta bi kiran sai ga kiran ya sake shigowa da wannan special number din, dagowa tayi dan duk a tunanin ta Hajiya Zeenatun ce, sai taji muryar wanda bata yi zato ko tsammani ba.


"Ina kika ajiye paper din da na baki jiya?"


Kawai abinda ya fara fada kenan ba gaisuwa ko sallama, yanayin yadda yayi maganar kamar wanda akayi wa dole yayi kiran, kafin ma ta bashi amsa ya sake watso mata tambayar cikin muryar sa da ta shiga ciki sosai ta shake.


"Nasa ta akan table sir, good afternoon."


"Ban ganta ba, dole ki dinga summiting komai idan kin san zaki yi fashi." Ya fada a hasale


"Ba fashi nayi ba sir, yau Thursday dama Sir Kamal yace Monday - Wednesday zan dinga zuwa."


"I'm waiting for you, kizo ki bani ita."


Ya kashe wayar, tsaye tayi da waya a hannu kamar wadda aka dasa, sha biyu har da yan mintuna be tashi cewa tazo ba sai yanzu? Wanne irin abu me wannan? Ranta ya sosu sosai, tayi kamar kar taje dan tafi minti goma a tsaye tana tunanin kin zuwa din kuma ta kashe wayar tunda abin nasa kamar hadda rainin wayo, da tasan ma irin sa zata samu a wajen da ta gwammace ta karbi teaching dinta ko a kauyan ne yafi mata sau dubu. 

  Tana shiryawa tana tsaki haka ta shirya ta fito ta samu Addah Maimuna a falo ta fada mata yadda sukayi, ta tayata jajantawa sosai dan yau ba karamar rana ake a gari ba, kuma sha biyu ranar ta kwalle sosai ace ka fito haka kawai ba tare da ka shiryi hakan ba. Ta dan sha wahalar samun napep dan suma idan azahar tayi sai kaga duk sun rage zirga-zirga, da k'yar ta samu wani shima a hanya ya sauke ta, ta taka a kafa har zuwa office din. A galabaice ta shiga ga yunwar da take ji a ranar da ta dake ta. Kai tsaye office din su ta fara zuwa ta dudduba ko ina bata ga takardar ba, ta tambayi Abdulhakeem shima ya tayata dubawa babu. Sai ta fito ta nufi office dinsa dan tasan dama ta kai masa dan tayi mamakin ma rashin ganin da yace be yi ba. Knocking tayi a kofar ta dan tsaya jim shiru, ta sake kwankwasawa sai ga Zainab ta taso, dama tana kallon ta tun shigowar ta


"Oga ya fita fa."


"Ya fita? Yanzu fa ya kirani yace nazo."


"Toh ya fita dai, sai ki jirashi." 


Ta juya ta koma wajen zaman ta, ranta idan yayi dubu ya gama baci, bata san wulakanci a rayuwar ta wallahi, shi kuma taga alamun haka yake, kamar ma abinda yafi enjoying kenan a rayuwar sa, lallai dole Hajiya Zeenat ta shiga damuwa, dan zama da mutum da irin halin sa sai me tsananin hakuri. Office din su ta koma tana ta kunci, ta zauna bata sake kula kowa ba, ta ciro wayarta tana dannawa sai ga Oga Kamal ya shigo. Da mamaki yake kallon ta dan yasan yau ba ranar zuwan ta bace ba, zai yi magana ta riga shi


"Oga ne ya kira ni yace nazo wai be ga takardar da ya bani jiya ba."


"Aryan din?" Yace cike da tsananin mamaki


"Eh." Ta gid'a kanta


"Abun da mamaki, takardar fa tana wajena na bashi dazu, sai dai ko kafin na bashi ya kira kin kenan, maimakon kuma ya sake kira yace ki zauna ya ganta."


"Hmm." Tace kawai


"Shikenan tunda kinzo ma, zo na nuna miki wani waje" 


Tashi tayi tabi bayan shi, zuwa wata kofa da take kallon office dinsu, bud'e kofar yayi da key suka shiga ciki, ga mamakin ta sai taga kitchen din madaidaici, dauke da coffee machine, microwave da sauran kayan kitchen dangin su cups da spoon, yar madaidaiciyar kettle me dauke da kananan cups irin ta su Hamman ta ce ta ja hankalin ta, ta matsa wajen ta dauka tana kallo


"Waye yake shan irin shayin nan."


"Mune nan, ni da Aryan, dalilin ma dai samar da kitchen din kenan, dan gwara ni ma, Aryan baya wasa da shayin nan, ya zamar masa addiction wallahi."


"Kamar su Hamma na,suma kullum cikin sha suke, tun ban iya ba har na koya dafa musu, nima kuma na koyi sha."


"Kin iya dagawa?" Yace cike da murna dan dama suna tunanin yadda za'a yi


"Na iya sosai, har majlisa suke kaiwa ayi tasha wallahi."


"Shikenan wallahi, dama muna neman me dafa mana yadda aikin zai dinga tafiya sosai, ta kwana gidan sauki."


"Amma sai dai na dafa maka kai kadai, banda shi."  


Ta bata fuska kad'an ita a lallai haushin Aryan take ji, dama kuma ita bata iya rufa rufa ba, idan ka bata mata sai ta nuna amma bata da riko ko tsananin fushi


"Tuba muke, ai yanzu dole muyi miki biyayya, shima ba zai kara ba."


"Allah ko abinci banci ba, daga bacci na tashi kawai naga kira wai nazo, dama ya fada min da ya ganta, amma haka na dauko kafa ga rana wallahi kamar zan narke."


"It's not hygienic ko zauna a kitchen kuna gulmata."


Kofar dama a bud'e take shiyasa ma basu ji shigowar sa ba sam, kusan subucewa kofin yayi daga hannun ta dan bata zata zai shigo a time din ba, kuma bata ma san dalilin da yasa ta ke fadawa Kamal din ba, ko dan taga kamar ya sake da ita kuma yana kokarin jan ta jiki? Ji tayi kamar Hamma Haydar take fadawa wallahi shaf ta manta ma da waye shi da alakar sa da wanda take masa maganar tasa.


"Ba gulma bace ba, gaskiya ce ai Aryan, da sai ka kira kace ta zauna kawai."


"Menene yayi saura da ba'a saka ba?" 


Ya share maganar ya sako tambayar, 


"Komai an saka, har kuma an samu wadda zata kula da bangaren."


"Wace? Kasan dai i don't trust anyone."


"Raihana ce."


"Who?" Yace kamar be gane wacce yake nufi ba


"Gata nan a gaban ka."


"No, a samu wata dai.."


"Why?"


"We will talk about that later."


"Raihana please ki jirani a office ina zuwa." Kamal yace cikin rashin jin dadin abinda Aryan din yake wa yarinyar, ya rasa dalilin sa kuma ai ba haka yake wa su Zainab ba, ba kuma itace corper ta farko da aka fara kawo musu ba. Ajiye cup din tayi ta raba ta gefen su ta fice ranta babu dadi. Tana fita Kamal ya tura kofar ya dawo wajen sa


"Why are you like this dan Allah? Why are you soo mean to her? Me tayi maka?"


"Babu abinda tayi, aiki tazo ba gulma ba naga, me yasa zata zauna taana fada maka laifi na."


"Tsakani da Allah baka kyauta ba, ka kira ta kace tazo, bayan kasan ka samu paper din."


"Bayan na kiratan ba."


"Then you should have call her again kace ka ganta."


"I forgot." 


"Anya? Anya kuwa?"


"Me?"


"Ban gane maka ba kwata-kwata."


"Ba zaka taba ganewa ba kuma ba."


Ya bud'e kofar yayi ficewar sa.


 ***Ko da ta fito daga kitchen din bata tsaya ko ina ba, tayi ficewar ta dan ba zata iya zama ba, yayi masifar bata mata rai yau din nan, me ya dauki kansa? Me yake ji dashi? Ta manta shaf da kiran da Hajiya Zeenat tayi mata kuma duk shi ya rikitata,sai da taji wayar ta na kara ta tuna tana ciro ta taga Hajiya Zeenat din ce.


"Dan Allah Anty kiyi hakuri wallahi mantawa nayi ban kira ba."


"Ba komai 'yata, nasan ba zaki da gangan ba, ya aiki?"


"Lafiya Lou, ina wuni?"


"Lafiya alhamdulillah, dama kira nayi naji babu wata matsala ko?  Ina nufin bangaren Aryan kinsan halin nasa sai hakuri."


Kamar me jiran kiris, kawai sai ta ji hawaye na sakko mata, ta share su cikin muryar kuka tace


"He's very rude Allah Anty, ya tsaneni bansan me nayi masa ba."


"Subhanallah, me ya faru?"


"Bansan me nayi masa ba, komai nayi ban iya ba, a gabana sai yayi ta fadamin magana, ni wallahi na gaji."


"Nasan zai aikata fiye da haka, amma dan girman Allah kiyi hakuri, kiyi hakuri a madadin sa, kiyi hakuri."


Jikin ta ne yayi sanyi jin yadda Hajiyan take bata hakuri, har sai da taji nauyi da kunya, taji dama bata fada mata ba.


"Ya wuce in sha Allah, ba zan sake damuwa ba ma duk abinda zai yi mun saboda ke Anty."


"Nagode sosai Raihana, nagode."


"Ba komai."


"Akwai wata alfarma da nake nema a wajenki Raihana, wani taimako nake so kiyi min dan hakan ne kadai  zai taimaka Aryan ya rage wannan halin nasa, taimakon sa zanyi amma baya so kowa ya taimaka masa, yana da yar matsala ne wadda ba kowa ne ya sani ba, kuma baya shan magani ko kad'an, duk da bani da hujjar hakan saboda ya toshe duk wata hanya da zamu gane amma ni nasan baya sha din, akwai in da yake boye su, tun wuri gwara a shawo kan matsalar kafin abun yazo yafi karfin mu, tunda bani da wata shaida shiyasa na kasa yin komai akai, dan ko nayi yunkurin fadawa Alhaji sai na kasa saboda zai bukaci shaida, shiyasa nake so ki taimaka min mu ceto shi daga fadawa cikin wahala. Dan Allah Raihana "


"Bana jin akwai abinda zaki nema a wajena na kasa yi miki in sha Allah, zanyi komai dan ganin kinyi farin ciki."


"Nagode sosai Raihana, nagode zan neme ki idan an kwana biyu, zaki ji abinda ya kamata kiyi ta nan bangaren ki."


"Shikenan, Allah ya rufa asiri, nagode."


"Amin nice da godiya."


   Dariya suka kwashe da bayan ta ajiye wayar,


"Wawuyar yarinyar halin ta sak na mahaifiyar ta, dama ai barewa bata gudu danta yayi rarrafe."


"Yaro be san wuta ba sai ya taka ai Hajjaju, ke din duniya ce in dai ta wannan fannin ne."


Dariya suka kara yi a tare.


"Da alamu tarihi ne zai maimaita kansa."




*RUMBUN K'AYA*🔥


*DAUDAR GORA*🔥


*IDON NERA*🔥


*A RUBUCE TAKE*🔥


*KI KULANI*🔥


*_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊


*Nasan zakuce ya da murmushi haka?*


*Wanda bai shigo ba bazai gane ba*


*Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️


*KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU*


*KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?*


*KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?*


Littafi daya---400

Biyu---600

Uku----800

Hudu-----1k

Biyar din duka----1200


*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥


0022419171

Maryam sani

Access bank


*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*


09166221261


🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪

*Ina yan uwa 'yan nijer?*

*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*


+22799643131


Littafi daya---450CFA

biyu---650CFA

uku----850CFA

hudu----1050 CFA

Biyar----1250CFA


*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*


*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*


*Thanks for choosing us*🔥

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post