Rumbun Qaya hausa Novel Page 5

Rumbun Qaya hausa Novel Page 5

 

Rumbun Qaya hausa Novel Page 5

*RUMBUN QAYA*


  

           Free Page 5


©️®️ *_Hafsat Rano_*


ZAFAFA 2023🔥🔥🔥🔥🔥


_____________


_*MAAB LUXURY HOME!!* Sabuwar duniyar hamshakan mata da ƴaƴan gata.💞_


_*GIDAN* ƙawa da ƙawata gidajen da suka cika gida._ 


_*SABUWAR DUNIYAR* Amare da uwargidan data amsa sunanta ƴar gaban goshi._


_*MAAB LUXURY HOME* wata duniya ce ta ƙawa da ƙawata gidajenmu da kayan ƙyale-kyale na burgewa da ɗaukar hankalin duk wani mai kallo_. 


_*SUNYI FICE* Fice irin na ɗaya a cikin tsara, sune na farkon fari, a farin da za'a kira fari a kowace irin duniya._


_*A GAREMU* ba sitturu na alfarma da kawa ne kawai ke tabbatar da mu hamshakai ba. Sai mun haɗa da ƙawata gidajenmu da kayan MAAB LUXURY HOME zamu kasance cikakkun ƴan gata ababen kallo da nunawa sa'a koda a cikin dubun da sukafi dubu._


_*MAAB LUXURY HOME* sun takaita mana dukkan wahalar nema ko order a kasashen ketare ta hanyar wadatamu da galla-gallan kayayyakin adon gidajenmu_


_*MAAB LUXURY HOME.* Duniyar kayan Kitchen da decoration din gida na keta raini._ 


_*INA UWARGIDA INA AMARYA!!?* Ku ziyarci shagon mu dake No 22 Ahmadu Bello Way, Kano state. Ko kuyi order daga shafin mu na Instagram @maabluxuryhome. Ko Facebook @maabluxuryhome. Ko Ku nememu a lambar waya *08034631010*._


*_Mai azama shi za'a kira dana farkon fari😉. Bara nai sauri nawa suzo hannuna kafin a kwashe😁⛹🏼‍♀️⛹🏼‍♀️⛹🏼‍♀️._*.



••••••• Bata yi saurin shiga ciki sosai ba saboda bata san abinda zata tarar ba, bayan sa ya hanga da dukkan alamu yana tattare abubuwan da suke saman table din nasa ne, kamshin sa kamar dazun ya cika ilahirin office din. Juyowa yayi jin shigowar Kamal din sai kuma ya zagaya ya zauna a kujerar sa yana duban Kamal din da ya karaso sannan ya mika masa hannu sukayi musabiha


"Yau na makara."


"Nima yanzu na shigo." Yace yana daukar biro a saman table din


"Raihana, shigo mana." Kamal yace yana waigowa. Dagowa yayi da kansa Jin sunan da Kamal din ya ambata idanun su suka sarke, saurin kauda kallon sa yayi ya maida kan Kamal cikin son karin bayani


"Aryan ga Raihana, dama nace maka yau zata fara zuwa."


"Yayi." Yace yana dora biron akan wata takarda take gaban sa ya shiga signing


"Akwai wani abu da zaka ce mata?"


"Babu, tayi aikin ta yadda ya kamata kawai, and abide by our rules."


"Ok, Raihana wannan shine MD na company din nan."


"Goodmorning Sir."


"Morning." Yace a gajarce


"Zakiyi aiki a cash office zaki taimaka wajen shigar da records na duk sales da akayi a ranar,kamar yadda nace zaki dinga zuwa Monday, Tuesday and Wednesday."


"Ok sir, in sha Allah."


"Shikenan,ki jirani a waje zan zo na kaiki office din ki, duk wata matsala idan ta shige miki gaba akan aiki kizo nan office din kiyi masa complain "


Da sauri Aryan ya dago ya kalle shi, sai kuma ya saukar da kansa kasa ya cigaba da abinda yake yi. Godiya tayi ta fice da sauri dan jin ta take Baki daya ta takura da wajen, ga wani kallo da yayi mata da wasu irin idanuwan sa da suka sake dasa mata tsoron sa sosai. Tana fita Kamal ya mike shima, 


"Bari naje oga, sai an zo shan shayi "


"Me yasa kace tazo nan bayan ga su abdulhakeem nan ga ka, me zan mata?"


"Ka manta kai ne still incharge na wannan bangaren? Suma su Abdulhakeem din wajen wa suke zuwa?"


"Kana takura min wallahi."


"Kwana nawa ne wai tayi ta gama ta tafi?"


"Idan ka fita ka tura min Zainab." Yace yana cigaba da abinda yake yi, girgiza kai Kamal yayi ya fice yana murmushi k'asa k'asa, yasan ba karamin daga mishi kafa Aryan yake yi ba, be cika ja da duk abinda zai ce ba duk kuwa da halin sa, tasu tazo daya ya riga ya gama sanin lagon sa da yadda zai bi dashi, shiyasa ko Ya Nabeela wani lokacin sai ta nemi taimakon sa akan abinda ya shafi Aryan din.

    Mutum uku ne a office din Maza biyu mace daya amma ba bahaushiya bace ba, wani empty seat hade da desk dinsa ya nuna mata yace ta zauna sannan yayi introducing dinta wajen sauran sannan ya fita. Gaishe su ta sake yi tana karewa office din kallo da yayi mata kyau sosai, da tuni tana kauye a gaban board tana koyawa yara karatu, nan kuwa ga AC ga ba wata hayaniya sam, ba zata gaji da daina gode wa Hajiya Zeenat ba dan ta taimake ta sosai. Ranar bata yi wani aiki ba dan bata gama gane kan abubuwan ba, Abdulhakeem ne ma ya dinga nuna mata wasu abubuwan har lokacin tafiyar ta gida yayi, ta musu sallama ta fito. Tana tafiya a harabar company tana kokarin fita waje ya hango ta yana kofar office dinsa, saurin tahowa yayi ya sameta tana daf da kaiwa gate


"Raihana." 


Ya dakatar da ita ta hanyar kiran sunan ta, tsayawa tayi ta juyowa, ya karaso fuskar sa a sake.


"Ashe kin fara zuwa amma ko ki neme ni." Yace kamar irin sun dade da sanin juna din nan. Murmushi tayi masa wanda ya tsaya iya saman leben ta shima saboda tunowa da shi din waye a wajen Hajiya Zeenat, dan sam yanayin sa be mata ba tun ranar, yayi kalar yan iska daga yanayin kallon sa da yadda yake mata magana yana wurwurga idanun sa a ilahirin jikinta


"Ina wuni?" Tace tana jin ta a takure da mutanen da suke wucewa suna kallon su a tsaye


"Lafiya lou, zo muje kiga office dina, idan yafi miki sai ki dawo department dinmu, dan zama karkashin Aryan sai wanda ya shirya."


"No wanchan din ma yayi nagode, bari na tafi."


"Okh, muje na ajiye ki, tunda ranan kinki yau dai ba zaki ki ba."


"A ah nagode, zan tafi da kaina."


"Please let me drop you, kamar wani dodo, ke fa yanzu abokiyar aikin mu ce."


"Haka ne, kawai bana shiga motar namiji ne, an hanani a gida kayi hakuri."


"Ohh ohh okh!" Ya hau kid'a kansa kamar kadangare, sai kuma yace


"Hakan ma normal ne, sai gobe toh."


 Ya juya ya barta a tsaye, juyawar tayi itama ta karasa fita daga cikin wajen.


  ***Waya ta samu Adda Maimuna tana yi ko da ta shiga gidan, zama tayi ta jira ta gama sai ta fuskanci da Dadan ta suke waya, tana jin sanda Addah Maimunan tace gata ma ta dawo, sai ta miko mata wayar tace


"Dadah ce."


Karba tayi da murnar ta tace


"Dadah na on nialli e jam jam."


"Jam nalli, no mbadda?


"Jam tan, Alhamdulillah."



"Yanzu har Raihana ta girman da zata fara boye mana abinda yake faruwa da ita?"


"Dadah?" 


"Yaushe mota ta bige ki Raihana? Kuma har ki kasa fada min ko Hamman ki? Ashe kin girma har haka?"


"Dadah ba haka bane ba fa, bana so ki damu ne, kuma ba wani ciwo naji ba, dan kurjewa nayi sai hakan ma kuma ya zama alkhairi."


"Kin dai girma Raihana, ai shikenan, ki kula da kanki dan Allah."


"In sha Allah Dadah nah, ina Babbo? Da Hamma Hydar da Hamma Lamido?"


"Bakya kiran su a waya ne?"


"A ah ina kiran su, kawai wai dai."


"Suna lafiya duk sun fice sai ni kwal a gidan."


"Allah sarki Dadah na, dole kiyi missing dina wallahi."


"Ke ai naga kamar baki ma damu ba, duk wannan kawa zucin gidan tunda kika taho nan shikenan, bansan me Maimunatu take baki ba da har kika manta mu haka."


"Kai ina, ai ban manta ku ba wallahi, kullum da daddare sai na tuno gida."


"Ba wani nan."


"Allah kuwan da gaske."


"Toh yayi, kije ki huta naji an ce yanzu kika dawo, saura kuma ki dinga wasa da cikin ki yadda kika saba rashin son cin abincin nan."


"In sha Allah Dadah, shikenan zan kira anjima idan su Hamma na sun dawo."


"Haa nannde wonnde."


"Haa gonngo."


Tashi tayi ta kaiwa Addah Maimuna wayar ta dan ta tashi ta shiga ciki, sannan ta wuce dakin su ta cire kayan jikin ta, ta dan kwanta kafin anjima ta tashi tayi wani abun dan sai da ta fara lekawa ta kitchen taga an gama komai dama dai tasan da wuri ake gama girkin rana a gidan saboda yara yan makaranta da ake kai musu.


    ***Washegari ta sake shiryawa kamar jiya sai dai yau ta dan makara, a gaggauce ta shirya ko breakfast bata tsaya tayi ba, ta tafi. Tana zuwa ta ajiye jakar ta kenan Zainab ta shigo office dinsu tace tazo in ji oga, yadda tayi maganar fuskar ta a hade ba walwala, yasa Raihana ta zata wani laifin tayi, sai dai bata gane wanne ogan ake nufi ba sai da taga sun nufi hanyar office din oga kwata -kwatan, sai a sannan jikin ta ya saki dan bata son duk wani abu da zai hada ta dashi, wani irin kwarjini yake mata.

   Siririn medicated glass ne sanye a idon sa yana kallon computer, shigowar su ya saka shi dagowa ya kalle su kad'an sannan ya cigaba da abinda yake yi


"Sir gata."


"Ok you can go." Yace dai ya jawo drawer dake jikin table dinsa ya shiga dubo abu, juyawa Zainab tayi cikin yanayin da ya saka Raihana a tunani, sai ta lura tamkar zata bangaje ta sanda take juyawa amma kuma sai tayi saurin dauke tunanin hakan tayi mata uzuri kila haka yanayin ta yake ko kuma dai bata lura ba. 


"Ina kwana?" Tace daga in da take tsaye ta hade hannayen ta, ta damke su waje daya.


"Kina lafiya?" Yace mata bayan ya ciro abinda yake so ya ciro din


"Alhamdulillah." Ta amsa tsoron da take ji yana raguwa jin ya tambaye ta tana lafiya, sai kuma fuskar sa da take a dan sake ba kamar ranar ba, hakan ya bata kwarin guiwar sake matsowa ciki sosai dan da daga dan baya baya ta tsaya 


"Aiki nake so kiyi min, ki dauki wannan takardar kije ki shigar da duk wani information a cikin system din, kin iya excel?"


"Eh na iya sir."


"Ok, ki yi shi kamar yadda yake anan sai ki tura min komai ta wannan email din da yake k'asa , duk abinda baki gane ba kizo ki tambaye ni, I need it zuwa 12."


"Ok sir." Ta dauki takardar ta juya ta fita.

  

  Zaman ta kenan ta kunna system din wayar Abdulhakeem tayi kara, ya daga taji sanda yake cewa ok sir, ya katse sannan yace


"Oga Aryan yana kiran ki."


"Ni kuma? Yanzu na dawo fa."


"Toh dai yana kiran ki." Yace yana dariya ganin yadda ta zaro ido


"Ni wallahi bana son zuwa."


 Ta fada tana mikewa, bata ma san ta fada ba sai da taji Abdul din na mata dariya 


"Hala dai oga yana miki kwarjini, muma duk kusan hakan ce amma wallahi he's very very nice."


"I don't think so."


 Tayi gaba tana jin suna mata dariya shi da dayan da bata gama rike sunan sa ba. A kofar ta tsaya kamar ba zata shiga ba, ta dan juyo sai taga Zainab tana kallon ta, juyar da kanta tayi ta kwankwasa sannan ta tura kofar, babu kowa a ciki, sallama tayi a hankali jin shiru ya sakata juyowa da nufin komawa, sai gashi yana kokarin shigowa, saurin ja baya tayi dan kansa tsaye ya shigo saura kiris su yi karo, kamar be lura da abinda ya kusan faruwa ba ya wuce ya zauna.


"Sir gani."


"Na ganki ai." 


Sai da ya gama ja mata aji a yadda ta lura sannan yace


"A cikin rules dinmu, babu fashi sai ta zama dole , shima sai ka rubuto email na dalilin rashin zuwan ka, sannan kullum idan kazo sai ka dauki attendance na time din da kazo da kuma time din da ka tafi."


"Ok sir."


"Zo ki saka hannun ki anan yayi capturing." Ya nuna mata wata na'ura akan desk dinsa, zuwa tayi ta dora thumb din ta, amma sai yaki dauka, be kalle ta ba yana jin dai tana ta sakawa tana cirewa.


"Come to my office." Taji yace a waya kawai, sai kuma aka shigo.


"Sir gani."


"Zo ki rike hannun ta yadda zai yi capturing naga kamar bata iya ba."


Yace ya mike ya fice daga office din, wani abu ne ya tokare mata wuya, ta tsaya kawai Zainab din ta matso da nufin kama hannun ta, saurin hanawa tayi tace


"Zan iya da kai na." Wani kallo Zainab din tayi mata sai kawai tayi tsaki ta juya ta fice.


Gefen rigar ta, ta saka ta goge hannun sosai sannan tayi bismillah ta saka, sai gashi yayi, ta cire ta saka dayan hannun shima ya dauka. Murmushi tayi dan a rayuwar ta, ta tsani ace bata iya abu ba, duk yadda zatayi taga ta iya kuwa sai ta koya. Daga shi har Zainab din ta lura yan rainin hankali ne, itace secretary dinsa daga gani shiyasa komai sai yace ita.


  Tana tsaye ya dawo ciki rike da tarin wasu takardun, ya kalli na'urar ganin tayi sai ya dauke kansa daga kai yace mata shikenan, thank you tace masa tayi gaba cike da jin haushin yadda yake abubuwan sa, gashi daga gani yana da son aiki dan ko da yaushe cikin yin sa yake yi kamar wani agogo.



****Karfe sha daya da mintuna hamsin ta gama aikin da ya sakata, ta tattare dukka ta tura masa sannan ta tura copy din a nata email din. Kafarta ta dan mike da tayi mata tsami saboda zama ga bayan ta da ya gaji dan kusan awoyin ta uku chur a zaune tana aikin, bata so ya sake kiran ta kuma shiyasa tayi iya kokarin ta, ta yi masa aikin daidai yadda tasan zai yaba, yau gaba daya bata ga Kamal ba, kamar ma be zo office din ba, dan tabbas da yazo zata ganshi ko taji wucewar sa. 


   A gaggauce ya fito bayan ya karasa tattare dukkan aikin da yasan Daddy zai gani idan ya shigo, karfe daya da rabi jirgin su zai sauka, gashi yace masa lallai ya je ya dauko shi, duk da hakan yana cikin sharudan Daddyn amma sam baya so, musamman tafiya da zata hada shi da Adam waje daya, sannan idan yaje din abinda zai gani ba zai masa dadi ba, amma haka zai hakura dan yasan duk hanyar da zasu bi su hanashi aiwatar da abinda yake niyya zasuyi ne, dan haka ne ma ba zai basu kofar hakan ba.

   Waya suke da Kamal yana kokarin fita daga cikin building din, a daidai lokacin itama take kokarin fita dan dama sha biyu tayi zata dinga tafiya dan ba zata iya wunin da suke yi ba, an ce sai 4 suke tashi amma gaskiya ita tafiyar ta zatayi. 

     Bata ganshi ba kawai tafiyar ta take yi, shima kuma wayar da yake ta dauke hankalin sa baki daya, yana yi masa bayanin abubuwan da zai karasa idan ya shigo shi daga airport ba zai dawo office din ba sai gobe. Driver daddy ne zai dauke su zuwa airport din, Adam tuni ya fito yana zaune a gaban motar yana latsa wayar sa, daga kansa yayi da niyyar ganin ko Aryan din ya fito sai ya hange ta tana tafiya hanyar gate, da gaske yarinyar tayi masifar yi masa, kuma duk yadda zai yi sai yayi ko ta hanyar amfani da Mom dinsa ne ganin ta bashi dama, ba aure bane shi yanzu a gaban sa ba duk da ya isa ace daga shi har Aryan din sun yi aure, amma tabbas yana jin zai iya auren ta ko dan ma Daddy ya sake yarda dashi tunda an ce cikar kamalar mutum itace aure. Balle murfin motar yayi ya fito, fitowar sa ita ta ankarar da Aryan ya kalli wajen da ya nufa.


"Ina zata?" Ya tambayi kansa da kansa.


Wani kallo yaga Adam din yana mata duk da baya jin abinda yake cewa, yanayin yadda ta nuna tamkar ta kosa da maganar da yake mata, sai a sannan ne yayi mata kallo sosai, har yaso ketara kallon da shari'ah ta yarje ma mutum, tsaki ya samu kansa da ja, baya son Adam yana shiga duk wata harka da ta dangance shi, sannan bazai taba yarda mutum irin Adam yayi mu'amula da ita ba, duk da ba wai ya santa bane ba, amma dai tunda a karkashin office dinsa take toh dole zai yi protecting dinta daga mutane irin Adam, shaidanun zamani. Motar ya bud'e ya shiga sannan yace wa driver ya karasa wajen da Adam din suke tsaye, suna isa ya bud'e murfin kofar sannan yace


"Raihana, come in."


 Kallon sa tayi, yanayin fuskar sa da take a gimtse babu ko fara'ah daya, yanayin sa yayi mata kama da na wanda yake cikin tsananin bacin rai, ji tayi kamar ta juya ta zura da gudu dan yadda yake kallon ta 


"Bata shiga motar strangers, ko pretty?" Adam yace yana mata murmushi, hakan ya sake kular da Aryan ya kuma tabbatar da zargin sa akan Adam din


"Kuna bata mana lokaci, I said get in malama." Ya yi maganar a dan zafafe


Gefen mayafin ta ta damke da hannun ta, idanun ta suka ciciko, ya dauke kansa tamkar be gani ba, a hankali ta saka kafarta cikin motar, ta zauna daga karshen kujerar sosai sannan ta sauke kanta k'asa. Wani murmushi Adam yayi kawai, be ce komai ba, ya bud'e gaban motar ya zauna sannan driver yaja suka bar wajen.


   Shiru ne ya biyo bayan hakan a cikin motar, baka jin motsin komai tamkar babu kowa a ciki, hannu Adam yasa ya kunna Bluetooth din motar yayi connecting da wayar sa, hakan ya dauke shirun da sukayi ya maye gurbin sa da wakokin kudancin Nigeria. Daidai wani round about Aryan yace su tsaye, driver ya faka sukayi shiru, bayan mintuna biyar Kamal ya karaso a motar sa, yayi parking a bayan su sannan yace yazo, shi da Shahida kanwar sa da hajiyar su ne, daga asibiti suke abinda ya hanashi shigowa yau kenan sun kai Hajiya taga likita, bud'e kofar yayi sannan yace ta fito, ta fito a sanyaye suka nufi motar Kamal din, har kasa ya durkusa ya gaida Hajiyan ta amsa sannan ta saka musu albarka, suka gaisa da Kamal sannan yace ta shiga motar, shiga tayi ta zauna a gefen hajiyar ta gaishe ta. Shi kuma ya juya ya koma motar su, suka bar wajen.



LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*


*DAUDAR GORA Billyn abdul*


*KI KULANI hafsat xoxo*


*A RUBUCE TAKE Huguma*


*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*


*IDON NERA Mamuh ghee*


_LITTAFI DAYA: 400_

_LITTAFI BIYU: 600_

_LITTAFI UKU: 800_

_LITTAFI HUDU :1000_

_LITTAFI BIYAR: 1200_


_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_


_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_


_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_


_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_


_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_


_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_


ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN


MARYAM SANI

ACCESS BANK

0022419171


SAI A TURA SHAIDAR BIYAN 


09033181070


IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA


09166221261


*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*


+22799643131


Books biyar  1250CFA

Books hudu  1050CFA

Books uku  850CFA

Books biyu  650CFA

Bookk daya  450CFA


KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.


MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post