Wata Sakayya Hausa Novels page 27 - Novels Elite

Wata Sakayya Hausa Novels page 27 - Novels Elite

Wata Sakayya Hausa Novels page 27 - Novels Elite

πŸ‘©‍πŸ¦½πŸ‘©‍πŸ¦½πŸ‘©‍πŸ¦½πŸ‘©‍πŸ¦½πŸ‘©‍πŸ¦½πŸ‘©‍πŸ¦½πŸ‘©‍🦽

  *WATA SAKAYYAR* 

 *(  SAI ALAHIRA)* 

😭😭😭😭😭😭😭😭


By *nusaiba alkamawa*

 *PAGE 27**(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*Φ„Κ€Φ…Κ„Ι¨ΖˆΙ¨Ι›ΥΌΘΆ Υ‘Κ€Ι¨ΘΆΙ›Κ€Φ†*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*


Kokarin azawa akan tafarki,shi ne abu mafi muhimmanci da yakamata marubuta su kware akai,mu proficient writers association za mu yada wannan manufa.

*****

_______Koda mai wannan Mara lafiyar zaiyi mata ba harara ba wllhi bazata taba jin haushi ba,Dan wannan babbar dama ce arayuwarta, fitowar wannan aikin da tayi dama abinda ta dade tanaso ne ta samu damar da zata fito domin neman Dr jamal ta rama masa alkairin da yayi mata duk da tasan bazata taba iya biyansa abinda yayi mata ba amma dai zata kamanta, tausayi ma wannan Mara lafiyar take Ji sbd itama ta taba shiga cikin irin wannan yana yin, yanxu tasamu babbar daman. 

_____kokarin saukowa daga gadonsa taga yanayi da sauri taje ta rikesa tana kokarin taimaka masa ya hau keken, amma saiya hankadata ta bige da kujera duk da bataji ciwo ba, da kyar ya samu yahau kan keken ya tura abinsa zuwa bandaki bai dade da shiga ba sai gashi ya fito,ba tare da ya kalle ta ba yace "hada min coffee" ya fada kamar ba shine yayi maganar ba, ita kanta dan tana kusa dashi ne yasa taji amma daba'a kusa dashi take ba da wllhi baza taji ba, tashi tayi tafita, Amman batasan inda kitchen din yake ba, dawowa tayi inda suka tarar da wannan hajiyar ko ta nuna mata inda yake, aikuwa taci sa'a momy tana zaune tana kallo a tashar **arewa24**murmushi momy ta sakar mata ganin jiddah ta nufo inda take, tsugunnawa jidda tayi tana tambayar ta inda kitchen yake, au affuwan jidda laifina ne da ban nuna miki gidan ba, taso muje na nuna miki, mikewa jiddah tayi tabi momy, aikuwa saida momy ta xagaye da ita  ko ina sannan ta koma, ba abinda jiddah take ayyana wa axuciyarta illa gidan nan domin ya hadu Iya haduwa ankashe daula wannan kudinsu har yayi musu yawa cab aljannar duniya kenan ,  rashin Sani ashe ma kitchen din yana parlour nasa ta wajan corridor shiga kitchen din dake cikin falon nasa tayi, ita dai tasan ana hada mata coffe a gida amma batasan dame _dame inna Asabe take hadawa ba, ruwan zafi ta saka a cup sannan ta zuba suger cokali biyar tare da madara spoon uku sannan ta motsa masa ta kawo masa sai faman turiri ruwan yakeyi mika masa tayi ya karba ba tare da kallon kofin ba, ya fara sha, da sauri ya furzo dana bakinsa saboda wani irin zakin sugar da karnin madara daya sauka a harshensa, shi dama baya shan madara saboda tayar masa da zuciya takeyi, ga kuma uban sugar data lafta a coffe din sai murmushi takeyi tana kallon sa ita a daukarta yayi dadi ne, "zonan" ya fada a hankali yana murtuke fuska kamar bai taba yin dariya ba, zuwa tayi kusa dashi ta tsaya "zauna" ya sake fada kamar bayaso yana nuna mata gabansa a dadare ta zauna, kofin coffe din taga ya miko mata, "anshi kisha" ba tare da wani tunani ba ta karba tana kai kofin baki ta, da sauri ta cire kofin saboda itama ba ma'abociya son zaki bace ba, "wato so kike ki kashe ni ko shiyasa kika zabga min sugar haka, to wllhi saikin shanye sa kona dura maki shi yafada kamar baya son yin maganar " zazzare ido ta farayi zanchan gaskiya bazata iya sha ba, "sha mana" ya fada a tsawace jiki na rawa ta daga kofin ba ita ta diresa ba saidata shanye tana ajiye kofin saiga hawaye zar zar zar suna gudu akan kumatun ta, tabe baki yayi yana dauke idanun sa daga kanta, tura kekensa yayi zuwa bakin gado dakyar ya samu ya iya hawa gadon kwanciya yayi yana runtse idonsa, da dukkan alamu baxa su shirya da wannan bagidajiyar ba, gashi akaran farko ta fara masa shirme. 

"itama jingina tayi da kujera ta cigaba da kukan ta har bacci barawo ya dauke ta, Mommy ce tazo ta dubasu sai taga dukansu suna bacci Jidda a kasa ta jingina da kujera shi kuma gogan akan gado, ja musu kofa tayi tana murmushin ganin duk suna bacci babu ita mai kula dashi din babu shi marar lfy.

______Kamar ko yaushe Muhseen ya taso daga wajan aiki ya biyo danya duba Dr  Jamal, a falon kasa ya tarar da Mommy tana zaune da sallama ya shigo falon sannan ya duka har kasa ya gaishe ta, "lfy lau Muhseen ya aikin naku","Alhamdulillah, bari naje na dubo sa","to saika fito" tashi yayi ya nufi saman, "kee! ya daka mata tsawa, firgigit ta tashi daga baccin daya dauke ta, "dalla tashi kije ki hada min ruwan wanka ko shima din baki iya hadawa ba?" girgiza masa kai tayi tanayin hanyar toilet din daya nuna mata, tana shiga toilet din Muhseen na shigowa dakin, zama yayi a kusa da Jamal, "kai sarkin fushi yanzu kuma waya tabo ka naga kai kadai ne ma" dogon tsaki yaja, "wllhi Mommy ce ta kawo min wata yarinya wai itace zata rika kula dani, gashi kuma yarinyar babu abinda ta iya sai shirme, dazu fa nace ta hado min coffe shine taje ta zabgo sugar bakaji ba dana sha yadda kasan sugar kadai nake sha ga madara kuma ta sanya" tuntsure wa da dariya Muhseen yayi har yana rike ciki, "kace Mommy tayi maganin ka kaga tun ana naimo maka masu kula dakai maza yanzu gashi an kawo maka mace, macan ma wacce bata iya komai ba, ni wai to ina yarinyar take zanso na ganta" ya karasa maganar yana kara tuntsirewa da dariya, banza drJamal yayi masa ganin ma dariya yakeyi masa haka dai yaci gaba da tsokanar sa daganan yayi masa sallama ya tafi, Jidda bata wani sha wahalar hada masa ruwan zafin ba saboda kusan komai na cikin toilet din irin na gidan su ne, fitowa tayi tana masa alama da ta hada ruwan, "mtwss" yaja tsaki yana tura keken sa zuwa cikin toilet din sannan ya banko kofar toilet din da karfi, razana tayi tana tunanin dama haka wannan bawon Allah yake? 

______halinshi ba daya dana momy ba ahaka kamar mutumin kirki, amma kuma sai gashi yanzu yanayin abubuwa na rashin kirki, zama tayi a kasa ta zabga uban tagumi, in sha Allah ko dukana zai rikayi bazan taba gazawa ba zan jure in Allah ya yarda tunda na iya jure wahalar ummanmu ma .Comment dinku nake bukata more comments more typing

Ta hanyar link din group din πŸ‘‡

Follow this link to join my WhatsApp group

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post