Wata Sakayya Hausa Novels page 26 - Novels Elite

Wata Sakayya Hausa Novels page 26 - Novels Elite

Wata Sakayya Hausa Novels page 26 - Novels Elite

πŸ‘©‍πŸ¦½πŸ‘©‍πŸ¦½πŸ‘©‍πŸ¦½πŸ‘©‍πŸ¦½πŸ‘©‍πŸ¦½πŸ‘©‍πŸ¦½πŸ‘©‍🦽  

😭😭😭😭😭😭 


 *WATA SAKAYYAR*

        (Sai a Lahira)


πŸ‘©‍πŸ¦½πŸ‘©‍πŸ¦½πŸ‘©‍πŸ¦½πŸ‘©‍πŸ¦½πŸ‘©‍πŸ¦½πŸ‘©‍πŸ¦½πŸ‘©‍πŸ¦½πŸ‘©‍🦽


By

            *Nusaiba Alkamawa*


 *Free page 26* 


Ina taya yan uwa al'ummar musulmai murnar sallah, Allah yadada maimaita mana amen 🀲🏻sannan kuma ina jiran happy sallah na 😜


*****

______Tunda Hassana ta fara magana Jidda bata dago ta kalle ta ba harta dasa aya, sannan ta dago fuskar ta wanda duk ta jike da hawayan bakin ciki, ita ta rasa maita tsarewa su umman nata a cikin gidan nan da suke nuna mata tsananin kiyayya, maganar hassana ce ta katse mata tunanin da take "maza kije ki hado kayan naki kafin ta fito saura kuma ki bata mata lokaci wllhi inzo har dakin in ci ubanki" jiki a sanyaye Jidda ta fito daga falon tana kuka bangaransu ta nufo tana shiga ta tarar da inna Asabe a zaune tana jin radio, a razane inna Asabe ta mike ganin yadda Jidda take kuka har tana dan shidewa, "lfy mai wadan chan azzaluman suka kuma yi maki kuma, dazun nan fa suka fasa kwalba kika taka yanzu kuma dukan ki sukayi?" ji Jidda tayi inama dukan nata sukayi akan wannan aikatau din da akeso a kaita, da hannu ta ringa fadawa inna Asabe dukkan abinda yake faruwa ajiyar zuciya inna Asabe ta sauke cike da tausayin baiwar Allah Jidda, "karki damu insha Allah hakan saiya zame maki alkairi tunda kedai baki nufar su da sharri" haka Asabe ta taya Jidda ta hada kayanta sannan ta kulle su a cikin dan kwali ta daure su saboda batada ledar da zata saka kayan a ciki tana kuka inna Asabe na kuka haka suka fito lokacin Shamsiya itama ta fito, "to bakar munafuka ke kuma da kika biyota kina kuka kin isa ki hanata tafiya ne, wllhi kemah kin kusa barin gidan nan dan naga munafurcin ki ya fara yin yawa bakar munafuka kawai Allah yasa ma da xuciya daya kike rike da ita salatuf kawai, tafada tare da doka mata, wata uwar harara, dama hassana badai ido ba. 

" itadai inna Asabe batace komai ba sai kuka da takeyi tana rungume da Jidda, fisgota Hassana tayi ta turata a motar Shamsiya sannan itama shamsiyar ta shiga mota tana fadin "sai munyi waya kawata" daga mata kai kawai Hassana tayi tana daga mata hannu har suka bar gidan, sannan ta juya tana watsawa inna Asabe wani kallo mai wuyar fassarawa batare da tayi magana ba ta shige ciki ta bar Asabe na kuka a wajan gwanin ban tausayi. 

Babban takaicin jiddah ma bata ga jamal ba tana so tayi masa godiya yanzu yaxatayi? gashi number nasa na nemi paper na rasa, nadau alkawarin duk inda jamal yake saina dubo sa, Amman ta yaya? Ta wace hanyar? 


Wata xuciyar tace kawai kije asibitin kitambayi Dr muhseen, Amman kuma zai bani duk amso Shin dana nema? Nagama kamar haushina yake Ji. 


Kuma yaxanyi da wannan matar? 

Yaxanyi na tsere mata, anya kuwa idan nayi hakan nayi daidai, na tabbata idan hakan ta faru dani umma taji wannan labarin saidai wata jiddar badai ni ba 

Yanxu yaxanyi?

 Nace ba jiddah fans kubata shawara mana πŸ˜‰

_____maganar shamsiya ce ta katse mata tunanin keeeee banxa kijirani Anan yanxu xandawo saura kuma kitabamin wani Abu a cikin motar nan, kiga yacce xanyi dake, tafada tare da ficewa. 


_____Jiddah anya kuwa matar nan ba siyar da ke xatayi ba, bata da tausayi kawai ki gudu kije kinemo jamal, haka xuciyarta take saka mata, Ai kuwa xuciyar tayi nasara Dan jidda kama kofar take tana kokarin fita, wani layi ta shige wanda lungu ne ba yacce xa ayi, a Iya ganota, talabe. 


Dawowa shamsiya tayi Amman bata ga jiddah ba kardai yarinyar nan ta gudu? To kodai gida ta koma Ai kuwa da saita gane yan garin su hmm waya ta dauka da niyar Kiran aminiyar tata Amman me? Jiddah tagani tana nufo inda take, cikin tsananin fushi ta kifawa jiddah kyakkyawan mari, wanda  saida taga stars kee Dan uwar ki ina kika je? Nuni jidda tayi mata da hannu fitsari naji shine naje wani gida nayi, fisgota tayi hartana bigewa ta saka ta a motar taja. 

Wato abinda yafaru shine, jiddah sauya shawara tayi anya kuwa nayi wa kaina adalci? Yanxu idan sukayi tunanin na 'bata fa, ya inna asabe da baba garxali xasuji, kawai naje gidan aikin idan anbani albashina saina gudu, naje na nemo jamal din nayi alkawarin saina nemo shi duk inda yake. 

To kunji dalilin dadowar jiddah. 

_______Suna zuwa gidan basu sha wani wahala wajan shiga ba saboda mai gadin ya riga yasan Shamsiya, dayake shamsiya badai shishshigiba , suna zuwa suka tarar da Hajiyar tana karanta jarida, "aa Shamsiya yau kece a gidan namu, bismilla ku zauna mana" zama Shamsiya tayi a kusa da Hajiya ita kuma Jidda ta zauna a kasa, kan wani laulausan carpet , "Hajiya dama naji makwabciyata tace kina naiman wacce zata rika kular maki da yaro shine na kawo maki wannan nasan zata iya kula dashi saboda tana da hankali amma fa bata magana"  tausayin Jidda ya kama Hajiya jin ance bata magana,gata yarinyar kyakkyawa kamar ma ba yar kasar nan ba "amma Shamsiya kina ganin zata iya kula dashi kuwa kinsan fa miskili ne na ajin farko","karki damu Hajiya insha Allah zata iya","to shikkenan  ngd duk wata zamu rika biyan ki dubu dari biyu da hamsin yayi maki" Hajiya ta fada tana kallon Jidda, "karki damu Hajiya yayi mata sosai ma, amma ni za'a rika bawa kudin ina kaiwa mahaifiyarta" Shamsiya ta fada tana bankawa Jidda harara, hawayen da suka zubo mata tayi saurin gogewa saboda shamsiya ta gargade ta a mota tashi tayi tanawa Hajiya sallama sannan ta tafi tabar Jidda a gidan.

______Dakin da Jidda zata rika kwana Hajiya ta nuna mata sannan tace, "muje na nuna maki dakin wanda zakina kula dashi dan Allah ki kula min da yarona sosai kinji ko? Tunda yayi hatsarin mota lafiyar tasa yanxu sai ahankali " a sanyaye Jidda ta daga mata kai a dai _dai lokacin da suke shiga dakin, Dan mama da yake kwance ya tsurawa silin ido yaji an turo kofar dakin an shigo ko bai dago ba yasan Mommyce a hankali ya yunkura ya zauna yana jingina da fuskar gadon, zama Mommy tayi tana nunawa Jidda dayar kujerar amma saita zauna a kasa murmushi Mommy tayi dan ta yaba da hankalin ta,tare da ladabinta "wannan shine wanda zakina kula dashi a tare suka dago ido suna kallon juna, shi jin ance wacce zatana kula dashi shiyasa ya dago, itama jin ance wanda zatana kula dashi shiyasa ta dago, carab idonsu ya sarke a na juna wani irin zir yaji tun daga kansa har babban dan yatsar kafar sa, ita kuma gabanta ne ya fadi ganin wanda take muradin gani koda kuwa a mafarki ne, murza idonta tayi wai ko shine yake mata gizo amma sai taga ashe ba shine ba idon natane yake mata gixo dai,wannan ba  jamal bane ba Dan kama sukayi kadan Amman wancen fuskar shi ba haka take ba, kuma wannan hatsarin mota yayi kuma sunan shi Dan mama, maganar momy ce ta da katar dasu daga kallon da sukewa junansu tace "inaso kana binta a hankali domin kuwa bata magana, daga wannan yar aikin ko kace bakasonta to wllh ka saka a ranka bazan kara samo maka mai kula dakai ba saidai ka rika kula da kanka kaji dai na gaya maka" tana gama fadin haka ta Mike,tare da kallon Jidda, "ki zauna dashi koda zai bukaci wani abun" ras haka Jidda taji maganar dan wannan shine karo na farko da zata fara kebewa da namiji wanda daga ita sai shi a cikin dakin, fita Mommy tayi tana ja musu kofa, a hankali ta dago idunta tana sauke su akan wanda aka kira da suna Dan mama harara ya banka mata yana jan tsaki da sauri ta sunkuyar da kanta kasa tana murza yan yatsunta.

WhatsApp no 09030567767 

Called no 07036162215


Kuyahkuri mutane na, karku yi min magana kuji shuru anyi min hacking din account ne Amman yanxu nasauya number WhatsApp din, gata asamaπŸ‘† ngd sosai 

Share plx

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post