Wata Sakayya Hausa Novels page 28 - Novels Elite

Wata Sakayya Hausa Novels page 28 - Novels Elite

Wata Sakayya Hausa Novels page 28 - Novels Elite

😭😭😭😭😭😭😭😭

 *WATA SAKAYYAR* 

         *SAI ALAHIRA* 

👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽


By

            *Nusaiba Alkamawa*


 *PROFICIENT WRITERS* *ASSOCIATION*

FACEBOOK ALKAMAWAS GLOW 

INSTAGRAM NUSAIBA ALKAMAWA 

WATTPAD NUSAIBA ALKAMAWA 

 *Free page 28* 

*******

Yana fitowa daga wanka ya ganta raku'be, a gefen kujera tsaki yaja yana dauke ido daga kallon ta, yace "a fita zan saka kaya ko dama an saba ganin namiji babu kaya shiyasa bazaki tashi ki fita ba, wato nima in saka kayan a gabanki ko?"ras haka taji maganar ta dake ta, bataji dadin yadda ya fassarata ba, ita da kanta ma yake a sunkuye tunda ya fito jiki a sanyaye ta tashi ta fito kasa ta sauko Mommy ta gani itama tana kokarin hayewa saman hannunta dauke  da tray din abincin Jamal, "yauwa gashi dama abincin ku zan kawo maku amma tunda kin sauko gashi ki kai maku sai kuci" daga mata kai Jidda tayi tana karbar tray din daga hannunta, cike da ladabi, koda taje kofar dakin ta kusa minti goma tana tunanin ta shiga ko karta shiga, daga karshe dai ta yanke shawarar kawai ta shiga a zaune ta tarar dashi akan kujera yana danna laptop dinsa, kyau taga ya kara yi mata cikin shigar da yayi, Dan Dr jamal badai kyau ba, wando tiri kwata ya saka sai riga haka marar nauyi yarta shan iska dai haka, tunda ya kalle ta sau daya bai sake kallonta ba amma kuma yanajin idanuwanta suna yawo a jikin sa, "bana son kallo fa, na tsani a dunga kallo na" ya fada batare daya dago ba, abincin takai masa gabansa ta ajiye masa, alama tayi masa data zuba masa banza yayi mata ganin haka yasa ta kara komawa gefen kujera ta rakube kamar dai ko yaushe, saida ya gama abinda zaiyi sannan yace tazo ta zuba masa abincin, tasowa tayi cike da natsuwa ta fara zuba masa abincin bada yawa sosai ta zuba masa ba, mika masa tayi ya karba babu yabo babu fallasa ya fara cin abincin. 

"ita kuma wajan zamanta ta koma ta sunkuyarda kanta kasa, tana tunanin rayuwarta, wai sai yaushe ne dadi xaixo mata ne itama? kodai bata da rabon jin dadin duniya ne? Indai kuwa hakane Allah ya Dauki rayuwarta ko taJe taji dadin lahira, tunda aka haifeta batasan menene wani wai shi dadi ba, ita dai kawai tasan farin ciki shine sanda iyayenta suke raye, Allah yayi wa *iyayena* (sunan next novel dina *iyayena* ) Rahma ameen, Amman xanso nagansu muhadu da juna nasanar musu irin ukubar da ake shayar dani, hmmn *wata* *sakayyar sai alahira* tafada da dankaramin bakin ta wanda yake pink colour me kyau. 


"saida ya gama cin abincin yasha ruwa sannan yace, "zo ki kaini baranda zansha iska" to tace cike da sanyin halin ta, turasa tayi yana nuna mata hanyar barandar harta kaisa wajan zama sukayi jiddah kuwa banda xare ido babu abunda take awajan, dama ga idanun nata tubar kalla farare kal kuma dara_dara wanda yake cike da tarin gashin ido xara - xara gurin yayi matukar yin kyau. 

_saida aka fara kiran sallar magriba sannan yace ta mai dashi daki turasa tayi zuwa daki sannan ya shiga toilet ya dauro alwala sannan ya fito ya tada salla a zaune, itama dakinta na kasa taje tayi salla sannan ta dawo saman ko yanada bukatar wani abu, tana shiga babu dadewa saiga Mommy ta shigo da abincin dare a hannun ta, ajewa tayi tana kallon kulolin abincin ranar dataga alamar mutum daya ne yaci, "Jamal kaci abincin kuwa","ehh Mommy naci ga plate din danaci nan ma","to ita Jidda taci ne" girgiza mata kai yayi yana mamakin dama tare aka hado musu abincin?  amma mai yasa Mommy zata hada musu abinci da wannan kazamar yarinyar, amma ta wani bangare na zuciyarsa yana tausaya mata ace har yanzu mutum baici abincin rana ba, dage kafada yayi alamar ita ta sani, a bangaran Jidda kuwa ita kadai tasan irin yunwar da takeji dan dama da safe ma bataci abinci ba Hassana ta korota suka taho ita da Shamsiya, kuma data kawo masa abincin bayan yaci itama baice ta zuba ba, duk da yunwar da takeji amma saita ki zubawa saboda gudun karta yi laifi,Dan ma tasaba Ji fiye da haka, Dan agida saita kai magriba bataci abinci ba idan inna Asabe batanan ita dataga abin ci kuwa harsai inna Asabe ta dawo, dayake inna Asabe bata taba xuwa unguwa ta kwana ba sbd kulawa da jiddan. 

________abincin daran da Mommy ta kawo ta zuba mata, tuwan shinfaka ne da miyar kubewa da nama data sha manshanu, hannunta na kakkarwa ta karbi abincin ta faraci hannu baka hannu kwarya, shi kansa DR Jamal tausayi ta basa ganin yadda takecin abincin yasan cewa laifinsa ne, "gaskiya Dan mama baka kyauta ba kabar ta da yunwa","yi hakuri Mommy ni bansan tare kika zubo mana ba itama kuma bata fadamin ba yafada xuciyarsa najin haushi sbd akantane momynshi take masa fada kuma agabanta salon taraina shi, shifa baya son raini. 

 *Hassana*

Ai wllhi ina gaya maki nice nan nayi sanadiyar mutuwar su , daga karshe itama zan san yadda zanyi na kawar da ita daga doran duniya bayan na amshe dukkanin kadarorin ta " sosai hannun Asabe yake kakkarwa saboda jin abinda Hassana take cewa ashe dama mugun halin hassana har yakai tayi kisa? Kai duniya ina xakije damu ne aiko wllhi saina tona mata asiri,kuma saina fada jiddah kar wataran tazuba mata guba a abinci Dan yacce ta tsane ta haka, tayi taka tsantsan da ita dan xatayi iyayin komai sbd duniya,Allah sarki ko suwaye hassana ta kashe oho?Amman dagaji wani ma kusan ta ne maana Dan uwanta,, tsabar firgitar datayi batasan lokacin da tray din hannun ta ya fadi ba datazo kawowa Hassana abincin ta, shine taji wannan mummunan zan cen. 

"a firgice Hassana ta fito dan ganin waye a bakin kofar saboda ta tabbatar koma waye ya rigada yaji abinda take cewa saboda da karfi take wayar, amma koda ta fito saita tarar babu kowa.

Nikuwa aunty nuseee  naja ajiyar xuciya nace alhmdllh tunda bataga ko waye ba. 


Share

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post