*H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Part 02
Page 19
Hafsat ce a wani birkice sanye da hijabi ruwan qasa,fuskar nan cike taf da bala'i,tun sanda ta dawo taji sunyo gida da abbas din hankalinta yatashi,kullum fatarta da addu'arta yarinyar ta tafi kenan,sai gashi ta dawo rayuwarta tsundum
"To mayya natacciyar dole,da kika tashi dawowa ai saiki jira girki yazo kanki,bawai ki biyomin miji kihau aikin da ba naki ba" sosai maganar tata tayi mata ciwo,kamar ba zata tanka mata ba,amma saita dago daga gyaran throw pillows din da takeyi ta kalleta
"Maita da naci ga miji inajin isace wannan,wadda bata isa ba ko tayi babu riba,mukan da mukeyi alhmdlh akwai riba, miji kuwa babu wata rana da na kebe da zan tsame hannuna daga bashi kulawa saboda na girkina bane muddin yana da buqatar kulawata,ke meye ya hanaki tsaiwa ki bashi kulawar idan har kin damu dashi?" Ta fadi kanta tsaye tana kallon idanun hafsat da mamaki ya kasheta.
Turqashi!,anzo wajen,yau ta samu dama,tanajin babu abinda zai hanata cin uban yarinyar yau abinda ta jima tana buri,kamar widad din ta karanci hakan,kuma bataso tayi abinda zai tada abbas di daga bacci,don haka tayi hanyar kitchen da dan saurinta
"Dawo mana qaramar mara kunya kiga yadda ake yinta yau a fidda raini" hafsat ta fada tana bin bayan widad,dama abinda widad din keso kenan,don haka tadan daga qafa,tana shiga kitchen din ta tsaya tana ajjiye plate din hannunta,dai dai sanda hafsat ta qaraso ta dora hannunta a kafadar widad da nufin damqota.
Tankwabe hannunta widad tayi cikin fushi tana kallonta
"Sakeni,karki sake gigin riqeni,idan raini kikeso a fidda ki bari ya gama baccinsa ya fita a gidan ya zaman dagani sai ke,a sannan zan nuna miki cewa jaa da baya ga rago ba tsoro bane,shashasha wadda har yau batasan ta girma ba" ta dire maganar da tsaki mai mugun qarfi.
Tsananin mamaki ya sanya hafsat din mutuwar tsaye tana kallon widad,cikin fushi ta yunquro a karo na biyu kafin tace komai widad ta rigata yin magana
"Kika sake kika dora hannunki a jikina.... wallahi tallahi sai nayi miki wanka da wannan ruwan zafin,sauna kawai,shashasha"tayi maganar tana fidda manyan fararen idanunta waje a kan hafsat din.
Abu makamancin wannan bai taba hadasu da wida din ba,don haka furucinta ya tabata sosai,sai taja da baya tana tafa hannuwa
"Ashe da 'yar kalare nake zaune?,dama kanawa 'yan sara sukane mazanku da matanku?,to shi wanda ya baki daurin qarqashin yimin rashin mutuncin bari na tasoshi" saita juya tana haramar fita a kitchen din.
Ai widad bata barta takai qofar ba ta sanya hannu ta fincikota saiga hafsat warwas a qasa,ta isa bakin qofar kitchen din ta tsaya riqe da qugunta
"Azzaluma mara imani,wanann baccin dai yau sai ya yishi wallahi duk baqincikinki da baqin halinki" sai kawai taja qofar kitchen din ta kulleta aciki,bata da wata hanyar fita kuma saidai tabi ta qofar baya ta kitchen din ta fice,saita isa qofar part din nasa shima ta kulle,sannan ta saki ajiyar zuciya tana jan tsaki a ranta.
Sam ta daina ragawa matar,zata nuna mata ita din bakanuwa ce,duk da ba jininsu bace amma kuma cibiyarta na bunne anan,tana jjn surutanta da zage zagenta sama sama har ta daina ji,da alama tabi ta qofar bayan ta fice.
Yayi bacci kuwa sosai,don bashi ya tashi ba sai dab da magariba,a sannan widad din tayi wanka a nan sashensa ta sauya shigarta da wani sky Blue din material me kyau,ta daure kanta da band ta kuma dora dan yalolon mayafin material din,affan na kwance daga gefe cikin farar overall yana bacci abinsa shinfide cikin farin towel.
Tunda ya fito yaga dukansu sunyi masa kyau uwa da dan nata,karon farko da ya fara ganin mai jego mai tsafta irin haka,abinda bai saba gani ba,idan hafsat na jego idan kaji ana jaga jaga ko itace,duk wani kalar qarni da bashi bashi zaka jishi,idan anyi magana takance jego take,dama wannan ai shine jegon inji hausawa,sallamawa sassanta dama yakeyi gaba daya,saidai tazo nashi da ziyara ta wuce.
Ta daga kai daga wayar dake hannunta tana duba saqonnin watsapp suka hada ido,ya sauke mata murmushi yana jin zuciyarsa tana yin sanyi,ya samu nutsuwa kaso hamsin cikin dari daga qunci da rudanin da zuciyarsa ke ciki,ya durqusa a hankali yayi kissing affan dake baccinsa cikin qauna, qamshin da jikin yaron keyi ya ratsa hancinsa,ya daga kai yana sake kallonsa
"Kullum kamanninmu da muhammad sake fitowa takeyi" ya fada da sassanyar muryarsa,ta saki dan murmushi
"Sosai.......kun nunamin son kai ai" ta fada tana dan masa hararar wasa,sai ya saki murmushi yana cewa
"Ba komai,next time by now ya samu yaruwa,ita na tabbatar zatayi miki karar" ido ta fidda sosai tana kallonsa sannan ta langabar da kai
"Habba mana uncle....." Kai ya jinjina yana tarar numfashinta
"Yes.....inason yara da yawa babyn uncle,mutuwar hajiya tasa naji ina son in tara yara masu yawa sosai,just pray Allah ya bamu nagari da zasuji qanmu"sai ta jinjina kai tana cewa
"Ameen".
Bai fita sallar magariba ba sai da yaci abinci ya sake wanka,kafin ya dawo ta sake gyare komai,ta budade falon da qamshi yadda zai masa dadin zama.
Sai da akayi isha'i ya dawo,ya zauna a falo suna taba hira,yana kan kujera tana zaune a qasa,qafarsa saman cinyarta tana matsa masa qafafunsa a hankali cikin wani salo da ya sake saukar masa da nutsuwa,kamar an jehota saiga hafsat ta sake shigowa falon tana kumbura.
Kallo daya widad tayi mata ta dauke kai kamar batasan Allah yayi ruwanta ba a wajen tana ci gaba da tausawa abbas qafarsa,yayin da abbas din ya tsirata da idanu yana kallonta ba tare da yace komai ba
"Daddyn mimi,zuwa nayi na gaya maka ka jawa matarka kunne sanna kayi mana tsakan........"
"Dakata da Allah"ya fada da kakkausar muryarsa yana daga mata hannu
"Bana buqatar wata hayaniya ko tashin hankali,idan ba zaman lafiya bane ya kawoki ba..... please stay away from here" yadda yayi maganar yana nuna kamar ta gundureshi yasa ranta ya quntata sosai
"Adalcin da zakayi kenan?,ba zaka tsaya kaji abinda akayimin bama.....dama kaine kakar daure mata gindi shi yasa kullum take kallon mutane sa'aninta,to wallahi......"
"Shut up" ya miqe tsaye a zafafe yana nuna mata hanya
"Fita banason hauka" hawaye ne suka balle mata
"Yanzu a gabanta kakemin haka abbas?,na rantse da Allah......" Wani mahaukacin mari yakai mata wanda widad ta tabbata inda ya sameta saita rasa haqoran gaba,Allah ya taimaketa ta goce,ba shiri ta juya tana fita daga falon,hannunta dafe da kuncin nata cikin kuka kamar wadda marin ya sameta.
Hannunsa cikin kana ya zauna yana yamutsashi,ya samu ciwon kan ya ragu amma tana neman maido masa bara bana,miqewa widad din tayi tayi mazauni gefans kamar zata shige jikinsa,da kalamai da hikimomi data koya ta samu nasarar saukeshi,ya dinga sauke ajiyar zuciya yana matsa hannunta dake cikin nasa,ba shakka mace ta gari rahama ce,inda bai samu widad din ba ashe da haka zai qare rayuwarsa cikin wahala da baqinciki?.
A daren tason ya barta ta kwana sashenta ta kira hafsat din ta kwana tare dashi,tunda ita din na abinda zata iya masa amma yace bata isa ba,muddin ta tafi ranta sai ya baci,shiba wani abu yake buqata ba a situation din da yake ciki ba,koda batayi masa komai ba kasancewarta a damansa yafi komai kwantar masa da hankali.
Kwanan daga fuskanci widad din tayi ya sake ingizata sosai,wutar qiyayya ta sake ruruwa a zuciyarta,ranar tayi kukan fili tayi na boye,ta kuma tsinewa duk wata kishiya dake duniya.
Washegarin da akayi addu'ar bakwai suka shirya komawa kaduna bakin aikinsa,yabar widad a nan don ta gama arba'in dinta,taso komawa kano amma muhsin yace tazo kenan,dan tsoho alhj salim ya goya masa baya,hakama abbanta,don dole ta zauna a nan,amma ta koma gidan hajjaa ne saboda yadda gidan har yau yake bata tsoro.
********To sannu a hankali kwanaki suka ci gaba da tafiya,al'amuran rayuwa kuma sukaci gaba da gudana yadda suke a baya,duk da ciwon rashin hajiya yana zukatansu,amma dole a yadda da hukuncin ubangiji a kuma rungumi rayuwa a duk yadda tazo.
Zamanta gidan hajjaa taci gaba da samun kulawa,tana kuma sake gogewa da rayuwa da sanin makamarta.
Sanda sukayi arba'in affan yayi wata qiba gwanin sha'awa,yaron kamar ka saceshi ka gudu saboda kyau da wani kwarjini da yake dashi,farat daya yake shiga ran kowa,hakanan itama widad din,kana kallonta zakasan lallai girma da hankali ya soma gameta,ta samu hutu da nutsuwar rai sosai a tattare da ita,ta zama wata big madam,ta kula da jikinta da kyau ciki da waje.
Ranar da sukayi arba'in ranar abbas da yammaci ya diro,da safen sunyi waya da tace masa basuyi arba'in ba sai jibi,saboda batason yace mata zaizo,akwai abubuwan da takeson qarasawa,to ashe yana lissafe tsaf da kwanakin.
Dariya nujood ta dinga yi mata sanda aka saukeshi a setting room,tana zaune dafa'an a qasan carfet sanye da wata riga me qaramin hannu mai kama jiki kamae robber,sai palazzo pants daya zauna mata sosai ya kuma bude yadda ya kamata daga qasa.
Harara ta watsawa nujood din ta miqe tana cewa
"Karki bari aji kanmu dake wallahi" tayi maganar tana zare ribbon dinta da yayi sakwa sakwa tana gayara gashinta,duk da cewa itama taji dadi qasan ranta,don ba qaramin kewarsa tayi ba,to amma kuma taso ta kammala komai ne
"Bani nakar zomon ba" ta gama gyarawa tsaf ta duqa zata dauki affan nujood ta rigata tana cewa
"Rufa masa asiri,kada a jawo masa a matse dan bawan Allah,ku gama gaisawar tukunna sai na kawo miki shi" ta fuskanci jan magana nujood din keji,sai bata sake ce mata komai ba ta juya ta fice.