*H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Part 02
Page 20
A tsaye yake yana fuskantar qofar shigowa falon,hannayensa duka zube a aljihun trouser din dake jikinsa,qananun kaya ne a jikinsa da sukayi matuqar dacewa da lafiyayyar fatarsa da kuma qirar jikinsa dake bayyana halittarsa ta qaqqarfan namiji.
Tun kafin ta qaraso ya saka hannunsa ya zare baqin gilashin fuskarsa yana qureta da kallo,totally ta sake canza masa,kamar ba widad dinsa ba,a yanzun wata cikakkiyar mace yake gani,wadda komai nata ya cika goma cif cif,kama daga kyan halitta zuwa qirar jikinta,yanayin takunta mai daukan hankali wanda a baya yafi kama da na shagwaba,a yanzun ya zama wani irin taku me aji.
Itama shi take kallo sanda ta shigo setting room din,uncle din nata ya canza,yadan rame kadan amma fatarsa tayi fresh sosai,manyan idanunsan nan masu matuqar kwarjini da fusgar hankalin suna tsaye kyam a kanta,sai kawai ya bude mata hannayensa,batayi qasa a gwiwa ba ta tafi a tausashe ta fada,ya maida dukka hannayensa ya kulleta gam yana sauke ajiyar zuciya yana rufe idanunsa
"Welcome back abbas" ya furta da murya can qasa,saita daga kanta sa sauri tana duban fuskarta,dai dai sanda shima ya bude idanunsa ya zubasu cikin nata
"Back from where?" Murmushi ya saki,ya kama tsinin hancinta yadan riqe sannan yace
"from an unhappy life to a life full of joy and happiness" murmushi ya subuce mata,tayi juyi me kyau cikin qirjinsa,tana sake tuna kalaman sha'awa da tace indai mijinki yana jin kece rayuwarsa,indai mijinki yana jin bashi da sauran farinciki da walwala sai idan yana tare dake,lallai kincika mace,kin amsa sunan daya cancanci a hada miki da yabawa.
Matseta yayi gam cikin jikinsa yana sansanarta da kyau,duk sai qamshinta ya ida rikitashi,ya fara kai hancinsa ko ina a jikinta yana sansanawa,kafin Wani lokaci sai ya nemi ya birkice mata gaba daya.
Itama da qyar ta saita kanta,tadan tureshi tana cewa
"Uncle,gidan surukanka kake fa" dauke fuskarshi yayi daga inda ya boyeta cikin jikinta,yana dan jan hancinsa kamar me mura,ya lalubo nutsuwa da qyar ya azama kansa
"Oh.....haka.....ina fata kin shirya tafiya" noqe kafada tayi
"Uncle,ban gama shiryawa ba,da saura fa" kai ya girgiza,ba zai iya tafiya ya barta ba a yau din,don shi kadai yasan yadda yakeji,shi kadai yasan irin azbtuwar da yayi watannin data dauka basa tare
"Pack your stuff we will go home,ko mu wuce a kawo miki kayan daga baya" duk yadda taso ya bari ko zuwa dare ne amma yaqi,dole hajjaa ta kira uncle muhsin a waya ta gaya masa zasu wuce
"Har sai an gayamin banda abinki?, shi da matarsa?,tunda ya tako da kansa yazo ya gaza haquri zuwa randa sukayi dashi ai kinga akwai dalili"
"Amma uncle,akwai abubuwan da ba'a gama hada mata ba ko.kayanta ma bata shirya ba"
"Kinga please stop it......ta bishi kawai,koma meye a aika mata dashi daga baya,tabar hada kayan sawar nata nujood takai mata su gobe ko jibi" hakanan aka bi umarnin uncle muhsin din,sukayi sallama sun cika da kewar affan tun kafin ma su qarasa barin gidan.
Sanda suka isa gidan lawal ne ya buda masa gate yana masa sannu da zuwa,daga haka ya saka kai zai bar wajen,sai abbas din yayi kiransa,ya sanyashi debe dukka kayan da suka shigo dasu,yadan rusuna ya gaida widad,ta amsa tana mamakin yadda yau ya gaidata din ma,don dan dakin hafsat ne,ba wani magana bace take hadata dashi ba wanda ya wuce gaisuwa,gaisuwar ma da sai idan sunyi clashing sosai ba yadda zai wuceta.
Ba kowa a gidan dama sai mai gadi,sai kuma lawal din da yana shirin fita suka dawo,don haka bayan ya fice gidan sai ya sake zama shuru.
Tare sukayi aikin komai da komai,suka gyara part dinsa sannan suka koma suka gyara nata.
Cikin lokaci kadan gidan ya koma fes,iska mai dadi hade da wani lallausan qamshi ya shiga kai kawo,ta gyarawa affan kwanciya saman dan qaramin gadonsa da abbas yasa aka hada masa,sannan ta fidda kayanta ta shiga wanka.
Tana gama zare towel din jikinta ya tura qofar toilet din ya shigo,ta waiwayo a hankali suka hada idanu,kowa ya kafe dan uwansa da kallon nan mai cike da shauqi da wata irin qauna mai fusgar hankali tare da kewa,ya zame idanunsa a hankali ya saukesu kan qirjinta,wani abu ya jashi kamar lantarki,sai ya gaza ci gaba da tsaiwa a wajen,ya shigo ciki sosai,ya maida qofar toilet din ya rufe.
Kayan jikinsa ya fara zarewa,har yanzu idanunsa yana kanta
"Bari nayi joining dinki,ruwanki yafi nawa dumi da qamshi" ya fada yana fidda qaramin murmushi hadi da kashe mata ido daya.
Kafada ta maqale a shagwabenta,kamar dai widad din nan da aka kawo masa lokuttan baya da suka shude wadda batasan komai ba
"Allah uncle wayo dai,iri daya na hada mana fa,kaje toilet din naka ka dub......" Bata qarashe ba ta tsinceta manne da jikinsa,abinda ya kusa sanyata shidewar numfashi saboda yadda fatar jikinsu ta hadu guri guda,daga nan bakin dukkansu ya mutu ita dashi,wani irin feeling mai qarfi ya dinga kewaya cikin jini da zuciyarsu,sai gashi gaba dayansu kowa ya birkice tsananin ita dashi,wankan da ba'a ida gamashi ba,suka zarce zuwa gadonta daya samu kyakkyawan gyara.
Kai tsaye zata iya kiran ranar da second first night dinta,don sai komai ya zame mata sabo kamar bata haihu ba,taci wuya a hannunsa,har shi kansa ya shaida hakan,tana rungume tsam a jikinsa,kwanyarsa cike fal da tunani,dama ana samun hakan bayan d'a ya tsaga jikin mace ya fito?,lallai da gaske mata suna suka tara,kamar yadda suka banbanta a abubuwa da dama haka suka banbamta ta wadan nan guraren.
Sati guda sukayi a bauchi suna bare wani amarcinsu,irin amarcin da a baya ma bai sameshi ba,a yanxun ya samu fiye da abinda yakeso,ya samu fiye da yadda yake zato,ya kuma samu fiye da abinda yake tsammani,gaba daya widad din ta gama zama cikakkiyar mace ta kowanne fanni,yana samun fiye da abinda yake buqata daga wajenta,bata fannin kwanciya kadai ba..... a'ah,ta kowanne fanni ma ta cike masa dukka wani gurbi.
Wannan yayi matuqar tasiri a rayuwarsa da zuciyarsa,ta sake shiga ransa da wani irin matsayi mafi girma da yakejin kaf kafin duniya a yanzu babu diya macen data takashi.
Randa suka cika kwanaki bakwai ranar suka tattara suka wuce kaduna,kai tsaye kuma ya zarce da ita sabon gidan da ya kama mata,ya kama haya ne saboda bashi da tabbacin zasu yita zama a Kaduna,koda yaushe yanayin aiki yana iya canzashi daga kadunan zuwa wani gari na daban.
Yayi mata ba zata matuqa,al'amarin kuma da ya faranta mata rai fiye da zatonsa,ko ba komai zata samu sakewa,ta rabu da wata matsalar,zata kuma tattara hankalinta ta kula da mijinta da kuma yaronta yadda ya kamata,gida ne two bedroom,kowanne da toilet a ciki,kitchen parlor da kuma dining area,sai madaidaiciyar harabar da zata iya dauke motar abbas din,yayi matuqar tsaruwa gidan,dole ya burgeka,an shirya komai bisa mizanin hankali da ilimi.
H AF S A T
Batasan cewa zata damu ba da gidan da widad ta koma din ba sai bayan ta koma din,tunda ita da kanta ta zaba cewar ba inda zata motsa daga nan gidan da suke,saidai ita widad din ta qara gaba ta barta,tunda itace babba,babu mai cire gwamnatinta.
Murmushi kawai abbas ya saki sanda take wannan bayanin cike da izza fariya da kuma alfahari
"Gwamnatinki saidai kuma wata,mai guri yazo mai tabarma dole ya nade abarsa" abbas ya fada cikin ransa,yana matuqar tausayin hafsat din amma ita sam bata tausayin kanta,yana hango mata rasa abubuwa da dama cikin rayuwarta amma ita bata gani,Allah ya sani,ko ra'ayin auren mata biyu baya dashi,ko meye ya faru tamkar itace ta bashi lasisin aikata hakan.
Widad kam cikin nutsuwa da kwanciyar hankali ta tsara gidanta ta kuma ci gaba da tafiyar dashi,cike da qwarewa da kuma gogewar da take sake samu daga mutanen dake tare da ita,cikin ikon Allah ta hadu da maqota na qwarai,macace mai matuqar karamci dake kallon widad din kamar qanwarta,jininsu ya hadu qwarai tashi guda,wannan ya sanya widad din taja babbar 'yar matar da ba zata wuce shekara sha daya ba a jiki,aminatu yarinyar nada matuqar hankali,ta iya komai ita kewa mamanta ayyuka da yawa,amma yawan alkhairan widad a garesu ya sanya maman tabar mata ita,rainon affan da sauran 'yan aikace aikace ita take mata,wannan ya sake bata nutsuwa a zaman gidanta,tana dame debe mata kewa kuma ta rage mata ayyuka,saita samu cikakken lokacin tsara duk wani abu da zai faranta ran abbas ya kuma sake zaunar da ita a ransa.
Gidanta yana dab da wajen aikin abbas,wanda ko a qafa zai iya takawa ya qaraso gidan nasa,abu na farko kenan daya soma hana hafsat sukuni,ta dinga tunani kala kala,a duk ranar kwananta bata da kwanciyar hankali harma ranar da ba tata ba,tana ganin a yanzu widad din ta fita samun kusanci dashi,kamar ko yaushe suna tare,kwata kwata a lokacin tunaninta bai bata hakan zai iya kasancewa ba,kawai a sannan tanaso ta nunawa widad ta koreta daga mazauninta ne don ta isa,ita kuma ta maye gurbinta,daga iya haka tunaninta ya tsaya.
F I T S A R I N F A K' O
Tunda ta dawo kusa ya daina cin abincin rana a ko ina sai gida,idan ayyuka sun masa yawa sai ya aiko yaransa su daukar masa,idan kuma ya samu chance da kansa yake dawowa yaci abincinsa cikin nutsuwa da kwanciyar hankali ya koma,wani lokaci ma idan akayi sa'a aminatu ta fita da affan ko suna dakinsa sai ya more lokacinsa sosai sannan yake komawa din,a wannan lokacin ya samu wata irin nutsuwa da kwanciyar hankali daya jima bai samu irinta ba,don har wata qiba da murjewa ya sakeyi,gaba daya hafsat da matsalolinta ya sanyasu a mala,dai dai da abincinta ba damuwarsa bane yanzu,ita kanta ta lura da wannan sauyin daya sake daga mata hankali matuqa,har take ganin widad din ta fara aiki a kanta ne da 'yan tsubbu don ta janye hankalinsa daga kanta,ko sau daya a tsukakkiyar qwaqwalwarta bata taba shawartarta ta duba inda ta gaza ta gyara ba.
********** Tunda ya sallameta a safiyar dazu data fita a girki ranta yake suya,komai nata yanzun ya koma yana shakulaton bangaro dashi,ta kalli inda ta ajjiye masa gantalallen breakfast din da ko ta kansa baibi ba ranta yana sake baci,zuwa azahar ta gaza daurewa,bayan mimi ta shirya kanta ita da nawwara ta zubasu a mota ta ajjiyesu a islamiyya duk da ba ita ke kaisu ba,sai kawai ta dauke kan motar tata tayi hanyar police college.