A RUBUCE TAKE (K'addarata) book 2 page 21

A RUBUCE TAKE (K'addarata) book 2 page 21

 

A RUBUCE TAKE (K'addarata) book 2 page 21

*H U G U M A*

*Arewabooks:Huguma*

A RUBUCE TAKE

       (K'addarata)

            Part 02


Page 21Riqe yake da hannunta gam cikin nasa,yana sauraren shagwabarta da 'yar qaramar muryarta mai taushi,murmushi ne yake fita kadan kadan daga saman fuskarsa,har bayason ta dakata daga magiyar da take masa, sosai muryarta take masa dadi,ta narke masa sosai,ita kano takeson zuwa,shi kuma baya jin zai iya barinta a yadda yakejinta cikin rayuwa da zuciyarsa a yanzun tayi nesa dashi.


            Wata farar long sleeve blouse ce a jikinta fara sol,sai mini side button skirt a jikinta mai tsaga daya baya shima fari sol,ta kame gashinta mai tsaho da sulbi a tsakiyar kanta,jikinta ba abinda yakeyi sai fidda tattausan qamshin turarenta daya hade da kabbasar da takewa kowanne kaya nata da mabanbantan qamshin turare.


        Tuntuni ta gama haddace yadda yake mutuwar son yaga tayi shigar qananun kaya,wannan ya sanya ta mayar dashi al'adarta,don zata iya cewa ba zata iya tuna sau nawa ta saka atamfa kace ko material a jikinta ba muddin tana cikin gidan,walau ran girkinta ko ba ranar girkinta ba,har ya riga da ya zame mata jiki,hakanan fararen kaya na mugun yi mata kyau,da yake kuma ya hadu da mace mai tsafta idan ta saka saika dauka kowanne sabo ne bata taba sakashi ba.


          Gidan ba kowa shi yasa ta baje masa tabararta sosai,har yaji kamar bazai iya komawa gurin aiki ba,dama cin abincin rana ya dawo dashi,affan yana wajen aminatu,tun daxun gab fa zata gama abincin rana ta goyashi suka shiga gidansu.


         Waiwayowa yayi,har yanxu murmushi na bisa fuskarsa yana dubanta,sai ya zare hannunsa daga nata


"Baby......wallahi kinason yau nayi satar kwana kenan,da irin wannan shagwabar taki zan kasa kaiwa yayarki kwananta fa" kai ta girgiza tana dan bubbuga qafa


"Nidai ba ruwa na,abinda nace kawai inason naje kano,sanya ranar Aafiya za'a yi fa"


"Ba yanzu ba baby.....idan bikin ya taso dai zakije" jikinsa ta shige tana fadin


"Don Allah.....don Allah" dai dai sanda aka angizo qaramar qofar dake jikin gate din gidan aka shigo.


            Idanuwanta a kansu,zuciyarta na wani irin bugawa,wannan shine karo na hudu da zuciyarta ke raya mata yana gidan yarinyar,kuma idan tazo din take cimmasa,bata taba kuskuren zuwa bata sameshi ba.


          Waiwayawa sukayi gaba dayansu suna kallonta,widad ta janye idanunta tana jan tsaki can qasan ranta,ko daya bata sani ba,bata kuma gane dalilin wannan safarar da take musu a gida ba,bayan ita tunda tabar gidanta bata sake koda marmarin taka qafarta ba,idan ta shiga unguwar ma,mutanen da sukayi zaman arziqi tajewa jaje ko taya murna,daga nan kuma bata qarawa ko ina take dawowa gida abinta,duk da tanason ganin mimi amma haka take haqura.


          Dage tayi sosai,ta mannawa abbas din kiss a goshi a tausashe sannan tace


"Allah ya kiyaye hanya,im gonna miss you baby" ta danyi rolling idanunta hadi da daga masa hannu,taja baya a hankali tana takawa zuwa cikin gidan,da gayya take juya mazaunanta da kyau,duk kuwa da cewa koda batayi hakan ba salon tafiyarta ne dake tafiya da abbas din ainun.


           Tare sukabi bayan nata da kallo shida hafsat din,nashi kallon na zallar qauna tare da jin wani iri,kwana biyu kawai da zaiyi ba tare da ita ba sai yakejinsu kamar shekara dubu,duk da zai leqota a qalla sau biyu a wuni kafin ya tashi a office,yayin da kallon hafsat ke cike da wani mugun baqin kishi,wanda a wannan lokacin inda zata samu dama tabbas saita nakasta wannan surar da akemata barazana da ita.


         Kasa jure ci gaba da kallonta tayi,sai take ganin kamar taqi sauri ta shige falonta ne da biyu,ta maido dubanta ga abbas din,saidai gaba daya hankalinsa baya kanta,kamar ma ya manta a inda yake tsaye,wani abu yazo ya tsaye mata a wuya,har taji ba zata iya magana ba,sai kawai ta juya da mugun sauri ta koma cikin motarta,wadda ko kasheta batayi ba saboda tsabar sauri ta shiga ta rufe murfin da mugun qarfi,taci ribas ta fice daga layin.


          Qarar buga murfin motar ne ya dauki hankalinsa,ya juya yana kallon qurar data tayar,sai a sannan ma komai ya dawo masa,yaushe sukayi da ita zata fita?,ya gyada kai ransa na mugun sosuwa,ya taka yana fita a gidan ya nufi tasa motar don ya koma office.


         Gudu kawai take shararawa a hanya,sauran masu ababen hawa dake bin hanyar sunata binta da kallo,wasu na kaucewa wasu suna Allah wadai da ita,kuka takeson yi amma idanunta sun soye,a bisa qa'ida ai ya shiga lokacin girkinta,karo na hudu kenan tana ganin irin haka,dama wannan shine dalilin da ya sanya ya canza mata gida ya kaita kusa da office dinsa?,zaizo zasu hadu,yau din saidai kowacce wacce.


              Batasan abbas din ya fita bacin ran fitar da tayi ba tare da izninsa ba,ba kowanne sakarci yake dauka ba ko kuma ya qyale,tunda suke da widad koda wasa bai taba kamata da laifin yin leqe bama bare har takai ga fita,fitarma irin tata mara tushe bare ma'ana,tunda me tazo yi gidan widad din a wannan lokacin?,abinda ta saba?,bin qwaqwafi da bin diddigin yarinyar da ta haifeta?,bai taba jin widad tayi zancanta ko ta damu da lamarinta ba,amma ita ko yaushe damuwarta widad,ko yaushe qorafinta yana kan widad din,sai yaushe ne zatayi hankali?,yaushe zata gyara halinta?.


          Lokacin da ya koma gida baibi ta kanta ba,hidimarsa ya shiga yi da yaransa,hatta da abincinta ma bai nema ba,ya shiga kitchen ya dafa musu wani bayan ya tambayi yaransa me sukeson ci.


          Banza ya bawa ajiyarta suka baje a qasan carfet da yaran suka hau cin abincinsu,kamar ma baisan da wanzuwarta cikin falon ba.


          Ta sake cika tayi fam kamar zuciyarta zata fado saboda yadda take mata ciwo,cikin sa'a za'a ce ko rashin sa'a mimi tace


"Mummy ke bakyacin abincin?"


"Zan tsinka miki mari,aiba a yunwace kika ganni ba ko?" Sauke idanunsa yayi a kanta a nutse,sannan ya motsa labbansa


"Tashi kibar nan gurin" a dan fusace ta kalleshi,amma a kallo dayan ta karanci bacin ran dake kwance cikin qwayar idanunsa,saita miqe da wani irin qarfi tana kade jikinta,amma kuma ya dakatar da ita ta hanyar cewa


"Ki miqomin key din motarki yanzun nan" ya bata umarni nakai tsaye ba tare da ya ko dubeta ba


           " a mamakance ta juyo tana kallonsa,amma ko kallon inda take baiyi ba,ta dauke kai ta jinjina sannan ta taka zuwa ciki,ta dauko key din ta dawo ta ajjiye masa ta wuce daki wasu hawaye masu zafi suna qwace mata.


        Koma wanne karin magana bahaushe yayi akan kishiya,koma meye aka fada akan kishiya tabbas ya dace da ita,wasu baqaqen dabi'u da halaye da batasan dame zata kwatantasu ba abbas din ya koyo,saidai koma meye ita ba zata taba bari widad din taga faduwarta ba.


*_A N K U M A   M A C E   T A H A I F I   M A C E inji bahaushe_*           Watan affan bakwai dai dai wanda yayi dai dai da samun qarin matsayin abbas din ya sake samun wani promotion din daga DSP(deputy Superintendent of Police) zuwa SP(superintendent of police) din gaba daya,wani irin ci gaba da budi yaketa samu tako ina wanda bai zaci samunsa haka a kurkusa ba.


        Randa aka saki signal sunansa ya fito widad din na falo a kwance,sanye take da wata armless chiffon gown,yatsunta na hannu da na qafa sunsha jan lalle jajir gwanin sha'awa,basu jima da dawowa daga wankin kai ba ita da aminatu,ta dauki affan suka fice sai ita kadai a gidan,gashinta mai tsaho santsi da baqi yayi kyau sai sheqi yakeyi,wannan gyara ne daya zame mata jiki jiddin zaka sameta cikinsa.


          Yau din ba ranar girkinta bane,sai a gobe zata karba girki,amma ta gama shirya tarbar abbas din tun a yau din,ta gama komai,zuwa yanzun yadda abbas din keyi a kanta ya daina damunta,ta riga ta saba,ya zamar mata jiki,hasalima tausayi yake bata,don ta tabbatar inda yana samun kulawa yadda ya kamata daga wajen hafsat itama zata samu sauqin wani abun,to amma ita daya ce ke iya kashe masa qishirwar komai,ita kadai ke tsaye a kansa take samar masa nutsuwa da kwanciyar hankali.


          Tunda ya duba sunansa yaga ya fito yaji har cikin jiki da zuciyarsa ita yafi dacewa ta fara sani,a nutse yake tuqa motarsa bakinsa dauke da hamdala da godiya ga Allah fili da badini,don yayi masa dukkan wata baiwar da rufin asiri,kuma dama a rayuwa baka taba samun komai cif cif dari bisa dari.


          A kofar gidan ya kashe motarsa sannan ya fito,yasa key ya buda gidan yana sanya kai,yau gaba daya aiki ya sashi a gaba,ko zuwa ya dubasun da yakeyi baiyi ba sai yanzun da ya samu break,amma da yake gwanar alkunya ce tare da yi masa uzuri,da sukayi waya ita ta fara bashi uzuri ma kafin ya bata.


          Lumshe idanunsa yayi sanda ya tura qofar falon,sassanyan qamshin nan na kullum da kullum dai shine a falon cakude da sanyin ac da aka daidaitashi dai dai da buqatar dan adam.


           A duniya gidanta ne waje na farko da yake fara saukar masa da nutsuwa a rayuwarsa,bazaiqi ya dawwama a cikin gidanta ba kaf rayuwarsa,yasan bazai rasa komai ba,ba kuma zaiyi kuka da Komai ba.


         Tana daga kwancen ta daga fararen idanunta masu girma ta.kalleshi,ta sakar masa murmushi tana miqewa daga kwancen ta zauna tana dubansa


"Welcome home sir" tsaiwa yayi ya moqe kafadarsa kamar qaramin yaro yana kallonta


"Ban yarda da wannan qwangen da akeson yimin ba" saita miqe da sassarfa ta isa gareshi,ya buda mata hannuwansa kamar yadda suka saba ta fada jikinsa,ya maida hannun ya lullubeta gam cikin qirjinsa yana sauke ajiyar zuciya,kamar yaron da yayi kuka ya qoshi 


"Alhamdulillah ala kullin ni'am.......na samu promotion,now am SP abbas" wani irin qanqameshi ta qara yi cikin wata siririyar qara


"Seriouse abbin affan?"


"Da gaske nake sarauniyata" ya fada a tausashe yana shafa sumarta da taja hankalinsa sosai,qamshin jikinta kuma yana neman birkitashi,yana jin yadda bugun zuciyarta ya qaru saboda murna,zamewa tayi a jikinsa ta kama hannuwansa dukka biyun,ta dinga jera masa addu'ar samun nasara tare da fatan alkhairi mai yawa a rayuwarsa,har sai da qwalla ta cika idanunsa,zuciyarsa ta tabu sosai.


        Mutum daya...... mutum daya ke tsaiwa tayi masa irin wannan,hajiyarsa,zayaso ace yau tana raye taga abinda ubangiji yaketa yima rayuwarsa.


           "Zan samu abinci madam" ya fada yana langabe mata kai,a gabanta kawai yake komawa hakan,inda zaka ganshi a fagen aiki zaka dauka bashi bane.


           Kafada ta noqe tana tura baki gaba


"Girkin mummyn mimi ne fa daddyn mimi" girarsa ya daga


"Yes i know....amma kinsan banason cin abincin waje baya ina da mata har biyu,gida kuma yanzun yamin nisa,infact ma abincinki nakeson ci,in kuma ba za'a bani ba to shikenan" ya fada yana komawa kamar wani abun tausayi,dole ya sanyata ta saki wata shagwababbiyar dariya


"Ni na isa na hanaka abinci?,zauna sosai na zubo maka" tayi maganar tana miqewa,saiya riqo hannunta ta baya,ya kashe mata ido daya


"Zafi nakeji,hadamin ruwa nadan watsa tukunna,yau aiki zai riqeni inajin har wajen isha" kai ta jinjina masa,saita sauya akalarta zuwa bedroom dinsa ta hada masa ruwan kamar yanda ya buqata sannan ta fito ta gaya masa ta wuce kitchen.


          Tana tsaka da shirya masa abincin taji yana kiranta,ta ajjiye warmer din ta fito.


            Tana tura qofar toilet din unexpected kawai taji an fincikota,ko kula dashi ma batayi ba,bata zame ko ina ba sai cikin bathtub,ta jiqe jalaf har saman kanta,tabi jikinta da kallo sannan ta waiwaya tana kallonsa ta gefe,don tuni ya mata masauki cikin jikinsa


"Daddyn mimi......"


"Shshshs....."ya fada yana dora yatsantsa saman labbansa


"Karkice komai,minti biyar kawai zakiyi ki tafi,ba abinda zan miki,kawai ina buqatar ki a jikina kamar haka" bata iya masa musu a wannan bangaren,saboda tasan koda ransa bai masa dadi ba bazai nuna mata ba,uwa uba kuma tasan ba inda zai samu hakan sai wajenta,saita lumshe ido kawai ta jingina da jikinsa.


           Sun kusa mintuna goma a haka sannan ta samu ta zame,haka ta fita da kayanta suna diga,sai data shiga bedroom dinsa sannan ta ciresu,ta dauki bababn towel dinsa ta daura ta nufi qofar fita don ta koma nata bedroom din ta saka wasu kayan.


             Gabanta yayi mummunar faduwa sansa ta bude qofar dakin,don kwata kwata bata tsammaci ganin mutum cikin falonsu ba,ta kafeta da idanu wani bacin rai yana taso mata,ita din wacce irin dabba ce?,don ta wuce a kirata mahaukaciya,haka kawai saika buda gidan mutane ka shigo babu sallama babu komai?,ba neman izini kamar naka gidan,yau kuwa zata nuna mata ta fita hauka da danyan kai,idan akace ta sake zuwa mata gida ba zata qara ba,saita fasa shiga nata dakin,ta tako a hankali ta nufi gurin tv dake aiki.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post