A RUBUCE TAKE (K'addarata) book 2 page 22

A RUBUCE TAKE (K'addarata) book 2 page 22

A RUBUCE TAKE (K'addarata) book 2 page 22

*H U G U M A*

*Arewabooks:Huguma*


*_A RUBUCE TAKE_*

       (K'addarata)

            Part 02


Page 22         Gifatatan da tayi shi ya fahimtar da hafsat dake zaune tana huci fitowar ta,ta bita da kallo daure da towel din daya bayyanar da kyakkyawar surarta da farar fatarta dake ta glowing mai daukan hankali saboda gyara da mai da sabulan wanka masu kyau data samu.


         Qamshinta ya cika mata hanci,ta gaza dauke idanunta daga kanta har zuwa sanda ta isa gaban tv din ta kasheta.


           Kashe tv din tayi sannan ta dawo ta sake wuceta kamar batasan Allah yayi wata halitta ba a wajen,ta sake nufar bedroom din abbas din cikin takun na isa,tana shiga ta maida qofar ta rufe hankalinta kwance.


          Gefan gadon ta koma ta zauna tana qissima abubuwa da yawa cikin ranta,bata taba ganin mace kidahuma irin hafsat din ba,sau tari idan ta zauna tana nazarin rayuwar abbas din tausayinsa kamata yakeyi,yana da matuqar kirki sanyin hali da qoqarin sauke haqqin da ya rataya a wuyansa,yana da mugun haquri,mutum ne mai nisan haquri sosai da kuma idan aka qureshi fushinsa yakanyi tsahon da ba kasafai yake sakkowa da wuri ba,tako ina babu digon match atare dasu,idan ka kalleta ka kalleshi ba zaka taba zaton miji da mata bane,to amma kuma kowanne bawa da kalar tasa qaddarar,TASHI QADDARAR KENAN.


           Yayi mamakin ganinta a zaune daya fito,yana goge jikinsa sa towel yana tsokanarta


"Ko nazo na qarasa aikina ne kawai mu samu ladan me gaba daya?" Ya fada yana kashe mata ido,saita dan jefa masa hararar wasa yana karya wuya


"Naqi wayon.....na yarda ka kashemin jiki,kazo dai ka rakani kitchen saimu debo kayan abincin gaba daya" 


"As you wish maaaa" yadda yayi maganar sai ya bata dariya,gefe guda kuma tausayinsa ya kamata,tasan yanzun nan jahilar matarsa zata jagula lissafi da kuma nutsuwar da ya samu.


          Tana gaba yana biye da ita daure da towel shima,yadda widad din ta tsara ma ranta kuwa haka ya kasance, idanun hafsat din a kansu ya fara sauka,saita miqe tsaye cak kamar wadda aka yiwa barin wuta,yayin da abbas ya dubeta cike da mamaki,take zuciyarsa ta fara tafasa


"Da izinin waye kika fito?" Ya tambayeta da kakkausar muryar,maimakon ta amsa shi saita sauke dubanta ga widad


"Shegiya la'ananniya,dama nasan yana wajenk......."


"Dakatamin......karki qara kuskuren kirana da wannan sunan,idan ba haka ba wallahi zakisha mamaki na......tunda kike haukarki kinga na taba bi ta kanki?,saboda ni ba take nake ba,ta mijina nake,shine a gabana,ya samu farinciki da nutsuwa daga gareni,ta yadda zan tsaya gaban kowa na amsa suna na na mace,bawai muna mata ba,sannan zanji gamsuwa ba mata na rako duniya ba" ta qarashe maganar tana watsa mata wani banzan kallo,kallon da ya kusa fin maganar da widad ta yaba mata zafi,sai ta fige mayafinta ta watsar da jakarta


"Yau saina nuna miki wace mace wace muna mata"


"Karki kuskura ki sake taku ko guda daya idan ba haka ba yau zakiga abinda baki taba gani ba daga gareni" abbas ya fada idanunsa na sauya launi


"Wuce" ya juya yana gayawa widad,saita fara taku a nutse fuskarta fes da murmushin d hafsat taji kamar ta watsa mata garwashin wuta a fuska.


           "Kana gani fa......kana kallon gaskiya kake taketa?,sau nawa ina kamaka a gidan nan abbas?"


"Tunda kwartanci nazo yi saiki tsayarmin da haddi,da izinin wa kika fito nace miki!!!" Ya daka mata tsawar da sai da cikinta ya kada,amma taurin zuciya da tsaurin rai ya sakata ci gaba da tsaiwa tana dubansa


"Dole ne ka fake a bayan na fita baka sani ba,tunda idonka ya rufe ka manta sanda na gaya maka bani da lafiya ko" kallonta yakeyi yana jin kamar ya yanke mata hukuncin da zuciyarsa ke raya masa ko zai samu sassauci daga abinda yakeji a ransa na zallar bacin rai


"Idan kika qara minti daya tsaye a nan wallahi saikin raina wayonki" abinda ya fada mata kenan ya juya ya koma dakinsa.


          Tana kuka wurjanjan ta fita a gidan ta wuce titi ta samu abun hawa,bata jin zata iya jurar ci gaba da zama a garin kaduna,bata da sauran amfani a wajen abbas,ba wata soyayya ko qauna data rage tsakaninsu.


          Tsaf ta shirya abincin ta fito dashi bayan ta sauya kayan jikinta,da taga baya falo saita wuce bedroom dinsa.


         Ko towel din jikinsa bai cire ba,yana zaune a gafen gadon dafe da kansa,ta ajjiye abincin a nutse tausayinsa yana kamata,ta tako a hankali ta zauna gefansa tana dafa kafadarsa hadi da kiran sunansa a tausashe.


        Hannunsa dake dafe da kansa ya sauke, sannan ya dagashi zuwa gareta yana duban fararen idanunta da nashi idanun da suka rine


"Kayi haquri....."


"Na gaji widad.....na gaji,nayi duk iya bakin qoqarina,na kuma yi irin haqurin da nake ganin zan iya,shekara nawa?,shekara nawa amma har yau babu sauyi?,har yau jiya iyau,sai yaushe zata canza?"


"Mai haquri baya taba tabewa daddyn mimi,kaci gana da haquri ko don yaranka" dan shuru yayi sannan ya fara magana a sanyaye


"Ina da dubban hanyoyin da zan hukuntata,amma ta kowanne fanni idan na duba mafi yawan hukuncin da duk zan mata sai ya shafi yarana,inda ace bamu da zuri'a ko daya da ita,wallahi wallahi bazan zauna da ita ba" maganar ta daki widad sosai,don duk wanda yake wajen yadda maganar ta fita daga bakinsa zai fahimci tun daga qasan zuciyarsa ne.


         Sosai tayi qoqarin kwantar masa da hankali da dadadan kalamai da ban haquri,ta tayashi sukaci abincin tare duk da ba yunwa takeji ba,sannan ta taimaka masa ya sake shiryawa cikin wasu uniform din,don idan ya watsa ruwa da rana kamar haka baya maimaita kaya,takan tsokaneshi da cewa


"Ban taba ganin police din da kayan aiki sukewa kyau irinka ba,hakanan ban taba ganin dan sanda mai tsafta kamar ka ba" murmushi yakeyi sannan yadan harareta


"Kina nufin qazamai ne kenan?" Takan maida masa murmushin hadi da salute nashi 


"Afwa nake nema yallabai,ni na isa na fadi haka,kada kasa hukumar 'yan sanda ta kamani"


"Waya isa,wane mutum,kina da Abbas turaki" ire iren hirarrakin da suke sakawa basa gajiya da junansu.


            Relief din da ya samu daga wajenta yasa zuciyarsa ta sauka sosai,ya kuma yi aikinsa cikin sukuni,sanda ya tashi komawa gida sai yaji kamar ya koma gidan widad din,amma hakan bashi yiwuwa,kodon yaransa da kuma hakkin Allah dake kansa.


            Daya koma din kamar wancan lokacin,baibi takan komai nata ba,hidimarsa yayi dasu mimi,gefan abincinta ma bai kalla ba,saida sukayi baccin ua debesu ya wuce dakinsa dasu,yabar musu gadon ya kwanta saman sofa bed.


            Da safe da wurwuri ya shiryasu ya wuce aiki,ya ajjiye mata kudin cefane,bayan ya zabge fiye da rabin abinda ya saba batan,yana sane yayin hakan,don yanason ko yaya ne ya horata taji a jikinta.


            Koda aka tashi daga aikin gidan widad ya wuce,bai koma ganinsu ba yadda ya saba,bai kuma kirata ba,baisan ya akayi ba washegari suna waya da lawal kawai yaji muryar su mimi,tsananin amaki ya cikashi


"Suwa nakeji kamarsu mimi?"


"Eh....eh sune" yadan fada a daburce,saboda yasan yadda akayi tahowar,baiso kuma yaji wani bayani daga bakinsa ba


"Ok,shikenan yayi" abinda ya fadi kenan,don ba hurumin yaron bane suyi kowacce magana dashi ba,suka gama maganar da zasuyi ya kashe wayar.


         Duk yadda yaso yayi controlling fushinsa amma ya gaza,tattarawa tayi ta koma bauchi ba tare da izininsa ba kenan kwatankwacin abinda tayi masa wancan karon da yayi sanadiyyar haramta mata kaduna kwata kwata kenan?,sai ya sake daukar wayar ya fara kiranta.


           Sai da yayi mata miscal biyar bata daga ba,abinda bai taba yiwa wani dan adam ba,ya sauke wayar ya shiga gurin rubuta saqo ya aika mata da saqo kamar haka


_Ki wuce gidanku har sai na nemeki_


Abinda ya aika mata kenan a taqaice,saqon da yayi mugun gigita mata hankali,ta fara kiransa babu qaqqautawa,amma sai shima yayi biris,daga qarshe ma da kiran yayi yawa sai ya kashe wayar gaba daya,widad dake zaune gefansa tana tayashi shigar da wasu bayanai system dinsa batasan abinda yake faruwa ba,sai da taji yana ta jan tsaki sannan ta kalleshi


"What's...."


"Shshsh....."ya fada yana dora yatsantsa saman labbansa yana dan lumshe idonsa,saita dage kafada da gira tana murmushi,bata sake cewa komai ba taci gaba da tayashin,yayi qoqarin shima tattara duk wata damuwar hafsat din ya watsar.


             Kwana uku rak kawu hassan yayi kiransa,yace a jirashi sai ya shigo weekend,weekend din da baije ba sai da bayan wata guda cif!.


            Widad sam batasan me ake ba,taga dai ya dawo gidan gaba daya,ta kuma sake samun wata sabuwar zazzafar soyayya da kulawar data dinga sakata jin kunya muddin cikin mutane suke,takan tambayi kanta wai wacce irin soyayya abbas din yake mata?,tasha tambayarsa amma shima baida amsa illa yace


"Min indillah" daga qarshe itama haka ta barwa ranta daga Allah ne,saidai tabbas ZUCIYA TANA SON ME KYAUTATA MATA,TANA KUMA QIN ME MUNANA MATA KOMAI SOYAYYAR DA ITA ZUCIYAR KE MASA.


           Suna sauka a bauchi ya wuce gidan kawu hassan din,don akwai maganganun da zasu tattauna,yanason wannan karon su halarci bikin qara musu girman da akayi,itama bata zauna ba tace zata je gidan uncle muhsin,da fari ya hana don mugun kishinta yakeyi,yace ta jira ya dawo ya kaita.


           Amma ta kafe da roqo da nacin ya barta,don akwai abinda take shirya masa,batason kuma ya sani sai ranar,daga qarshe da qyar ya yarda idan ya isa gida zai turo umar ya dauki motarsa guda daya ya kaita,ta saki murmushi sanda yake fita


"Uncle dina" ta fada qasa qasa cikin murmushi,wani kaffa kaffa yakeyi da ita,hatta da kayan sawarta yanzun ya hanata saka wasu muddin fita zatayi,yafi ganewa kowanne dinki ma ayi mata doguwar riga sakakkiya.


            Abbas sun tattauna sosai da kawu hassan harma da yaaya sa'id da Bashir akan batun hafsat din,sun tausheshi sosai sun bashi haquri,yace yaji,amma su qyaleshi,ko zai maidata ba yanzun ba,ya fara gajiya yana son shima ya huta,ba wanda ya tilastashi a lokacin,babban wansa yaaya sa'id ne yace


"Shikenan,zan nema kawun nata zamuyi magana,amma dai ka daure kaci gaba da haquri ko don zuriar da Allah ya qaddara a tsakaninku"


"In sha Allah" ya fada cikin girmamawa,sun qyaleshin,suka ajjiye batun suka shiga tattauna sauran maganganun da ya shafesu.


           Kafin yabar gidan ya bawa umar key din motarsa yace ya dauko masa su mimi,saboda yanason su koma kaduna tare,ko don makarantar yaran.


          Abinda yayi matuqar bata mamaki da daga mata hankali kenan,a dauko su mimi fa?,to me yake nufi?,kada fa ya zamana ta fita kenan a gidan gaba daya,kada yarinyar ta zama sanadiyyar fitarta haihata haihata a gidan,ta kadu don irin hakan bata taba faruwa a tsakaninta dashi ba,amma ummanta ta kwantar mata da hankali


"Kada ki damu,ki bada yaran,kinsan muddin ina raye bazan bari irin haka ta faru dake ba" hakanan ta daure ta hada musu tsummokaransu.


            Kafin abbas din ya dawo ita ta rigasu dawowa,ta gyara bangarenta da nashi,ta dora abinci,sanda yaran suka iso ta gyarasu fes ta canza musu kaya,sai gashi sun sake sunata walwala abinsu,musamman mimi data dinga fadin


"Nidai wajenki zan zauna anty", murmushi kawai widad tayi


"Dama ta wajena ce ke" abbas na zaune yana binsu da kallo,sai yakejin gidan nasa ya sake masa dadi, widad nata kai.kawo tana hidima dasu,affan yana hannun su mimi suna masa wasa,wanda inda mahaifiyarsu na nan basu isa su samu wannan damar ba.


          Waya ta shiga daki ta amsa,koda ta fito sai ya tsareta da ido,daga bisani kuma murmushi ya kubce masa


"Madam.......tsakani da Allah ban yarda dake ba,me kike shiryawa silently" dariya takeson yi amma bataso ta bashi qofar da zai gane plan dinta


"Siyar dakai zanyi" tayi maganar tana kashe masa ido daya,wani qawataccen murmushi ya subuce masa yana jin kansa fes cikin wata irin walwala


"Girmanki ne,don kin siyar da DSP,har IG ma zaki iya siyarwa,duka girmanki ne" sai dariya ta qwace musu su duka biyun.


           Washegari bayan ya fita ta kuma tambayarsa zasu fita ita da yaran gaba daya,ya langabe kai a inda yake zaune


"Babyn uncle.....ki jirani zuwa dare na kaiki please,wallahi banaso...... inajin kishin ki fita a kalleki,banason kihau motar haya"


"Allah uncle ba zamu jima ba,kuma inda zanje din basa fitowa ai da daddare,don Allah ka turon umar ko ko muneer,saika bamu aron daya motar taka ya miqamu ya dawo damu" 


"Shikenan nan,amma awa biyu kacal na baku"


"In sha Allah bazan wuce haka ba" ta amsa masa a ladabce.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post