A RUBUCE TAKE (K'addarata) book 2 Page 7
Health College

A RUBUCE TAKE (K'addarata) book 2 Page 7

A RUBUCE TAKE (K'addarata) book 2 Page 7

H U G U M A

Arewabooks:Huguma

A RUBUCE TAKE

       (K'addarata)

           Part 02

Page 07

Wuni hafsat din tayi tana zirga zirga cikin gidan,bata falo bata kitchen,ita kuwa widad hakan bai hanata zagewa ta shiryama uncle abbas dinta abinci lafiyayye ba, hafsat din na zaune daga falo sanda qamshin ya fara mata sallama,ta baza qofofin hancinta, Zuciyarta na gaya mata ko daga babban sashen hajiya na gidan qamshin ke fitowa?,to amma data nutsu da kyau saita gane daga kitchen din gidansu ne,mamaki ya daskarar da ita a wajen,ta gaza daurewa ta nufi kitchen din kamar zata dauko wani abu.

          Qamshin da tayi arba dashi yafi na falon,ta gefan ido take kallon yadda yarinyar keta aikin girkinta komai da komai tsaf,kai bakace girki takeyi ba,zarcewa tayi da dauko ruwa zuciyarta na wani irin tsalle daga qirjinta saboda zallar kishi,ta dauka ruwan ta juyo ta fito,saita ajeshi kawai gefanta ranta yana baci.

        Tako ina yarinyar ta bata mata tsari,komai na yarinyar canzawa yakeyi ko tace tama canza totally,komai nata a yanzun na cikakkun matan aure ne,yaushe ta iya girki mai bada matsiyacin qamshi haka?,cikin wadanne watannin ne da bata banbancesu ba?.

             Tana tsaka da wannan nunqufurcin da tunanin harta gama komai ta kuma fito daga kitchen din zuwa dakinta,a nan yaran suka ganta,suka ruga da saurinsu suka bita dakinta,a sannan bata da kuzarin hanawa,don tayi nisa cikin tunani da lalubowa kanta mafitaa

         Sosai yaran suka sake suna wasansu a dakin nata,ta fidda chocolates ta basu ta shiga wanka,ta fito tana baza qamshin shower gel dinta mai taushin qamshi,ta tsaya gaban madubi ta soma gyara kanta.


           Tunda wuri yake qoqarin yaga ya kammala duka aikinsa ya dawo gida,duk wani motsi da zaiyi tana maqale cikin ransa,haka yayita kokawa da ayyuka don ya samu dawowa gida da wuri ya kasance da ita,amma hakan bai yiwu ba,sai yamma liqis sannan ya samu ya ture wasu ayyukan ya fito.


            Sai daya tsaya ya siya dukka nau'in fruits din da yasan tana so,ha hadama yaran da kayan kwadayi sannan ya dauki hanyar gida,cikin ransa yana jin wani zallar nishadi da farinciki,wata walwala da baisan tushenta ba ita ke wanzuwa saman fuskarsa,lokaci lokaci yakan saki murmushi idan ta fado masa a rai,a haka har ya cimma gida,yadan dannan hon mai gadi ya dage masa qofar.


         Sautin hon din motarsa daban yake a kunnuwan widad,ta lumshe ido dai dai sanda ta gama shirya kanta tana duban kanta da kanta cikin madubi


"Ga daddy nan fa ya dawo" tace da yaran tana dan dubansu,wani shauqi da qaguwar riskarsa tana ratsata,sai takejin kamar tayi shekara ne bata rab'i uncle din nata ba


"Yau sai na riga kowa zuwa taro daddy" mimi ta fada tana tattare kayanta,murmushi widad ta saki


"Zamuga waye zai riga wani" sai ta dauki turare ta sake feshe jikinta,sannan ta nufi qofa da sauri tana yiwa mimi gwalo,wannan ya sanyata zubda kayan ta miqe tana qyalqyala dariya


"Allah anty saina rigaki" ganin yarinyar ta biyota sai ta dan saka sassarfa tana mata dariya tayo gaba mimi din ta rufo mata baya.


           Dai dai sannan hafsat da taji muryarsa daga waje suna gaisawa da ma'aikatan gidan ta fito falon,daga kujerar dake daura da bakin qofa ta zauna,ta yadda idan ga shigo idanuwanta zasu iya gane mata komai,uwa uba ma tasan babu wanda ya isa ya keta idanunta ya tsallaketa ya isa gareshi,ta baza dukka idanunta tana qarewa gyaran da aka yiwa falon zuciyarta kamar ta fito,lallai ba shakka sai taci uban yarinyar,sai tayi maganin dukka wannan kinibibin nata,taja qwafa tana karkada qafafunta.


         Yana doso part din ransa yana sake yin fari,tun bai isa falon ba ya tabbatar ya koma saitinsa yadda yakeso,qamshi mai sanyi ke hudowa ta tsakanin labule da qofar yana fitowa har harabar gidan,ya buda qofar falon a nutse bakinsa dauke da sallama,hafsat din ta miqe tana dan sakin murmushi tare da amsa masa sallamar.


           Taku biyu tayi zuwa gaba da niyyar amsar jakar hannunsa muryar widad hade data mimi ta karade falon.


             Hankalinsa da nata gaba daya ya koma kansu,sanda suke rige rigen tarbarsa kowa yanason ya fara isa a tsakaninsu.


          Sosai ta fusgi hankalinsa ta kuma tafi da dukkan nutsuwarsa,yadda take tahowa da sassarfa yaji ya masa kadan,ya fara takawa shima ha ruskesu,cikin sa'a ta riga mimi isa,ya bude hannunsa ta fada jikinsa tana fadi cikin dariya


"Oyoyo daddyn mimi" sosai yake kallon fuskarta da narkakkun idanunsa dake kanta,yasa hannu ya daga fuskar tata yana murmushi wanda yafi kama da dariyar farinciki


"Kinwa 'yarki wayo ko?"


"Dama na gaya mata,sai na rigata" saita jefawa mimi gwalo,yarinyar ta tabe baki kamar zata saki kuka,sai widad din ta miqa mata hannu tana sakin dariya


"Taho.....taho mimin dadd......" Sautin kuka shi ya maida hankalinsu duka ga hafsat,duk sai sukayi sak suna dubanta,har ga Allah abbas din ya manta da wanzuwarta a wajen gaba daya,widad tasan tana gurin amma batajin zata iya fasa abinda ta saba yiwa uncle din nata,uwa uba kuma dazu da taji yana cika baki da tinqaho akan uncle din,abun ya bata haushi amma saita qyale kawai,tana ji a ranta zuwa yanzu ko meye mommy hafsat din tayi mata ta daina qyaleta.


           Kuka sosai takeyi,kafin abbas ya samu damar cewa wani abu ta juya da sauri ta nufi dakinta,batason yarinyar taga hawaye har haka a fuskarta saboda gudun raini.


          Bayan wucewarta sai suka koma kallon kallon a tsakanin,a nutse ya zare widad daga jikinsa yana cewa


"Ina zuwa" yabi bayan hafsat din,tabe baki widad tayi ta dauki.jakarsa daya aje a wajen suka wuce dakinta ita da mimi,yarinyar nata murnar tare daddy ya tarbesu,saidai sama sama widad din ke amsawa,don dukka hankalinta nakan abbas din.


        A nutse ya tura qofar dakin ya shiga,tana daga zaune bakin gadonta tana sharar qwalla,ya taka ya isa gabanta ya tsaya kawai kallonta hannayensa goye a qirjinsa


"Me akayi miki?" Ya jefa mata tambayar data sakata dago kai idanu jiqe da qwalla ta dubeshi,wani baqinciki ya tokare mata wuya,wato baisan me yayi ba?


"Bakasan me kayimin ba abban mimi?,ko yaushe baka da burin da ya wuce ka wulaqantani ka tozartani a gaban yarinyar nan,nice na fara welcoming dinka,amma tana fitowa ka kasa tarata ka koma kanta saboda tsabar cin fuska" iska ya furzar daga bakinsa yana gyara tsaiwarsa


"Yanzu wannan shine abinda yakai ayi masa kuka?" Shuru tayi bata amsa ba tana ci gaba da goge qwalla,baisan yadda takeji ba a yanzun,da bai tsaya kanta yana magana fada fada ba


"Dole sai kinyi haquri kin dauke kai,akwai banbancin shekaru a tsakaninku, infact ma ta riga ta saba ita kadai take rayuwa a gidan nan,wasu abubuwan sai a hankali zata dainasu" saiya fara takawa zai fita a dakin,ta bishi da kallon takaici,bataso ya shigo dakin ya fita haka da sauri,tana so ko yaya ne ta bata masa lokaci yadda zata dasa zargi a zuciyar yarinyar,tunda ta lura zuwa yanzu zaman kishi sosai takeso suyi,ta wuce wancan lokacin da zata dinga juya ta da raina mata wayo yadda taso.


        Sunansa ta sake kira,cike da qosawa ya tsaya ya waiwayo,saita taso ta iso gabansa ta fada jikinsa ta fashe da kuka sosai,ba yadda ya iya haka yasa hannu ya tallafeta,rigimar hafsat din tayi yawa,matsaloli kala kala marasa tushe balle makama,qanqanin abu saita hurashi ya zama babba,har yau ta kasa gane girmanta balle ta riqeshi.


"Bansan me yasa kakemin haka ba,bakasan yadda nakeji a zuciyata ba" ta fada cikin kuka,tilas ya bata lokaci yana lallashinta tare da nusashe da ita cikin hikima,saidai abinda bai sani ba,duk abinda yake fada tana bi ta bayan kunnenta ne,burinta kawai ya jima a dakin.


          Ta samu yadda takeso kuwa,don ya jima yana jan hankalinta kafin ya baro dakin bayan ya umarceta data sake gyara dakin, saboda tuni ya fara fita daga kamanninsa a kwanki uku kacal,baya jin kuma zai jura,ba kamar bauchi bane,a yanzun bashi da wani dakin daban da zaice zai kebance a cikinsa.


          Bacci ya dauke mimi sai widad dake zaune gefan gadon,ta cika tayi fam,bata taba jin bacin rai irin wannan ba,shi yasa sam ko ganin mummy hafsat din batasonyi,tana jin wani zafi a zuciyarta duk sanda ta fahimci ko taga sun kebe,koda yayi sallama saita zumbura baki ta miqe ta nufi toilet kawai tana amsa masa ba tare daya tsaya a nan ba,qaramin murmushi ya saki bayan ya kalli agogo,sai a sannan ya fuskanci laifinsa,ya qarasa bakin gadon ya duqa ya dauki mimi ya maidata wajen hafsat sannan ya dawo dakin,ya jingina da mirror yana jiran fitowarta.


         Kamar bata ganshi ba sanda ta fito daga bandakin,ya bita da kallo yana sake tantance kyan da tayi,wani abu na motsa masa a ransa game da ita,a strong desire,idanunsa na zagawa bisa jikinta,bomshort din jikinta yayi masifar fidda shape na qugunta,kaman ana fusgarsa haka yaji,ya isa gareta cikin sassarfa ya jawota jikinsa.


         Abun yazo mata a bazata,wanann ya haifar da motsi a cikinta,abinda yayi matuqar firgitata tunda bata bata taba ji ba,a zabure ta saki ihu da ya sanya abbas riqeta da kyau yana lalubar abinda ya faru,hafsat kuma dake maqale a bakin qofa tana jiran jin taqaddamar da zata faru a tsakaninsu sanadin dadewarsa a dakinta ta sake gyara tsaiwarta da kyau,dadi yana cikata da jin ihun widad din,may be ta masa wani rashin kunyar ne yaji bazai iya jurewa 'yar cikinsa tayi masa haka ba ya kaiwa bakinta bugu.


      "calm down.....menene?" Kasa amsa masa tayi sai hawaye da ya fara bin idanunta,ta kama hannunsa ta dora saman cikinta,dai dai sanda motsin ya ratsa tafin hannunsa ya aika saqo kwanyarsa,sai kuma ya tsaya cak.


        Sosai ya shiga mamaki da tunani,ya dubeta cikin mamaki


"Yaushe ya fara irin wannan motsin?"


"Bai taba yi ba sai yau" ta fada tana sharbe hawaye,qaramin murmushi ya saki,saita saki baki tana kallonsa


"Karki damu,zan kira dr yanzu nayi mata bayani,zauna a nan ki nutsu,don't bother".


          A nutse ya zaunar da ita sannan ya lalubi wayarsa ya fara neman number din dr maryam,daya daga cikin personal doctor dinsa.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post