Rumubun Qaya page 62

Rumubun Qaya page 62

Rumubun Qaya page 62

RQ

   62

***Da safen wuri Ya nabeela suka zo gidan ita da Khadija, lokacin raihana ko tashi ma batayi ba sai aryan din tare da su hydar a falo suna zaune suna magana. Ammyn ma bata tashi ba har lokacin baccin take yi. Zuwan su ne yasa ta tashi bayan yazo ya dan taba ta kadan ta tashi da sauri, murmushi ya sakar mata yana nuna mata agogon hannun sa dake nuna lokaci, sosai tayi mamaki dan bata dauka zata iya bacci har haka ba. A kunyace ta sakko ta wuce toilet din dakin shi kuma ya sakko kasa suka bishi da kallo Ya nabeela ta harare shi a wasance tace


“Wai ina kanwata ne?”


“Bacci take yi sai yanzu ta tashi.” 


Yace yana zama a gefen Hydar bayan ya zare hannayen sa dake zube a cikin aljihun dogon wandon shaddar sa da farar shirt da ta dan kamashi.


“Ga breakfast chan toh na kawo muku, sai ku tashi nasan baku ci komai ba.”


“Kamar kuwa Anty Kinsan yunwa muke ji.”


Hydar yace yana dariya


“Ya kukayi da Sadeeq din?” Aryan ya tambaya


“Sun dauko hanya ai ma ai, babu available flight yau dole sai dai subi mota, Dadah ma nake tausayawa zaman motar dan kwana biyu tana complain din kafa sosai.”


“Allah sarki, Allah ya Kawo su lafiya. Sai suke ji labari me dadi.”


“Wallahi Anty, Alhamdulillah!”


“Ina mutanen gidan ne?” 


Ammy tace tana budo kofar dakin da take bayan ta farka kusan mintuna goma kenan. Tashi sukayi dukkan su, suka karasa wajenta Lamido ya riko ta ganin kamar har yanzu da jiri a tare da ita, dakin ya maida ita suka shiga dukka shi kuma aryan ya dauki jakar Kayan raihana da Ya nabeela ta kawo mata ya haye saman. Wanka tayi tana tsaye tana tunanin kayan da zata saka bayan ta maida na jikinsa duk sai taji ta takura, ba zata iya zama da kayan ba dan ita a kaidar ta bata maimaita Kayan da ta saka sai an wanke. Turo kofar yayj ya dire jakar a tsakiyar dakin sannan yace


“Ammy ta tashi, ki shirya ki sakko su Khadija suna jiran ki.”


Da kai ta amsa ya juya ya jawo mata kofar ita kuma ta dauki kayan ta saka a gaggauce kin ammyn ta farka. Kasan ta sakko ta tarar da Ya nabeela da Khadija a falon bayan sun fito daga dakin duk sai taji kunya ta kamata ganin yadda suke kallon ta musamman Ya nabeela da take mata kallon tsaf kamar me shirin gano wani abu. A daddafe ta karaso tsakiyar falon tayi saurin dukawa kasa ta gaida Ya nabeelan da sauri tace


“Tashi tashi daga kasa, ba’a zaman kasa musamman tiles din nan me shegen sanyi, yanzu sai sanyi ya shiga mutum.”


Tashi tayi ta zauna a gefen Khadija suka gaisa sannan ta nufi dakin da ammyn take. Tana zaune Hydar na bata tea ta shiga, ta kalle ta kadan sai kuma ta cigaba da shan tea din har Raihanan ta karaso ciki ta zauna a gefen Ammyn suka sakata a tsakiya ita da hydar. Cup din ya mika mata sannan ya mike


“Karasa bata sai tayi wanka time yana tafiya.”


“Ok.” Tace ta shiga bata tea din tana sha a hankali tana ta kallon raihanan amma bata ce komai ba. Sai da ta gama bata tsaf sannan ta shiga toilet din ta hada mata ruwan wanka tazo ta taimaka mata ta kaita har toilet din ta nuna mata yadda zatayi sannan ta fito ta hau gyara dakin , ta gama ta fito mata da kayan da zata saka hade da Hijab sannan ta zauna ta jira ta fito ta kuma taimaka mata ta shirya sannan tace ta zauna tana zuwa. Wajen su Ya nabeela ta dawo Ya nabeela tace zata raka Khadija asibiti daga nan zata dauko su amna daga school amma zasu dawo da yamma. Sallama sukayi mata suka tafi dama ba kowa yan mazan sun shiga ciki shiryawa za’a kaita rijiyar lemo gidan malamin nan, shi kuma Aryan zai je Office yaga abinda ya kamata yayi kafin su dawo. A tare suka shirya suka fito harabar gidan aryan ya dauki karamar motar sa su kuma Malam Yahya ya dauke su suka wuce Rijiyar lemon shi kuma ya wuce Office.


****Kayan jikinsa yake so ya sauya zuwa na gida sannan yaje yaga abinda yake faruwa. Dukkan ranakun nan a cikin busy yake akn wani babban case da yake da yakinin zai kara daga darajar sa dan kuwa da kasan zuciyar sa yana jin zai iya barin aikin nasa nan kusa wanda yasan hakan bata yiwuwa a yanayin aikin nasu sai ka taka wani mataki. Familyn sa na bukatar sa a yanzu fiye da ko da yaushe, daga Baban nasa har Daddy suna bukatar Hutu a Halin yanzu domin dukkannin su girma ya kamasu sannan yasa aryan kadai ba zai iya cigaba da kula da companies din nasu shi daya ba, abubuwan zasuyi masa wahala at least Shima yana bukatar ya huta sosai ya fuskanci rayuwar sa da ta iyalin sa. Apartment dinsa ya koma ya shirya cikin kananan kaya marasa nauyi saboda yadda garin ya hade yake neman zubda ruwa. Direct in da aka ajiye Adam din da yaran sa ya wuce da knsa. Khadija ya kira yana driving ya saka wayar a jikin motar har ya isa suna waya sai da yayi parking sannan sukayi sallama ya fito ya kulle motar. Dakin da yasa aka ajiye su Adam ya wuce yana zuwa aka bude masa kofar ya shiga. Babu wadattacen haske a dakin amma yana iya hango Adam din a kwance a kasa gabansa da wani kwanon abinci. Shi kadai ne a dakin sauran yaran an maida su sashen masu kula da masu manyan laifuka domin an kamasu da laifin kidnapping, shigo da manyan makamai da amfani dasu wajen cutar al’umma. Ya daku sosai yayi likis dan dama yace kada su raga masa ko kadan domin yaron ya riga ya kaishi karshe shiyasa yasa suka masa liks ya zama ko mikewa baya iya yi sai jan ciki da yake yake karasawa dan gaban pit din dake hade da dakin idan zai yi bukata. Zarnin d dakin yake yi ya hana Kamal daurewa ya yayi saurin ficewa zuwa Office dinsa ya zauna ya rufe kofar sannan ya jona system dinsa mail din aryan ya shigo masa. Be duba mailbox dinsa ba tun kwana biyu saboda yayi busy dan haka ne yasa be san Aryan din ya turo masa ba, budewa yayi yana relaxing sosai akan kujerar sa ya shiga duba documents din zuwa video da yake attached da write up din.

  Yanayin yadda ya shigo Office din ya saka kowa shan jinin jikin sa, a daure tamau fuskar sa take be ko tsaya yayi attendance ba yayi wucewar sa Office ya bude ya shiga. Uwar iyayi zee tana zaune ta mike ta dauki files din dake ajiye a desk dinta ta nufi Office din duk kuwa da kallon kar ki je din da chomzy ta aikata mata amma tayi tafiyar ta bayan ta gyara jikinta. Knocking ta yi tana kara daidai ta fuskar ta, ya dago yana kallon kofar yasan babu me zuwa duk kuwa da yanayin da ya shigo sai zainab, yarinyar ta sakè da yawa zai yi maganin ta kuwa dan ya dawo aikin sosai kafin tafiyar tasu. Sakè kwankwasawa tayi a zafafe yace


“Waye!!!”


“Zainab ce Sir.”


“Na neme ki?”


“Mmm dama sir files din nan ne da mukayi magana jiya.”


“Na saka ki kawo mjn ne?” 


“No sir na dauka zaka…”


“Kije sai na neme ki da kaina.”


Kamar an buge mata guiwa haka taji, ta waiga reception din taga duk ita suke kallo, gashi tasan ko basu ji abinda suka ce ba zasu gane korar da yayi, kamar kasa ta tsage ta shige ciki haka taji, ta rasa ma ya zatayi, tunowa da tayi da toilet a chan gaba sai kawai ta wuce, taji sanda chomzy da Ali da Fadila suka kwashe da dariya, ta kuma san ita suke wa dariyar.kuka ta fashe dashi a toilet din kukan takaici, ga wata zazzafar soyayya da take masa amma ya kasa ganewa. Sai da tayi kukan ta gama ta wanko fuskar ta fito ta koma Seat din ta, ta bude jakar ta, ta shafa powder da janbaki sannan ta rataya jakar ta fice ba tare da ta ce ma kowa komai ba. 10mint da tafiyar ta ya kira reception din Ali ya daga yace ya karbi file a wajen Zainab ya kawo mishi office.


“Ta fita sir.”


“Ta fita!? Ina taje?”


“Bamu sani ba, ta fita dai cikin fushi.”


“Check her table ka kawo min files din.”


“Ok sir.” Ya ajiye wayar. Bama ta da hankali, idan kuwa haka zatayi zai iya bata suspension taje chan tayi ta haukanta.****Ba kamar karon farko da akayi ma ammyn addua ba, wannan karon abun ya dasu zafi sosai domin ashe duk suna nan babu wanda ya tafi, dama malam din yayi tunanin hakan shiyasa wannan karon yaki raga musu sam, ya dinga ragargazar su da ruwan addua da ayoyin Allah suna gunjin kuka sosai, sai da ya tabbatar yayi musu babbar illah, sannan ya nemi su fice su barta bari na har abadah. 


“Ina zamu? Ka riga ka kone mu.”


“Ku koma chan wajen wadda ta turo ku.”


Ya basu amsa yana Kara daga ruwan zai sakè shekawa, ihu suka saka sai kuma ammyn ta hau attishawa ba kakkautawa tana wata irin mimmikewa tsawon lokaci tana a haka kafin a hankali ta shiga sauke ajiye zuciya. Duk yadda raihana taso boye kukanta, ta kasa kuka take sosai kamar zata shide, kukan tausayin zaluncin da akayi ma ammyn. Kallon ta hydar yayi yace ko zata je waje? Malamin yace a barta itama akwai bukata a duba ta, haka akayi kuwa itama aka yi mata amma ita babu komai. 


“Kina azkar ko?” Ya tambaye ta.


“Inayi malam.”


“Masha Allah, ki cigaba Karki daina, azkar tsari ne sosai amma sai wanda ya gane, ita kanta mahaifiyar ku da bata addua da abin sai yafi haka, domin so akayi a haukata ta, ta shiga duniya karshe ta mutu irin wannan mutuwa ta wulakanta, amma karfin addua da azkar din da take ya sa ta tsallake wasu tuggun, dan haka ku dage da azkar kamar yadda manzon Allah SAW ya koyar damu, in sha Allahu babu wani mutum ko aljan da zai samu damar cutar daku.”


“In sha Allahu Malam, mun gode sosai Allah ya saka da Alkhaiiri.”


“Amin ya Allah, zaku cigaba da kawota yanzu duk Asabar da lahadi muna cigaba da yi har sai mun samu ta samu lafiya gaba daya.”

“In sha Allah, mun gode.”

Sallama sukayi ma malam din suka shigo mota da ammyn da tayi shiru bata ce komai ba sai kanta da ta rike da yake mata wani irin ciwo. Dafa mata kan raihana tayi ta shiga yi mata addua tana tofa mata, sai kuma ta jawo kanta ta dora a saman cinyar ta, ta cigaba da matsa mata kan a hankali.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post