A RUBUCE TAKE (K'addarata) book 2 Page 8


Health College

A RUBUCE TAKE (K'addarata) book 2 Page 8

A RUBUCE TAKE (K'addarata) book 2 Page 8

*H U G U M A*

*Arewabooks:Huguma*

A RUBUCE TAKE

       (K'addarata)

           Part 02

Page 08

Bai jima yana kira ba aka daga,suka gaisa cikin yanayi na sanin juna,sannan yayi mata bayanin dalilin kiran nata idanunsa akan widad da dukka ta sauya lokaci daya tayi wani laushi,idanunta cike da tsoro.

"Indai cikin yakai watannin da zaiyi motsi ai zaiyi dama,hakan kuma alamu ne na cikin lafiyayye ne,watansa nawa?" Kai ya girgiza

"Bansan watanninsa ba"

Dan murmushi ta saka mai sauti

"An gaisheku gaskiya,ina ganin gobe ka kawota asibitin sai ayi mata scanning da komai da komai,har EDD dinta sai mu gani,amma kace mata kada ta damu,babynta ya fara rayuwa sosai cikin qoshin lafiya ne" godiya yayi mata ya ajjiye wayar,ya saka hannayensa a aljihun uniform dinsa daya kasa cirewa tun shigowarsa gidan, idanunsa a kanta yana sakar masa murmushi,duk da cikin tsoro take amma hakan bai hanata basar dashi ba,zata miqe ya kamo hannunta da sauri ya sakata cikin jikinsa yana sansanarta kamar wata 'yar mage,yunqurin tureshi takeyi amma yaqi bata dama


"Ka koma wajen hafsa kawai" ido ya fidda yana dariya


"Yau kuma?,hafsa zalla?"


"Eh sunanta ne ai" ta fada tana dan murguda bakinta,har qasan zuciyarta tana jin kishi yana tsunkulinta,juyo da ita yayi suna fuskantar juna


"Yanzu dai na gane,kishi ne kikeyi,to ayimin afuwa" kafada ta maqale


"Ni ban haqura ba,saidai idan zaka kaini na siyo ice cream" kai ya girgiza bayan ya fidda ido


"So kike ki debarwa babyna sanyi?,bayan dr tace da alama lafiyayye ne?" Fuska ta kwabe ta langabar da wuya,yadda tayin tilas tasa yace


"Shikenan ki shirya,amma yau kawai" cikin farinciki ta amsa masa,tuni har ta manta komai ta fara shiryawa,shi kuma ya fara rage kayan jikinsa don ya shiga ya watsa ruwa,wanda already ta hada masa,yana shiryawa shima yana tsokanarta akan cikin,ita kuwa kunya takeji,saida tayi masa kamar zatayi kuka sannan ya qyaleta.


           Sai da qafafunta suka gaji da tsaiwa bata sake jin komai ba,uwa uba da taga lokaci yana matsowa na fitarsa zuwa masallaci,dole taja jikinta tabar gurin tsakanin kokwanto da rashin tabbas na samuwar matsala a tsakaninsu,saita koma dakinta tabar dan space tana leqensa,har ya fito daga dakin tsaf dashi ya wuce masallaci yana baza qamshi,saita koma bakin gadon ta zube tana riqe da kanta,idan akwai abinda ta tsana a duniya shine taga walwala da zaman lafiya na gudana a tsakaninsu,dole ta sake kashewa tsinanniyar yarinyar kudi,dole ta sake aiki a kanta.


       Sai da yasa yara suka kirata sau uku akan ta fito suci abincin dare sannan ta fito,dai dai lokacin da widad ta fito daga kitchen dauke da babban try data zuba.


         Kofta(ire iren abincinsu ne na 'yan yemen da ake sarrafashi da nama).


         Hafsat din na shirin zama sai taji qafafuwanta zuwa bayanta ya sage,da qyar ta danni zuciyarta ta zauna zuciyarta na wani irin tuquqi da suya,wannan zallar cin fuska ne kawai abbas din yaso yi mata,banda haka ta yaya zai kirata cin abinci jikin yarinyar da wadan nan kayan?,duk kuwa da cewa ta dora wata 'yar kyakkyawar farar riga mai budadden gaba,amma hakan baikai ga boye dukkanin adonta ba.


         Da ido kawai take bin abincin,sunata walwalarsu tsakaninsu,abbas din yana tsokanar mimi widad na tare mata,ta gama serving kowa suka fara ci a nutse.


         Har qasan zuciyarsa yakejin nutsuwa tana saukar masa,ba shakka lafiyayyen abinci mai daddadan dandano ma rahama ne a rayuwa,bashi ba,hatta mimi ta soma santin abincin,abun ya taru.ya yiwa.hafsat yawa,duk yadda qamshin abincin ya karade falon yake tsinkar da yawu amma sai taji ya fice mata aka,ta ture plate din ba tare da tace komai ba ta saba yusra a kafadarta,tana gyara zaninta daya tattare.


           Sai da yakai lomar kufta din bakinsa sannan ya daga kai a nutse ya dubeta


"Ya haka?,ina zuwa?" 


"Bazan zauna a nan ba tarbiyyar yara na ta lalace ba,don ba wajen zama bane,ta saka wasu kaya fingil fingil yarana suna zaune suna kallonta?,ke nawwara......mimi ku tashi muje" ta fada a tsawace,haushin yadda yaran ke wasoson abincin yana sake qureta


          Bata fuska dukkaninsu sukayi,saboda sudai suna jin dadin abincin sosai


"Mommy ki zauna kici,da dadi wallahi" mimi ta fada fuska a narke,abunda ya sake hasala hafsat din ta kwaza mata tsawa,sai abbas din ya daga mata hannu


"Kinga ya isa,jeki abinki ke daya" yadda yayi maganar tayi mugun baqanta mata,nan da nan hawaye suka cika mata idanu,sai ta girgixa kai kawai tayi gaba da sauri hawayen nason subuce mata.


        Ko tunata babu wanda ya sakeyi,abunda yayi masifar baqanta mata rai kenan,don tayi tsammanin zai biyo bayanta kamar dazun,saidai a maimakon haka ma sai tashin motarsa da taji,koda ta fito Parlor din wayam babu kowa,saita zauna anan hawaye na qwace mata,ya wankin hula yake shirin kaita dare?,saita miqe zumbur ta koma dakinta tana lalubar wayarta.


          Cikin kwanakin girkin widad din gaba daya hafsat ta tsangwami kanta,ta rasa nutsuwa bare sukuni,bata daki bata falo,komai widad din zata aiwatar idanuwanta suna kai,hakan ko kadan bai damu widad din ba,don zuwa yanzu ta fahimci meye ma'anar kishiya da abinda zamansu yake nufi ita da hafsat din,ko daya idanunta bai sanya widad din ta fasa duk abinda ta saba yi ba,hasalima yi tayi kamar bata gane ba,kamar dai har yau wautar quruciyan ne ke dibanta,abinda ke masifar hargitsa hafsat din,tana ganin kamar abbas din yana biyewa duk abinda takeso ne,yana kuma fifitata a kanta,wannan ya sanya ya ta sake cin alwashin wargatsa komai da lalata duk wani farinciki na widad din kota tsiya kota tsiya tsiya,sam ba zata gajiya ba.


          Ta gaza shuru ta gaza haquri da yadda yarinyar ke gudanar da komai kamar wata babbar mace,cikin kwanakin komai na gidan tsaf yake a kammale,bata bari komai ya lalace ko a barshi wasarere,tun daga cikin kitchen zuwa parlor dinsu,duk kuwa da yadda hafsat din keta qoqarin ganin ta watsa komai,widad din taja yaran a jiki,ta koya musu yadda zasu bar waje da kyansa bai lalace ba,ta koya musu koda sweet suka sha inda zasu saka ledan,abun ya yiwa hafsat din ciwo,tayita jaraba tana fadan su yar amma qememe sai suqi,kada ma mimi taji labari,maganar anty widad awajenta kamar fadar Allah,hafsat tayi dukan tayi banbamin ta hanata zuwa duk inda take amma kamar turi,abun ya soma taruwa yana mata yawa,ta rasa inda zata taro,yaran ko abbas din?,dole ta zauna ta fidda kudi sosai ta turawa ummanta,tana hasashen samun mafita.



*******Yammaci ne lis,inda suke zaune cikin falon ita da yaran suna kallo,duk da cewa girkin hafsat dinne,amma ko alamun shirin dora girkin dare batayi ba,hasalima tana daki kwance abinta.


           Hakan gaba daya ba damuwar widad bane,don dama da qyar take kaiwa labari da abincin hafsat,wani irin girki mara tsari mara fasali kuma,sam ko a ido bashi da wani qayatarwa bare kakai ga bakinta,Allah ya bata wani irin kurman ciki da har yanxu ya gaza nunawa a jikinta,saidai can cikin jikinta tana jin wasu sauye sauye da ita kanta tasan wani muhimman al'amari ne yake tunkarota,takan zauna tayita lissafin scanning din da dr tayi mata,wai cikinta watanni shida harda kwanaki,ta sha ganin ciki amma itadai ba haka taga ana ciki ba,tasha tsayawa gaban madubi amma bata ganin komai idan ba turoshi gaba tayi sosai ba,duk da yana motsa mata sosai amma yabi jikinta da kyau,ya qarawa breast dinta cika ne sosai,abinda ke matuqar daukar hankalin abbas kenan kamar zai zauce mata.


         Waya ce a hannunta tana duba wasu sabbin recipe da Chief deeja Berver ta basu,tana yi tana murmushi,saboda yadda take fahimtar komai kamar a gabanta akeyi,har ya fada hasashen yaddaa gobe zata tashi kan gidan da nau'in kalolin sabbin girke girke.


        Taji qarar bude qofad sarai,amma bata ko kalli bakin qofar ba,don tasan wacece,sai taci gaba da duba wayarta kawai ba tare da tako motsa ba.


          Idanuwan hafsat din a zube fes akanta,ko wacce rana tana kwana ta tashi da mamakin yadda yarinyar ta gaza tabuwa,duk kuwa da kudin data kashe akanta,sai wata 'yar qaramar nasara data samu,wadda har yau wannan nasarar bata gamsar da ita ba,don bata ga wata alama ta shiga damuwa ko qunci daga wajen yarinyar ba sam,duk kuwa da cewa a yanzun tana iya juya wasu abubuwa na gidan,wanda a kwanaki ko watannin baya bata isa ta juyasu ba.


"Ke mimi..... nawwara,uban me kuke zaune kukeyi a nan?" Ta jefawa yaran tambaya tana zare idanu a kansu,cikin tsoron kada ta hanata zama mimi ke kallonta,yayin da nawwara tayi qirmisisi abinta


"Baba me gadi ne ya kawo kayan abba,yanata buga qofa shine na bude masa"


"Da kika bude masa kuma sai kika samu waje kika zauna?,ina kayan suke?"


"Suna dakin anty widad".


           Wani abune yazo ya tsaya mata a rai,ta kalli widad da har yanzu bata kalleta ba koda sau daya,miskilancin yarinyar yana qona mata rai,tanaso tayi mata cin mutunci wasu lokutan,amma bata kulata ma bare ta bata dama


"Ke.....ki tashi ki debo kayan wankin abbansu ki kawomin nan" cak ta tsaya da danna wayar,saita daga kai a hankali karon farko ta kalleta,daga samanta cukurkudadden gashinta data daura dankwalin atamfa,zuwa jikinta dake sanye da rigar atamfar da wuyanta ya yima yawa,ta sauko ga fallen zaninta wani kalar atamfar daban.


         Kamar zata fashe da dariya amma kuma bacin ran da take ciki ya zarta tayi dariyar,don cikin kwanakin kawaici kawai takewa hafsat din,ta dauka har yanzu wai widad din dai data sani ce?,cikin kwanakin gaba daya ta fito da wata sabuwar gadara cikin gidan,komai ta taba komai zata gyara ko zatayi amfani dashi sai ta tsoma mata baki,tana tutiyar cewa gidanta ne,yadda takeso haka za'a yi,yadda taga dama haka takeson ta gani.


          Koda ranta ya baci bata taba tsaiwa tabi ta kanta ba,abu daya ta lura kamar abbas ya kasa dai daita hakan,abinda ita kuma takejin tazo maqura,ba zata lamunta ba itama.


"Dakina nima akwai wajen ajiya" amsar data bata kenan a taqaice taci gaba da danna wayarta,abinda ya harzuqa hafsat din kenan


"Ba shawara nake baki ba,umarni ne" sake sauke wayar tayi ya dubi idanunta da kyau,ta gaji da rainin hankalinta,kusan fiye da rabin komai da komai na abbas yana dakinta,tunda shine asalin dakinsa,amma ko sau daya bata taba nuna damuwa ko tayi qorafi ba,shine yanzu 


"Ajiyar ce akace miki ni ban iya ba?,wai meye damuwarki?,naga dai kayan mijina ne ko?"


"Miji?,ni kike cewa mijinki ne?,turqashi!,wallahi saina nuna miki isata,saina nuna miki ni wacece,kuma wadan nan kayan saikin fiddosu" ta fada tana nunata da yatsa,kamar ma batasan me take ba, saita bawa banza ajiyarta taci gaba da abinda takeyi,ita abinda bata sani ba,tana jin zafinta fiye da yadda ita takejin nata,tana kishin uncle abbas fiye da yadda ita take kishin nasa,saidai ita an gaya mata,matsayinsu daya hasalima gaba take da ita,dole tayi respecting nata,amma ko daya bataga alamun daukar girma a wajenta ba.


         Banbami tahau yi tana sauka akan yaran,ta tattarasu ta wuce kitchen dasu,widad ta tabe baki taci gaba da abinda takeyi,saidai can qasan ranta zuciyarta tana mata zugi,ta gaji da rainin hankali irin na hafsat din,ta kuma daina daga mata qafa.


          Ko daga kitchen din tana jiyo masifarta da kuma mitarta,ta kasa zaune ta kasa tsaye,daga bisani ta kashe girkin data dora ta dauki yusra suka fito


"Sai maganinki,bazan zauna qaramar yarinya dake kina maidamin magana ba kamar sa'arki" abinda ta fada kenan tana ficewa daga falon.


         Gyara kwanciyarta ma tayi tana maida hankalinta ga kallo,tsahon mintuna kusan goma sha biyar saiga maari matar me gadinsu tayi sallama,widad ta miqe ta zauna cikin fara'a da yake mutuniyarta ce sosai,suka gaisa sannan tace


"Hajiya ce tace ayi kiranki" mamaki sosai ya kama widad din,hajiya kuma?,irin hakan bata taba hadasu ba illa iyaka gaisuwa


"Bari na fito muje tare" ta fada tana miqewa tayi daki,maari tabi bayanta da kallo cikin tausayawa yarinyar,Allah ya hadata da BAK'AR KISHIYA.


               Tana sallama ta hangi hafsat daga zaune tana bawa yusra nono,a nutse widad din ta qarasa tana gidata,sama sama ta amsa mata fuska a hade,tun daga nan sai itama widad din ta kama kanta.


"Kinsan alaqata da babanki?" Ta fada kai tsaye,saita dubeta sannan ta girgiza kai,tadai san suna da alaqa amma batasan wacce iri bace,kwanaki da ummu tazo mata suna yawan zama suna hira,hakanan itama tana aiko mata da abinci kullum


"Kamar qanwa nake a wajen babanki,wannan dalilin ya sanya nayi kiranki,mummyn mimi ta kawo qararki,ki shiga taitayinki,banason rashin kunya da diban albarka,kizo ki sameta da mijinta da komai nata amma ki dinga qoqarin nuna kinfi kowa iyawa?,ki dinga yi mata isa da gida?"  Wani abu ne ya taso mata,taji sam ba zata iya daukan zancan ba,don haka ta runtse idanu tayi nesa da tunaninta na tsahon wasu mintuna kafin daga bisani ta miqe


"Ai bansan gidanta bane ba,amma yanzu na sani" abinda tace kenan ta soma takawa tana yin gaba,duk sai suka bita da ido,nauyi da kunyar yadda yarinyar tayi yana kama hajiya,yayin da hafsat ranta ya baci,ta kawo qarar wajenta ne saboda taji akwai alaqa a tsakaninsu,amma kuma haqarta bata cimma ruwa ba.


       Ranta yanatason ya baci amma tana qoqarin dannewa,tayi nasarar korar wannan,taci gaba da sabgoginta,bata ce ga sanda hafaat ta dawo ba,ta daiji motsinta cikin kitchen da kuma qananun mitocinta qasa qasa.


         Kwance tayi a dakinta har aka kira magrib,ta shiga toilet dinta ta sake wanka sannan tayi alwalar sallar magariba,wanna din sunnarta ne,ta riga ta saba koda bata da girki sai tayi wankan nan ta canza kaya,abinda hafsat din tayita son ganin ta hanashi faruwa,a cewarta ba ranar girkinta bane,don me zata dinga fitowa tana mata kwarkwasa da turare da kwalliya,saidai bata samu wannan nasarar ba.


         Ana idar da sallah taji alamun shigowar abbas din,duk sanda ya shigo gidan koda motarsa na anesa,ko motar office ce ta ajjiyeshi daga nesa sai taji hakan cikin jikinta,har zuwa sanda ya shigo sassan nasu, tanajin muryar su mimi suna masa oyoyo,taso tashi amma sai taji duka bata da interest akan hakan,kuma ma tasan bazai wuce minti uku bai qaraso dakinta ya dubata ba,don haka taci gaba da zama tana qarasa addu'o'inta da bata rabo dasu.

 

      Tun tana zuba ido harta soma qosawa,shuru bataji sake jin motsinsa ba,ta kalli agogo minti kusan ashirin kenan,tana sauke ido yayi dai dai da tashin muryarsa daga parlor yana kiran sunanta,duk sai taji banbarakwai,abinda bata saba dashi ba,amma kuma yau da gobe sai Allah,sai ta miqe a nutse tana gyara hijabinta sanan ta nufi qofa,gefe daya tana jin yadda cikinta yake qara tauri,wanda ita daya keji da ganin hakan.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post