Daudar Gora book 2 page 37

Daudar Gora book 2 page 37

 

Daudar Gora book 2 page 37

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲      

  ✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨

           (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)

            𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (37)

.........Da sauri ta sake maida natan kan nasa ta danne ta hanashi motsawa. Fuskar data kumbura yabi da kallo yana sake tsuke tashi, babu alamar wasa tattare da shi ya ce “Miye kuma?”.

       “Ni wlhy ba sai ka taɓa ba zan yi da kaina, kuma ai yama daina”.

            (Yarinyar nan zata kasheni wlhy) ya faɗa acan ƙasan ransa yana mai ture hannun nata ya matsa wajen. Zabura ɗaya tai ta kanannaɗe jikinsa tana fasa ƙara dan taji zafi na gaske. Yanda ta faɗo jikin nasa a bazata, ga hannunsa da yake ƙoƙarin toshe kunne saboda ƙarar da tai har cikin kansa. Baya sukai su duka, shi ya faɗa kan bayansa ita kuma tana a kansa. Bashi da zaɓin da ya wuce riƙota kawai. Wani irin dab-dab da juna fuskokinsu suka kasance, har hancinansu na gogar juna. Hakama idanunsu sun sarƙe cikin juna. Wani irin al'amari da ya sake rikita mata lissafin data manta da zafin ciwon da take ji ta gano cikin tsakkiyar ƙwayar idanunsa, da sauri ta kauda ƙwayoyin idanun nata a cikin nashi da son zame jikinta gaba ɗaya tsigar jikin nata na wani irin tashi, numfashinta kam fita yake da sassarfa. Hannunsa dake saman ƙugunta yasa ya sake maidota jikin nasa. Zafin da taji wajen bigewar ya sata matse fuska, sai kuma ta tura baki tana buɗe idanun nata kan ƙyaƙyƙyawar fuskarsa da gaba ɗaya kwarjininsa ya sa takeji ta kamar a wani kogon dutse suke a matse.

        Yanda taki yarda ta sake kallonsa ya sa yaji murmushi na zuwa masa. Amma tsabar iya miskilanci da jin kai sai ya haɗiye kayansa yana ɗan lumshe idanun da sake buɗewa kan ƙyaƙyƙyawar fuskarta da tai wani takwaf-takwaf kamar zata saki kuka. Cike da son ta magantu ya ɗaura hannunsa kan inda ta bugun da ƙyau, murya a shaƙe kamar mai raɗa ya ce, “A kira Doctor?”.

       Yanda yay maganar yana busa mata numfashinsa kan fuskarta ba ƙaramin yamutsawa tsigar jikinta tai ba. Cikin sauri ta jujjuya masa kanta tana ƙara ƙwaɓe fuska. Ita kanta bata sanin sanda take masa shagwaɓar nan, kawai samun kanta take a hakan. “Ni dai ya daina, ka barni na tashi ba ƙyau”.

       Kafeta yay da kaifafan idanun nasa da suka sake shanyewa can ƙasa, cikin wani irin salon ɗagesu ya furta, “Mike nan?”.

           A hakali saman lips. Idanunta a rufe ta nuna yanda suke tana kauda kai. Wani makirin murmushi ya suɓuce masa a karo na farko, a hankali ya juyata suka koma kwance a gadon su duka kan hannayensu suna fuskantar juna. Baya tai yunƙurin ja ya tareta da hannunsa ya sake maida fuskarsu daf da juna. 

      “Nace na gama da ke ne?”.

    Iffah fa gaba ɗaya ji take ma bada Shahan-shan take tare ba wani aljanin ne yazo mata a siffarsa. To inba haka ba taya za'ace ma Shahan-shan ne wannan. Mutum data sani ko kallo mutane basu ishesa ba, gaskiya wannan aljani ne, aljanin da ta jima tana gani kafin shigowarta masarautar nan....     

            Iskar da ya busa mata kan fuska ya sata jan numfashi mai nauyi alamar dawowa hayyacinta. Ya ɗan yamutse fuskan ta sa dake tsuketa, sake maida idanunta tai ta rissinar. Shima sai ya lumshe nasan ya ɗan sake buɗewa kanta yana motsa lips ɗinsa a hankali kamar wanda akaima dole. “Shi kuma wanda ya biya sadakinsa fa?”.

         Idonta a rufen kanta tsaye, duk da muryarta a kasalance alamar ta fara laushi ta ce, “Kai dai ai baka biya ba, dan ta ƙarfi aka kawoni masarautar nan dan a lasheni kamar yanda aka lashemun yayu na”.

    Da ƙyar ya iya gimtse murmushin da ke son kufce masa ya sake tsuke fuska a zahiri duk da ita bama kallonsa take ba. Daɗin biye mata yake ji, dan haka cikin ƙara ƙasa da murya ya ce, “In ma ban biya ba ai lokaci ne zai nuna. Mun taɓa lasar wani ne a gabanki zaki mana sharri?”.

      “Babu wani sharri. So babu adadi ma”.

   “Sai ki faɗa dawa-dawa muka lasa a gaban naki?”.

     “Matarka da ta mutu mana. Kuma nima dan namana da ɗaci ne yasa kuka kasa, dan nifa nafi ƙarfin mayu, kaima nasan tsorona kakeji yanzu haka”. Ta faɗa da ƙarfin ikon son tabbatarwa tana wani ƙara tsuke fuska.

          (Bazaki kasheni ba yarinyar nan) ya faɗa a zuciyarsa yana danne dariyar dake taso masa. A zahiri kam hannunsa ya maida a ƙugunta dai-dai inda ta bugu yana wani lumshe idanu da buɗewa, a hankali yake murza mata wajen batare data farga ba duk da tana ɗan jin zafi kaɗan-kaɗan. “Yaushe kika fara gano inajin tsoron naki? Dan nima dai naga kamar tsoron naki nakeji da gaske. Da alama baki barni haka ba kema mayyar ce ko?”.

         Lips ɗinta tai wani irin turawa tana ƙwaɓe fuska, ita ala dole taji haushi yace mata mayya, “Ni ALLAH ya kiyaye na zama mayya. Tsorona kuwa tun randa ka fara ganina mana, kuma inba tsoro ba miya maidaka Ajmaal ka dinga naɗar min sirri...”

     Yanda ta ƙare maganar da yin takwaf-takwaf da fuska kamar zatai kuka ya sashi jan wata irin wawuyar ajiyar zuciya jin numfashisa na fisga, kansa har ya fara masa ciwo saboda ya gaji da surutun, itako oganniyar ya fahimci ko'a jikinta ma. Cikin nuna alamar gajiyawar har cikin harshensa ya ce, “Ashe dai ni kike jin tsoron, saboda na kasance Ajmaal duk wani sirrinki na sani?”.

       Idanunta da ke rufe ta buɗe fes a kansa, cikin son dakewa ta ce, “Hu'im lallai ma tsoro fa? To kaima ai naka sirrin na a tafin hannuna basai na faɗa ba”.

           “Ni ɗin?”.

     Ya faɗa a fisge yana waro duk girman idanunsa kanta. Jikinta tai ƙoƙarin janyewa da ga nasa dariya na taho mata ganin yanda ya waro idanun, a nata ganin ai ya tsorata ne. Sake riƙota yay suka koma daf-daf fiye ma da ɗazun, cikin wani salon da ke neman girmar kanta ya kai hancinsa kan wuyanta yana busa mata numfashinsa. Da wani irin karyayyar murya data sata zabura can ƙasan maƙoshi ya ce, “Faɗamin wane sirrina kika sani? Na yi alkawarin zan ƙara miki da wani ma yanzu duk ki haɗa”. Yanda yay maganar numfashinsa ma sauka saman wuyanta tare da murza hannunsa wajen ciwonta batare daya fargaba babu shiri ta zabura zatai magana, rufff ya rufe bakin da tausasan pink lips ɗinsa. Ɗifff komai na jikinta mai aiki da motsin ruhinta ya tsaya cak da aikin na wucin gadi kamar yanda nashi ya kasance. Idanunsa ya lumshe a hankali da sake buɗesu kan fuskarta, kafin ya kai hannunsa baya ta ƙeyarta ya tura yatsun kan tattausan gashinta, a hankali ya fara warwaro ribbon ɗin data ɗaure gashin a tsakkiya da juya lips ɗin nasa kan nata ya mirginata suka sake komawa kan hannayensu ta ɗaya ɓarin yanzu ma suna fuskantar juna. Wannan ne karo na farko da hakan ta faru a tsakaninsu, abune kuma da bai taɓa faruwar ba, hakan ya sata shiga cikin ɗimuwa da gigita, dan da wani irin salon dake neman ɗage numfashin nata da ga gangar jikinta yake juya lips ɗin nata cikin nashi tamkar ba Shahan-shan ɗin nan ba mai tsananin miskilanci da izza da ƙasaitar mulki, wanda hatta magana wahala take masa. Murmushinsa kam abune mafi tsada ga duk wanda ya sanshi. Gaba ɗaya duk sai ta daburce jikinta ya shiga rawa, ciwon ma da ƙafar ke mata da ƙugun ta nemesu ta rasa... (🤭Bily ki kiyayi kanki🏃)          Da alama Shahan-shan Eshaan ya tafi, tafiya irin mai toshe kunne daga jin ko wane irin motsin sauti da ke a doron duniya, dan dukkanin takaicinsa akan waɗan nan lips ɗin masu masa tsiwa yau da alama sai ya hucesu. Ita kanta ɗalibar tasa tun zaburar farko da tai na dawowa hayyaci bata sake motsin kirki ba. Sai da taji hannunsa na ƙoƙarin shiga cikin ƙaramar rigarta ta sake zabura da ƙoƙarin dafe hannun nasa da nata tana son janye lips dinta da ya riƙe da nashi cikin kar-kar-war jiki. Babu alamar zai bata damar da take buƙatar, dan da gani dai yayi zurfi shi kam. Da sauri tasa dukan ɗan sauran ƙarfinta wajen jan jikinta baya, kamar zai riƙota sai kuma ya barta yana mai rumtse idanunsa da sukai wani irin mahaukacin kaɗawa jazur da ɗan ƙarfi. Baya ta juya masa tana mai dunƙule jikinta dake tsuma har yanzu waje ɗaya. Tunda Ummu ta haifeta tai hankali tai wayo babu wani da ya taɓa kai hannunsa inda Tajwar Eshaan ɗin ya kai yau a jikinta, kai itafa ko riga bata yarda ta saka gaban su Arfa ma dake yayunta tsabar yanda take jin kunya. Amma yau sai ga abinda batai zato ba, da ga mutumin da batai tsammani ba, wayyo ita Fhareedah ta ga takanta. Wani irin yarrrr yarrrrr take ji kamar har yanzu hannun nasa na'a jikin nata ne tsabar yanda ta firgita. Ɗaya da ga cikin filos ɗin da aka ƙawata gadon ta fisgo ta ƙanƙamesa a ƙirjinta dan ta kasa nutsarwa waje guda, da gaske ta tsorata tsoro irin wanda batajin ta taɓa shigarsa a rayuwarta, sai kawai wasu hawaye masu ɗumi da bata san na minene ba suka shiga rige-rigen sakko mata a kan fuskarta.

         Ajiyar zuciyar da take ja mai tafiya da kamar shashshekar kuka-kuka ta sakashi buɗe lumsassun idanunsa da sukai wani irin shanyewa sosai, akan bayanta data juya rigar ta ɗage sosai saboda tattareta da yayi ya sauke su. Ya ɗan rufe ya ƙara buɗewa yana mai ƙarema bayan nata fari sol kallo. Wani irin harbawa zuciyarsa ta sakeyi da ɗan ƙarfi lokacin da idanunsa ke sake sauka kan wannan dai tawadar ALLAHr babba da ke a ɗan sama-saman bayan nata ta gefen kafaɗar dama. Da sauri yake ɗan girgiza kansa alamar hakan bazai yuwuba kama ce kawai da ga ALLAH. Ta inama hakan zata faru? (Kai noo.. noo.. ba haka bane) ya faɗa a cikin ransa da kaushi sosai yana ɗauke idanun nasa da ga wajen. Sai ma ya miƙe a matuƙar kasalance, zama yay ya ɗan bata baya, cikin muryarsa dake a matuƙar sarƙe ya furta, “Ga wani sirrin nan nawa na baki ki haɗa ki adana min”. 

       Batare da ya sake yarda ya kalleta ba ya nufi bathroom kawai yana mai sake ƙaryata zuciyarsa da taƙi amsar dagiyar tasa kan abinda idanunsa suka sake gani yau ma a jikintan........✍️

     _Oh ohh girma ya daɗi🥱🚴🚴🚴🚴_

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_

_LITTAFI BIYU: 600_

_LITTAFI UKU: 800_

_LITTAFI HUDU :1000_

_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI

ACCESS BANK

002241917

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN 

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 96 09 67 63

Books biyar  1250CFA

Books hudu  1050CFA

Books uku  850CFA

Books biyu  650CFA

Bookk daya  450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post