Abban Sojoji Complete book 2

Abban Sojoji Complete book 2

Abban Sojoji Complete book 2

*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*


  *🔥The Father Of Soldiers🔥*


   ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ ﺭﺍﻓﻴﺖ❤‍🔥💞💘💖


*Story & Written by*

*Hafsat Bature Muhammad*


~💋BOSSLADY💋~


_Sabuwar Marubuciya, mai tafe da sabon salo💫_


*Abban Sojoji part 2*


*EPISODE 1*Meaning Of Name *AMANI*  means *wish* arabic name ne na mata🌹ina faɗin ma'anarsu ne saboda masu tambaya, sunaye ne masu kyau mutun zai iya amfani dashi in yana so wa baby girl ɗinsa😍Ruwan sama ake yi sosai garin, yanayin yayi wani irin daɗin gaske, ga wata irin ni'imtacciyar iska wadacciyar da ta gauraye ko'ina, wurin ƙarfe 5 na marece ne amma sai kayi tunanin dare ne sosai saboda Lullumin da garin yayi, a wannan yanayin kowa na ƙumshe a bedroom ɗinsa saman gadonsa, lullu6e da bargo, baka jin hayaniyar komai ko'ina tsit a cikin gidan 😊


zaune suke acikin mota suna tattaunawa su biyu, Hafsat ce tare da wata Hamshaƙiyar mata wadda bansanta ba, jikinta na sanye da tsadadden leshi Ash colour, fara ce kana ganinta kasan taji hutu Over ya zauna mata, ita ce a mazaunin driver yayin da hafsat ɗin ke gefen ta suna tattauna wa,

 Hafsat ta natsu tana sauraronta " Naci sa'a da nasamu address ɗinki kuma na same ki cikin sauƙi, kuma ina fata zaki taimaka mun wurin cimma burina,' matar ta faɗi tana kallonta, 

   Hafsat tace "ina sauraronki me kike so inyi miki ne "?

  Murmushi matar tasaki kafin tace "Kafin na faɗa miki abunda nakeso, pls ina so ki fara bani acct number ɗinki," 

   Bin ta da kallo hafsat tayi cikin mamakin jin abunda matar tace,

 Amma batayi musu ba, ta shiga karanto mata numbar acct ɗin, ita kuma tana kwashe wa a wayarta dake hannunta, 

  Bata jima da gama karanta mata numbar ba sai ga Alert ya shigo a wayarta ƙirrrr!

  Cikin sauri hafsat tasa hannu ta ɗauki ƴar purse ɗinta dake asaman Laps ɗinta ajiye, ta zugeta ta ciro wayar jiki na rawa ta duba, gabanta ne taji ya faɗi rass !! Ganin Alert na 6millions abun kamar a mafarki take ganinsa 

  Cikin tsananin mamaki ta ɗago ta kalli matar tare da cewa "Wannan fa? Na menene?

  dariya matar tayi kafin tace " akwai wasu tagwayen Yara da Marshal Omar ya kawo gidan nan, Sunan su Hosana da Jahad,'

  Jin sunan da ta ambata yasa hafsat kallonta cikin mamaki,.

  Taci gaba da cewa "Ba wani aiki bane mai wahala, so nake subar gidan nan ! Suyi nesa da Marshal Omar..........' 

  Cike da mamaki hafsat ke kallonta , babban abunda ya ɗaure mata kai shine yadda akai tasan cewa Marshal Omar ya kawo yara acikin gidan,.

  Daker ta iya cewa "Saboda Me za'ae hakan? 

  "Saboda basu da amfani," matar ta bata amsa a taƙaice,

   Shiru hafsat tayi tana kallonta acikin zuciyarta tana Was wasi akanta,

  "Wacece ke? Taya akai kikasan sunan Tagwayen tare da kuma sunan Omer?

  "Ba buƙatar wannan, Kawai kiyi mun abunda nace in aikina yayi kyau nayi maki alƙwarin zan ninka miki abunda na baki har sau uku,


  Hafsat tace "To shikenan ni zan wuce ciki sai kin jini"  


    Murmushi matar tasaki tare da cewa "sai mun sake haɗuwa," 

  fito wa hafsat tayi daga Motar ta rufe mata sannan ta wuce cikin gidan da hanzari saboda ruwan dake sauka ajikinta, 


Yayin da ita kuma Matar taja motarta ta fuce daga gidan fuskarta ɗauke da murmushin nasara, 


tana shiga cikin babban falon ba kowa kai tsaye bedroom ɗinta ta wuce, cire kayan jikinta tayi shaf shaf ta canza izuwa riga da wando, ta ɗaure gashin kanta a baya, tana tsaye gaban Mirror tana tunanin maganar Matar nan data kawo mata ziyara sai ga Aunty Babba ta faɗo ɗakin tana faɗin "Hafsat wacece waccan matar da tazo wurinki yanzu"?

  Juyowa hafsat tayi tana kallonta tace "Nima bansanta ba address ɗina aka mata shine tazo da buƙatarta," 

   "Wace irin buƙata kenan"? Aunty babba ta tambaya tana kallonta,

  Hafsat tace "Tayi mun magana akan cewa tana so in raba twins ɗincan da Omar ma'ana subar gidan nan gaba ɗaya, Suyi nesa dashi" 

   tsoki aunty babba taja tare da cewa "Ita kuma wacece ita isasshiya? halan Omar take so ne shiyasa ta biyo ta wurinki?.

  "Bana tunanin hakan, Nafi tunanin Tasan Yaran ne shiyasa take son azubar dasu," 

   "To ke kuma kin amince da buƙatarta kenan"?  

   Murmushi hafsar tasaki tare da cewa "eh mommy na amince da hakan, saboda anan take ta bani miliyan shida kuma tace muddin aikinta yaci ka zata ninkamin abunda tabani ynx," 

   tuni aunty babba ta haɗe fuska rai a6ace tace "Amma ke shashashar ina ce? Kawai daga zuwan mata sai ki amince mata da buƙatarta? matar nan fa Omar take so shiyasa takeson a salwantar mata dasu," 

   "Koma dai menene Mommy ni bazan bari kuɗin nan su wuce ni ba, saboda ina cikin buƙatarsu, daddy baya sakarmun kuɗi yadda ya dace ke kuma tanadin ki na zuwa wurin bokane kema fa bakya bani ko sisi Burinki akan hayaam da Abrah ne," .  

  Matsawa Aunty babba tayi kusa da ita tana cewa "Hafsat Anya kina cikin hayyacin ki kuwa? Ni kike faɗama haka"? 

   "Na faɗi wani abune daba dai dai ba? ta tambaya tana kallon mommyn nata, Ido cikin Ido

  Sassauta Murya Aunty babba tayi a ƙoƙarinta nata fahimtar da hafsat tace "duk wannan tanadin da nake saboda kanmu ne fa ! Ƙaruwar mu ce, in har naci nasara akan burina Hayaam tasamu RAFAYET ita kuma Abra tasamu MARSHAL OMAR mune zamu ji daɗi, don haka am commanding u ki tattara kuɗin da tabaki ki mayar mata dasu yanzun nan !!!! ta faɗi a tsawace

  Dariya hafsat ta kwashe da ita hada tafa hannu bayan ta tsagaita tace "Mommy kenan !! nima fa lashe Money ce kamarki, bazan bari garabasar nan ta wuce ni ba!! Akace da arziƙi a gidan wasu ƙwara agidanku, kai agidan nakuma kwara a ɗakinku, a ɗakinku ɗin ma ya faɗo akan ka, don haka ni baxan mayar mata da kuɗinta ba!!!!!!!!!

  Gaba ɗaya hankalin aunty babba ya tashi don alamu sun nuna cewa Hafsat fa kamar bata cikin hayyacin ta, cikin ruɗi tace "Hafsat anya kina cikin Hayyacinki kuwa"?

 Shu'umin murmushi hafsat tasaki sannan tace "Kwarai kuwa! nice dae ƴarki Hafsat ɗiyar general ishaq, jika ga Abban sojoji" 

  Jinjina kai aunty babba tayi tabbas an samu matsala, domin kuwa tasan Hafsat bazata ta6a fasa abunda tayi niya ba, 

  Huci kawai take yi tana jinjina kanta a ƙarshe ta fuce daga ɗakin,

Duk wannan suratan da Hafsat su kayi da aunty babba a kunnan Hosana wadda ke la6e a ƙopan ɗakin, jin Takon tafiyar Aunty babba yasa ta gudu izuwa cikin store ɗin da suke,

 "Ina kika je hosana bakya jin magana ko? salon sai sun ganki? Mun samu yau sun ƙyale mu basuyi mana komai ba, 

  Jahad ce ke wannan maganar wadda ke atsaye tana kallon hosana,

Murya na rawa hosana tace "Jahad naji abunda su Hafsat ke cewa ita da Momynta,"

   "Me suke cewa ne"? Ta tambaya tare da matsawa kusa da Hosanar don taji dakyau,

  Hosana ta kora mata bayani tun daga farko har ƙarshe,

  Jahad ta jinjina kai tare da cewa "Ashe buri yayi kama da mutun, shiyasa ta tsane mu kenan saboda tana tunanin cewa Omar zai iya son ɗaya daga cikinmu, ran nan tace mun batason mune saboda mun shiga tsakaninta da abun harin ta, Yanzu nagane inda ta dosa, To amma wacece matar da hafsat ta haɗu da ita yau? Wadda ke son A zubar mata damu!? 

  "Ni inaji araina jahad so suke su rabamu da ƴa'ƴa Omar kawai," hosana ce tayi maganar ido cike tab da kwalla don bata son duk wani abu yanzu dazai rabasu da Omar,

   "Insha Allah burinsu bazai ta6a cika ba Hosana, baza su iya raba mu ba da yaya omar ɗinmu," tayi maganar tare da janyo hosana suka rungume junan su

__________________________________________


Tuni sun kammala aikin su na dinner, har sun kammala jerawa a dining Kowa ya bama cikinsa an ware, yanzu gidan ya ragu ba laifi kasancewar tun week ɗin daya wuce aka tura mutun Huɗu Aiki, Irfan jabeer, khaleed da Fawan duk basa nan, yanzu wanda suka ragu Acikin gidan Haroon, twins, junaid, Sai Marshal Omar da Sgr duk da basu cika zama cikin gidan ba suma, always working saboda suna bada gudummuwa sosai shiyasa koda yaushe suna headquater ɗinsu don ana buƙatarsu sosai game da insecurity ɗin qasar tamu, kasancewarsu kwararrune a6angaren aikin soja dama sun kasance international Armies, kowace ƙasa aduniya suna bada gudummuwarsu wurin kame tantirai sune maganin ƴan Iska, shiyasa sunansu ya shahara a faɗin duniya duk inda suka je, ansansu girmamasu ake gani kamar kamar me (Tiger da Lion) Kenan ba wasa 😇😇😇 


SEHRISH

Shiga bedroom ɗinta tayi Wurin isha prayer, duk ta rame kamar ba Reeshi ba, alwala ta ɗaure a toilet, ta shimfiɗa sallaya, ta gabatar da salla, bayan ta kammala ta naɗe hijab da sallayar ta tura a wardrobe ɗinta, komai nata a slow take yinshi saboda rashin kwarin jikinta da fargabar da take fama dashi na Haroon,


   Haye wa tayi saman gadonta tare da janyo pillow ta rungume tunani kala kala a ranta, hawaye ne suka soma gangarowa daga idonta sbd  tuna yadda haroon ke ta6a jikinta, hannu tasa tana share su, daga bisa ni tayi lamo tana tunanin duniya, 

Tana cikin wannan halin taji an kwankwasa ƙofa, shiru tayi bata Yi magana ba cike da tsoron waye ke mata knocking, ji tayi an sake buga ƙopar muryar na rawa tace "wanene"?

   Muryar junaid taji yana cewa "Sehrish ni ne," 

   Ajiyar zuciya tasaki jiki na rawa ta sauko tare da karasawa wurin kopar ta buɗe,

   Gabanta ne yayi mugun faɗuwa ganin haroon hankali tashe tace "Kaineeee !!!!" a tsorace tayi maganar jikinta na rawa,.  

     Fashewe da dariya haroon yayi tare da wuce ta yashi ga ciki yana cewa "ƴar shila ni ne, ae nasan bazaki buɗe ba shiyasa nayi maki muryar junaid don na lura kuna good time dashi,' 

    juyowa tayi tana bin shi da kallo a razane,.  

     "Me ya kawo ka"!?

"Abunda yasa ba kawo ni, Yau nazo ne ayi ta taƙare, Haƙƙina nake son ki bani," 

   Cikin shessheƙar kuka sehrish tace "Me kake nufi wai !!! Wani haƙƙi ka ke dashi akaina? Dan Allah kabarni nayi rayuwata cikin salama !! Ka rabu dani mana !!

   ta6e baki haroon yayi tare da cewa "Na amince zan rabu dake, amma bisa sharaɗi ɗaya"? Ya faɗi yana kallonta fuska a ɗaure, a lokacin tadawo tsaye front of side drawer ɗinta tana facing ɗinshi,

   Gabanta na faɗuwa tace "Menene shi"? Cikin sanyin murya tayi maganar

   Haroon yace "Your Virgin!! shine abunda nake so,and if u do so i wll be out of ur life" 

   Fashewa da kuka sehrish tayi cikin tsananin jin ƙunci da raɗaɗi aranta, tuni zufa tagama wanko mata kamar wadda aka tsamo daga cikin ruwa, tsanar haroon take ji kamar kamar me, tarasa amsar da zata bashi sai faman kerma take,

   A tsawace haroon yace "Ke !!! Ki amsa mun kin amince ko baki amince ba"!?

  A Firgice tace "Na'amince" ita kanta batasan ta bashi amsar ba saboda tsoratar da tayi da tsawarsa,

  Wani irin shu'umin murmushi haroon yasaki, bin shi da kallo tayi ganin yasa hannu yana zare belt ɗin wandonsa, tuni ta runtse ido ganin gashin jikin shi, bakomai ya faɗo mata arai ba fa ce Sgr shine namijin da take so tafara kasancewa dashi arayuwarta bata buƙatar wani namiji in ba shi ba, shi take so ta mallakawa komai nata muddin ta mallake sa,

   Jiki na rawa ta zura hannunta ta baya, taci sa'ar damƙar fititalar Kwan dake gefen gadonta, kafin haroon ya ɗago ta daddage da iya ƙarfin ta na ƙarshe ta ɗago da fitilar dake hannunta ta kwaɗa masa a tsakiyar kai !!!!! Ji kake KWASSS !!! A razane haroon ya ɗago jin saukar fitilar kafin yayi wani yunƙuri tuni Sehrish tabi ta gefensa ta watsa da gudu sai cikin toilet ta datse ƙopa sosai, ta sulale daga jikin ƙopan zuƙunne tana kuka don tasan dole haroon ya ɗauki matakin abunda tayi masa,

  Ba ƙaramin buguwa haroon yayi ba, don wurin harya fashe Ae kuwa rai a tsananin 6ace yace "Ke don ubanki ni kika fasa ma kai"?

  Sehrish dake acikin toilet murya cike da kuka tace "Ba dai ubana ba sai don Uban Mai zagi !! Fasiƙi ɗan iska insha Allah bazaka ta6a cin nasara akaina ba, sai Allah ya nuna maka iyakarka, wulaƙantacce kawai ƙazami mai warin baki," 

  Tuni idon haroon sunyi jawur kamar garwashin wuta, ransa yayi mugun 6aci bai ta6a tunanin yarinyar zata iya mayar masa da martani ba, amma sai gashi yau ta zage shi tass,

   "Bazan ƙyaleki ba, sai na wulaƙanta rayuwarki ba dai kina acikin gidan nan ba kuma zaki fito ba, zamu haɗu ne wlh," Ya faɗi tare da tunkarar hanyar fita yana mayar da belt ɗin wandonsa daya fara cirewa,.(ba'aci nasara😂)

   Sehrish batayi shiru da bakin ta ba taci gaba da cewa " Ta Allah bata ka ba wlh !! Mugu azzalumi mummuna kawai, da wasu idanuwan ka kamar na Mujiya ni ina kokwanton Cewa anya kai Jinin Abban sojoji ne !! Sbd duk ƴa'ƴansa ba Fasiƙi irinka," 

  Jinjina kai haroon yayi kawai yana huci, ya tura ƙopar ɗakin ya fuce,


   Wani sabon kukan ta sake fashewa dashi, tana faɗin "wayyo Allah na nasan haroon baxai ƙyale ni ba, nashiga uku........' 

   Jiki na rawa ta miƙe ta nufi wurin bathroom cabinet ɗinta, akwai wasu Chemicals dake ajiye cikin toilet ɗin masu illah ga jikin mutun tamkar poison suke, ta riga ta yankewa kanta shawarar kwara ta kashe kanta ta huta da fitinar haroon,

   Hannunta har kerma yake yi, wata ƙaramar roba ta ɗauko mai ɗauke da chemical ɗin, buɗe murfin tayi yayin da idonta ke zubar da hayawe, bakowa ya faɗo mata arai ba face Hosana Jahad, junaid, Aunty azmee uwa uba Burin ranta, yanzu shikenan duk zata rasa su? Zata mutu tabarsu? 

Runtse idonta tayi aranta tana faɗin "bani da wata manufa face wannan, kuyi haƙuri ku yafe mun bazan Iya cigaba da rayuwa a wannan duniyar ba mai cike da tashin hankali, ban ta6a cutar da kowa ba, amma gashi wani nason cutar da rayuwata ....................."

    Cikin sauri ta shiga zazzaga hodar abakinta


A dai dai lokacin Motocin Sgr da marshal Omar suka shigo cikin gidan atare jiniyarsu ta karaɗe ko'ina har cikin kunnan Sehrish

   Zuciyarta ce taji tayi wani irin bugu, nan take kuma zuciyarta tace "Yanzu kin amince ki mutu baki cika burinki ba!? ke fa musulma ce ! Kin kuma son hukuncin wanda ya kashe kansa da gangan!!

   Runtse idonta tayi hawaye na zuba, fuskar sgr kawai take tunawa da fuskar su hosana da jahad,

  "Ina son sake sashi a idona," ta furta da wani irin sound, nan take tayi wurgi da robar chemical ɗin dake hannunta, cikin hanzari ta shiga amayar da wanda ke bakinta agaban  basin, fanfo ta kunna tashiga kuskure bakinta da hanzari ta kora aman, sannan ta wanke face ɗinta ta fito,

   tana tafiya zuciyarta na ƙara bata ƙwarin guiwa da cewa "Saboda wani shashasha zaki halaka kan ki, share hawayenki sehrish kina da damar rayuwa, wani banza bai isa ya tarwatsa miki burinki ba," 

  Gyara jikinta ta shiga yi saboda tana son zuwa kai mishi dinner ɗinshi shi da Omar don ta son da yunwa suka dawo, duk da tana tsoran kada suci karo da haroon a fitarta,

   dama riga da wando ne ajikinta, gashin bakinta kawai ta manna, ta gyara hular kanta da mayafin da take naɗe hular dashi, bayan ta kammala ta buɗe kopan cikin fargabar ta fuce,.

   Ko'ina haske fauuu gidan cikin sanɗa ta wuce kitchen taji sanyi aranta ganin babu kowa,

  Cikin hanzari ta shirya ma Omar nasa a tray, a palor ɗinsa takai masa babu kowa aciki alamar yana cikin bedroom ɗinsa, ajiye masa kawai tayi ta fuce, izuwa kitchen ta sake shirya wani a tray sannan ta wuce upstairs part ɗin BABBAN YAYA


Haryanzu jikinta kerma yake, kuma bata fasa maganar shan poison ɗin nan ba, burinta ta sanya Sgr a idonta 4 the last time before tabar duniyar, Baiwar Allah

  Babu kowa a palor ɗinsa tsit kake ji sai ƙamshin dake tashi, shiga ciki tayi ta ajiye masa a saman table ɗinsa,

     Tsayawa tayi tana faman sauke ajiyar zuciya yayin da idonta ke cike taf da hawaye, kamar daga sama taji muryarsa ta cikin bedroom ɗinsa yana faɗin "who's There"?

   Runtse idonta tayi saboda jin sanyayyiyar muryarsa, daker ta dai daita natsuwarta tace "Tukur ne mai aiki," 

 Voice ɗinsa tasake ji yace  "Come In! i wanna see YOU Right now," zaro ido sehrish tayi jin abunda yace wato ta shigo ciki yana som ganinta 😳😳😳😳😳


Dake ta dai dai ta natsuwarta, ta tafi izuwa cikin bedroom ɗinsa kamar yarda ya umarta ta shiga da sallama"Assalamu alaikum" 

"Wa'alaikum salam" ya amsa mata,

tsaye yake agaban mirror jikinsa sanye da sleeping dress riga da wando Milk colour masu ɗigon² baƙi ajikinsu ba ƙaramin kyau su kayi mishi ba, turarurruka yake ta fesa ma jikinsa, 

   Sam tagaza janye idonta akan shi daker ta iya cewa "barka da dare" ya amsa mata da "Yawwa" sannan ta ƙara da cewa "Gani" 

  Hannu yakai ya ɗauki kalbar turaren SHUMUKH ya feshe shi sannan ya mayar ya ɗauki wani turaren na Jar yana fesawa, mutun ne mai tsananin son ƙamshi shiyasa baya gajiya da bin jikinsa da turare,

   Shiru sehrish tayi zuciyarta na ɗar ɗar, kusan 15 minsa sannan Boss Man ɗin yace "Ni zan zo ne"? Ya tambaya yana jiran amsa,

  Cikin sauri sehrish ta ƙarasa hankali atashe ta tsaya daga bayansa jikinta na rawa,

  Cikin natsuwa yaso ma magana" Wacece ke"?

  Waro ido waje sehrish tayi jin abunda yace murya na rawa tace "Ni.....mai.....aiki...ne ...." a wani irin slow sgr ya juyo kai tsaye ya tunkare ta gadan gadan, a tsorace sehrish ke ja da baya tana kallonsa tuni zufa ta gama wanko mata sharkaf a jikinta, 

  Sam idonsa basa a kanta ƙasa suke, har sai da suka ƙurewa bangon gaba ɗaya, yarfa hannu sehrish ta shiga yi a tsananin tsorace take karanto addu'o'in da duk suka zo mata abakinta, kuma abayyane take yi saboda tsaban ruɗi tuni ƴan hanjin cikinta sun motsa, gaba ɗaya jikinta rawa yake yi kamar wadda sanyi yakama,

  Hannunsa yasa ya daki wall ɗin data ke manne ajikinsa ya aza hannun anan jikin bangon ya dafe sannan yace "ƙarya ke bana so arayuwata, am gonna ask u some questions idan aka min ƙarya za'a fuskanci matsala," 

   Ya faɗi yayin da idonsa ke a lumshe tamkar a datse suke ba don komai ba sai don gudun kada mai aikin ya Sume a ƙaro na biyu saboda launin ƙwayar idonsa dake razanar da shi, .

   Kallon shi kawai take yi zuciyarta na bugawa da ƙarfi, daker take haɗiye yawu ga wani fitsari daya matse ta tunda taji ya ambace ta da mace tasan cewa ya gano ta kenan,

     "maca ce ko Namiji"? ya tambaya yana jiran amsa,

  Shiru tayi tana tunanin amsar da zata bashi, muddin tamasa ƙarya wannan ba ƙaramin shaqa zata sha ba,

  Wannan shirun da tayi masa shiya fusata shi, buɗe Blue eyes ɗinsa yayi duka akanta , ta firgita sosai amma sam ta sanƙare ta gaza motsi da alama suman tsaye tayi

     Hannunsa yasa ya damƙi hular kan sehrish yayi wurgi da ita tare da mayafin duka, nan take sumar kanta tasoma warwarowa tana saukowa saman kafaɗarta, kyakkyawan sumar kanta mai matuƙan kyan gaske ga laushi, 

     mayar da hannunsa yayi saman gashin bakin da take sawa ya cire shi shima, nan take ainihin kyakkwar fuskar reesh ta bayyana a matsayim mace 😊😉

    sam fa bata motsi idonta sun kakkafe sun ƙame, kamar wata saƙago haka tayi, 

  jinjina kai sgr yayi maganar Adams ta tabbata, yayi mamakin ganin yarinya ƙarama kamar wannan da ƙarfin halin Yin shigar Maza tazo gidan sojoji aiki, ko nawa aka biyata don tayi hakan? Ya tambaya aransa, sam shi baya tunanin ta haura 12years saboda ƙarantarta dayake gani agabansa Ko shouder ɗinsa tsayin sehrish bai kai ba, daga tsaye inda yake yana kallon tsakiyar kanta saboda ba ƙaramin tsayine dashi ba, kowa yazo gabansa kallon ƙarami yake masa,

    Janye hannunsa yayi daga jikin wall  ɗin da sehrish take sannan yayi tattaki izuwa inda fridge ɗinsa yake, buɗewa yayi ya ɗauko bottle water mai sanyi sannan ya dawo inda take tsaye,

    ya buɗe murfin ya yayyafa mata, a wani irin firgice sehrish ta girgiza ta dawo in sense ɗinsa, sai faman zazzare kyawawan idanunta take, bin chest ɗinsa tayi da kallo izuwa face ɗinsa cikin tsoro, hannu tasa ta shafa sumar kanta gabanta ne ya faɗi jin wayam babu yar hularta, hankali tashe ta wurga idonta inda sgr yayi watsi dasu.........nan fa tashiga faɗin "innalallahi wa'inna ilaihirraji'un dan Allah kayi haƙuri.....nashiga ukuna........' tana kuka tana magana , gaba ɗaya yayi mata rumfa tamkar Zaki haka take ganin sa agabanta 😳😳😳


   Idonsa na kumshe yana sauraronta left hands ɗinsa na riƙe da bottle water ɗin, yayin da ɗayan hannun kuma ya mayar dashi jikin bangon ya dafa, sehrish kuma na agabansa suna fuskantar juna, 

    "haɗiye wannan kukan bana so" cikin hanzari sehrish ta dakatar da kukan tashiga taitayinta, bakomai take kallo ba fa ce damtsen hannunsa, tunani kawai take yarda zai kai mata naushi tabbas tasan sai dai Uwarta ta haifi wata (Hafsat bature ana magana) 😂

Cikin natsuwa yasoma magana__________________________________Abt payment 300 ne, still muna free pages ne wanda suka shirya 08103884440 sumin magana 

👍

*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*


  *🔥The Father Of Soldiers🔥*


   ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ ﺭﺍﻓﻴﺖ❤‍🔥💞💘💖


*Story & Written by*

*Hafsat Bature Muhammad*


~💋BOSSLADY💋~


_Sabuwar Marubuciya, mai tafe da sabon salo💫_


*Abban Sojoji part 2*


*EPISODE 2*


*💞LAFAZI WRITTERS ASSOCIATION*💞
Cikin natsuwa ya soma magana "tambaya biyu kawai Wacece ke? Kuma waya turo ki"? 

   Cikin rawar murya sehrish tace "Ni ba kowa bace ba, kuma babu wanda ya turon.......'. Interrupting ɗinta yayi da cewa "ki mun magana a hankali don bana fahimta sosai," 

    Gyara muryarta tayi sannan taci gaba da cewa "Sunana Sehrish, kuma ni babu wanda ya turo ni, banzo da nufin na cutar da kowa ba, aiki kawai nake don nasamu kuɗi........' buga wall ɗin da yayi yasata dakatawa a tsorace "Nace wa ya turo ki!!? 

        Hankali atashe tace "Allah shine shaidata, wlh ni babu wanda ya turoni, banzo da nufin na cutar da kowa ba, ƴan uwana ne Basu lafiya an kwantar dasu asibiti ana buƙatar kuɗin aiki shine na nemi aiki gidan wata hajiya...............sehrish bata 6oye masa komai ba ta faɗa masa tass dalilin zuwanta da dalilin yin shigarta na maza batayi masa ƙarya ba ko kaɗan, ta ƙarasa masa labarin tana faman zubda hawaye tsoranta wane hukunci zaiyi mata don tasan watan Cin Ubanta ya tsaya, shiru su kayi na wani lokaci, kafin daga bisa ni Babban yayan yaja da baya ya juya


 bedroom ɗinsa ya shige kafin daga bisa ni, ya fito hannunsa ɗauke da wayarsa wuri yasamu ya zauna saman sofa ɗin sannan yaba sehrish damar ta matso kusa, sai da tafara tattara hularta da mayafin da yayi watsi dasu, ta ruƙesu a hannunta sannan jiki asanyaye ta matsa inda yake kamar wadda tayiwa sarki ƙarya, jikinta sai faman kerma yake,

   yace "su nan su? da sunan state  da sunan hospital da aka kwantar dasu? and the date!? 

    Murya na rawa tace   "Hosana Sayyad, da jahad sayyad an kwantar dasu a Fmc katsina........"


 duka ta faɗa masa hada date ɗin da aka kwantar dasu duka don bata manta ba,

     danna wayar yashiga yi kafin daga bisani ya danna calling, ta soma ringing, nan take aka ɗaga wayar suka soma magana, 

  Duk sehrish na tsaye tana kallonsa yadda yake speaking anatse,

    Bakowa ya kira ba face Babban Likita, dama already sai da yafara tura masa message na sunan yaran da bayanan dayake son sani sannan yakira, kuma anci sa'a On duty yake,'

   Tabbas yayi mamakin ganin kiran Surgeon general rafayet, kuma yayi mamakin jin sunan yaran da yakeson aduba mishi files ɗinsu, tabbas yasan yaran, waɗanda Omar ya taimaka daga wurin Police, ranshi ne ya bashi cewa may be Omar yasanar mishi game dasu ne that's why yake neman Information akansu , without wasting time Babban likita ya binciko masa files ɗinsu Hosana Da jahad na rashin lafiyarsu duka bayanan ya masa snaping dinsa ya tura masa ta whatsapp ɗinsa,

 bayan sun kammala phone ɗin, Sgr ya shiga whatsapp ɗinsa ya duba, sai ga Files ɗin yaran na rashin lafiyarsu raɗau da sunansu ajiki Hosana Sayyad Da Jahad Sayyad, 

   Ajiyar zuciya yasaki yanzu ya shaida maganar Yarinyar duba time yayi dare yayi ga wani bacci daya ke ji gashi ko dinner ɗinsa bai cin ba, Ga yarinyar nan dake tsaye duk a tsorace don yana ganin yadda yatsun ƙafarta ke kerma,

    gyaran murya yayi sannan yace "You're not guilty of anything, the mistake you made shine shiga na maza after knowing that it is forbidden in Islam for a girl to dress like a male,' yayi maganar yana danna wayar hannunsa...

   Murya na rawa Sehrish tace "bazan ƙara ba........' 

   Jinjina kansa yayi kafin yace"As from now i don't wanna see u wearing this dress again! u can go" ya bata Umarni ta tafi

    Wayyo Allah sam sehrish ta gaza rufe bakin ta don mamaki, kama hanyar fita tayi tana waiwayansa da kansa ya shiga saving dinner ɗinsa yana ci,

   Tsantsar farin ciki ne ya cika sehrish sam ta rasa inda zata tsoma ranta, ae tana fita daga part ɗinsa ta buga Wani uban tsalle na murna fuskar nan kamar wacce akayiwa Albishir da gidan Aljanna, watsa wa tayi da gudu gudu sauri sauri tana tattaka Stairs ɗin tana saukowa down a babban falon dama ba kowa nan fa tashiga rawar murna tana zagaye sofas ɗin dake a falon kamar wata yar baby, 

    Duk wannan abun da take yi akan idon Sgr domin kuwa ya biyo bayanta ashe yana daga can Upstairs yana kallonta, don bai cika yarda da mutane ba shiyasa yayi following back ɗinta don yaga reaction ɗin da zata yi bayan da ta fita daga part ɗinsa,

  abunda yayi tsammani ba shi ya gani ba,  zura hannayansa yayi cikin aljhun wandon baccinsa yana kallon Ikon Allah, 

   Sam sehrish bata son babban yaya yana kallonta ba, ita kaɗai tasan farin cikin da take ciki, ta jima tana mamakin yarda Sgr ya kasance mai matuƙar sauƙin kai har haka a tunaninta zai bata horo mai tsanani daga nan akore ta kuma daga gidan,

   Nace "*Sehrish ba ke kaɗai ba hatta Hafsat bature da sauran makaranta labarin rayuwarki sunyi tsammanin hakan tabbas Surgeon general Rafayet ya bamu mamaki, haƙiƙa shi ɗin na daban ne*"😍

Yanzu abunda ya rage wanda take yi ma fargaba shine sauran matasan gidan shin zasu amince a ranar da ta bayyana kanta a matsayin mace !? Uwa uba Abban su,kuma tuna wannan yasa jikinta yin sanyi, dakatawa tayi daga yin wasan da takeyi na zagaye gujerun babban falon, jiki a mace ta kama hanyar bedroom ɗinta, ranta ne ya bata cewa akwai mai kallonta, Cikin sauri ta juya ta kalli upstairs a time ɗin har sgr yabar wurin ya koma part ɗinsa

    Ganin wayam yasa ta sauke ajiyar zuciya,ba ɗakinta ta wuce ba ɗakin aunty azmee ta wuce don sam tagaza daina murna tafison ta sanar mata abunda yafaru yau ɗin nan da zafi zafinsa,

   Haryanzu hannunta na ruƙe da hularta da mayafin duka ta ƙanƙame su, tsayawa tayi a ƙopar ɗakin tana bubbugawa ,


Azmee dake zaune saman darduma tasha hijabi ajikinta ga qur'ani agabanta hannunta kuma na riƙe da Cazbaha sai faman gyangyaɗi take yi, jin bugun ƙopa yasata cewa "Wanene"

sehrish dake tsaye a bakon ƙopan tace"Nice aunty azmee"

  Murmushi azmee tayi tare da cewa "Ashe bakiyi bacci ba," tayi maganar tare da tashi daga dardumar ta buɗe mata ƙopa,

  Shiga ciki sehrish tayi tana faman zabga murmushi,

  a ɗan ruɗe azmee ke kallonta bayan ta rufe ƙopan tace"Yau wata rana! Sehrish kece da Murmushi haka a fuskarki? Wane albishir ne akayi maki?Cos I forgot when last naga wannan annurin a face ɗinki" cikin mamaki azmee ke wannan maganar kafin ta mayar da idonta kan Hular sehrish dake ruƙe a hannunta ta kuma cewa "Ikon Allah yau kuma hularce da mayafin duka a hannu?

  Dariya kawai sehrish take yi daker ta tsagaita tace "Aunty azmeee abun mamaki! Abun farin ciki !"

   Cike da ɗoki azmee tace "menene shi?

    Nan sehrish ta shiga zayyana mata abunda ya faru tsakaninta da Babban yaya daga farko zuwa ƙarshe

 Baki washe azmee ta ɗaga hannunta sama tana cewa "Alhamdulillah ! Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah subhanahu wata'ala naji daɗin wannan lamarin sehrish domin kuwa Babban yaya shine nafi ji dama, gashi kuma cikin sauƙi ya amince wayyo Allah murna bansan inda zan sa kaina ba don daɗi" cike da jin daɗi azmee ke magana fuskarta a washe

   Sehrish tace "Amma aunty azmee su fa sauran kina ganin zasu amince in suka sani"? Ni ina tsoran ta yarda zan fara fitowa a matsayin mace cikin gidan nan," tayi maganar murya asanyaye tana kallon azmee

    Ƙarasawa azmee tayi ta dafa kafaɗarta sannan tace "Sehrish matsalarki tazo ƙarshe! tun da har babban yayansu ya amince ba ki da sauran damuwa, Abbansu ne kawai zamu jira muji ta bakinsa, yanzu abunda nake so dake kije kawai ki kwanta kiyi bacci zuwa gobe zamu ga yadda badaƙalar zata kaya idan matasan gidan nan suka ga tukur mai aikinsu a matsayin Mace lallai akwai tashin hankali, " azmee tayi maganar da dariya a fuskarta, sehrish kuwa dafe saitin zuciyarta tayi tana zazzare ido tace "Allah sa su amince suma,"

   "Insha Allah" azmee tabata amasa afterwards suke yi sallama, sehrish ta koma bedroom ɗinta cike da zullumi haye wa tayi saman gadonta, ta janyo pillow ta rungume tana sakin murmushi tunawa da haɗuwarsu ta yau da babban yaya, Allah kenan a daren nan Haroon ya ƙuntata mata, har tayi addu'ar sai Allah ya nuna masa Iyakarsa akanta, to yanzu ga Iyakar tasa nan muddin sauran suka amince da ita kuwa, taci alwashin sai ta Ci mutuncin Haroon 😡👊 

A fili tasoma magana " gajan haƙuri kenan Irin na ɗan adam, yanzu da na kashe kaina da shikenan nayiwa kaina, ashe Allah yana dab da kawomin sauƙi arayuwata," ta faɗi tana faman murmushi wani irin nishaɗi take ji ayau , ta kuma cewa "Anya ma zan iya bacci kuwa? gashi ina fargabar mai zai faru gobe? kwara kawai nayi Bacci na goben tayi saurin yi, AYI TA, Ta ƘARE kawai🙅, In jalasa jalasa 😂 in Zahaba Zahaba shine kawai 😅😂😹😹😹


tana gama faɗan hakan bacci yayi awon gaba da ita, kai kana ganin yadda reesh ke bacci kasan tana cikin kwanciyar hankali,


 murmushi Hafsat Bature tayi tana kallonta wadda ke tsaye shigowarta kenan ta window tabiyo da suffar Farar Tantabara kasancewarta Aljanar sehrish, hannu tasa tajanyo bargo ta lullu6e sehrish dashi sannan ta 6ace 6aaat..............😇

______________________________________


Kwance suke acikin store ɗin su biyu abunsu, kamar yadda Jahad ta saba yi musu dabara, na jera masu jarkoki su koma kamar single bed sai su kwanta suna facing ɗin junansu sam bacci yagaza ɗaukarsu zullumin su mai zai biyo ba? Wata alƙibla rayuwarsu zata fuskanta yanzu? 

  "Jahad idan Aunty hafsat ta zubar damu ina kuma zamu dosa"? Hosana ta tambaya tana kallon jahad wadda ta zuba mata ido,

   Cikin sanyin murya tace "Nima kaina bansani ba hosana, ina tsoran hakan," ta faɗi zuciya a karye

  Hosana tace "Dama Allah ya ɗauke mu yakai mu duniyar sama ko? ko duniyar taurari inda ba mutane muyi rayuwarmu mu kaɗai tare da yaya Omar tunda kowa baison mu shi kaɗae ke son mu ko?  

  Wannan maganar ta hosana tasa jahad fashe wa da dariya daga kwancen da suke ta rinƙa 6a66aka dariya kaman kamar me,

  Hosana ta ɗan 6ata fuska don ita bada wasa tayi maganar ba,

  Daker jahad ta jinkirta da dariyar tace "Sorry hosana dole nayi dariya mana, wa kika ta6a ganin an ɗauke daga nan an kaisa sama ? 

Shiru tayi tana zumbura baki, jahad taci gaba da cewa "sannan kince tare da yaya Omar kaɗai zamu tafi saboda yana son mu, Shin kin manta da Sehrish ne"? Ita kuma fa? akwai wanda yayi mana wahala ne kamarta? sehrish tana son mu fiye da kowa na duniyar nan, saboda mu tashiga duk wani hali da take ciki ayanzu duk da bansan yaya rayuwarta take ba...............wani irin kuka ne yaci ƙarfin jahad har takasa ƙarasa maganar da take yi,

Nan take jikin hosana yayi mugun sanyi tunawa da Sehrish ƴar uwarsu mai tsananin son su da ƙaunarsu, tuni itama idonta sun cicciko da hawaye murya na rawa tace "Ya Allah hada sehrish za'a ɗauke mu akai mu duniyar Taurari.....' 

   dakatawa da magana tayi ganin Jahad dake kuka ta fashe da dariya, wato tayi tazarce daga kukan da take Zuwa dariya ba don komai ba sai don jin abunda Hosana ke cewa, share hawayenta tashiga yi tana faɗin "Hosana wasan ya isa haka, muyi magana ta hankali, yanzu yaya za'ayi yaya Omar yasan halin da muke ciki kafin Hafsat da Momynta su sa azubar damu yakamata muyi tunanin hakan in ba haka ba zamu shiga wani mugun hannun ne ko mu ƙare rayuwarmu adaji..............' jinkirtawa tayi da maganar tana sauraron shawara daga wurin hosana,

   "To ya zamuyi mu sanar mishi jahad? Bayan kullum waccen matar mai kama da samudawa mai kumatun alkubus tana tsare mu da ido duk in yazo tana hanamu kwakkwaran motsi," 

  Shiru jahad tayi tabbas dole su nemi mafita in ba haka ba, zasu fuskanci tashin hankali

   Can tayi wani dogon tunani tace "Hosana mai zai hana, mu samu paper da biro sai mu rubuta mishi, in yazo sai ki lalla6a kisan yarda zakiyi ki tura masa a aljihunsa? Ko da rungumesa ne sai kiyi kamar yarda kikayi a asibitin nan kin tuna"?

  Murmushi hosana tasaki anzo inda keyi mata ƙaiƙayi kallon jahad tayi tace "Shawara mai kyau, amma taya zamu rubuta mishi to? Bamu da paper ba biro jahad," 

    Shiru jahad tayi kafin tace "Akwai !!! Na tuna acikin wannan ɗakin da Momyn hafsat takaimu acikin wannan ƴar lokar naga Memo da biro," 

   Cike da farin ciki hosana tace "dama ƙopa a buɗe take, yau ta manta bata rufe mu ba, jahad ki lalla6a ki ɗauko ki rubuta masa," 

  Miƙewa jahad tayi tana faɗin "Zan fita dan Allah hosana karki biyo ni, nasan halin ki, in kika ja asirin mu ya tonu kashin mu ya bushe mu duka," 

   Murmushi hosana tasaki tana cewa "sai dai in baki daɗe ba, kinsan ina jin tsoro fa nikaɗae anan,"

   "Karki damu yanzu zan dawo,"

"To shikenan," hosana ta bata amsa,

Ficewa Jahad tayi cikin sanɗa take tafiya babu kowa wayam sai hasken daya gauraye ko'ina, 

Wuce wa ɗakin tayi a hankali ta tura ƙopa tashige cikin hanzari ta nufi drawer ta zaro gidan farko ajikinta, anan taga memo ɗin da biron data gani, 

   Fiddo su tayi jiki na rawa ta aza memon asaman drawer ɗin dayake ƙaramace, daga zukunne jahad ta soma bude papers ɗin sannan ta aza biro ta soma rubutu kamar haka 

     _ya Omar naji ma inaso na faɗa maka halin da muke ciki, wlh bamu jin daɗin zama agidan nan, saboda basu son mu, uban aiki suke samu har bugun mu suke yi, dan Allah ya omar in kaga wannan takardar ka taimaki rayuwarmu kamar yarda kayi niya ka tafi damu inda kake rayuwa_

    Kamar daga sama Jahad taji ance "Sannu da Ƙoƙari"!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!

  Jin wannan maganar a bayanta yasa jahad dakatawa da rubutun da take yi, hankali a matuƙar tashe idonta sun firfirto azare, jikinta ya soma wata irin kerma, Tuni Zufa ta soma gangarowa daga fuskarta da jikinta don bala'e hatta paper ɗin da take rubutun asamanta ta jiƙe sharkaf da gumin da take fitarwa....

Domin sauke wannan littafin a wayarku danna download da ke kasa

Abban sojoji book 2


Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post