Ayyukan Wikipedia Da Mahimmancin Shafin Ga Hausawa

Ayyukan Wikipedia Da Mahimmancin Shafin Ga Hausawa

Ayyukan Wikipedia Da Mahimmancin Shafin Ga Hausawa

Baban burin Wikipedia shine samar da ilimi na kowani fanni ga masu karatu ko bincike don ilmantarwa da samar da bayanai na abubuwa daban daban da anfanar al'ummar duniya baki ɗaya musamman waɗanda basu da ikon zuwa makaranta kuma a kyauta ta hanyar amfani da fasahar zamani.  Ranar 15 Janairu 2001 ne aka ƙirƙira shafin Wikipedia a duniya, bayan kwana biyu da yin rijistan shafin a yanar Gizo (Internet) Jimmy Wales da Larry Sanger suka fara yin editin a shafin (wato sanyawa da ɗaura muƙaloli akan ilimi).

Daga farawarta, Wikipedia ta karaɗe duniya aka samar da ita cikin harsunan duniya daban-daban, haka yasa zuwa shekara ta 2006 Wikipedia ta zama mafi girman insakulofidiya a duniya baki ɗaya da kuma kasancewa ɗaya daga cikin shafukan yanar gizo guda 10 da aka fi ziyarta a duniya.

A zuwa watan Janairu na wannan shekara ta 2023, dukkanin shafukan Wikipedia na kowane harshe suna da jimillar muƙaloli sama da miliyan 61, wanda hakan yasa suke samun sama da mutane biliyan 2 masu ziyartar shafin a kowane wata da kuma samun yin editin a sama da miliyan 15 cikin kowane wata  (aƙalla 5.7 adadin edit ake samu a kowace daƙiƙa).

Wikipedia tana bada dama ga kowa da kowa don yayi rubutu a shafin ko ya gyara abinda wani ya rubuta, ko nazari da bincike kyauta don anfanar Al'umma. Wikipedia na shirya tarurruka na ƙarawa juna sani a kowacce shekara da ake kira da Wikimana da kuma ƙananan tarurruka da wikilan masu gyararta suke gudanarwa a sassan duniya baki ɗaya ciki har da Najeriya.

Wannan ayyuka na Wikipedia yana gudana ne cikin harsunan duniya mabambanta, sai dai harshen Hausa har yanzu na fuskantar ƙalubale inda akwai tarihi da al'adun mu da ilimomi da fasahohin Hausa har yanzu ba'a sanya su a shafukan ba don sanin su waye al'ummar Hausawa da inganta zaman takewa tsakaninsu da maƙwaftan su.

Don haka wannan babban dama ce ga kowa da kowa don ya riƙa ziyatar shafin don bincike ko saka ilimi aciki, wannan zai taimaka mana wajen rubuta tarihin mu na gaskiya da goge rubutu da aka yi akan mu na ƙarya.  Zaku iya tuntuɓar Gidauniyar Hausa Wikimedia Foundation a shafukan ta don neman ƙarin bayani da nuna maku yadda ake amfani da shafukan Wikipedia a kyauta


Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post