Wa ya Kashe Rukayya? Page 10

Wa ya Kashe Rukayya? Page 10

Wa ya Kashe Rukayya? Page 10

*WA YA KASHE RUKAYYA*?

*DAGA ALƘALAMIN*

*FIDDAUSI SODANGI*

*LITTAFAN MARUBUCIYAR*

1 Ƴar gata 

2 Aliya

3 Waheeda

4 A zumuntar mu

5 Real Amani

6 Kwadayi mabudin 

7 wahala.

8 Jawaheer

9 Ni da surukata.

10 Makira.

11 Ruguntsumi.

 12 Gimbiya Ameenatu

 13 Mugun tsartse.

  14 Muhibba.

  15  Dan hakin daka raina.

 16 Zamani.

  17 Mugun makoci.

  18  Har a zuciya.

  19 Kai ne gatana.

  20  Maryama.

  21 Kaine sanadi.

  22 Kaddara ta riga fata.

  23 Aminiyata ce.

24. Gobara daga kogi

25. Wa ya kashe Rukayya.

🔟

A ranar suma Aminan nata suka tattara suka dawo garin Kano tare da zuwa har gidan su Amal ɗin suka danka mata ɗiyarta Amatulla wacce ta ke ta zillo tunda taga uwar nata tana so ta ɗauke ta.

  "Congratulations Lailah, kawai sai ga ciki...."

  Dariya suka fashe da shi gaba ɗayansu banda Laila da tai kicin-kicin da fuska tana watsa masu harara.

  Amal tace "wlh ko idanuwanki zasu faɗo ƙasa sai mun faɗi ato"

  Nan ta fara kwaikwayon muryar Laila a lokacin da ta ke ce masu ita da yin ciki sai nan da shekara biyar ko shida lokacin ƴarta ta girma sosai.

   Dariya suka sake kwashewa da shi Rahma tace "waima ku tsaya wai kuwa kun lura da cewa Laila jarababbiya ce naga dai sau ɗaya kawai Faisal ya kawo mata ziyara a cikin wata ukun nan a zariya amma wai shi ne har tayi ciki daga haɗuwa ɗaya, Allah abin godiya".

  Ta ƙare maganar tana kwashewa da dariya.

Tsaki Laila ta yi tace "banzaye ƴan sa ido kawai".

Rukayya tace "To wai ku meye naku mace da mijinta ku ka sani ko akwai mai taya shi ban ruwan ne..."

Ahmad da baice komai ba tunda aka fara maganar sai yanzu ya magantu jin Rukayya za tai barin zance.

  "Share su Laila ai su ma dai auran nan zasu yi nan kurkusa ma kuwa insha Allahu, ke Amal ai kece abar a tausayawa dan Malan Alin nan da gani bazaiyi sauki ba".

"Uhmm Kanku ake ji dai"

Father ne ya shigo gaba ɗaya suka miƙe suka gaida shi Amal taje ta rungume shi cike da farinciki dan bata ganshi ba tun dazu da ta dawo ya fito sai yanzu.

   "Nayi kewar ka sosai Father"

  Ta faɗi tana sake shigewa jikinsa.

  "Nima nayi kewarki daughter ina taya ku murna congratulations once again "

"Thank you sir" suka amsa gaba ɗaya .

A hankali ya kai kallonsa kan Amatulla da ke ta wasa abinta, janye Amal yayi a jikinsa ya miƙa hannu ya ɗauki Amatulla da ke ta wangale masa baki.

  Gabansa ne ya yanke ya faɗi garin irin kamar da yarinyar ke yi da ɗiyar ta shi.

Kai tsaye ya aika masu tambayar gaba ɗayan su yana kallon fuskokinsu.

  "Ina ku ka samo yarinya haka?"

Amal ce ta sake matsowa kusa da shi tace "Father dama mun bari ne sai mun dawo gida gaba ɗaya sai muyi maka bayani"

Ahamd ne ya karbe zancan da cewa "Father tsintar ta muka yi a zariya wata uku kenan, wata rana munje Kaduna gaisuwar wani ɗan ajinmu da ya rasu munyi dare muna dawowa kawai motar mu ta lalace a wani daji, a lokacin ma ruwa ake muka firfito mu duba shine muka ji kukan baby da bamu so mu ɗauko taba saboda mun tsorata amma sai Amal ta bada shawarar dauko ta, to shi ne kawai muka dauko ta".

Wani irin kallo Father ke masu babu ko kiftawa dan dai shi sam bai yarda da zancan nasu ba mai kama da tatsuniya gashi kuma ko makaho ya shafa yasan yarinyar tana kama da Amal ɗin, amma kuma wata uku kenan da ƴan kwanaki rabonsa da diyar tasa kuma baiga wata alama ta ciki ko rashin gaskiya a tare da ita ba, kawai dai abin ya kulle masa kai ne.

"Uhmm to kun kaita wajan hukuma ne a lokacin ko ya akai?"

Rahma tace "A'a Father bamu je ba"

Sake jinjina kai yayi yace"to yanzu gidan marayu zaku miƙata ko?"

Da sauri Amal ta tari numfashinsa wajan cewa "A'a Father mun yanke hukuncin riƙe ta zamu kula da ita gaba ɗayan mu amma a wajena zata zauna".

Jinjina kai Father ya yi badan ransa yaso ba sai dan farinciki da ya ke  hangowa a idanuwan ƴar tasa game da ɗiyar.

       *BAYAN SHEKARA ƊAYA DA WATA DAYA*

 Amal taci gaba da rainon Amatulla cike da kauna da shakuwa irin ta ɗa da mahaifi Aminan nata suna taya ta kulawa da ita da hidimta mata ta kowace fuska.

Sun kammala shekara ɗayan su a law school harma an rantsar da su a matsayin lauyoyi masu hazaka a yanzu aiki ne kawai ya rage su fara.

A bangare ɗaya kuma Aliyu ya ci gaba da kafa kansa a wajan Amal tun tana sharesa hardai ta hakura saboda tsananin naci irin tasa a dole ta saki jiki suka fara zazzafar soyayya na bugawa a jarida.

Father ya yi farinciki sosai da wannan soyayya ko ba komai yarsa zatai aure a babban gida gidan mutunci karin daɗawa ma Aliyu na masifar sonta kamar ransa har mamakin irin wannan soyayya ya ke.

         *******

"Mum da gaske fa na samu matar aure zanma kawota ki ganta ta haɗu sosai ga hankali da natsuwa"

   Aliyu ya kare maganar yana kallon fuskar mahaifiyar tasa yana jira yaji abinda zata ce dan tuni ya gama maganar da mahaifinsa.

"Uhm ƴar gidan waye? Waye ubanta a ƙasar nan? Kuma a wani gari ta ke, meye matakin karatun ta?"

"Mum ba ƴar kowa bace marainiya ce a gidan marayu ma ta taso yanzu tana zama da uban rikonta a garin Kano, gidansu yana nan a GRA, matakin karatu lauya ce basu dade da gamawa bama, na haɗu da ita lokacin da nayi aikin nan a ABU Zaria.

Yamutse fuska tayi tare da galla masa harara tace "Yanzu Aliyu irin matar da ka ke so ka aura kenan? To ni batai min ba bana sonta babu ruwana da wata wai lauya ce batai ba, duk matan da ke Abujan nan ka rasa inda zaka samo mata sai yar gidan marayu?".

  Ta kare maganar a fusace cike da kyankyami da kuma tsanar da taiwa talaka.

"Mum ina sonta sosai ina kaunar ta kuma nasan kema zaki so ta idan ki ka ganta, sannan kuma zatai maki amfani a siyasarki kasancewarta na lauya dole zaki bukaceta.

   Daga haka ya mike tana kwalla masa kira amma bai tsaya ba.

Safa da marwa ta shiga yi a cikin palon tana ta jan tsaki haɗe da ƙwafa.

  Daga ƙarshe ta nufin bangaran mai gidan ta iske shi kishingide yana hutawa.

"Yanzu Daddy kana kallon abinda Aliyu ke niman aikatawa baza ka tsawatar masa ba zaka turo min shi".

  "Yanzu duk yan matan duniya Aliyu ya rasa wacce zaice zai aura sai yar gidan marayu wacce batada wani cikakken asali, nifa tun sanda na fahimci ya faɗa soyayya kullum yana hanyar Kano nasa akai min bincike akan yarinyar kuma nasan komai akanta babu abinda ban sani ba dan haka ni dai ban amince da wannan auran ba in dai da yarda ta za ayi".

"Nafisa wai menene abin tada jijiyar wuya akan abinda shi da kansa yaji ya gani yace yana so a haka? Kindai san babu yadda za ai Aliyu yayi abu haka nan kai tsaye ba tare da bincike ba, ba a jayayya da lamarin aure baki san abinda Allah ya boye ba, shawarar da zan baki shi ne ki kwantar da hankali ayi abinda ya kamata kindai san halin ɗanki idan yaso abu".

       ******

Cikin faɗa Amal tace "Wai lahiya kuwa Ruky kin saka mun haɗu gaba ɗaya amma kinyi shuru kina ta kallonmu"

Rahma tace "Ni sai naga ma kamar bata hayyacinta, ke wai ko kin shawu ne?"

Laila wacce watan ta biyar kenan da haihuwa inda ta samu ɗa namiji ta kyalkyale da dariya tace "ji wani iskanci wai ko kin shawu ne".

Ahmad ne ya ɗan dafa kafaɗun Rukayya yace "Ƴar uwa gaya mana mike faruwa kinji?"

Ajiyar zuciya Rukayya ta sauke ta jawo system din da ke gabanta ta kunna masu, gaba ɗaya suka zurawa system din ido suna kallon video din data kunna masu.

Wata mata ce sanye da kayan asibiti ta ɗauko baby tana ta kalle-kalle alamar rashin gaskiya har zuwa sanda ta bar Asibitin da alama bata san akwai cctv ba a cikin asibitin da harabar asibitin ba dan kuwa ko lullube fuska batai ba tas ake ganinta.

Kallon kallo suka suma bayan ƙarewar video ɗin. Amal ta kalli Rukayya tace "To meye ma'anar wannan video ɗin ni dai ban fahimci komai ba sannan kuma ku kalli date din 2021 kenan abin ya faru ne shekara biyu a baya to mu meye haɗin mu da wannan Rukayya"

Ajiyar zuciya Rukayya ta sauke tace "Me ki ke ci na baka zuba ai ba shi kenan ba".

  Nan ta sake saka masu ɗayar video din, shi kuma wata mata ce ke kuka tana faɗin "Ƴa tace ita kenan Allah ya mallaka min ta saceta kuma ta gudu a yau ƴan sanda suka tsinci gawarta a wani daji a zaria dan girman Allah duk wanda yaga wannan yarinyar ƴata ce ya taimaka min domin Allah ga hotonta nan"

  Sai ga hoton Amatulla tana ƴar wata shida rangaɗadau ya fito tas a jikin hoton. Tana ta kuka tana sake rokon wanda yaga marainiyar ƴarta ya taimaka mata, nan ta bada number da za a iya samunta da shi daga nan kuma video ɗin ya kare.

Ajiyar zuciya suka sauke gaba ɗayan su suna kallon juna ba tare da kowa yace uffan ba.

Rukayya ce ta yanke masu shirun tace "A YouTube naci karo da shi ɗazu ina duba wani abu, a tun lokacin da abin ya faru aka saki video din amma dukkan mu babu wanda Allah yaba ikon gani sai ɗazu dana ganshi".

Amal ta katseta da faɗin "To shi ne me? Meye abin wani ɗaga hankali anan kedai kinsan ko giyar wake muka sha baza mu kai yarinyar nan ba, dan kuwa wlh kama mu za ayi ba dan komai ba sai dan gawar wancan matar, yau da ace kawai tsintar ta mukai sai muje mu kaita amma babu abinda zamu iya yi yanzu saidai kawai tayi hakuri saboda anan ma muna kulawa da yarinyar kuma ina sonta ina kaunar ta fiye ma da yadda uwar nata ke sonta".

Haka sukai ta tattaunawa daga karshe suka zabi yin shirun kawai dan suna ganin shi ne mafi alkairi a garesu gaba ɗaya.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post