Daudar Gora book 2 page 49

Daudar Gora book 2 page 49

 

Daudar Gora book 2 page 49

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲      

  ✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨

           (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)

            𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (49)

........Ƙyaƙyƙyawan bowl ɗin data ɗauro saman tray mai ƙyau shima da tambulan ɗin madara yabi da kallo. Ta ajiye a saman ɗan table ɗin data janyo kusa da gadon kasancewar a baki-baki ya ke zaune shi ta ɗaura. Bowl ɗin ta buɗe tana ɗan kallonsa ƙasa-ƙasa kamar yanda yake binta da shegen kallon nan nasa. A saman lips ta furta “Kana son shi?”. Gasashen naman da ke ta tashin ƙamshi mai tada kwaɗayi ya ɗan kalla. Batare da yace komai ba ya kamo hanunta da ke riƙe da murfin ya zaresa ya ajiye. Riƙota yay ya zaunar a kusa da shi. “Sai dai in zaki bani da kanki. Hannuna ciwo suke min”. Yanda yay maganar acan ƙasan maƙoshi matuƙa ya sata kallonsa da sauri, ido ɗaya ya kashe mata da sakar mata wani lalataccen murmushi daya nema raba jikinta na numfashinta. Da sauri ta maida kan ta risinar zuciyarta na wani masifar harbawa da sauri-sauri. 

      Hannunta ya riƙo cikin nasa ya ɗan murza yana ƙara narkar da idanunsa kan fuskarta. Cikin sake tausasa harshe da cigaba da murza hannun ya ce, “A duk lokacin da kike tare da Eshaan ki kallesa abokin ki, amininki, yayanki, kai harma ƙaninki idan ya kama, sannan farin cikin ki. Ina son gidana da iyalina su kasance aljannar duniyata da duk inda naje na dawo da damuwa za'a goge min shi da farin ciki, duk sanda kaina ya ɗauka zafi za'a sanyaya min shi da nishaɗi. Duk sanda na shigo da farin ciki za'a tayani yi har ma a ninka min shi da wani da yafi wanda nake tare da shi. Anan Eshaan sunansa Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed MIJIN Fhareedah (Iffah) bint Zayyan ba Tajwar Eshaan ko Shahan-shan ba. Ki raineni kamar jariri a fadarki, Ni kuma mai sallamawa ne gareki duk rintsi TAURARUWA TA”. 

        Wata irin nutsuwa ce ke ratsa mata zuciya, tabbas tana jin daɗin kasancewa da shi, amma har yanzu bata san mi takeji game da shi ba. Ita dai kawai yana burgeta, a cikin ado ko saɓanin hakan. Sannan duk da taji ciwo da a jikinta da jigatuwa a jiya batajin haushinsa ko jin bai ƙyauta ba, dan koba komai tayi ilimin addini, tasan hakkokin mace akan mijinta, tasan hakkokin miji akan matarsa, tasan muhimmancin aure da fa'idarsa. Ta kuma san Shahan-shan bazai taɓa sakinta ba koda ace zata buƙaci haka. Mammy ta sake tisa mata fiye da abinda ta sani, har ma da wanda zatayi domin tabbatar da kanta a matsayin ɗiya MACE a gabansa ko gaban waninsa.

      “Wayyo!”.

   Ya faɗa yana matse ciki, da sauri ta kallesa. Ya yamutse fuska kamar gaske shi adole yunwa yake ji. 

           Cike da nuna damuwa ta ce, “Sorry”. Sai kuma ta ɗakko tray ɗin saman cinyarta. Cokali ta ɗauka zata ɗiba naman ya riƙe hannun. Kallonsa ta sakeyi da mamaki. Cikin ɗan ɗage gira ya ce, “Nikam da hannu nake so”. Komai batace ba ta ajiye cokalin kawai, tare da ajiye trayn ta miƙe, bayi ta nufa bata wani jima ba ta dawo da alama hannu ta wanko. Tray ɗin ta sake maidawa saman ƙafarta bayan ta koma inda ta tashi ta zauna ta ɗebo naman ta kai bakinsa. Hannun ya riƙo da ƙyau ya ƙarasa da naman bakinsa yana lumshe idanunsa, harda sakin siririyar ajiyar zuciya. Ita sai ma abin ya bata dariya harda murmusawa. 

      Wani irin sanyi da nutsuwa yaji har cikin ranta ganin tayi murmushin. Dan gaba ɗaya yau bakin ya mutu kamar ba ita ba, shi kuma yafi son yaga ta saki jiki da shi tana ƙiriniyarta da surutu kamar da. Sosai yaci naman har hakan ya bata mamaki, hakama madaran. A hankali ta rumtse idanunta sanda yake tsotse yatsun hannun abin kamar da gayya. Da gayyar kuwa yake yi, dan yana kallon yanda take faman matse ido yana murmushi a zuciyarsa....


      Bai bar ɗakin ba sai da ana kiran sallar magriba. Yace ta shirya kafin ya dawo zata rakasa wani waje. Da to ta amsa masa kanta a ƙasa, dan duk wannan abun da ake bata yarda su haɗa ido sai da kuskure. Bayan fitowarsa alwala a bathroom har ya wuceta ya dawo da baya, kama ta yay ya miƙar tsaye da ga zaunen da take. Fuskarta ya ɗago dan taƙi yarda ta kallesa, shima bai matsa da sai ta kallesan ba ya manna ma goshinta sumba mai lafiyar da har sai da ta sanya jikinta motsawa. Idanunta a rufe har sai da ya fice sannan ta buɗe tana sauke nannauyar ajiyar zuciya, ita har yanzu ta kasa sabawa da salon nasa sam.

         Sai da ta ɗan ƙara gasa kanta kamar yanda Mammy tace ta dinga yi akai-akai sannan tayo alwala ta fito gabatar da sallar magriba. Bayan ta idar zama tai tunani mai zurfi akan Tajwar Eshaan, mutum nan nada abubuwan ban mamaki ɓoyayyu, tabbas ta yarda hatsabibin kansa ne kamar yanda su Miran Arshaan ke faɗa. Gaskiya tana buƙatar sanin yanda akai su Babiy suka kasance a wata ƙasa bayan su Miran Jasim sun mata ƙaryar ya kashesu. Kenan video ɗin data gani jabu ne ko mi?. Rashin amsa da buƙatar samunta ya sata miƙewa ta gabatar da sallar isha'i da ake kira. Bayan ta idar ta shiga gyara jikinta dan haka kawai take ɗokin fitar duk da bata san ina suka nufa ba. Tsaf take cikin ɓakar doguwar rigar abayar datai mata ƙyau, sai veil ɗin nan da in aka naɗa yake yi kamar baby hijab fari. Fitowa tai tsabar zumuɗin son fitar ta su. Ɗakin da suka kwana ta nufa duk da bata zaton ya isa dawowa salla.

     Kusan a tare suka ɗaura hannayensu kan handle ɗin ƙofar, ita ta tura shi kuma ya ja batare da kowanne yasan da ɗan uwansa ba. Cak ta tsaya kanta a ƙasa tana mai rumtse idanunta dan wata irin kunyarsa takeji har cikin ƙashinta. Ga kwarjini mai irin mamaye waje ɗin nan da ya ƙara mata. Kusan minti ɗaya suka kwashe a wajen ita bata tanka ba shima bai ce ba. Tasan in zasu kwana ma zai iya, dan haka ta ɗan saci kallonsa ta gefen ido. A hankali ta janye idanun nata ganin yanda ya kafeta da shegen kallon nan nasa mai hanata sukuni. Sai ta samu kanta da in inar faɗin, “Barka da dawowa”. Ƙaramar ajiyar zuciyar da bata ji ba ya yayi a ciki, batare da ya amsa gaisuwar tata ba ya ƙarasa fitowa, fuskar babu fara'a sam kamar ko yau she, sai wani irin ƙwarjini mai cika idon mai kallo, a fisge ya furta, “Muje” yana raɓata ya wuce cike da takun nan nasa ɗaɗɗaya. A hankali ta ɗan sauke numfashi dan jinta take kamar an ɗaureta a wajen, sai kuma ta bisa da kallo ƙasa-ƙasa tana mai tsarkake sunan UBANGIJI mahaliccin wannan ƙyaƙyƙyawar halitta. (Ƙyau dai kam ALLAH ya bashi, sai dai miskilancin nan da jin kai ɗin nan da ke zagaye da shi) ta ɗan narke fuska kamar zatai magana, sai kuma ta fasa ranta fal tunanin ina ma zasu je a daren nan?, rashin mai bata amsa ya sata ɗan zabura tabi bayansan. Ganin ya nufi lift.. taji duk ta tsure. Ita dai harga ALLAH abin nan baya wani birgeta. Dan indai ta shiga sai tayi hajijiya. Shiyyasa ya zamto sai ta riƙe wani dan batama taɓa gigin shiga ita kaɗai ba. Jiki a saɓule ta shiga, jin ƙofar ta rufe kanta ta rumtse idanu da sauri, sai kuma ta buɗe akan yatsansa da ke ƙoƙarin danna inda yake buƙatar suje. “ALLAH ina jin tsoro” ta faɗa kamar zatai kuka. Sarai ya jita, amma sai bai nuna yaji ba ya gyara tsaiwarsa bayan ya danna 2 floor. Iffah da ke jin kamar ta fasa kuka a hankali tai yunƙurin zamewa dan gara ta zauna zai fi mata sauƙi. Babu zato taji an riƙo mata hannu, kafin ta iya ko buɗe idanunta tajita cikin jikinsa da ke fidda wani irin sirrintaccen ƙamshi mai ratsa zuciya da ɓargo da bazata taɓa iya mantawa ba. Da sauri ta buɗe idanunta sai ko cikin nasa da ke kallonta, dole ta maida nata ta rufe da sauri zuciyarta na wani irin bugawa da sauri-sauri, tabbas bazata mance wannan turaren ba, dan turarene da ta dinga fafitikar nema a washe garin da aka ɗakkota da ga sashenta cikin dare aka maidata nashi. Kenan da gaske shi ɗinne ya je ya ɗakkota kokuwa yaya akai? Dan wannan ƙamshin dai shine. Tsaf ya fahimci inda ta nufa, kuma a randa ta dinga neman turaren ya sani sarai, abinda bata sani ba ya ajiye abinsa ne kawai inda bataima zaton ganinsa ba ko kawowa a ranta zai ajiye ɗin. 

        “Zamu kwana anan ne?”. Ya faɗa a ƙasan maƙoshi yana kallon ƙyaƙyƙyawar fuskarta da ke kwance a kan ƙirjinsa. Idanun ta buɗe, sai kuma taja jikinta baya kunya na wani mamayeta. Ɗauke idanunsa yay da ga kallonta ya fice, itama sai ta bisa tana sauke ajiyar zuciya a jajjere, sai kuma ta saki murmushi dan ita da kanta kunyar kanta taji. Wata hanyar da batama san da ita a wajen ba suka nufa, koda yake bawai ta taɓa shiga wani waje a floor 2 ɗin nan bane bayan falo, shima a randa Malikat Haseenat ce ta kawota da suka biyo komai daki-daki ba kamar yanda yay ba yanzu.

        Inda suka shigo ɗinne ya sakata tsayawa turus tana kallonsa. Sai kuma ta ɗan waiga ta kalli hanyar da suka fito, ita fa gaba ɗaya notikan kanta sun kwace, ta ma rasa ta yanda zata misalta ta inda wannan hanyar ta ke a zahirin cikin gidan, dan ita shaidace tsakanin sashensa da na Malikat Bushirat akwai nisa. Duk da sunyi ƴar tafiya suma amma sai gasu cikin sauƙi. Kallonsa tai fuska a marairaice kamar ba Iffah'r nan matsiwaciya ba da ya sani ta ce, “ALLAH tsoro nake ji”. Kallonta yake da shanyayyun idanun nan nasa masu kaifi kamar bazaice komai ba, sai kuma jitai a hankali kamar mai raɗa ya furta, “Nima tsoron nake ji ai”. Idanu ta ɗan waro alamar mamaki tace, “Kai ɗin?”. Kansa ya ɗan kaɗa mata da lumshe idanunsa ya buɗe duk a lokaci ɗaya. Sai kuma ya kai hannunsa kan nata ya matsota jikinsa. “Ki ƙaramin ƙarfi”. Ya faɗa yana rungumeta cikin jikin nasa. Daburcewa tai ma ita gaba ɗaya. Tai ƙoƙarin ɗagowa ya hana hakan. Dole ta haƙura tai luff tana mai shaƙar ƙamshin da jikinsa ke fitarwa mai azabar daɗi. Kusan minti biyu suka kwashe a wajen kafin ya ɗagota a hankali, ƙin yarda tai su haɗa ido sam, shima sai bai matsa ba ya ja hanunta kawai yana ɗan murmushin da iyakarsa maƙoshi suka shige.........✍️


           

_🚴Babbar magana, ga Malikat Bushirat ga Iffah yaya wasan zai kaya🥱_



   

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*


*DAUDAR GORA Billyn abdul*


*KI KULANI hafsat xoxo*


*A RUBUCE TAKE Huguma*


*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*


*IDON NERA Mamuh ghee*



_LITTAFI DAYA: 400_

_LITTAFI BIYU: 600_

_LITTAFI UKU: 800_

_LITTAFI HUDU :1000_

_LITTAFI BIYAR: 1200_


_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_


_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_


_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_


_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_


_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_


_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_


ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN


MARYAM SANI

ACCESS BANK

0022419171


SAI A TURA SHAIDAR BIYAN 


09033181070


IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA


09166221261


*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*


+227 96 09 67 63


Books biyar  1250CFA

Books hudu  1050CFA

Books uku  850CFA

Books biyu  650CFA

Bookk daya  450CFA


KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post