A RUBUCE TAKE (K'addarata) book 2 page 28

A RUBUCE TAKE (K'addarata) book 2 page 28

A RUBUCE TAKE (K'addarata) book 2 page 28

 *H U G U M A*

*Arewabooks:Huguma*


*_A RUBUCE TAKE_*

       (K'addarata)

            Part 02


Page 28        Ba kowa a falon,saita saka kai zuwa bedroom dinsa,ta isa bakin qofar ta murdata ta tura tana saka kanta ciki.


          Dai dai sanda yake  tsaye gaban madubu yana goge kansa da fuskarsa da qaramin towel,ya qurawa fuskarsa idanu da kyau,sai kace wanda yake karantar wani sabon abu daya tsiro masa a fuskar,saidai duka ba haka bane, zuzzurfan tunani da ya cika zuciyarsa fal.


            A hankali idanunsa suka sauka akanta ta cikin madubin dake gabansa,amma sai ya janye idon yayi kamar bai ganta ba yaci gaba da goge jikinsa.


            Ko sau daya a tsahon zamansu bata saba ganin haka ba,don haka bata kawowa ranta wai ya ganta ba,saita fara takowa cikin shagwabar nan tata data saba masa tana cewa


"Ya da haka uncle?" Ta fadi tana kebe fuska kamar zata sakar masa kuka,duk kuwa da cewa ranta cike yake fal da wasi wasi.


          Bayajin zai iya kallon fuskarta a sannan,saboda wasu abubuwa da zuciyarsa ke sake saqa masa a kanta,sai ya barta bai tanka mata ba,har ta iso bayansa,ta rungumeshi tsam ta bayan,tana dora hannuwanta saman ruwan cikinsa.


         Qamshin turarenta da abaya yafi qaunar ji fiye da komai,a yanzun sai yaji dadinsa yana sauyawa zuwa wani abu da yafi qyama hadi da tsanar shaqa


"Uncle?" Ta sake kiransa a shagwabe,kanta kwance a gadon bayansa.


            Ajjiye towel din hannunsa yayi saman madubin,sannan ya saka dukkan hannuwansa biyu ya zare hannunta dake saman cikinsa,har zata fara masa tabarar tata ya waiwayo suka hada ido,sai tayi sak tana kallonsa.


          Wani abu take gani yana wulgawa cikin qwayar idonsa, irin abinda bata taba gani atare dashi ba,wani irin kallo da ya sanyata jin ta muzanta gaba daya,kallon da ya sakata ta daburce ta kuma rude,sai kuma ya dauke kansa daga dubanta ya taka gaba zuwa wajen drower dinsa don ya fidda kaya,ta taka da hanzari ta cimmasa,ta kama murfin drower din da nufin budewa ta zaba masa kayan kamar yadda ta saba masa amma sai ya dakatar da ita da kakkausar muryarsa


"Stop,bashshi kawai" abinda yayi mugun sanyaya mata jiki,yau me ya samu uncle?,me ta aikata masa yake zuwa da baqin halayen da bata taba ganin irinsu tattare dashi ba.


           Tsabar mamaki yasa tayi sakato tana kallonsa,har ya ciro kayan ya dawo gefan gado ya fara fidda na jikinsa don ya saka wadan nan.


            Har yau bata iya kallonsa naked don haka ta russunar da idanuwanta,amma jin muryar hafsat daga falo tana doso dakin ya sanyata zabura ta isa gabansa,ta dauki rigar ta fara ware masa fuskarta qunshe da murmushi tana jira ya gama saka boxer din ya karba,a haka idan ka kallesu saika dauka soyayya ake bugawa a lokacin.


          Sak hafsat din tayi wani idin abu na bugunta


"Kan jar uba!,kada dai ace wannan plan din ma score zero point," shine ya fara zuwa mata ka,da kuma irin kudaden xaga narka.


           kamar ta juya da tea flask din kuma saita fasa ganin ya ganta,ta tufa qofa ta shiga idonta akan widad da babu alamun akwai abinda yake damunta.


          Cikin son nuna bariki ta qaraso cikin daki


"Gashi abban mimi,akwai wani abu da kake buqata kuma?" Kai ya girgiza mata,saita jinjina kai


"Alright,idan akwai sai kayimin magana" 


"Thanks" kawai yace muryarsa can qasa, saita juya tana ficewa kamar babu abinda ya dameta dasu,saidai can qasan ranta tana jin kamar ta juyo ta dawo cikin dakin ta kora widad din.


"Ehen......yauwa uncle,ni zan saka maka da kaina please,ka barni na samu wannan ladan" ta fadi a shagwabe da qarfi tana kallon bayan hafsat,dai dai sanda taga tana shirin ficewa a dakin.


           Aikuwa maganar ta daketa sosai,don da qyar ta iya cinyewa bata waiwayo ba,saita dan qara sauri cikin tashin hankali ta fice ta isa sassanta.


           Kallonta yake kai tsaye cikin idanunta,yasa hannu ya damqe rigar dake hannunta


"Jiya ina kika je?" Gabanta ya fadi,wani tsoro da shakkar gaya masa ya kamata,saita saki murmushi


"Jiya?,bako ina,ina gida" idanunsa duka ya lumshe


"Ya Allah,ta tabbata......lallai ta tabbata"


"Please do me a favor" ya furta idanunsa a lumshe ba tare daya bude ba,don bayason kallon fuskarta kwata kwata


"Name uncle?"


"Stay away from here,i need space" gaba daya sai jikinta ya hau rawa,to amma saita hanawa zuciyarta samun rauni


"Ok shikenan" ta sakar masa rigar ta juya a sanyaye,harta kusa fita ta jiyo lallausar muryarsa yana cewa


"Karki matsawa kanki,ki kwanta a sashenki kiyi baccinki" da qyar ta hadiye wani abu da ya taso mata,ta gyada kai ba tare data juyo ba ta fice da sassarfa.


            Sai daya tabbatar ya kulle sashen nasa sannan ya dawo ya zauna,wani baqinta na sake ninkuwa a ransa,zarginsa kuma na sake tabbata, widad da baisanta d qarya ba ko misqala zarratin yaushe ta fara qarya?,lallai akwai qamshin gaskiya a dukka abinda yake zargi.


               Wata baqar zuciya da baisan ta inda ta shiga qirjinsa ba ta dinga kambama abun tare da qara masa muni a idanunsa,wanda daga qarshe ta tayashi yanke mummunan hukunci akan widad din.


            Karon farko a rayuwar aurensu da Wani abu me suna bacin rai da batasan ta inda ya samo asali ba ya raba makwancinsu a ranar da yake girkinta ne,ranar da babu ranar da uncle din yake zumudin zuwanta irinta,ta rungume affan tsam a qirjinta tana ta juyi,ta lalubi bacci kaf a idanunta ta rasashi,ba irin tunanin da baizo kanta ba,amma saita taushi zuciyarta take gayawa kanta wata damuwa yake ciki wadda qila bayaso su sani,tunda a gabanta hafsat ma ta fice,amma bataso haka ba,batason ya dinga aje damuwa a ransa,tafison suci gaba da sharing problems dinsu tare suna samo solution yadda suka fara tun farko.


          Sai tsakiyar dare ta samu bacci ya dauketa,kiran sallar farko kuma ta farka a firgice saboda wani mafarki mara dadi da tayi,sanda ta idar da sallar asuba ta fuskanci saqo ya shigo wayarta,data duba saita saki murmushi,zuciyarta na saki daga damuwar data kwana cikinta,ranta yana mata fari sosai


_ki shirya around 10 zaki rakani katsina,wani aiki ya tasomin,but basai kin shigo ba,idan kin shirya kawai ki fito gaba daya_


           Dadin da taji a ranta yasa ta miqe tun lokacin ta fara shiri,ta fara da hada masa lafiyayyen breakfast,farfesun kaza da yaji spice masu dadi,sannan ta masa hadadden spicy tea,gefe daya ga wani irin chips dake cakude da qwai,sannan ta gyara sashen,tayi wanka,sai a sannan affan ya farka, yaron yana da haquri sosai,ba kasafai yake hanata aiki ba,ta dagashi tana masa miqa hadi da karanta masa addu'ar tashi daga bacci sannan ta rungume shi tana kissing dinsa hadi da tambayarsa


"Ka tashi lafiya uncle dina na kaina?,yau kaji baccin ka daban ko?,munyi missing daddy dukkanmu,karka damu,we have a trip tare da daddy,na tabbatar we will enjoy it in sha Allah" saita saki murmushi tana shafan kan yaron,sannan ta miqe dashi ta masa wanka a toilet suka hau shiryawa.


             Kayan data sawa yaron ya dace sosai sa shigar atamfar da tayi,atamfar tayi mugun karbarta kamar don ita aka bude kamfani atamfa,ita kanta sanda ta tsaya a gaban madubi tana kallon fuskarta a tsakiyar mayafin kanta ruwan zuma sai data burge kanta,ta saki murmushi tana jin dadin yadda kullum take sake zama cikakkiyar mace me iya dressing me fusgar hankalin mijinta, cikakkiyar macen da duk inda ta shiga za'a waiwaya a kalleta,ta tashi daga sakaltacciyar widad din ummu,ta zama classy madam din abbas turaki.


           Fahad ne ya shigo yana gaya mata


"Uncle yace ki fito anty" 


"Breakfast dinshi fa,kace a kawo masa na gama" 


"Okay bari na gaya masa" sai ya juya ya fita,ba jimawa ya dawo ya gaya mata yace he's okay,bazai iya cin komai yanzu ba,sai abun yayi mata banbarakwai,bata taba masa tayin abinci koda ba ranar girkinta bane ya tankwabar bare kuma ranar girkinta,don haka sai ta share wannan maganar ta shirya abincin cikin wani basket mai kyau da daukan hankali,na musamman ne da tasa akayi mata da dukka favourite colors na abbas din don saboda shi din, kome zatayi tana yin sa da colors ko yanayin da tasan zabinsa ne,bata taba duba nata choice din,wannan ya sake sawa ta kama zuciyarsa da kyau.


         Fahad ta bawa kwandon,ita kuma ta kulle sashen nata,ta saka affan a kafadarta ta fito.


             A seat din baya yasa fahad ya saka kwandon,karon farko da ya rasa duk wata sha'awa na cin abincinta,bama abincinta kawai ba,gaba daya yayi loosing komai da yakeji a kanta,sanda ya daga ido ya hangeta tana takowa,gaba daya ta haske farfajiyar gidan da wani irin kyau da qamshinta daya fara aika saqon tahowarta kowanne sashe na gidan,ita da yaron sunyi wani kyau na kusamman kamar fure,saiya dauke kansa ya maida gefe,yana jin zuciyarsa na masa matsanancin bugu kamar zaya fado daga qirjinsa,abubuwa hiyu suna gogayya cikin qirji guda daya lokaci guda SO YAYYA DA KIYAYYA,soyayyar nason tasiri,amma wani abu mai nauyi yana tasowa ya danneta yana baiwa qiyayyar damar wanzuwa a farfajiyar qirji da zuciyarsa,zuciyarsa na kwadaita masa ya sake kallonta,don ta fito a kamar da yakeso,amma tsananin haushinta ya danne wannan muradin da ransa ke dashi,don haka kafin ta qaraso ma ya shige cikin motar yana haki qasa qasa.


        Mamaki ya sake cikata,da kansa a irin wannan lokacin yake takowa ya karba affan daga hannunta ya bude mata motar ta shiga sanan ya miqo mata shi,jiki a sanyaye ta qarasa motar ta bude ta shiga ta zauna, qamshinta ya qarasa baibaye ilahirin motar


"Ina kwana uncle" ta gaaidashi tana dan rusunawa,ya amsa a taqaice ya miqa hannu yana karbar affan,tsam ya rungumeshi a qirjinsa hana jinjina hukuncin da zai yanke wanda har yaron zai shafa,amma dai wannan shine maslaha a wajensa,don yana ji a zuciyarsa bazai taba iya zama da fasiqar mace ba


"Why widad why?,ta ina na gaza?" Ya fada can qasan ransa yana jin wani ciwo,saiya sunkuya a sanyaye yayi kissing goshin yaron ya saka masa dariya kuwa,sai zuciyarsa ta karye,ya miqa mata shi ba tare daya sake kallon fuskarta ba,don kallon fuskarta na gaya masa wani fa ya taba tabata,wani ya taba rabar wanann jikin nata,wani ya taba kwanciya da ita yadda kakeyi,tunanin da yake sakashi jin kamar zaiyi bindiga.


        Duk yadda taso yaci abincin ya qiya,dole ta qyaleshi,tayita sako hira a hanyar tafiyar amma yana banzatarwa,ta jinjina kai tana mamakin wacce damuwa ce haka ke damunsa?,don kada fa takura masa daga qarshe sai tayi shuru itama, motar kamar ta kurame,tafiya mara dadi data fara yi dashi tsahon rayuwarsu dashi,har daga qarshe bacci ya dinga daukarta,dama yau din bata samu tayi baccin nata data saba ba.


           Lokacin da zasu gifta kano sai taji kamar ta sauka yaje ga ummunta,amma dole ta danne,koshi bata cewa komai ba,batason ta dameshi da magana,tunda ta fahimci a yanayin rashin son magana yake.


           Sai bayan azahar sannan suka isa magariba,ta ware idanunta sosai tana jin kewa da shauqin mommynta,tana jin dama ya ajeta wajenta duk da rakiyar aiki tayi masa,ga mamakinta sai taga ya dauki hanyar gidan nasu,ta kasa haquri sanda taga sun shiga unguwar su


"Na gode uncle" kansa kawai ya daure ya gyada mata ba tare da yace komai ba.


           A qofar gidan yayi parking,cikin sa'a usama daya daga cikin qannenta maza da mamarta ta haifa a gidan ya fito,cikin zumudi da murna ya qarso wajen,suka gaisa da abbas sannan ya fidda mata kayanta


"Kakaimin jakar kazo ka karbi affan" saboda yadda taji qafarta da mararta duka sun riqe mata gam.


           Yana shiga ya fito ya karbi affan din suka shige ciki suka barta,ta buda murfin motar,saidai har a sannan abbas din baice mata komai ba,sai ta dakata da fitar ta waiwayo


"To sai yaushe kenan?,sannan a nan zaka sauka?" Kai ya girgiza mata alamun a'ah,ya bude bakinsa da yakejin kamar ya manne yace


"Ki zauna kawai,sai lokacin dana gama aikin,zanzo na daukeki" duk da yanayin da yayi mata maganar yana saka mata rashin jin dadi a ranta,saboda ba yanayin daya saba mata mu'amala dashi bane,amma jin zata dan zauna a gidan ya mata dadi,tanason kasancewa sosai da mamarta,don tana jin dadin haka,uwa uba tana qaruwa da abubuwa masu yawa,sajta jinjina kai 


"Allah ya bada sa'a,yasa a gama lafiya, zamuyi kewarka nida affan" ta fadi a sanyaye da wani abu dake bugun zuciyarta wanda batasan meye ba


"Ameen" ya fada muryarsa a qasa


"Ba zaka shiga ku gaisa ba?" Tayi masa tayi,abinda bata taba ba kenan sai yau 


"Later" ya fada a gajarce,saita jinjina kai kawai,ta saka qafarta ta fice a motar jikinta a mugun sanyaye kamar wadda aka zarewa laka.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post