Daudar Gora book 2 page 48

Daudar Gora book 2 page 48

 

Daudar Gora book 2 page 48

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲      

  ✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨

           (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)

            𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (48)

........Sam kalamansa babu abinda suke ƙara mata sai suka a zuciya. Amma sai ta dake ta ɗaga masa kai kawai tana ɗan murmushin ƙarfin hali. Tare da kai hanunta saman fuskarsa ta shafa da faɗin, “ALLAH yay maka albarka”. A hankali.

      Murmushi ya mata shima a karo na biyu yana mai lumshe idanunsa da buɗewa lokaci guda ya ce, “Amin nagode Ammie, ALLAH ya ƙara miki lafiya da tsohon rai mai albarka” akan lips ɗinsa. Da ga haka ya ɗauka shayin da ya samu Jasrah na bata ya cigaba da bata da kanshi. Sha take tana kallonsa tare da ƙara tabbatar da zancen uwa. Dan kuwa babu abinda kake gani a tattare da shi sai nutsuwa da tarin cikar kamala. Fuskarsa kam sai shining take da ɗaukar idon tabbatar da shi ango ga duk mai iya kallonsa. Ga wani kamshi da take ji can ƙasa-ƙasa a cikin nasa da ke bata tabbacin na mace ne. Hawayen da ke sake taso mata take dannewa, dan yanzu kam tama fi buƙatar kowa ya fice a barta ita ɗaya saboda tana buƙatar ganawa da uwa. Dole ta samu mafita, dan bazata taɓa barin yaronta ɗaya tilo ya sake kusantar mafi zama maƙiyarta ƙololuwa ba. Ko zatai yawo tsirara sai taga bayan yarinyar nan, sai taga ubanda ya tsaya mata, sai taga ƴar uban wacece ita, mita taka ne haka da zata zamewa cikar burinta barazana, burin data ɗauka tsahon shekaru tana ginawa da kauda duk wanda ya nema shiga gabanta koda a kuskure ne. Itace fa ƙi gudu sa maza gudu. TA-ƘURYA sa maza ƙurya. Wutar gobara kasheki koda taro sai an dace. Matar Shahan-shan ɗin RUMAN uwar Shahan-shan. Never for ever ta faɗi ƙasa a dalilin ƴar cikinta da da'ace ɗan cikinta auren wuri yayi babu abinda zai hana ya haifeta”.

      Ganin kamar ta ɗan saki jikinta har tasha magani bayan tea ɗin da tasha Jasrah ta haɗa mata ruwan wanka sai kawai yay musu sallama dan sallar la'asar na gabatowa. A can ƙasan ransa kam hankalinsa ya rabu biyu ne. Wani na nan wani nakan Iffah da itama ya baro cikin halin da ya jefata. Sosai Jasrah taji daɗin zamansa tare da su ganin yanda ƴar uwar tata ta ɗan sake, hakama Malikat Bushirat ɗin ta nuna jin daɗinta a zahiri, amma ita kaɗai tasan ƙunci da ɗacin da ke zagaye da ruhinta......


       ★★.....


    Barci tayi sosai dan har akai sallar azhar bata farka ba. Daneen Ammarah da ke a sashen zaune takan leƙata lokaci zuwa lokaci. Sai kusan 3 ta farka. Yanda ta ɗanyi dama-dama fuskar ta saɓe sosai da kumburin ido ya sata jin sanyi a zuciyarta. Ga zazzaɓin ma ya sauka da ciwon kan. Ta rage rakin zafi-zafin sai dai idan ta motsa da ɗan ƙarfi takan cije lips. Ruwa mai ɗumi sosai Daneen Ammarah ta haɗa mata. Da taimakonta ta ƙara sit bath sannan ta barta tai wanka da karasa kimtsa jikinta. Kafin ta fito an sake gyara ɗakin da kunna masa turarruka komai ya ɗauki haramin ƙamshi. Kayan da aka kawo da ga sashen Malikat Haseenat masu ƙyau da ɗaukar idanu ta ajiye mata ta fice da ɗan mata short not ta ajiye. 

          Cikin dabara ta fito tana cizar lips. Jinta take sakayau kamar iska zata iya ɗaukarta. Ga bakinta ɗaci sosai. Hatta tsamin da jikinta yay ɗazun yanzu duk ya saki sai can da idan ta motsa take jin ciwon kaɗan-kaɗan. Yanzu ko data shiga ruwan zafi da sake gasa jikinta ma sai ta ƙara jin daɗi ko'ina ya miƙe mata. Ta ɗan ji daɗin rashin ganin Mammy, dan kunyarta take ji ALLAH dauriya kawai take yi. Da kanta ta ɗan daddogara ta shirya cikin ƙyaƙyƙyawar abayar baƙa da tasha adon duwatsu sai walƙiya take. Harda b&p a cikin kayan. Salla ta fara gabatarwa a daddafe, tai azhar tai la'asar da taga lokacinta yayi. Tana sallar Daneen Ammarah ta sake shigowa har sau biyu. Sai da ta idar ta lura da ƙyawawan kwanikan dake ajiye. Tana kan sallayar zaune Daneen Ammarah ta sake dawowa. Zama tai a kusa da ita tana tambayarta yaya jikin. A shagwaɓe ta amsa mata cewar da sauƙi. Daneen Ammarah tai murmushi kawai batare data sake cewa komai ba. Sai ma abinci da tai ƙoƙarin zuba mata da taimakonta kuma ta ɗan ci dan girki ne na musamman da ga Mammah. Taji daɗin yanda taga taci gasashen naman da ɗan kirki, ta bata magunguna sannan tai zaman busar mata gashi da ɗazun ba'ai ba. Tsaf ta gyara mata shi ta ɗaure sannan ta gyara mata fuska da ƙara saka mata wasu turarruka masu masifar ƙamshi da bata san da su ba. Ta kuma sakata yin tsugunno kan wasu turarrukan dai bayan wanda tai wanka da su a bayi lokacin da zatayi. Daneen Ammarah ta sauke duk wani nauyin da takeji tai zaman yima Iffah nasiha da bata shawarwarin da zasu taimaka mata a matsayin da take a yanzun mai banbanci da na baya. Sosai nasihar ke shigarta yanda ya kamata, da ga karshe ta sanya mata albarka tari-tari sannan ta dore mata wayar Tajwar Eshaan da ta gani akan side drawer ta riƙe dan ta ɗebe mata kewa kafin ya dawo, ta kuma kunna mata television ɗin ɗakin ma ta ajiye mata remote kusa da ita da parpcorn da Mammah duk ta aiko mata cikin kayan abincin lunch.

       Ji Iffah tai kamar tai kuka, dan tsoro take ji a sake barinta da ga ita sai shi a yanzu. Ita kaɗai tasan abinda ta fuskanta a daren jiya a hannun bawan ALLAHn nan. Ita kanta Daneen Ammarah tausayin barin nata take. Amma yaya zatayi sai kawai ta zaɓi binta da addu'a dan bata so ya dawo ya sake taddata a sashen.. Ajiyar zuciya ta ɗan sauke da haɗiye hawayen da suka ciko mata idanu, wani irin kewar ƴan uwanta take ji fiye da ko yaushe a yau ɗin nan. Ganin zata saka kanta a damuwa tai musu addu'ar samun rahamar UBANGIJI ta ɗauka remote ɗin da Mammy ta ajiye mata ta kunna tv. Searching channels ta farayi a hankali harta samu inda wani film mai ƙyau ya ɗauka hankalinta, sai dai film ɗin akwai abun tsoro a ciki. A kan lips cikin disashiyar muryarta ta furta, “Bari muga kozan iya”. Tana gyara zamanta ta jingina da fuskar gadon tare da ɗaukar popcorn ɗin ta tasa a cinya tana kaiwa baki da ɗaɗɗaya....


        Koda wasa bataji shigowarsa ba, dan hankalinta gaba ɗaya ta maida shi ga kallon film ɗinne, duk da atsorace take kuma, wani gun ma har sai ta ɓoye fuska an ɗan wuce take iya cigaba da kallon. Zamansa kusa da ita da saukar numfashinsa a gefen wuyanta ya sata ƴar zabura harda shirin fasa ƙara. Guntun murmushinsa ɗin nan kamar na dole ya saki yana riƙota. “Hy relax”. Ya faɗa cikin raɗa kamar mai tsoron aji su.

     Idanunta ta rumtse da ƙarfi ta sake buɗewa zuciyarta na wani irin gudu da sauri-sauri dan ta tsoratan fa da gaske. Cikin tura baki ta juya idanunta da har yanzu basu gama bajewa gaba ɗaya ba tai masa ƴar hararar data nema tsarga masa zuciya. A hankali ta ce, “ALLAH kaban tsoro ka nema afuwa na”. Yanzun ma murmushi ya sake yi, batare da yace komai ba ya gyara zamansa yana ɗaura kansa a kafaɗarta idanunsa akan television da take kallo. Cikin raɗa-ɗara da kamo hanunta da ke cikin popcorn ɗin ya kai wanda ta ɗakko guda ɗaya bakinsa yana faɗin, “Babu tayi ne?” ya ƙare maganar da kallonta. Da sauri ta kauda idanunta da ga kallon da take masa ta maida ga tvn cike da basarwa, a shagwaɓe ta ce, “Gashi kaci ba'a baka ba. Ina yini”.

      Idanunsa ya ɗan lumshe da buɗewa ya tashi da ƙyau yana matsota jikinsa sosai kanta da bayanta suka koma saman ƙirjinsa, yayinda take a tsakkiyar ƙafafunsa. Ita duk jitai zaman ma ya bata kunya, amma ya ta iya dole ta dake dan Mamy ta mata nasiha sosai akan ta saki jiki da mijinta karta bada wata ƙofa da zai yi dana sani kan auranta ko tunanin mallakar wata mace saboda gazawarta. Ƙafarsa ɗaya ya ajiye a ɗan dogare yanda ta sake samun jin daɗin zaman. Kusan mintuna biyar bai sake cewa komai ba itama bata sake ba idanunsu duk suna a tvn. Yayinda yake kamo hanunta da take ɗibo popcorn ɗin yana kaiwa bakinsa. Cikin maganar nan tasa kamar ta dole ya ce, “Kinci abinci?”.

       Kanta ta ɗaga masa tsigar jikinta na tashi saboda yanda yay maganar cikin kunnenta. Hannunsa na dama ya saƙalo saman cikinta yana shinshinar wuyanta. “Ban yarda ba, mi kika ci?”. 

            Cikin ƴar in ina da son janye jikinta amma ya hana hakan ta ce, “Mammy ta bani gasashen jan nama da madara”.

       “Uhm ƴar gatan Mammynta. Shine baki rage mun ba kuma? Gashi ina jin yunwa sosai banci komai ba tun wanda kika tsammin”.

    Ita gaba ɗaya jitake kamar an canja mata shi da wani ba Shahan-shan ɗin nan miskili mai shariya da magana ma sai ya jinjina ta ba kafin yayi, duk da a yanzun ma ɗaɗɗaya yake yinta kamar abun dole. Kasa cemasa komai tai, dan gaba ɗaya ita yamasa ta daina fahimtar film ɗin ma. Shi kansa baima san mi yake ba, abinda kawai ya sani ta gama mamayesa da komansa. Tsananin begenta yake da jin ƙishin sake kasancewa da ita. Amma zai daure bazai aikata ba kodan tausayinta, ballema ɗinki da akai mata. Da ƙyar ya ɗan dai-daita kansa, itama cikin ɗan rawar murya ta ajiye popcorn ɗin zata miƙe. Riƙeta yay kamar mai tsoron ta gudar masa😬. A shagwaɓe tana narke fuska ta dubesa, sai kuma ta risinar da idanun da take ƙyaƙyƙyaftawa, “Zan samo ma abincin ne fa”. A hankali ya saki hanun nata yana lunshe idanu da sake buɗewa a kanta gaba ɗaya launin idanunsa ya canja. Yanda take tafiya kaman a hahharɗe kuma a hankali yabi da kallo, tausayinta duk sai ya sake mamayesa. Yaso ya dakatar da ita, amma sai maganar kuma ta masa wahala dan yunwar kuma yakeji da gaske. Tun madarar da ya sha a wajenta da ɗan naman nan bai sake cin komai ba. Koda ya shigo bayan sallar la'asar kuwa baiko kalla dining room ɗin ba ya shige. Wanka kawai yay ya canja kayansa ya taho dubata tunda yasan a yanda ya barta sharɓan da safen nan.........✍️   

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*


*DAUDAR GORA Billyn abdul*


*KI KULANI hafsat xoxo*


*A RUBUCE TAKE Huguma*


*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*


*IDON NERA Mamuh ghee*_LITTAFI DAYA: 400_

_LITTAFI BIYU: 600_

_LITTAFI UKU: 800_

_LITTAFI HUDU :1000_

_LITTAFI BIYAR: 1200_


_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_


_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_


_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_


_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_


_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_


_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_


ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN


MARYAM SANI

ACCESS BANK

0022419171


SAI A TURA SHAIDAR BIYAN 


09033181070


IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA


09166221261


*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*


+227 96 09 67 63


Books biyar  1250CFA

Books hudu  1050CFA

Books uku  850CFA

Books biyu  650CFA

Bookk daya  450CFA


KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post