Daudar Gora book 2 page 50
Health College

Daudar Gora book 2 page 50

 

Daudar Gora book 2 page 50

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲 

  ✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨

           (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)

            𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (50)

........Zaune take kan gado tun bayan idar da sallar magrib da Jasrah ta taimaka mata tayi kafin ta wuce. Idanunta tsaye suke ƙyam a waje guda alamar tayi matuƙar zurfi a tunani, dan sam hankalinta ma baya a cikin duniyar mutane, ya tafi ga yanda zata shawo kan uwa ne kwai da kuma gusar da Iffah datai kane-kane a cikin rayuwar ɗanta, dan tasan abinda uwa ta faɗa babu fashi bazasu taɓa canja sharaɗinsu ba inhar bata ƙarasa cika alƙawransu ba. Ita mai bada labari ce akan bijirewar da surikinsu (Tajwar Abdul-majeed) yayi da abinda ya biyo bayan hakan, dan har yanzu hukuncin uwa na biye da su daki-daki wanda shine ma maƙasudin komai akan kanta yanzu haka da tushen faruwar komai akanta. Tun ɗazun gaba ɗaya hankalinta a tashe yake. Tana ta ƙoƙarin kiranyen uwa amma babu alamar zata ziyarceta, wannan shine mafi zama ƙololuwar tashin hankalinta a yanzu. Motsi da ƙamshinsa ya sata ɗago manyan idanunta farare tas da a yanzu launinsu gaba ɗaya ya koma jazur har baka iya gane baƙin ma da ƙyau. Duk da fushin da take da shi bai hanata jin sanyi da ganinsa ba a cikin ranta, dan da gaske shine abu mafi ƙololuwar soyuwa a gareta a kaf abinda take ganin ta mallaka a duniya. Kafesa tai da kallo cike da so da ƙauna, sai dai tana ƙoƙarin dannewa a zahirance. Wani irin harbawa zuciyar Iffah da girarta ta dama sukayi a lokaci guda, tai saurin ja ta tsaya da ƙoƙarin son janye hannunta da ke a cikin nasa. Amma sai yaƙi sakinta har sai da suka isa gaban Malikat Bushirat da sai yanzu ta lura da Iffah da ke faman ɓoyewa a bayansa. Hannunta ya jawo a hankali ta dawo gabansa idanunsa akan Malikat ɗin dake wani irin kallonsa. Sassanyan murmushi ya saki kaɗan dai-dai yana sakin hanun Iffah'r da kaiwa duƙe ya kamo na Malikat Bushirat ya saka na Iffah ciki sannan ya ja da baya zuwa bakin gado ya zauna abinsa tamkar baiga kallon da Ammien tasa ke masa ba. A wani zafi Malikat Bushirat ta yarfar da hannun Iffah'r tana watsa mata mummunan kallo. Iffah da kanta ke wani irin yamutsawa tun shigar hanunta cikin na Malikat Bushirat ɗin ta buɗe idanunta da suka kaɗa jajur. Amma sai taƙi kallon kowa a cikinsu tama risinar da kanta da faɗin “Ammie ina yini?”.

       “Mi wannan tazo yimun nan?”.

    Ta faɗa ranta a matuƙar ɓace tana maida kallonta ga Tajwar Eshaan maimakon amsa gaisuwar da Iffah tai mata. Shiru kamar bazaice komai ba, ran Malikat Bushirat ya ƙara sosuwa matuƙa, duk da sanin halinsa ne dama hakan. Sai da ya mula dan kansa sannan ya dubeta yana ɗan guntun murmushin daya sake harzuƙa Ammien tasa. A hankali ya motsa lips ɗinsa yana lumshe idanu da buɗewa. “Ammie! Munzo mu baki haƙuri ne, ta kuma dubaki....”

       “Haƙuri? To nace mata ina buƙatarsa ne. Saiful-malik ka fita idanafa ko. Ka fita idona karka bari akan yarinyar nan mu samu matsala da kai. Ita bata kai matsayin da zata zama ko abin kallona ma balle har na saurari wani abu da ga bakinta. K! Tashi ki fitar min anan, karna sake ganinki a cikin idanuna, inba hakaba sai kinyi nadamar sake maimaita wannan kuskuren.....”

          “Ammie....!”

     Da sauri ta ɗaga masa hannu, “Na faɗa maka bana buƙatar jin komai daga gareka, kuma ina akan bakana na sai ka saketa. Inba haka ba Eshaan zan baka mamaki da ga nan zuwa safiyar gobe in har baka janye garkuwar daga bama yarinyar nan ba tare da takardar saki uku..”

       Wani irin lallausan murmushi Iffah ta saki kamar ba'a kanta ake dambarwar ba. Ta ɗago a hankali ta dubi Malikat Bushirat, sai kuma ta maida kan Tajwar Eshaan. Haɗa ido sukai, ta sake sakar masa wani murmushin da yafi na farko neman wargaza masa lissafi. “Mutuwa da rayuwa gaskiya ne *_Sultan_*, kamar yanda ƙaddara da jarabawa suke abokan rayuwar kowane ɗan adam. Ammie tayi gaskiya, ban cancanci GARKUWA da ga gareka ba, sannan kuma igiyar aurenka bata dace da  cigaba da zama kan mace irina ba. Nima a yau na fahimci komai, na gano komai, babu abinda ya rage kuma, tabbas babu. Ka bani dama zan bata haƙuri da kaina, zan kuma fahimtar da ita yanda zata fahimci komai dan nasan yanzun ma bayin kanta bane masu zuga ne..”

          Kallonta kawai yake a narke da jin ƙaunarta na ƙara ratsashi. Wayonta yana rinjayar duk wani ƙarfin ikonsa a zahirance. Ya fahimci tana son ya basu wajene. Sai ko ya miƙe a hankali yana kai waya kunnensa kamar wanda ke shirin kiran wani.

       Wani irin shegen murmushi Iffah ta sake saki idanunta akan Malikat Bushirat da ke jin kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu. Itace wannan yarinyar zata nunama ɗanta da ke matsayin Shahan-shan tacika mace a garesa. Iffah dake danne dariya ta wani kashe mata ido ɗaya da kaɗa mata yatsun hannunta biyu akan fuska. “Hy my Mather in-law ya da suman zaune haka tun ba'a fara wasan ba. Kin damu kanki da saki-saki kokin manta ɗanki sarki ne, bai isa sakin mace haka kawai bai sai da hujja mai ƙarfi? Oh!! Kina son a sakeni saboda na zame miki ƙadangaren bakin tulu ko? Ayya!! Ayya!! Mather in-law kinyi sakaci ai, kinyi sakaci tunda har kika bari Fhareedah bint Zayyan ta kasance ɗaya da ga cikin Zawjata-almilk. Kinyi sakaci tunda har ɗanki ya zama a tsakkiyar tafin hannuna. Kinyi sakaci tunda har kika yarda hanunki ya taɓa jikina a karo na farko yau ma karo na biyu kika sake. My Hamāh idon Iffah buɗe yake tun a randa ta shigo wannan masarautar, sannan biye nake da takun kowa hatta ke kanki. Dan haka nice zan baki mamaki kafin safiyar goben da kika sharɗanta masa idan baki bi a hankali ba ba kece zaki bada mamakin ba. Bara na buɗe miki zancen a bayyane, naba ɗanki gubar dafin macizai a cikin madara badan ya mutu ba, sai dan na kusanta da shi. Dan wannan hanyar ce kawai zata bani damar zama a sashensa din-din, saboda na tabbatar duk wadda ta kasance tana aikata ko yana aikata ɓarnar da kisan matansa da ma duk wani mugu mai ɓoayyen nufi a kansa bazai barni ba zai yi yunƙurin ganin ya kashe ni tun a cikin kurkukun, shiko bazai bari ba zai bani kariya dan dole-dole yana son sanin dawa mukai aikin ai. Kinji na farko kenan” ta ƙare maganar da ɗage mata gira. Sai kuma ta juya idanunta masu rikita lissafin Malikat Bushirat da har yanzu basu gama saɓewa ba. “Na biyu tun a randa aka kawoni gidan nan kika zama suspect ɗina na farko. Dan nagano matsanancin tashin hankali a cikin idanunki lokacin da naƙi shan madarar da kika saka a bani. Kinji na biyu in-law. Na uku randa nake kwance asibiti dalilin rigar da aka sanya mun akwai kallon da kikai mun da ya saka na ajiyeshi a ƙyaƙyƙyawar ma'adana. Na huɗu randa kuka zaunar dani akan kunaso na koma sashen Eshaan da zama danna gano muku wai shike kashe matansa ko wanine. kai jama'a” ta faɗa tana ƙyalƙyalewa da siririyar dariya. “Wlhy kinada basira in-law. Kin iya makirci da in har mutum bai san ainhinki ba sai ki gama halakashi bai sani ba. A ranar na fahimci abubuwa da yawa a cikin kalamanki, kawai kina ɓoye kanki ne cikin ruɗanin bayin ALLAH. Uhhm kin ɗan birgeni fa. Randa Eshaan yasha gubar dana bashi shirunki ba yana nufin baki da abin faɗa bane, ni nasan kinfi kowa zama a ƙololuwar bala'i dan naga haka a cikin idanunki. Randa kika bashi umarnin ya sakeni na gano abinda ke bakiyi tunanin zan gano ba a cikin ƙwayoyin idanunki da taɓa jikina da hanunki yayi. Hhhhhh Iffahr nan da kike gani batta a inda kika ganta batta, tafi ƙarfin zama ƴar wasan kura, ni ɗin hazabibiya ce fiye da yanda kike tunani Mamana. A yau kuwa shigar hanuna cikin naki ya sake tabbatar min da ke ce, ke ce Malikat Bushirat da ke hallaka matan ɗanki da kika haifa da cikinki. Mi kike buƙata ne? Minene a ranki ne? Minene burinki ne? Mi kike son zama ne? Bayan duka ALLAH ya baki?. Ki faɗa min, ni kuma na miki alƙawarin taimakonki bazan kuma tona asirinki ba ko dan daraja da mutunci da kimar ɗanki, dan bazan bar ZUCIYAR MIJINA ta buga ba a dalilin son zuciyarki. K uwa ce garesa, kuma ina kallonki da wannan kimar ne har yanzu saboda mutuncinsa Ammie. Sai dai bazan iya yafe miki jinin ƴan uwana guda biyu ba. Kar kiyi sakaci da wannan damar, in ba haka ba ki sani da ga yau wannan lokacin na yaƙi ne, tabbas na yaƙine...”

      Tabbas Malikat Bushirat a sume take, sumar da kunne na ji ido na gani amma gangar jiki bata motsawa. Suma irin na mamaki da tsantsar tashin hankali. Dan babu abinda ake iya gani sai wutar masifar da ke ci a tsakkiyar idanunta da ke kallon Iffah. Iffah da tuni ta fahimci haka murmushi ta sakar mata da buga hanunta na dama dake dunƙule a tsakkiyar na haggu tai alamar yanka wuya a saitin wuyanta tana kashe ido da cije lips.

        Wani irin miƙewar zabura tayi kamar wadda aka dawoma da dukkan karfinta dai-dai da dawowar Tajwar Eshaan ɗakin. Fashewa Iffah tai da kuka da durƙushewa gaban Malikat Bushirat da ta miƙe tsaye a zafafe. Ta riƙo duka ƙafafunta tana kukan da faɗin, “Ammie nasan zaki fahimci dukkan bayani na, kuma zakimun adalci a cikin dukkan abinda ya farun nan. Nima ba laifina bane tirsasani sukayi da mun barazanar ƙarar da ahalina dama ku musamman ke da kike mahaifiya ga adalin shugabanmu. Ni kuma a shirmena idan na bashin za'ai saurin kaisa ga likita kafin ma dafin macizan yay tasiri. Ki yafe min Ammie nayi kuskure da wauta ki yafe min.....”

        Gaba ɗaya Malikat Bushirat sai ta sake mutuwar tsaye. Eh lallai yau taga masifa, anya yarinyar nan mutum ce kuwa? Shikam mai gayya da aikin yay wata irin tsaiwar da ko bai fito fili yace komai ba Malikat Bushirat da kanta ta hango abinda ta hango a cikin idanunsa da ke tsaye ƙyam akan Iffah da ke a gurfane gabanta. Tabbas idan tai wani abu a yanzu akwai matsala, zakuma tayi kuskuren da yafi na yarda da shigowar yarinyar nan masarautar nan. Haɗiye abinda yay mata tsaye a maƙoshi tai da ƙyar, ta ranƙwafa ta kamo kafaɗun Iffah ta miƙar da ita tsaye. (Ya ALLAH hawaye fa share-share a fuskar Iffah kamar gaske😂). Bata da zaɓin da ya wuce rungumeta itama tana matsar ƙwallan ƙarya ta shiga faɗin. “Ban san haka bane Ibnati, miyasa kika ƙi fahimtar da ni da ban miki irin wannan mummunan zaton ba ai. Kiyi haƙuri ki gafarceni”........✍️

    _Wannan yarinya ta zama abin tsoro gaskiya😂. Ahe haka take🥱🥱Ni wannan ƴa ta Babiy kodai sunada sarauta ne a ƙauyen Jumna bamu da labari. Wannan hayen izza na ɗauran kai gaskiya😂_

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_

_LITTAFI BIYU: 600_

_LITTAFI UKU: 800_

_LITTAFI HUDU :1000_

_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI

ACCESS BANK

0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN 

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 96 09 67 63

Books biyar  1250CFA

Books hudu  1050CFA

Books uku  850CFA

Books biyu  650CFA

Bookk daya  450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post