Daudar Gora book 2 page 52

Daudar Gora book 2 page 52

 

Daudar Gora book 2 page 52


𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲      

  ✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨

           (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)

            𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (52)

.......Duk da barcin dake cikin idanunsa tattaresa yay ya ajiye gefe guda ya tattara dukan hankalinsa kan littattafan da Malikat Haseenat ta bashi. Inda zuciyarsa ke zallon zuwa kawai ya nufa bayan ya ɗan karanta tarihin mafarin komai. Babu bambanci da wanda Mammah ta bashi, dan haka ya ajiye gefe da burin sai ya nutsu zaiyi komai daki-daki. Bai san adadin shekarunta ba, amma sai ya ƙiyasta da adadin shekarun da yake kallonta da su. Yaci karo da kusan huɗu da yay dai-dai da hasashensa, a ciki uku na mata ɗaya na namiji, gefe ya maida na namijin, ya ɗauka wayarsa yana kallon natan da na sauran matan uku kozai dace da wanda zasuyi dai-dai. Wani irin masifar harbawa zuciyarsa tayi ganin tambari na ƙarshe bashi da banbanci da natan. Bayanin dake ƙasan tambarin na tabbatar da dashi aka haifeta, a duk ma wanda aka haifa a tsakanin lokacin ita kaɗaice wadda aka haifa da shi sauran duk yimusu shi akayi. An haifi mai tamnarin a daren ranar juma'a 22 a shekarar 2003 uku ga wata. Sai dai ita kuma ta rasu ne bayan haihuwarta da kwana uku. Wani irin kai hannu yay saman kansa ya yamutsa sumarsa yana ambaton sunan ALLAH. Ya akai haka? Ta yaya ma? Idan har ya tabbata ita ɗin ce ya akai take raye bayan ance kuma ta mutu? Idan kuma waɗan can ɗinne iyayenta tayaya suka bar masarautar ma? Ko bata mutum ba suka ɓoyeta sukace ta mutum? Kai ina akwai dai abinda ya kamata ya sani, farko ma shekarunta ita. Sannan sanin asalin iyayenta. Lokaci yayi da zaisa a maidosu ƙasar ruman...


      ★★......


  Kanta sara mata yake da ciwo mai azaba. Ga wani irin ja da idanunta sukai. Ƙofar da suka fita kawai ta tsurama ido tamkar suna a wajen har  kusan awanni uku bayan fitarsu. Sosai take jin ƙuna mai raɗaɗi a zuciyarta. Har yanzu ta kasa yarda a ido biyu take, ta kasa yarda a zahiri komai ke faruwa, ta kasa yarda ita ta-ƙurya wata ta tsaya a gabanta tai mata wannan cin kashir. Ta kasa yarda ita ta ƙurya yau wani ke tabbatar mata yasan itace silar mutuwar matan ɗanta. Ta kasa yarda, ta kasa yarda da komai.

         “Ta-ƙurya!!”.

    Muryar UWA ta shiga cikin kunnenta a bazata. Firgigit ta kai dubanta ga inda taji sautin kuryar. Ita ɗince kuwa, zaune cikin kujerar nan tata. Yanda fuskarta ke tsuke hancinta na fidda hucin ɓacin rai sai ta ƙara muni ga mai kallo. Idanunta jajur ta ƙara buɗewa akan Malikat Bushirat da itama kallonta kawai take babu alamar jikinta na aiki bayan fitar numfashi. 

            “Kin bani kunya ta-ƙurya. Kin bani kunya da har kika kasance a haka kan wata ƙaramar barazana da ga ƴar cikinki. Ashe bazaki iya yaƙin ba kika amsa takardar gayyata? Dama duk baki shirya zuwan irin waɗan nan ranakun ba......”

       “Uwa ya kike so nayi? Ya kike so na kasance?. Ni fa yarinyar nan ta kalla cikin idona ta faɗamin abinda bayan ni da ke babu wanda ya sani a kaf duniya. Ni yarinyar nan ta shiryama makirci a gaban ɗana dana zama sanadin zuwansa duniya, wanda dukkan gwagwarmayata akansa ne da tabbatar da wanzuwarsa a matsayin da yake yanzu, wanda da shi take ado, da shi take taƙama da jin kanta ita har takai mace abar kallo. Uwa shiyyasa nace miki ki kasheta tun a farkon farawarta amma kik......”

       “Na faɗa miki na ƙara faɗa miki kashe wannan yarinyar kai tsaye ba abune mai sauƙi ba. Domin akwai wani ɓoyayyen al'amari da yake zagaye a kanta. Tsaye nake kuma akan ganoshi dare da rana dan ba dake kawai ta shirya yaƙin ba har dani nan kaina. Sai dai abinda bata sani ba ni nafi ƙarfin iyawarta, zan kuma tabbatar mata da hakan nan kusa. A cikin sharuɗɗanmu kin tafka kurakurai da yawa ta-ƙurya, ciki harda kasa bamu alƙyabba da ke a sashen mai babban ɗaki. Tun a ranar farko kin kasa shayar da yarinyar nan madara, bayan gagara yimata wankan turare da saka mata alƙyabbarmu. Kinyi yunƙurin kasheta da hanunki bayan na sanar miki hakan babban kuskure ne amma kika ƙi jina. Kinyi kuskuren kasa saka ido har aka kaita sashen Ajlaan bada saninki ba. Kinyi kuskuren kasa haɗiye abubuwa da dama dangane da ita. Waɗan nan abubuwan dama wanda ban lissafaba sun taimaka mata wajen buɗe ƙofar samunki ta inda bakiyi zato ba. Babban na ƙarshe daya buɗe komai kasancewarta da jininki matsayin abu guda, bayan kuma tun a farko mun sanar miki mune zamu bama Ajlaan matar aure mai kwaranye ƙishinsa....”

          “Na amsa dukkan laifina gareki Uwa, ina kuma mai neman afuwa da agajinki karki barni na faɗi ƙasa a gaɓar da maƙiya ke burin ganin bayana. Ki faɗi mi kuke buƙata na diyyar laifukana komai wahalarsa zan zama mai cikashi da gaggawa ni bazan kasance mai butulci irin wanda akai miki a baya ba. Ina son yarinyar nan tayi nadamar sanin kanta ma balle ni a karan kaina”.

     “K mai ƙoƙarin cika sharuɗɗa ce ta-ƙurya shiyyasa bana iya dogon fushi da ke. Kije an yafe miki, sai dai ki shirya dan shirinmu na yanzu zai zama a saman na bayane. Zaki biya diyyar kurakuranki da jinin baƙaƙen shanu goma, na raƙuma goma, na baƙaƙen karnuka goma suma. Jariri sabuwar haihuwar kwana uku kamar yanda akai a wancan karon mai tambarin masarautar nan. Bayan sati guda zaki cika mana da jinin ɓarin ciki na mata biyu masu sabon shigar ciki ɗan watanni huɗu. Tare da namijin hadimi sabon aure shima da yay kwanciya da mace sau ɗaya. Da ga yau madarar da Ajlaan zai koma sha zata dinga fita da ga hanunki ne, akwai shayi da yake sha a kullum kisa a nemo miki mai masa nomansa ya noma da wannan irin amaimakon wanda yake noma masa, ɗakin zai dawo tafin hanunki komai sai da umarninki zai aikata shi. Tana makirci da ɗanki a tsakkiyarku, kenan sai kibi ta ƙarfin ikon shi da ke a hanunki da ga yau. Zamu sama mata amintacciyar hadima, dan haka ta koma sashenta da zama. Muna akan bakanmu, waccan yarinyar zata shigo domin da ga gareta kawai muke buƙatar magajin daular ruman kiyi gaggawar ganin an ƙulla aurensu. Da ga shi har ita ki tabbatar sun sha wannan ruwan, shine zai hanasu sake kasancewa da juna har abada”.

       Cike da farin ciki Malikat Bushirat ta amsa tana jera godiya ga uwa cikin gurfana. Ji take gaba ɗaya duk wani ɓacin ranta da tashin hankali sun kwaranye kamar ma ba'ayi ba...

    “Uwa sai dai akwai hadimin nan daya sakata a ruwa, Saiful-malik ya tabbatar min yana haninsu”.

            “Wannan bashi da wani muhimmancin da zai dameki, dan baisa ke wacece ba ai”.

    “Amma Uwa ita ai ta sani, baki ganin zata iya yin yanda kowa zai fahimci ni ɗin ce?”.

        “Bata isa sanarma kowa ba koda shi Ajlaan ne, dan akwai soyayyarki a zuciyarsa fiye da yanda duk wani mai hasashe ke zato”.


   Nidai bilynku na ce, “humm”🥱     ★


       Ta farka sau ɗaya yin fitsari taga baya ɗakin, sai hakan ya ƙara mata nutsuwa. Sai dai kuma can cikin dare ko tace gabanin asuba taji an mata wata irin runguma data sakata farkawa a firgice. Gabanta faɗuwa yay lokacin data tabbatar da shine. Muryarta har kakkarwa take na son magana. Sai dai ma kafin ta furta ya ce mata “Shiiii!!” dole ta haɗiye tai luf. Yamutsata ya dingayi da jagwalgwalata yanda yake so, ta riga ta gama kaiwa maƙura a ruɗewa. Sai dai bai mata komai ba har aka ƙwala kiran salla ya miƙe a gadon ya nufi bathroom. Kusan mintuna goma tana nan kwance lamo da share hawayen da ta sha na tsoro ya fito da alamar wanka ma yayi. Luff tai bata motsa ba  har ya gama tsane gashin kansa ya wuce wajen canja kaya. Wuff tayi ta tashi zuwa bayi, lokacin da ya fito cikin shirin massalaci ya nufi gadon da shirin tadata ya samu wayam. Shi yama zata barin ɗakin tai, sai kawai ya fice abinsa gudun kar ya makara kuma.


       Koda ya dawo da ga salla Gym ya wuce abinsa cike da ƙoƙarin danne abinda ke damun gangar jikinsa da ruhinsa. Wani irin mugun motsa jiki ya ringayi na tashin hankali duk dan ya samarwa kansa nutsuwar manta abinda ke bijiro masa. Sai dai maimakon samun nutsuwar da yake buƙata hankalinsa ne ma ke cigaba da tashi. Ya ɗauki tsawon awa biyu a Gym ɗin kafin ya fito, ya koyi zufa sharkaf kamar wanda yay iyo a cikin ruwa. 

         Tana tsaye gaban gadon tana canja bedsheet ya shigo da sallamar nan tasa ciki-ciki. Ɗan juyowa tai kaɗan ta dubesa sai kuma ta ɗauke kanta. A can ƙasan maƙoshi ta ce, “Good morning”.

        “Ya kike?”.

    Ya faɗa a taƙaice yana cigaba da mata kallon mamaki. Kamar zai share dai ya kasa haƙuri. “Waya saki wannan aikin?”. A ɗan shagwaɓe ta ce, “Ni na sa kaina, shike nan mutum bazai motsa jikinsa ba sai dai komai ai masa ni bana so”. Takowa yay gabanta gab sosai, tare da riƙo hanunta da ke riƙe da filo. Ɗagowa tai ta kallesa. Zata maida ya girgiza mata kansa. Dole ta haƙura, sai dai tai ƙasa-ƙasa da idanunta. Shikam dai idanunsa ƙyam kan ƙyaƙyƙyawar fuskarta da yau dai ta gama komawa normal kamar komai bai faru ba, ya ɗan matsa hannun a hankali yana ɗan huro iskar bakinsa kan fuskar tata. “Akwai muhimman ayyuka da yawa da zaki motsa jiki ai ba sai wannan ba Niger”.

         Fuskarta a ɗan narke ta ɗago idanunta da ƙyau tana dubansa, “Wannan ma fa Mammy ta ce ni ya kamata na dingayi yanzu ba amintaccenka ba. Nima kuma kaga dai a gida Ummu ko mu bata yarda mu gyara ɗakin Babiy, ko bata da lafiya sai tace bari ta ɗanyi ko sama-sama”.

      Gaba ɗaya ta sake narkar da shi a halin da yake ciki, bai ma san sanda ya furta, “Kowane salonki kasheni yake autar mata”. Yanda ya faɗa a narke da kai hannunsa ya shafo jikinta sai taji kunya. Da sauri ta juya masa baya tana rufe fuskarta da tafukan hanunta. Shima murmushin yayi ya ajiye filon yana nufar bathroom. Sai da taji shigewarsa sannan ta buɗe idanunta ta cigaba da aikinta. Haka kawai take jin kanta cikin wani irin nishaɗi yau....


       ★★.... ★....


   “Mammah wai yau ma zakije zaman kotun nan kema? Naga kamar kina jin ƙafar nan sosai fa?”.

        Ɗan murmushin ƙarfin hali Malikat Haseenat ta saki idonta akan Daneen Ammarah mai maganar. “Karki damu ai bawani ciwo take mai yawa ba. Ke dai yi sauri ki bani kunun nan nasha, kin sanshi ɗan ƙa'ida ne akan bin lokaci”.

    Ƴar dariya Daneen Ammarah tayi kawai, da ka ganta itama zaka fahimci tana cikin farin ciki. Da ga ita har Malikat Haseenat ɗin tun jiya fuskokinsu sun kasa daina murmushi, da dare kam zama sukai suka dinga hirar Iffah. Su kansu sun kasa gane ta yanda akai yarinyar ta shiga ransu matuƙa har haka, kuma take ma ƙara shiga a kullum musamman ma ita Daneen Ammarah ɗin da kwanakin nan taketa mafarkai da ta kasa gane kansu.........✍️


      

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*


*DAUDAR GORA Billyn abdul*


*KI KULANI hafsat xoxo*


*A RUBUCE TAKE Huguma*


*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*


*IDON NERA Mamuh ghee*_LITTAFI DAYA: 400_

_LITTAFI BIYU: 600_

_LITTAFI UKU: 800_

_LITTAFI HUDU :1000_

_LITTAFI BIYAR: 1200_


_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_


_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_


_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_


_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_


_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_


_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_


ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN


MARYAM SANI

ACCESS BANK

0022419171


SAI A TURA SHAIDAR BIYAN 


09033181070


IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA


09166221261


*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*


+227 96 09 67 63


Books biyar  1250CFA

Books hudu  1050CFA

Books uku  850CFA

Books biyu  650CFA

Bookk daya  450CFA


KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.


MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post