Daudar Gora book 2 page 54

Daudar Gora book 2 page 54

 

Daudar Gora book 2 page 54

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲     

  ✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨

           (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)

            𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (54)

.........“Ko zaka iya gane mutum idan ka sake ganinsa”.

    “Sosai ma kuwa. Dan akwai ma cctv footage na abinda duk ya faru a tsakaninmu batare da shi ya san inada camara a wajen ba.” ya ƙare maganar yana duban shugaban jami'ai. Ya fahimci mi yake nufi, dan haka ya miƙe ya miƙawa Sayeed Hanifud-Din flash da ke a hannunsa, anan take kuwa aka saka flash jikin lap-top aka kai gaban Tajwar Eshaan, sai ko ga duk abinda ya faɗa ɗin dalla-dalla.

        An shigo da wanda ya amso dafin macizan, wanda ya kasance amintaccen hadimi ne ga Miran Jasim, kowa ya sani kuma a masarautar nan, dan tun yana a matashin saurayi ma yake tare da hadimin, shine ke masa duk wasu ayyuka na sirrinsa dama na mugunta.  Ai Miran Jasim baima san yay wata iriyar zaburar tashin hankali ba jikinsa na kakkarwa. Yayinda gaba ɗaya kotun ta ɗauka ƴan ƙananan magana har sai da aka tsawatar. Sayeed Hanifud-Din da shima dai gaba ɗaya jikinsa yay sanyi da al'amarin ganin daga inda ya fito, dan koba'a faɗa ba komai a bayyane yake. Fuskantar hadimin da gaba ɗaya ya fita hayyacinsa a hannun jami'ai yay. “Bama buƙatar wani kwana kwana da ga gareka ko ja'in ja, faɗar gaskiyarka na nufin zaka iya samun sassauci, zaɓar yin taurin kai kuwa ya rage naka. WANENE YA SAKA?”.

        A hankali hadimin ya ɗago ya ɗan dubi inda su Miran Jasim suke, idanu suka haɗa da Miran Arshaan da yake masa kallon ƙasa-ƙasa yana wani ɗan motsa yatsunsa. Ajiyar zuciya ya ja a hankali, kafin ya maida dubansa ga Sayeed Hanifud-Din. Kai tsaye babu wata kwana-kwana ya ce, “Shugabana Miran Jasim ne ya sakani....”

      A take kotun ta ɗauki wani irin ihun ƙarajin Miran Jasim da ya zaburo kan hadimin nasa, sai da jami'ai suka rirriƙesa. Yayinda jama'a suka hau salati suma har sai da aka tsawatar. Hadimin ya cigaba da faɗin, “Sai dai ni ban san mizaiyi da ita ba, amma a gabana ya zubashi a cikin madara ya bani madarar yace na kai sashen Zawjata-almilk nace daga sashen uwar masu gida. Bani da ikon cemasa a'a, amma nayi niyyar ƙin kaiwa sai dai nasan zai iya sawa a bibiyeni idan nai hakan zai halakani kuma, dan haka na cika umarninsa amma ni duk tunanina ma Zawjata-almilk ɗin zai ba. A ranar nata ƙoƙarin ganin samun ganawa da ko amintaccen adalin shugabanmu ne amma hakan bai faruba, da ga ƙarshe ma sai naji wai ashe shine za'a bama madarar ta hanyar Zawjata-almilk ba kamar yanda nai tunanin itace zai bamawa ɗin ba. Kuma zan faɗi gaskiya, ba laifin Zawjata-almilk bane ba asiri yay mata kan duk yanda yaso haka zaiyi da ita, daga baya itama zai kasheta...”

        Duk yanda akaso samun nutsuwar kotun kam hakan ta gagara. Salati kawai kake ji da la'antar Miran Jasim da akeyi. Iffah ta saki wani irin shegen murmushi tana mai kallon Miran Jasim da yay sumar tsaye. Sai kuma ta maida kan Miran Arshaan da gaba ɗaya yay sharkaf da zufa. Wata dariya ta ƙyalƙyale da shi a zuciyarta tana faɗin (tun banzo kanka ba) a zahiri kam baka isa fassara yanayinta ba.

        A ɓangaren Miran Arshaan kam ya ɗauka makircinsa ne yay tasiri kan Miran Jasim. Dan kuwa hasalima shiya tura hadimin ya shiga jikinsa duk tsawon wannan shekarun da suke a tare, dan kawai ya san duk wani motsinsa, sai dai abinda bai sani ba a yanzu hadimin ba aikinsa yake ba aikin Iffah yake yi, ita kuma ta zaɓi tattara laifin ga Miran Jasim a karan kanta saboda haka ta tsara binsu ɗaɗɗaya, shi kuma zata cigaba da jansa a ƙasa har zuwa gaɓar da take so......

     Wata irin daddagewa da fashewa da kuka da Miran Arshaan yay ne ya katse mata tunaninta. Ta zubama drama ɗin tasa ido dan ya wani daddagene ya fashe da kuka yana duban Miran Jasim kai kace daɗa duniya har zuciyarsa ne. “Jasim! Jasim Akhi mu zakama haka? Kai da kanka zakaci amanar ɗan uwanmu ka zama jagoran shirya halakashi. Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un... Mi kake bukata ne? Miye ɗan uwanmu bai mana na gata ba a wannan duniyar? Ya riƙemu tamkar yanda Abie (Tajwar Abdul-majeed) zai riƙemu, amma mu mu kasa riƙe jininsa ɗaya tilo a duniya da bashi goyon bayan mulkin da ALLAH ya ɗaura masa. Dama na jima ina zargin kana ƙwaɗayin mulkin nan ne, ban tabbatar da hakan ba sai randa aka samu kayan tsafin daka saka a kujerar da adalin shugabanmu yake zama, kaƙi zuwa kuma wajen meeting da ga ƙarshe ma baƙin cikin an ganoka ka nema halaka iyalinka” ya sake fashewa da kuka.

     Wata irin mahaukaciyar shaƙa Miran Jasim da jikinsa ya hau kakkarwa ya kaima Miran Arshaan, da ƙyar kuwa aka ɓangaresa yana faɗin sai ya kashe Miran Arshaan ɗin.

     Duk da wannan dambarwa mai gayya mai aiki Shahan-shan na zaune ne yana binsu da kallo ta cikin gilashinsa. Shi kansa a wannan gaɓar sai ya shiga ɗan ruɗani, dan a iya bibiyar rayuwar uncle's ɗin nasa da yake yi tun lokacin da ya fara zarginsu a tare suke aikata komai sai dai a sirrance ne kam. Kuma ita kanta Iffah ta sanar masa su biyu ne ai, amma yaya akai hakan ta kasance komai ya juye kan Miran Jasim shi kaɗai.....

      Tamkar Sayeed Hanifud-Din kam yasan mike ransa ya ambato sunanta. “Ko Zawjata-almilk nada wani ƙarin bayani akan alaƙarta da Miran Jasim da har hakan ta kasance tsakaninsu?”.   

      Shiru kamar Iffah bazata motsa ba, sai kuma ta yunƙura da ƙyar fuskarta jage-jage da hawaye. Handkherciff ɗin da Malikat Haseenat ke miƙo mata ta amsa ta goge fuskar sannan ta fuskanci kotu bayan ta saci kallon Tajwar Eshaan da takeji a jikinta kallonta yake, dan tun ɗazun takejin kaifafan idanunsa a kanta. Hakama Malikat Bushirat kallonta takeyi. A nutse cikin nuna rauni ta ce, “Ni ban san mizan ce ba, amma abinda na sani kawai bani da wata alaƙa da shi nikam, hasalima ban sanshi ba a zahirance sai a randa aka nunani gaban duk iyayen wannan gida mai albarka. Kuma ko'a ranar bazan iya cewa ga kamaninsa ba. Sai a randa Zawjata-almilk farko ta rasa ranta ne dai-dai da rasuwa sayeed Khairul-Bashar na nufi sashen mai girma Shahan-shan hankali tashe dan ina son tabbatar da abinda al'umma keta faɗe akan shine ke kashe matansa. Ina tsaka da dube-dubena akan gawar suka shigo tare da shugaban jami'ai, Ni kuma sai naji tsoro na ɓuya, bayan an fita da gawar ashe shi ya ganni shine ya dawo da baya. Na tsorata amma sai ya ce na nutsu muyi magana, zai rufamin asiri amma yana so muyi aiki tare. Ya ɗan mun maganganu dai da yawa. A ranar ya kawo min maganganu masu ruɗarwa, mafi girma a cikinsu nunamin video cewar adalin shugabanmu ne ya halakamin iyayena da tsafin maciji kamar yanda naga alamar saran maciji a jikin Zawjata-almilk da ta rasu, ya kuma sanar min nima na tsira zanyi ba dan haka nima nayi takaina. Nazo mu haɗa hannu mu yaƙesa dan baza'a hukuntashi ba. Ni a lokacin maimakon cemasa wani abu ma ruɗani na shiga da tashin hankali akan iyayena, dan haka bamma gama saurarensa ba, ganin bana a hayyacina ya tashi ya fita. Sai kuma A ranar 9 ga watan 2 dai nanma na samu kiransa misalin ƙarfe takwas na dare. Nayi matuƙar mamakin hakan, dan bai ɓoyemun ba ya sanar min aiki fa yake son miyi tare kamar yanda ya faɗa a waccan ranar amma zai sanar min wani abu. Ban katsesa ba nace ina saurarensa. Ya sanar min magana bazata yiwu ta wayar landline ba, amma ga number ɗinsa na kirashi direct video call. Har lokacin ban kawo komai a raina ba, duk da dai inajin tsoro ganin shiga uncle ɗinsa ne, idan na faɗama wani bama za'a yarda dani ba. Dan haka nabi umarninsa na kira ɗin dan bangama sanin yanda akeyi anan ɗin ba. Tun daga wannan ranar ban sake fahimtar komai ba da ga yanda yake bibiyata sai da nakai madara ga adalin shugaban wannan ƙasa ya sha. Daga nan na fara fahimtar makirci ne musamman yanda ya dage akan sai an kaini kurkuku. Bayan an kainin kuma ya bini har can yana faɗamin maganganun banza harda na rashin ɗa'a”. Ta fashe da kuka mai cin rai, wanda a yanzu kam da gaske kukan take, dan kalmar KARUWA da Miran Jasim ya ce zai maidata na mata raɗaɗi har yanzu a cikin rai.

       Dolene yanda Iffah ke bayanin yasa kaji hawaye yazo maka, kuma ko kai waye sai kaji ka yarda da ita. A nan ɗin ma fa ruɗewa kotun ta sake yi, yayinda Miran Jasim ke hargowar sai ya ɓatar da ita, sai ya shafe babin rayuwarta baki ɗaya ita da Miran Arshaan da sukaci amanarsa. Babuma wanda ke saurarensa sai ALLAH wadai da ake jifansa da shi da tausayin Iffah da gaba ɗaya a yau kowa ya fahimci an mata makircine ashe. Dama can wasu da yawa tunma a randa ta aikata suke faɗin bayin kanta bane, tayi ƙankanta da aikata laifin ita ɗaya. To sai gashi yau kam komai ya fito filin ALLAH. Kotun tai bala'in ɗaukar turiri har sai da Tajwar Eshaan da kansa ya tsawatar. Dan danan kowa ya nutsu kotun tai tsitt. Ya ɗauka tsahon mintuna uku babu alamar zai ce wani abu, kafin ya nisa da ƙyar cikin maganar nan tasa a fusge kamar wanda akaima dole. Da ƙyar ya iya danne zafi da raɗaɗin da zuciyarsa ke masa kanjin wai uncle ɗinsa yama matarsa magana ta rashin ɗa'a, amma ta ɓoye masa.

         “Alamu da kalaman Jasim ibn Abdul-majeed Aliy Qutb sun tabbatar da duk abinda aka sanar anan game da shi ya aikata. Sai dai duk da haka wannan kotu mai adalci zata bashi damar sanar damu dalilinsa na aikata duk wannan a zama na gaba. Za'a tsaresa a kurkukun da Zawjata-almilk tai rayuwa har zuwa ranar da kotu zata sake buƙatar ganinsa a gabanta. Wannan kotu kuma ta wanke Zawjata-almilk da ga zargi, tare da bada damar kawo bokan da yay sihirin gaban shari'a shima. Tanada damar shigar da ƙara itama a karan kanta game da amfani da ita da Jasim yayi. Daga ƙarshe ni Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed Aliy Qutb ina shigar da ƙara nima bisa yunƙurin kashe min MATA da akayi har karo biyu ta hanyar yimata allurar guda da jefata cikin ruwa...” da ga haka ya miƙe anutse cike da salon nan nasa yayinda ya bar jama'ar kotu gaba ɗaya a yanayin mutuwar zuune da kalamansa na ƙarshe. Malikat Haseenat kam murmushi ta saki mai sanyi da ƙayatarwa, hakama Daneen Ammarah. Yayinda zuciyar Malikat Bushirat ke bugawa da wani irin sauri-sauri a cikin ƙirjinta dake yin kamar zai buɗe.

           A ɓangaren Iffah kam idonta akan Miran Jasim ne, a cikin iska ta rubuta *_FINAL_* da yin alamar yanka wuya ta kashe masa ido ɗaya........✍️      _Mai RUMAN sai kayi takanka kaima to, dan da gaske Iffah kaza zata koma uwar tone-tone 🥱_


    

   

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*


*DAUDAR GORA Billyn abdul*


*KI KULANI hafsat xoxo*


*A RUBUCE TAKE Huguma*


*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*


*IDON NERA Mamuh ghee*_LITTAFI DAYA: 400_

_LITTAFI BIYU: 600_

_LITTAFI UKU: 800_

_LITTAFI HUDU :1000_

_LITTAFI BIYAR: 1200_


_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_


_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_


_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_


_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_


_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_


_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_


ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN


MARYAM SANI

ACCESS BANK

0022419171


SAI A TURA SHAIDAR BIYAN 


09033181070


IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA


09166221261


*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*


+227 96 09 67 63


Books biyar  1250CFA

Books hudu  1050CFA

Books uku  850CFA

Books biyu  650CFA

Bookk daya  450CFA


KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.


MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post