Daudar Gora book 2 page 55

Daudar Gora book 2 page 55

 

Daudar Gora book 2 page 55

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲      

  ✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨

           (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)

            𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (55)

.........Wani irin faɗawa tai saman gado  cike da farin ciki tana sakin siririyar dariya. Babu abinda take hangowa sai idanun Miran Jasim da na Malikat Bushirat harma da Miran Arshaan. Tai wani irin juya ta sake juyawa a gadon sai kace tarwaɗa. “Kina lokacinki Fhareedah bint Zayyan”. Ta faɗa a fili tana sake ƙyalƙyalewa da dariyarta kai kace an mata albishir ne da dawowar su Babiy ƙasar ruman. Yanda take ji kam kamar ta tashi tayita taka rawa. Ɗaya da ga cikin burikanta ya cika, ya cika a gaɓar da ALLAH ya bata abinda baya cikin lissafinta. Tabbas zama mallakin Shahan-shan baya cikin lissafinta. Lissafinta na ɗaukar fansa ne kawai, fansar jinin ƴan uwanta da bazata iya yafewa ba. Sai dai kuma dukkan labarin ya canja, ya canja da canjawar shigowar su Miran Jasim cikin tattakinta batare data tsaro da su ba. Shigowar Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdul-majeed matsayin wani abu mai daraja a ciki labarinta batare da ta rubuto da hakan ba nan ma. “Ya rabba” ta faɗa a zahiri tana lumshe idanunta da sukai wani tar-tar na haske fuskarta na ƙara ƙawatuwa da murmushi mai ƙayatarwa......


       ★★..... ★...


    “Mammah duniya abin tsoro ce wlhy, duk da mun jima da sanin Jasim baya ƙaunar Abni sai yau ɗin da komai ya fito fili ya bani mamaki. Har zuciyata iya abinda nake kallonsa da shi shine nuna adawa kawai ga mulkin tunda shine burinsa. Amma wlhy ban taɓa kawo zai iya shirya halaka rayuwarsa ba haka. Wace irin rayuwa ce wannan wai ɗan uwanka jininka ya zaɓi cutar da kai akan abin duniya mai yankewa. Wai ina mahaifinmu da ya zama sanadin kawomu duniyar ma? A da shine a wannan kujerar, amma ya shuɗe kamar ba'ayisa ba, aka ɗaura ɗan uwanmu, shima ya shuɗe kamar baiyi ba, idan sukai haƙuri shima wataran bashi bane anan ɗin. Bazan boye miki ba Mammah, zuciyata ta fara min saƙe-saƙe da kokwanto akan rasuwar Haysam Akhi, haka Zawjata-almilk da muka rasa, anya kuwa hakan baida alaƙa da su Jasim Akhi ya karɓa makamancin tayin da muka jima da tsigesa a cikin jininmu?. Dan zuciyata ta fara rabuwa biyu bayan zargin mushirakar can data daɗe da shuɗewa a tarihinmu kamar akwai wata mai irin al'amuranta a yau zagaye da wani namu”.

         Malikat Haseenat da ke ta faman jinjina kai taja ajiyar zuciya mai ƙarfi tare da fesar da iska zazzafa da ga bakinta. “Tabbas duniya ta cancanci zama abar tsoro kam Ammarah, nima kuma kamar ke zuciyata ta fara rawa, ta fara rawa a wannan gaɓar har inajin ni kaina ban yarda da kaina ba. Tabbas mushirikar can ta shuɗe ita da tarihinta, amma sai zuciyata ta gagara nutsuwa da hakan duk da tsahon shekarun nan da suka shuɗe da kasancewarta. Babu abinda Jasim bazai iya aikatawa ba, musamman idan na kalla irin mugun zaman da mukai da mahaifiyarsa a masarautar nan. Dan haka shima kam yanzu abin tuhuma ne. Sai dai akwai wani furuci da yarinyar nan tayi yafa tsaya mun a rai, tun ɗazun kuma yake mun kai kawo....”

      “Wane furuci kenan Mammah?”.

  “Furucin bibiyar gawar Zawjata-almilk ta ƙarshe da muka rasa, inda ya zama sanadin haɗuwarta da Jasim. Lallai ina buƙatar ganawa da Zawjata-almilk”.

            Shiru Daneen Ammarah tai tana kallon Mammah, sai kuma ta nisa itama zuciyarta na mata kai kawo akan hakan. Eh tabbas wannan furuci abin a bibiya ne, dan sai a mahanga ya ke da nasaba da abu biyu. Shi kansa Jasim suspect ne a wannan case ɗin shima. Duk da dai duk Zawjata-almilk na baya da suka rasa ransu suke fara zuwa su ganta kafin kowa.....”

     Firgigita ta dawo hankalinta sakamakon taɓatan dan Malikat Haseenat tayi, taja ajiyar zuciya mai nauyi da sauke numfashi. “Yi haƙuri Mammah, wlhy na tafi wata duniyar tunanin ne nima. Za'ai bincike ga Ibnati ɗinne? Ko kuwa ya kike nufi?”.

           Kai Malikat Haseenat ta jinjina da faɗin, “Fara nemo min ita a waya”. 


     ★Har yanzu Iffah na kwance a kan gado cike da farin ciki da nishaɗi kira ya shigo a landline ɗin ɗakin. Wayar ta kalla kamar bazata tashi ba. Sai kuma ta miƙe lokacin da take gab da yankewa ta ɗaga. Ƙin yin magana tai, sai da Daneen Ammarah tai sallama sai kuma duk ta ruɗe. “Lah Mamy kece, Barka da wannan lokaci a gafarceni”. Murmushi Daneen Ammarah ta saki mai sanyi da ga can tamkar Iffah'r na gabanta, tana matuƙar ƙaunar yarinyar nan ta yanda ita kanta ma bata san adadi ba. A hankali ta nisa da sakin ajiyar zuciya ta ce, “Ba komai Ibnati, Mammah ce ke buƙatar magana da ke daman”. Tamkar Iffah na gaban Malikat Haseenat ne cike da girmamawa ta gaisheta duk da yanzun nan suke rabuwa da ga zaman kotu. Da ga can ta amsa mata cike da nutsuwa da dattakonta, kafin ta ɗaura da faɗin, “Mijinki ya shigo ne?”. A hankali Iffah da kalmar ta bama kunya da yi mata nauyi ta ce, “A'a Mammah”. Murmushi Mammah ta sakeyi da gyaɗa kanta ta cigaba da faɗin, “Idan har baƙya wani uziri bayan sallar isha'i ina son ganinki”.  Cike da girmamawa ta ce, “To Mammah insha ALLAHU”.

      Shiru tai tana kallon wayar bayan ta yanke. Zuciyarta sai faman mata kaikawo take da tunani kala-kala. Sai kuma ta ɗage gira da ɗan taɓe baki tana ajiye kan wayar ta miƙe. Ficewa tai da ga ɗakin ta nufi can saman ginin dan wajen na matuƙar ƙayatar da ita. Tana ƙaunarsa fiye da kowane waje a masarautar.....


       ★★......


  “Abu Harith kana lafiya kuwa? Tunda muka baro kotu ka kasa zaune ka kasa tsaye. Duk da dai nasan abinda ɗan uwanka ya aikata ga wannan bawan ALLAH dole ya taɓaka, amma sai nake ga damuwar taka da ruɗanin kamar sunma fi na kowa. Ka tuna nima fa ɗan ƴar uwata ce dat riƙeni tamkar uwa, sannan shugabanmu baki ɗaya. Mu dukanmu ya sakamu muka haukace akan baiwar ALLAHr yarinyar nan da bataji ba bata gani ba. Wlhy har kunyar haɗuwa da ita nakeji yanzu. ALLAH sarki Mammah tai ta son nuna mana gaskiya muna bijirewa, duk da ALLAH ne shaidata kai ne ka dinga ƙara tunzurani har idanuna sukai makancewar kasa hasashen komai gashi na ƙare da dana sani”.

         Kallonta kawai yake tana zabga zance ko haɗiyar yawu batayi, bata san jima yake tamkar ya shaƙota ba tsabar takaici da takura masa da tai. Shifa shi kaɗai yasan irin kalar tashin hankali da ruɗanin da yake ciki akan al'amurin nan. Da farko yayi zaton hadiminsa na aikine bisa aikinsa na tsawon shekaru da ya ɗaurasa a kai akan bibiyar ɗan uwansa, sai dai kallon da yarinyar nan Iffah tai masa sanda suke fitowa daga kotun ya matuƙar saka zuciyarsa neman bugawa. Idan har ya canka dai-dai lokacin da take shigewa *_Next..._* ta rubuta masa akan iska fa. Wannan kalmar itace ta tsaya masa a zuciya taƙi faɗawa sai faman kaiwa da komowa take.....

     “Ya ilahi Abu Harith!!”.

  Jasrah da ke hargowar ƙwala kiran sunansa ta katse masa tunani. Cikin ɓacin rai ya nuna mata ƙofa alamar ta fice masa. Rai ɓace take dubansa itama, har taji ta kasa haƙuri ta ce, “Kamar ya na fita bayan kuma magana muke? Wai shin kodai kaima da naka kashin ne a jiki banda labari, dan wannan yanayin naka kam ya fara sakani a ruɗani.....”

         “Jasrahhh!!!”.

    Ya faɗa cikin ƙarajin da ya sakata zabura. Cikin wata irin birkicewa da bata taɓa fuskanta da ga garesa ba ya sake nuna mata ƙofa. “Wlhy idan baki fita min ba sai na kwashe fuskarki da maruka. Banza kawai kin dameni, ki barni naji da abinda ya isheni ban san wawanci”.

          Ba ƙaramin tsorata Jasrah tayi ba kam, dan wutar bala'i ta gano ƙuru-ƙuru cikin idanunsa da kan fuskarsa. Cike da sassarfa ta nufi hanyar fita ranta a ɓace da tsawar da yay mata.... Tana gama ficewa yaja wani shegen wawan tsaki da raka bayanta da harara ya ce, “Tinkiya kawai, ban san damuwa”. A wani irin zafafe ya koma jagwab cikin kujerar ya zauna yana dafe kansa da ke sara masa da ƙarfin masifa. Dai-dai nan kira ya shigo wayarsa. Sharewa yay bai ɗauka ba har ta tsinke, sai kuma ga wani ya sake shigowa. Tsaki yaja da finciko wayar daga aljihu da niyar kashewa gaba ɗaya yaci karo da sunan Ameera Haifah ɓaro-ɓaro. Kamar bazai ɗaga ba nan ma sai kuma ya amsa a fusace da kaita kunnensa. “Ke kuma miye kike wani kirana a wannan lokacin bayan kin san mi ake ciki”.

        Da ga can cikin muryar tashin hankali ta ce, “Dolene na kiraka Arshaan. Dan tabbas akwai matsala. Matsala babba wlhy. Na kasa gane komai, ka saka zuciyata a ruɗani gaba ɗaya game da abinda ka aikata a kotu. Shin mi hakan ke nufi? Taya komai da muka aikata mu uku ya koma kansa shi kaɗai? Kai ne kai hakan kokuwa hatsabibin yaron can ne ya ƙulla mana gadar zare ta hanyar yar iskar yarinyar can. Wlhy kaina ya kwance gaba ɗaya, dan ALLAH ka zaɓa mana wajen haɗuwa yanzu da gaggawa kar zuciyata ta buga”.

          “Da zata buga ɗin ma da kowa ya huta. Please malama ki ƙyaleni bana buƙatar magana da kowa okay”. Ƙittt ya yanke wayar batare da jiran cewarta ba.


     ★


   “Ashe zan kasheka na kashe banza idan kace zaka zamar min matsala Arshaannn!!!”.

      Ta faɗa cikin ƙaraji da cije lips dinta jikinta na rawa. Wayar ta cilla saman gadonta ta cigaba da kaikawon da take tun ɗazun a cikin ɗakin. Tunda ta baro kotu ta gagara zaune ta gagara tsaye. Tasan in har Miran Arshaan ne ya shirya komai ga Miran Jasim hakan na nufin itama bazata tsira ba dan tare suke ƙulla komai. Idan kuma Tajwar Eshaan ne ya ganosu kama Miran Jasim kawai ba komai bane garesu face talala. Dole dole ma akwai wani abu da ya kamata ta sani, dole ta sanshi a yau ɗin nan yanzun nan basai gobe ba. Idan Miran Arshaan ya cigaba da wofantar da tuhumar da take masa to lallai zai ganta yanzu a sashensa kuwa. Sai dai duk ma abinda matar tasa zata zarga ta zarga. Ko kuma in ma ɓarewa zatai wlhy sai dai ta ɓare da su su duka amma bazata taɓa barin Miran Arshaan ya sha ba shima ko ya kaita ƙasa kamar yanda ya kai Jasim. A fusace ta sake fisgar wayarta ta hau rubuta masa dogon text message jikinta sai tsuma yake. Ga uwar zufa ta mata sharɓan kamar wadda taci gudu a cikin dokar jejin da babu komai sai sahara mai zafi da ta ɗauki zafin rana....


       ★★..... ★...


   Yi take kamar zata tsumbula cikin wayarta dake a hanunta. Ihu kawai ya rage ta kurma akan kiran Daneen Waheeda da take faman yi tun bayan fitowarsu kotu amma bata ɗaga ba. Ta bata lokaci da tunanin zatai kiranta in ta gani amma babu alamar hakan zata faru. Kuma a ƙalla kira na goma sha bakwai kenan take mata. Banda text message da zai iya zama biyar koma fiye da hakan. 

       Kamar almara aka ɗaga wayar, cikin rawa da kakkarwar jiki ta kaita kunnenta tana faɗin.........✍️



   

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*


*DAUDAR GORA Billyn abdul*


*KI KULANI hafsat xoxo*


*A RUBUCE TAKE Huguma*


*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*


*IDON NERA Mamuh ghee*



_LITTAFI DAYA: 400_

_LITTAFI BIYU: 600_

_LITTAFI UKU: 800_

_LITTAFI HUDU :1000_

_LITTAFI BIYAR: 1200_


_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_


_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_


_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_


_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_


_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_


_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_


ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN


MARYAM SANI

ACCESS BANK

0022419171


SAI A TURA SHAIDAR BIYAN 


09033181070


IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA


09166221261


*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*


+227 96 09 67 63


Books biyar  1250CFA

Books hudu  1050CFA

Books uku  850CFA

Books biyu  650CFA

Bookk daya  450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post