Daudar Gora book 2 page 57

Daudar Gora book 2 page 57

 

Daudar Gora book 2 page 57

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲      

  ✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨

           (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)

            𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (57)

.........“Kinci abinci?”.

    Kanta ta girgiza masa alamar a'a.

“Mi yasa?”.

“Banajin yunwa ne”.

       Shiru bai sake cewa komai ba har kusan minti ɗaya. Hannunsa da ke kan bayanta ya ɗago ya ɗaura saman goshinta data kwantar jikinsa, kan da zafi sosai har ma yana iya jinsa. 

     “Na miki addu'a?”.

Nan ma kan ta ɗaga masa. Komai bai sake cewa ba shima. Sai matsawa da su da yay zuwa gadon, tana a jikin nasa ya kai zaune itama ya zaunar da ita a cinyarsa. Addu'a ya fara mata a kan idanunta a lumshe, bayan ya kammala ta kwantar da kanta a kafaɗarsa tai luff tana sauke ajiyar zuciya a jajjere. Nan ma sun jima a zaman shiru kafin ya kirata muryarsa a can ƙasan maƙoshi. 

      “Mrs Eshaan?”.

   “Uhmyim”.

Ta amsa itama can ƙasa batare data ɗago kanta da ke a kafaɗarsa ba.

           “Miyasa kika ɓoye min?”.

      Bata fahimci mi yake nufi ba, dan haka ta buɗe idanunta da jan cikinsu ke ɗan raguwa a hankali ta zuba masa. Bazata iya jurar kallonsa cikin ido ba dan haka ta ɗauke su ta maida gefe. “Ban san akan mi kake magana ba Sultan”.

     Sai da ya ɗan furzar da hucin ɓaci ran da yake ta dannewa, a ɗan fusge ya furta, “Jasim! Miyasa kika ɓoyen ya sameki a kurkuku da maganar banza?”.

          Shiru kamar bazatace komai ba, sai kuma ta motsa cikin sauke ajiyar zuciya ta ce, “Kayi haƙuri, a lokacin ban san ta yanda zan tunkareka ba. Ban kuma san ta yanda zaka fahimceni ba. Kuma ai ALLAH ya kareni da ga sharrinsa tunda ga shi yau gaskiya tayi halinta”.

      Shiru baice komai ba, dan zuciyarsa tafasar kishi take har yanzu akan wannan kalmar, tafi komai tsaya masa a zuciya fiye da abinda Miran Jasim ɗin ya aikata masa dan ya jima da sanin dama suna farautar rayuwarsa. Sai maganar rashin fitowar sunan Miran Arshaan shima na masa kaikawo, kamar zai mata magana akan hakan sai kuma dai ya haɗiye kayansa da tunanin ko Miran Jasim ɗin ne kawai ya fiddo mata da nasa hali. Amma in bai manta ba ranar a kalamanta ta masa nuni ne da mutane biyu ko yace fiye da ɗaya. Hakan na nufin bayan Jasim ɗin akwai wani kenan. To miyasa ta ɓoye? Bashi da mai basa amsa baya kuma buƙatar sonji a gareta yanzu dan ransa duk babu daɗi yake ji.

      Itama da kanta ta fahimci hakan, dan fuskarsa a tsuke take fiye da sanda suka fita kotun. Sai duk take jin kuma babu daɗi. Dan haka kawai take jin tausayinsa. Idan har zai shiga damuwa saboda halin wancan karen uncle ɗin nasa, yaya zai kasance kuma a randa zai san mahaifiyarsa da kanta ke halaka masa matan aurensa da duniya ke kallonsa a mai halakasu tsahon shekaru. Kai kai wannan al'amarin fa na taɓa mata zuciya wlhy sosai matuƙa. Ajiyar zuciya ta ɗan sauke a hankali, sai kuma ta kai hanunta saman lallausan gashin sajen fuskarsa ta shafa. Murya can ciki ta ce, “Kayi haƙuri? Ka amsa da hannu biyu jarabawace. Badan UBANGIJI baya sonka ba ya jarabeka da su. Shi kansa mulkin ma da kake kai ai jarabawa ce. Kai numfashinmu ma kansa jarabawace a garemu, dan UBANGIJI ya azurtamu da shi ne domin yaga zamu kasance masu bin dokokinsa ne ko kuwa masu bijire masa”.

            Idanunsa da ke lumshe tun sanda ta ɗaura hanunta saman fuskarsa ya buɗe a hankali, sunyi zajur fiye da yanda ya shigo da su a ɗan birkice. Hannun ya kamo yana kallonta, cikin tsananin kasala ya ɗaura lips ɗinsa a tsakkiyar tafin ya sumbata. Sai da ta matse jikinta tsabar yanda jininta yay wata irin yamutsawa har cikin brain. Yunƙurawa tai da nufin tashi a jikinsa ya hanata hakan, sai ma fuskarta da ya kamo cikin tafukan hannunsa ya manne lips ɗinsu waje guda. A tare suka saki ajiyar zuciya Iffah na rumtse idanu da ƙarfi. A tsorace take matuƙa, amma ta danne ta ƙarfin tsiya domin taimaka masa ya samu nutsuwar zuciya kamar yanda Mammy ta mata nasiha akan a duk sanda taga ya shigo da fushi tai ƙoƙarin ganin ta cire masa wannan fushin da damuwar ta hanyar jansa jikinta da hira da raha ko nasiha. Idan kuma ya nuna bukatar wata hidimtawarta ko ita ta fahimci akwai abinda ke sakashi shagala ko kwaranyewar damuwarsa da wuri to tazama jaruma wajen aikatawa kota bashi haɗin kai. Tunanin a iya abinda yake yi ɗin baza'ai gaba ba ya sata sakar masa jiki harta fara bashi haɗin kai. Gaba ɗaya ta sake rikita masa lissafi, dan abune da bai zaton samu da ga gareta ba anan kusa haka. Tuni idanunsa sun rufe ya juyesu a gadon ya shiga yamutsata yanda yake so cikin nutsuwarsa, dan a rayuwa komai na Tajwar Eshaan babu gaggawa a ciki, koda kuwa yana a wani yanayi ne da zai iya canjawa sai kaga a zahirance babu wannan canjin na gaggawa garesa. Dan nutsuwa da ƙasaita a jinin jikinsa take yawo da harbawar bugun zuciyarsa. Jin al'amarin ya fara zarce ƙaramin tunaninta tuni ta fara son ƙwatar kanta. Sai dai kuma babu hanyar samun wannan damar da ga jaruminta. Shin yaya lafiyar giwa da ma. Balle kuma ita da kanta ta ɓalle liƙin.

        Duk yanda taso tuna masa ɗinkin dake a tare da ita babu alamar yana ma iya jinta balle fahimta. Burinsa kawai yake ƙoƙarin cimmawa a cikin rufewar idanu.......

      (🏃Tsun-tsun da ya ja ruwa🥱)

★★★.... ★...

         Da ƙarfi, ƙarfin ƙarfi yake buga kansa a bangon ɗakin kurkukun mai tsananin duhu da ta iya ƙaramin windown kawai ake iya ganin ɗan ziririn haske. Gaba ɗaya zuciyarsa ta bushe, zafi yakeji a cikinta mai tsananin tururi dake ƙona zuciya. Shi shi Jasim ibn Abdul-majeed Aliy Qutb ne wata ƙaramar ƴar iskar yarinya yar cikin cikinsa tai sanadin kawowa cikin kurkuku. Shi Arshaan da ya koya sanin kansa a wajensa zai yima cin amana? Shi hadiminsa da ya ɗauka tsahon shekaru yana kyautatama zai ci amanarsa a gaban maƙiyansa. Wace irin rana ce wannan, mai tsananin duhuwa da babu lissafinta a cikin duka lissafe-lissafensa. Ta yaya shi Jasim ibn Abdul-majeed Aliy Qutb zai yi irin wannan faɗuwar baƙar tasan a gaban ƙarfin ikon ɗan maƙiyansa kuma maƙiyinsa.. 

      Cigaba da buga kan yake da ƙarfinsa yana ihu mai tsananin ƙaraji da ya saka masu tsaron ɗakun kurkukun nasa da Tajwar Eshaan ya bada umarnin bama tsaro mai tsananin tsauri tsora. Cikin ƙarfin hali ɗaya a cikinsu ya ɗan leƙo, ta ɗan hasken da ya hasko da ga ƙaramin windown ya hango fuskar Miran Jasim da tai wani irin jage-jage da jini dan ya fasa goshinsa. A zabire yay baya yana zazzaro idanu. Ƴan uwansa ya sanarma, babu ɓata lokaci sukai kiran shugaban jami'ai suka sanar masa dai-dai da yanke jikin Miran Jasim da jini ke rinjayarsa ya faɗi ƙasa.....

         ★★... ★...

     Rungumeta yay tsam-tsam a cikin jikinsa idanunsa a lumshe. Jin kukanta yake har tsakkiyar zuciyarsa.  Dan kuka take sosai fiye dana daren shekara jiya kasancewar yau ɗin fami yay akan ciwo. 

      “Ni ka kaini wajensu Ummu”.

  Ta faɗa cikin kuka. Yanda tai magana tana sake ɓarke masa da kuka ga hawaye shaɓe-shaɓe harda su majina ya sa yaji dariya na yunƙuro masa. Kamar ba yanzu ta gama iyayi a kotu ba, dan duk abinda ta dingama Miran Jasim akan idonsa ne tsaf. Amma jiba yanzu a ɗan abinda bai taka kara ya karya ba ta koma abin tausayi. Ya fahimci sai ya dage matuƙar dagewa akan ɗorata a irin layin da yake buƙata ta hau inba hakaba ragguwa za'ai, bakinne kawai cike da zance da tsiwa. Bashi da burin sake wani auren bayan ita, dan haka dolene ta shirya karɓarsa a duk sanda yazo. Murmushin da ke neman kufce masan ya haɗiye da ƙyar da saka hannu yana goge mata fuskar data ƙwaɓe da hawaye. Cikin dadisashiyar muryarsa data ƙara komawa can ƙasan maƙoshi a fusge ya furta, “Am sorry bazan ƙara ba”.

         “Wlhy zaka ƙara, ranar ba sai da kace bazaka sake ba amma yau ka ƙara, ni bazan sake zama a sashen na a kasheni kwana na bai ƙare ba”. Ta ƙara ɓarke ma sa da kukan taɓara.

    Yanzu kam kasa riƙe dariyar yayi, dole ya murmusa har jerarrun fararen haƙwaransa masu ɗauke da siririyar wushirya na bayyana a zahiri. Bashi da zaɓin da ya wuce sake rungumeta a jikinsa tsam-tsam yay murmushinsa iya san ransa. (Shi kam wannan Fitinanniyar yarinya ALLAH ya bashi, kuma yana so da ƙaunar abinsa fiye da zaton mai hasashe). A zuciyarsa yake maganar yana bata sumbata masu ƙyau a wuya. Kafin ya miƙe ya ɗagata cak zuwa bathroom. Idanunta ta rumtse sosai da ƙanƙamesa ita a dole karya gammata jiki kar kuma ta gansa itama.

        Gashi yay mata mai ƙyau bayan ya duba yau baiyi ɓarna ba dan ciwukan wancan ranar ma sun warke sai abinda ba'a rasa ba, taimaka mata yay tai wanka, hawaye kuwa da ya ga ba dainawa zatai ba bai sake ce mata komai ba kansu. Da zasu fito cewa tai ita wlhy bazata iya ba sai dai ya ɗauke ta. Baice komai ba, illa murmushi da yay a zuciyarsa ya ɗauke ta cak suka fito tana faman tura masa ƙaramin bakinta. Ga idanu sunyi luhu-luhu na kukan da tasha. 

       “Idan baki bar turamin bakin nan ba zan maimaita ni babu ruwana”. Ya faɗa yana tsane mata laimar ruwan kanta da towel. Narai-narai tai da fuska zata sake masa kuka ya ɗaura yatsansa saman bakinta ya ce, “Shiiii!! Harda kuka ma”. Babu shiri ta haɗiye abunta da maida bakin da sauri. Murmushi ya saki ya cigaba da tsane mata gashin.. kiran da ya shigo ta waya ya sashi dakatawa su duka suka dubi wayar, kamar bazai ɗaga ba dan har tana gab da tsinkewa sai kuma ya kai hannu ya ɗauka batare daya matsa da ga gabanta ba ko ɗauke towel ɗin da ga kanta. 

      Cikin girmamawa shugaban jami'ai ya shiga gaishesa da ga can, a takaice ya amsa masa murya a dake kamar bashine ke hidimtawa ƴar yarinya ba. Da ga can shugaban jami'ai ya ƙara nutsuwa sannan yay masa bayanin abinda ke faruwa. Shiru kamar bazaice komai ba kafin ya nisa a ɗan fisge da maganar nan tasa ƙasa-ƙasa ya ce, “Doctor Afif ya je ya dubasa a cikin kurkukun”. Daga haka ya yanke kiran.

           Kallonsa Iffah tai da jajayen idanunta, gaba ɗaya ya sauya kamar bashi ba ya koma mata Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdul-majeed da ta fara gani a sashen Mammah. Muryarta a ɗashe saboda kukan da tasha ta ce, “Miya faru?”. Kamar bazai kulata ba yana cigaba da goge mata kan tsahon minti biyu kafin ya motsa lips da ƙyar ya furta “Jasim”...........✍️

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_

_LITTAFI BIYU: 600_

_LITTAFI UKU: 800_

_LITTAFI HUDU :1000_

_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_


_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_


_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_


_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_


_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_


ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN


MARYAM SANI

ACCESS BANK

0022419171


SAI A TURA SHAIDAR BIYAN 


09033181070


IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA


09166221261


*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*


+227 96 09 67 63


Books biyar  1250CFA

Books hudu  1050CFA

Books uku  850CFA

Books biyu  650CFA

Bookk daya  450CFA


KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.


MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post