Daudar Gora book 2 page 58
Health College

Daudar Gora book 2 page 58

Daudar Gora book 2 page 58

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲      

  ✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨

           (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)

            𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (58)

.......Bayan sallar isha'i cikin dauriya Iffah ta amsa kiran Malikat Haseenat. Tafiya take cikin dabara dan ko yau ɗin ma dai tanajin zafin, ga zazzaɓi tun ɗazu yaƙi saukar mata. Ita bata san randa zatai sabo da wannan al'amari ba kamar yanda ya faɗa mata ɗazun. Ta ɗan yamutse fuska da cigaba da tafiyarta a hankali, dan ita kaɗai ta fito babu wani ɗan rakkiya, Tajwar Eshaan ma yana massalaci tunda ya tafi sallar magrib bai shigo ba. Kaɗan-kaɗan take ɗan cin karo da hadimai, duk da ko'ina na masarautar zagaye yake da haske ba ganeta suke ba, sai dai yanayin shigarta kansa su mata gaisuwar girmamawa kamar yanda suke ma duk wani ahalin masarautar babba ko yaro. Hannu ta dinga ɗaga musu kawai dan batajin yin magana har takai sashen Malikat Haseenat ɗin. Nan ɗin ma bawani sun ganeta bane sosai, dan sanda take ƙoƙarin shiga falon Malikat Haseenat ɗin da sauri Banou tai niyyar dakatar da ita. Sai dai mi, kallon ido cikin ido da sukai ma juna ya sa Hadima Banou ɗin zubewa ƙasa cikin rawar jiki da tsananin kaɗuwa. Har taune harshe take wajen gaida Iffah da ke mata kallon tsaf kamar mai son gano ainahinta. Sai da ta mula dan kanta ta yamutsa fuska da watsa mata harara. “K! Har yanzu baki daina bibiyar mutane ba ko? Karki fasa ina tafe kanki ai”. Ta faɗa tana wuceta batare data amsa gaisuwar tata ba.

     Jagwab Hadima Banou ta zube zaune a wajen zuciyarta na wani irin masifar harbawa. Sosai take tsoron wannan baiwar ALLAH, dan ita kaɗai tasan mi take ganowa tattare da ita. Ta jima a wajen kafin ta miƙe cikin rawar jiki ta fita. Can baya ta nufa cikin ƙaramin garden ɗin Malikat Haseenat da takan hutawa, da ga cikin wasu dunƙulallun fulawoyi ta zaro ƴar tukunyar ƙasa da bakinta ke ɗaure da ƙyalla an nannaɗe da zare. Warware zaren tai har yanzu jikinta na rawa, abubuwane a ɗaɗɗaure ciki kamar tsokokin nama, haka ta shiga fiddosu tana ware wasu a ƙasa, sai da ta gama zaɓowa ta maida sauran ta sake ɗaurewa ta ajiye. Wanda ta fiddo ɗin kam ta kwance huɗu ta sakesu, biyu da ga ciki tasa a baki ta cinye tana faman tanɗe lips. Duk abinda take yi tanayi ne tana waige-waige, har dai ta kammala ta miƙe da sauri ta fito....


      Tarba ta mutuntawa Iffah ta samu da ga Malikat Haseenat. Dan an shiryama zuwan nata da zuwa na musamman kamar yanda akan yima Tajwar Eshaan idan zai zo. Iffah har mamakin hakan tayi, dan bata taɓa tunani ko tsammanin tanada kimar da wani zai mata haka musamman idan akai dubi da shekarunta da kuma gidan da ta fito na talakawa. Malikat Haseenat da ke binta da kallo kuwa a kallo ɗaya da taima takunta ta fahimci halin da Iffah take, idanu ta ɗan lumshe tana mai jin tausayinta, dama tasan bazai iya haƙurin barinta ta warke yanda suke buƙata ba ai, dole ne sai ta dage ma yarinyar da abubuwan da zasu taimaka mata batare data dinga jigata ba. A zahiri kam hannu ta ware mata alamar tazo gareta. Iffah da ke murmushi kanta a ƙasa ta ƙarasa a nutse ta ko shige jikin nata. Wata irin tagwayen ajiyar zuciya ta dinga saukewa a jajjere haka itama Malikat Haseenat ɗin. Kusan minti biyu suna a haka kafin ta zaunar da ita kusa da ita gab-gab dan har cikin rai take jin ƙaunar yarinyar nan.

           Duk yanda Iffah ta dinga nuna jin kunya Malikat Haseenat bata barta ba sai da sukaci suka sha a tare cike da farin ciki, suna tsaka da cin abinci ne ma Daneen Ammarah itama ta shigo. Cike da girmamawa Iffah ta gaisheta, ta amsa mata da kulawa cike da so da ƙauna. Bayan sun kammala hadimai suka gyara wajen, Malikat Haseenat kuma ta bama Iffah wata ƴar madara a kofi mai daɗin tsiya data kasa gane ma wace irin madara ce, dan an mata wasu haɗi ne na musamman. Ɗagawa ɗaya ta shanye ta ajiye kofin, ƙaramin bowl dake ɗauke da haɗaɗɗen haɗin zuma da dabino da ƙwa-ƙwa dama abubuwan da bata sani ba nan ma ta bata tare da ƙaramin cokali a ciki da zata dinga ɗiba kaɗan-kaɗan tana ci.

         “Hafīdah!”.

    Malikat Haseenat ta kirata a hankali. Amsawa Iffah tai kanta a ƙasa. Mammah bata damu ba ta cigaba da faɗin, “Kin san miyasa nace kizo ki sameni?”. Kai Iffah ta girgiza mata ta ce, “A'a Jaddah”. Malikat Haseenat ta kalla Daneen Ammarah suka ɗan sakarma juna murmushi kafin ta sake maidawa kan Iffah. “Magana nake so muyi mai muhimmanci dan nasan bazakimin ƙarya ba”.

      “Insha ALLAHU Jaddah”.

    “Ɗazun a zaman shari'ar can kinyi wata magana ce data kasa barin raina akan ganin gawar Zawjata-almilk da kikai. Shin ko akwai wasu alamomi da kika gani tattare da ita? Ko kuwa kisa ne kawai na kai tsaye da raunika?”.

       Shiru Iffah tai da ɗan mamakin tambayar a ranta, ta kasa gane wann al'amarin, shi mai matan yace bai taɓa ganinsu ba, bayanan suke mutuwa, kuma ko gawarsu baya gani. Shin itama Jaddah ɗin duk matsayinta a masarautar bata taɓa ganin gawarsu kenan amma har waɗan can rubaɓɓun su Jasim ke iya gani ko mi?.....

      “Ibnati”

   Daneen Ammarah ta katse mata tunani. Firgigit ta kawo numfashi da kallonsu, sai kuma ta maida kanta ta risinar tana mai sauke ajiyar zuciya. “Jaddah zan faɗa miki duk abinda kike buƙatar ji, amma dan ALLAH ki gafarceni nima zanyi wata tambaya”.

         “Bismillah”.

    Malikat Haseenat ta faɗa kai tsaye cikin bata dama. Numfashi Iffah ta ɗan fesar ta nisa. Kafin tace, “Jaddah na kasa ganewa, shin duk matansa da suka rasu kuma baku taɓa ganin gawarsu ba kamar yanda shima yace bai taɓa gani ba kenan?”.

      Daga Malikat Haseenat har Daneen Ammarah kallon Iffah suke mamaki fes a kan fuskokinsu. Daneen Ammarah ta ce, “Shi Abni ɗin ya faɗa miki bai taɓa ganin gawar matansa ba?”.

       “Har suna raye bai taɓa ganinsu ba ma yace”.

     Kallon juna Daneen Ammarah da Mammah sukayi, sai kuma duk suka dubi Iffah da itama su take kallo ta gefen ido. “Tofa babbar magana”. Cewar Malikat Haseenat. Daneen Ammarah ta ce, “Babbar magana kam, ta gaske ma Mammah. Ni kaina ma ya sake ƙullewa akan al'amurin”.

      “Dole ne kam Ammarah. Amma Hafida-ti bara na baki amsar tambayarki, masarautar nan nada tsare-tsare irin nata da ƙa'idoji, a ciki harda zama iya huruminka, dan haka ni bana a cikin masu hurumin kan duk abinda ya shafi Zawjata-almilk na Hafidi, wannan hakkin mahaifinsa ce, ni kuma nawa hakkin a kansu yake tunda sune matan ɗana. Wannan ne dalilin da yasa ban taɓa gani ba. Kema da kike ganina tsaye a kanki saboda matsalolin da aka samu ne da har yasa ita Bushirat janyewa da ga al'amuran ki, ni kuma naga bazan iya yardawa ba na ɗauka na adana”.

      Cike da gamsuwa Iffah ta jinjina kanta. Sai kuma ta cigaba da basu bayani akan abinda suke buƙata. Riƙo hanunta Daneen Ammarah tai kamar a razane ta ce, “Cizon maciji kuma?”. Cike da mamakin yanda suka razana Iffah ta gyaɗa mata kai. “Eh Mamy saran maciji. Sai dai da alama kafin ma hakan tayi yunƙurin kare kanta da har ya zamto ɗakin ya kasance a harmutse”.

      “Ya rabba! Uwa. Mammah tabbas wannan alama ne na UWA. Itace, itace azzalumar bata barmu ba. Bata barmuba Mammah, tana raye wlhy tana raye”. Daneen Ammarah ta faɗa tana riƙe kanta da ke mata wani irin sarawa ta fara layi kamar zata faɗi. Da sauri Iffah ta miƙe ta riƙeta cikin tashin hankali. Hakam Malikat Haseenat duk ta rikice, dan ta fahimci matsalar tsahon shekaru data shuɗe ce da ga garesu ke neman dawowa ga Ammarah ɗin kanta. Da ƙyar suka iya samu suka kwantar da ita, a tare suka dinga tofa mata addu'oi. sannu a hankali ta fara lafawa tana sauke ajiyar zuciya a jajjere sai kuma barci ya ɗauke ta mai nauyi. Ajiyar zuciya Malikat Haseenat ta shiga saukewa da sauri-sauri, yayinda Iffah sunan uwa da Daneen Ammarah ta ambata ke faman mata kaikawo ƙirjinta na wata irin bugawa....

       “Jaddah waye UWA kuma?”.

   Kalmar ta suɓuto da ga bakin Iffah batare da ta shirya hakan ba. Idanu kawai Malikat Haseenat ta zubama Iffah batare da tace komai ba. Har Iffah ma ta fidda rai da ga cewarta. Dan tsahon kusan mintuna biyar kafin Malikat Haseenat ɗin ta nisa. “Uwa. Uwa.. uwa.. sanin wacece uwa na ƙunshe ne a cikin labarin masarautar nan Hafida-ti. Labarine mai tsaho da ya zama a cikin manyan labaran da suka kasance da ZUCIYAR ahalin Aliy Qutb gaba ɗaya. Duk da ya shuɗe, shuɗewa ta tsahon shekaru da muke tsammanin ƙarnin ya shafe da fatan daina tunashi koda a cikin tarihinmu da alama hakan bamai yiwuwa bane.”

       “Jaddah idan na dage akan son na sani ban shiga cikin hurumin daba nawa ba? Dan ina matuƙar so da zumuɗin na sani ɗin”.

    Murmushi mai ciwo Malikat Haseenat ta yi, sai kuma ta zuba idanunta akan Iffah tana ɗan jinjina kai. “Baki tsallake huruminki ba Hafida-ti, tunda kin rigada kin zama mu mun zama ke. Sai dai dokar wannan zuri'a ta daɗe da sharɗanta goge wannan tarihin domin mantashi da daina tunashi garemu har abada...” taja nannauyan numfashi mai haɗe da ajiyar zuciya. “Da zan iya wofantar da buƙatarki da nace karki sake tambaya. Amma inaji a raina bazan iya ba, dan inhar dai da gaske baya ce ke son dawowa ta maimaita kanta kamar yanda nake hasashe a kanki tun zuwanki masarautar nan dolene labari biyu ya dawo a lokaci guda domin kasancewarsu cikin juna duk da raina namin wasi-wasin taya hakan zata kasance bayan anyi ruwa ne an ɗauke ƙasa ta shanye kayanta?”.

       Sam Iffah bata gane cuɗaɗɗun kalaman ƙarshe ba, dan haka ta tsurama Malikat Haseenat idanu kawai ko ƙyaftawa babu. Murmushi Malikat ta sakar mata tare da lumshe idanu ta buɗe a kanta lokaci guda. “Idan har zan samu warwarewar lissafina zan sanar miki abinda kike son sani Hafida-ti. Zan sanar miki tarihi da tushen kasancewar uwa a cikin tarihin wannan DAULA kamar yanda kike buƙata”.

      A hankali Iffah ta saki murmushi mai ƙayatarwa da jinjina kanta. “Nagode sosai Jaddah, ALLAH ya ƙara girma da lafiya mai albarka da tsahon rai”.

      “Amin”.

Malikat Haseenat ta amsa tana gyara zamanta cikin wheelchair ɗinta da fuskantar Iffah da ƙyau........✍️


       _A muma to bara mu gyara zaman.🥱😂_



   

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*


*DAUDAR GORA Billyn abdul*


*KI KULANI hafsat xoxo*


*A RUBUCE TAKE Huguma*


*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*


*IDON NERA Mamuh ghee*



_LITTAFI DAYA: 400_

_LITTAFI BIYU: 600_

_LITTAFI UKU: 800_

_LITTAFI HUDU :1000_

_LITTAFI BIYAR: 1200_


_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_


_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_


_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_


_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_


_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_


_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_


ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN


MARYAM SANI

ACCESS BANK

0022419171


SAI A TURA SHAIDAR BIYAN 


09033181070


IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA


09166221261


*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*


+227 96 09 67 63


Books biyar  1250CFA

Books hudu  1050CFA

Books uku  850CFA

Books biyu  650CFA

Bookk daya  450CFA


KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post