Rumbun Qaya hausa Novel Page 22

Rumbun Qaya hausa Novel Page 22

Rumbun Qaya hausa Novel Page 22

RUMBUN QAYA


©️®️_Hafsat Rano_


        Page 22
****Sautin bugun zuciyar sa ne ya sauya bayan fitar Adam din, ya runtse ido sosai tsoro na shigar sa, tsoron maganganun Adam din wanda yake da yakinin tabbas akwai  wanda yake taimaka musun kamar yadda yace, amma waye? Ba zai iya dubawa ba dan yasan zuciyar sa zatayi bugawa ma baki daya musamman idan ya samu wanda yayi matukar yadda dashi da laifin.


"Ya Allah!" Ya furta a hankali yana sake chusa wayar sosai a cikin aljihun rigar sa yana son dauke hankalin sa wajen hakura da ganin abinda zuciya da gangar jikinsa basu amince masa da gani ba.


"Please oga karka daka ta, tashi dan Allah."


"Ba komai Habeeb, muje kawai."


"Ok ." Ya tada motar suka fita. 


    Tana zaune a office din suna hira da Abdulhakeem wanda ta kura fiye da rabin hankalin sa na kan wayar hannun sa, chatting yake da alama dan yanayin yadda yake amsa mata wata maganar zaka tabbatar da ya kasa hankalin nasa waje da yawa. Shiru tayi masa ta dauki wayarta itama kawai ta hau dannawa ko ta rage zaman dan babu abinda zatayi har Oga Kamal ta tambaya yace ya bari Aryan ya dawo. Tayi mamakin da be yi mata maganar abinda ya faru jiya ba, gashi tana son sanin halin da Daddyn yake ciki dan kusan kwanan zaune jiya tayi tana tunanin abinda ta ji, tabbas nishin mutum ne me cike da wahalarwa, tana rufe idon ta shi take hasasowa hakan ya hana ta samun isheshan bacci sosai. Wayar tace tayi kara ganin Hamma Hydar ne yake kira yasa ta dauka da sauri.


"Hamma na."


"Na'am kanwata, gani a garin naku."


"Kano?"


"Eh shigowa ta kenan."


"Laaa, shine baka fada min ba?"


"Wallahi zuwan urgent ne, Abby ya taso ni, kina ina yanzu?"


"Office."


"Ok, zan kiraki ki jirani zanzo na dauke ki."


"Ok Hamma, sai kazo."


  Tana cikin wayar taga fitar Abdul sai ya kasance babu kowa a office din, Zainab ce ta shigo rike da wani file ta dire mata a gabanta, takardu ne a ciki fal ta daga kai ta kalle ta


"Menene wannan?"


"Aiki ne, idan kin gama wasu na jiranki, dan na lura zaman dumama seat kawai kike yi, ko da yake kin samu masu daure miki gindi, farar kalar ke kwasar su da alama."


"Ke a matsayin ki na waye da zaki sakani aiki?"


"Hehe." Ta kwashe da dariya


"Wato kina da baki ashe, a gaban Oga sai ki dinga yin kamar tsohuwar munafuka, da haka kika yi amfani kenan wajen tura kanki gareshi, sai ayi mu gani ai, aiki kuma shine ya saki bani ba, dan ni bani da lokacin batawa akanki, idan zakiyi gashi nan, idan ba zaki ba ki barshi, idan ya dawo ya sake dole ai."


"Har shi ma bashi da hurumin sakani aiki dole, nasan rights dina dan haka ba zan ba, idan yazo sai ki fada masa nace ba zan ba, ke da suke biyan albashi sai kiyi."


  Kusan mutuwar tsaye Zainab tayi, bata dauka yarinyar na da gut haka ba, ganin ta take kamar doluwa a kullum, aikin Cynthia ne ba wani Aryan da ya sata, kawai neman rigima suke da Raihanan sai gashi ta nuna mata itama eh ce, juyawa tayi ta fita ba tare da ta sake magana ba, bayan kwafar da tayi kawai kuma bata dauki file din ba. Tashi Raihana tayi rik'e da file din, ta bi bayanta ta dire mata akan table tayi juyowarta tana sabani


"Gani jaka, ba zan ba wallahi."


 Tayi zaman ta, ta ma kunno kallo a wayarta ta dora akan table din tana kalla.

  Ta dade tana kallon har ta gaji ta koma game daga nan ta kashe wayar ganin rana tayi har lokacin tafiyar ta yayi, Hamma Haydar ta kira yace mata ta jirashi wani abu ne ya tsaida shi amma yana nan zuwa karta tafi. Jugum tayi a zaune dan wasu har sun soma tafiyar da kad'an kad'an har kowa ya yaye sai ita kadai sai Kamal da yake cikin office dinsa ya dukufa akan aikin da yake yi. Wani kiran Hydar din ne ya sake shigowa, sai dai wannan karon da sauri yace;.


"Raihana, ya sunan wanda kike PPA a wajen su."


"Oga Aryan ne, da Oga Kamal."


"Wai da gaske?"


"Eh sune, Ka sansu ne?"


"Kwarai kuwa, sai dai nazo zamuyi magana kawai."


"Dan Allah Hamma gaya min, menene?"


"Wallahi labarin me tsawo ne Raihana, amma ki bari nazo."


"Toh sai kazo." Ta ajiye wayar cike da zulumi da tunanin yadda akayi ya sansu.  

****Zuwan sa gidan Ya Nabeela ya hana shi aiwatar da abinda zuciyar sa take fada masa, kashe wayar tasa yayi gaba daya bayan ya karbi key dinsa a wajen Habeeb yace yaje kawai yayi zaman sa a gidan dan wani irin tsoro ne ya dinga shigar sa, tsoron abinda zai taarar. Har bayan azahar yana gidan sai a lokacin yaji nutsuwar tafiya yayi mata sallama yana sake danne zuciyar sa da ganin abinda zai tashi hankalin sa. Tuki yake a hankali ya ma sauka chan gefen titin dan ma kar ya hana masu sauri sai yan napep da suke ta daga masa hannu suna masa horn be kula su ba, da haka har ya kai office din ya samu gefe daya yayi parking ya ciro wayar ya kunna da niyyar kiran Kamal yaji ko yana office har lokacin dan haka babu mota a harabar wajen ko daya. Message din hoton da ya fito a saman notification bar din wayar ya dauki hankalin sa, hannun sa na wani irin rawa ya danna kan hoton wanda ya dauke shi direct zuwa kan chat din Adam din. Idon sa ne ya soma yi masa dishi-dishi kafin ya bud'e masa tar ya gani, hoton tane a zaune tare da Hajiya Zeenat, a cikin falon gidan su sanda take mika mata key din nan. Da sauri da sauri ya shiga bud'e sauran hotunan wanda duk itace a jiki suna magana da Hajiya Zeenat ko kuma tana murmushi. Audios din ya bud'e yana girgiza kansa da wani irin yanayi. Muryar tace ta bayyana tar a ciki tana shaidawa Hajiya Zeenat ta dauko key din, da sauri ya katse ya shiga wani, sai dai baya iya dire su har karshe yake kashewa ya kunna wani.


"Why Raihana? Why?" 


Ya fada da karfi yana balle murfin motar, ya fito ya nufi cikin building din da wani irin sauri.


   Tashi tayi daga zaman da tayi da nufin fitowa ta sauko kasa kawa ta jira Hamma Haydar din dan saman yayi mata shiru sosai dan bata ma yi tunanin akwai mutum ba. A hanya sukayi kicibis tayi wani irin mugun ja baya amma duk da haka sai da jikinsu ya hadu kanta ya bugu da gefen kafadarta. Ture tayi da iyakar karfin sa, tayi baya kamar zata fadi tayi saurin dafe bangon dake wajen."Me yasa? Me yasa zaki ci amanata?" Yace yana matso ta


Zaro ido tayi dan sai da yayi magana ta lura da yanayin da yake ciki


"Why Raihana?" Karo na farko da ya taba fadar sunan ta kenan, amma a yanayin da yake nuna tsantsar tsana da kiyayya


"Me nayi?"


"Baki sani ba?"


Girgiza kai tayi, ya cije lips dinsa na kasa da karfi yana wurga hannun sa baya, sai kuma ya sake matsowa ya bud'e wayar sa ya nuna mata hoton


"Wannan ma baki sani ba?"


"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun."


"Tell me, shima baki sani ba? Ko photoshop ne? Idan kince baki sani ba, wannan ma ba voice dinki bace ba?" Ya danna audio din 


"Na sani, na sani, amma zan maka bayani."


"Bana so! I don't want to hear anything from you, babu abinda zaki ce min, i hate you! bana son sake ganin ki a gabana, just goooo." 


"Dan Allah zan yi maka bayani, wallahi amfani tayi dani, she used me wallahi, ban aikata abinda kake tunani ba, dan Allah."


"Allah bana son ji, ki tafi kawai and don't ever show your face again."


"Please..." Ta hade hannayen ta waje daya tana kuka


   Juyawa yayi da sauri ya shige office din dake kusa da wajen, wanda bashi da maraba da hadadden falon gida. Kuka ta durkusa a wajen tanayi, kamar ranta zai fita, duk abinda ake Kamal yana sama be sani ba, Hydar ne ya kirata yace yazo, amma jin muryar ta yasa shi katse kiran kawai ya shigo office din kansa tsaye dan ko magana ta kasa. A kofa ya tarar da ita tana gursheken kuka, ya dago ta yana tambayar abinda ya faru, a cikin kuka take masa bayani wanda ya kasa fuskantar komai, sai dai ya fuskanci da Aryan ne.


"Ina Aryan din?" 


Yace,da hannu ta nuna masa office din, yace su shiga, tayi gaba yana biye da ita, yana son tabbatar da abinda yake zargi. A baya ya tsaye sanda suka karasa ba tare da ya shiga ciki ba.


   a Sanyaye ta turo kofar ta shigo, ta hange shi tsaye ya bada bayan sa yana kallon window hannun sa rike da curtains din, takowa ta shiga yi tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki, zuciyar ta na wani irin harbawa irin wanda bata taba ji ba. Motsin ta ya sashi juyowa kafin ya saki curtains din ya zuba mata ido cikin yanayin da yake nuna tsantsar bacin ransa. Ji tayi tamkar ba zata iya karasawa ba, kamar ta zube a wajen kawai tayi ta rusa ihu saboda tsananin tsoron da yake shigar ta. Da jan kafa ta karasa gaban nasa tayi saurin dukawa k'asa idanun ta na cigaba da zubda hawaye, hawayen bakin cikin abinda yake zargin ta dashi, ko da yake ta aikata din a baya duk kuwa da a rashin sani ne, amma bata taba zaton abun zai dawo musu a wannan lokacin ba


"Me ya kawo ki?" 


Yace cikin dashashiyar muryar sa dake fidda amon sautin yadda ransa ya kai matuka a baci. Shi mutum ne mara yarda sam, rayuwar sa ta baya ta sashi rashin yarda da kowa da ma komai, Ya Nabila kadai ya aminta da ita, ita kadai ya yarda ba zata cutar dashi ba, sai Kamal sai kuma zuwan ta rayuwar shi, ya yarda da ita fiye da yadda ya yarda da kan sa, har ya kan ji nutsuwa a duk lokacin da yake tare da ita, amma kuma...


"Dan Allah kayi hakuri." 


Tace cikin shashekar kuka, girgiza kansa yayi yana dauke kansa daga kallon ta dan ma kar zuciyar sa tayi masa rawa akan hukuncin da ya yanke, kar tayi rinjaye akan sa har ta sakashi karya alkawarin da yayi ma kansa na rashin kyale duk wanda ya ha'ince shi.


"Ki tashi ki fita daga nan wajen, I don't want to see you ever again."


"Please ka saurare ni, dan Allah ka bari kaji abinda zan fada maka."


Durkusawa yayi a gaban ta kafar sa daya ya choge ta yana duban ta idanun sa sun yi mugun kadawa 


"I hate mutane masu fuska biyu RAIHANA , haka nan bana sake yarda da wanda yaci amanata, ki tashi ki fita bana son ganin ki, get out of my life!!"


"Dan Allah..."


"I said get out!" 


Ya fada da karfi bayan ya mike tsaye, hannun sa na mata nuni da kofar, rud'ewa tayi kasancewar yau ne karo na farko da aka fara mata irin wannan tsawar, juyawa yayi ya sake bata baya yana jin yadda take kuka sosai, kukan da yake jin tamkar ana daddatsa masa jikin sa, kamar ana zuba masa garwashi a cikin kokon kansa. 


  Juyawa tayi da sauri harda dan gudun ta, ta fice daga wajen tana rusa kukan sosai, runtse idon sa yayi ya bud'e kansa da yake masa wani irin ciwo ya rik'e ya shiga matsawa a hankali zuwa kujerar dake gefe ya zauna yana tallafe kan nasa


"Sai kayi nadamar abinda kayi Aryan, sai kayi nadama a lokacin da bata da amfani." 


Dagowa yayi da sauri ya kalli kofar, matashin saurayin da a kalla zasuyi kusan sa'a ne a tsaye yana duban sa, fuskar sa ce ta shiga dawo masa zuwa wani lokaci me tsawo, kamar sa ce tun a lokacin be chanja ba, ba kuma yana tunanin ko da zata chanja din ya kasa ganeshi, tare aka hada su aka tarwatsa musu rayuwar su, aka raba su da mutane masu muhimmaci a rayuwar su


"Haydar?" Yace yana tashi tsaye da sauri


"Sai kayi nadamar abinda kayi ma kanwata Raihana, kana nan da zuciyar ka da rashin yafiyar ka, kanwata bata chanchanci mutum irin ka, kamar yadda ka rasa mu a baya, haka zaka sake rasa mu a wannan lokacin. Sai ya juya ya buga masa kofar da karfi


"Kanwata? Raihana? Raihana Nasir? BARRISTER NASIR MATAWALLE?" Duk a lokaci daya sunayen suka shiga amsa kuwwa a saman kansa 


"Ya salam!!" 


Yace da sauri yabi bayan sa, da gudun gaske ya dinga sauka daga stairs din yana hada bibiyu, harabar ya fito babu ko mota daya sai tasa, gaba yayi zuwa wajen masu gadi suka ce yanzu mota ta fita, gate din ya fita ya dinga waige-wage sai dai ko kurar su be gani ba, bare ya san in da suke nufa
*TUNA BAYA*


SHEKARU MASU YAWA DA SUKA SHUDE SUKA HAIFAR DA TARIN ABUBUWA MASU YAWAN GASKE, RAYUWAR GIDAN NASIR MATAWALLE DA AMININ SA IBRAHIM MUKADDAS.🖍️🖍️🖍️🖍️ MUN SHIRYA???? MU HADU A AREWA BOOKS😎😎😎ZAFAFA BIYAR.....× 2023

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥💥💥💥🔥🔥🔥🔥💥🔥💥🔥🔥💥🔥🔥💥💥💥💥💥🔥💥🔥🔥🔥🔥INA MAABOTA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR WRITERS? WANNAN KARON MA MUN SAKE DAWO MUKU DA ZAFAFAN LITATTAFAN MU, MASU DAUKE DA ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A ZUCIYA


KU GARZAYO. ZAFAFAN NA KU SUN SAKE TAHOWA DA WASU ZAFAFAN LITTATTAFAN MASU DIMBIN DARUSSA NA MATAKAN ILMANTARWA RAYUWAR MU TA YAU DA KULLUM...SAFIYYAH HUGUMA

A RUBUCE TAKE (KADDARATA)♥️


HAFSAT RANO

(RUMBUN QAYA)🥰


MAMUH GEE

(IDON NERA)🤩


NANA HAFSATU

KI KULA NI (MALLAKIN ZUCIYA)😘


BILLYN ABDULL

DAUDAR GORA (CIKI KA SHATA)💗


DUKA DUKA WADANNAN LITTATTAFAN ZASU ZO MUKU NE CIKIN FARA SHI MAI RAHUSA KAMAR KO DA YAUSHE. 


DUKA BIYAR DIN AKAN NERA DUBU DAYA DA DARI BIYU 1200


GUDA HUDU AKAN NAIRA DUBU DAYA 1k


GUDA UKU AKAN 800


GUDA BIYU AKAN 600


GUDA DAYA AKAN 400DADIN DADAWA, MUNA TALLATA HAJOJIN KU AKAN FARASHI ME SAUKIN GASKE! SANNAN GA BIYAN BUKATAHANYOYIN DA ZAKU IYA TUNTUBAR MU DOMIN ZAMA CIKIN SAHUN FARKO NA WANNAN SABUWAR TAFIYAR SABUWAR SHEKARAR SUNE;

MASU BIYA TA BANKI ZAKU BIYA A WANNAN ACCOUNT DIN BANK: ACCESS BANK 


ACCOUNT NAME: MARYAM SANI


ACCOUNT NUMBER; 0022419171


SAI A TURA EVIDENCE OF PAYMENT HADE DA ACCOUNT NAME TA WHATSAPP TA WANNAN NUMBER;  


09033181070
IDAN KUMA KATIN WAYA NE NA MTN SEKU TURO KATIN VTU/SHARE AND SELL KO NUMBER KATIN HADE DA SHEDAR SA TA WHATSAPP ZUWA: 09166221261


FARASHIN LITTTAFAN ZAFAFA BIYAR NA CHANJAWA DA ZARAR AN KAMMALA SU. SAI KU YI SAURI KU GARZAYA DOMIN A DAMA DAKU A WANNAN SABUWAR TAFIYAR SABUWAR SHEKARAR 2023🔥🔥🔥🔥🔥🔥💥KU GARZAYO A SAKE DAMAWA DA KU A WANNAN SABUBAR TAFIYAR MAI DAUKE DA SALO NA BAN MAMAKI. KAR KU BARI AYI BABU KU.DOMIN ZAFAFA BIYAR NA KU NE. 😘🤩

[05/01, 21:53] Billyn Abdul 2: 🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR MAZAUNA K'ASAR NIJER?*🤏🏾


*TO KU MARMATSO KUSA TA SAMU!!*🇳🇪🇳🇪


*MUN SAURARI KOKENKU MUN KUMA AMSA*


*Zafafa biyar dinku sun samo muku hanyar biyan naku kudin karanta litattafan zafafa har guda biyar din*


*ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE*


+22799643131


*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*


*DAUDAR GORA Billyn abdul*


*KI KULANI hafsat xoxo*


*A RUBUCE TAKE Huguma*


*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*


*IDON NERA Mamuh ghee*


*KUDIN LITATTAFAN ZAI KAMA KAMAR HAKA*


Books biyar  1250CFA

Books hudu  1050CFA

Books uku  850CFA

Books biyu  650CFA

Bookk daya  450CFA


*MUNA GODIYA DA SOYAYYARKU GAREMU AL'UMMAR NIJER,MUNA MUKU FATAN ALKHAIRI TARE DA GODIYA BISA ZABIN ZAFAFA BIYAR*🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post