RQ
Page 21
***Tashi tayi jiki a sanyaye ta bishi, su Zainab suka bita da kallo kamar zasu cinye ta. Sai da ta fara knocking a kofar dan ya riga ya shige sannan ta tura kofar ta shiga kanta a k'asa sosai tana tsoron hada ido dashi. Tana jin idanun sa akanta sanda ta shigo har ta karaso ta tsaya a gaban table din.
"Goodmorning sir." Ta maimaita gaishe shi jin yaki cewa komai
"Zainab bata fada miki ina kiranki ba?"
Girgiza kai tayi
"Bata fada min ba."
Waya ya jawo gabansa yayi kira
"Come please."
Yace kawai ya ajiye wayar. Cikin siritar da murya ta shigo tana gwalli tazo ta tsaya ta gefen kujerar sa
"Sir gani."
"Nace idan tazo ki turo min ita kamar ko?"
"Na'am?"
"Yes! Me yasa baki fada mata ba?"
Kallon bangaren da Raihanan take tsaye tayi,sannan tace
"Na fada mata sanda ta shigo, amma bata ji ba cox bata min magana ko nayi mata ni."
"Innalillahi!" Tace tana kallon Zainab din
"Eh a gabana kika gaisa da kowa kika ki kulani, ina ta miki magana kikayi biris kika wuce office na dauka ma kinji ne kawai ba zaki amsa bane ba."
"Ikon Allah!"
Kawai tace ba tare da tace komai ba kuma, abin ya tsallake tunanin ta gaba daya ma, shiyasa ta kasa cewa komai tana jiran gogan da ya kirawo ta yayi magana
"Excuse us please."
Ya cewa Zainab kawai ba tare da ya ce komai akan abinda tace din ba, sai data fara dan dukar da kai alamun respect sannan ta juya ta fita.
"Zauna." Ya nuna mata kujera, zama tayi a darare tana jiran abinda zai ce
"Ya jikin naki?" Yace yana kokarin bud'e computer sa
"Na samu sauki."
"Ok good, aiki zan saka ki, amma anan zaki zauna kiyi shi."
"Ok sir."
Takarda ya turo mata gabanta yace ta duba kafin ya gama shigar da komai, ta dauka ta fara dubawa shi kuma ya cigaba da abinda yake yana jin nutsuwa sosai na saukar masa.
***Yau baki daya Kamal be shigo office din ba, ya dai kira Aryan din ya sanar dashi ba zai shigo ba shiyasa ma aikin ya rinchabe ma Aryan din dole ya rarrabawa su Abdulhakeem aikin Raihana kuma na taya shi da wani anan office din nasa. Yanayin yadda aikin ya dauki zafi sosai ya saka sam basu gane lokaci ya ja sosai ba dan har azahar na neman kufce musu. Sallah yace suje suyi dukka sannan suyi lunch daga nan sai suzo su kara ko away daya be sannan kowa ya tafi. Tunda Raihana tazo office din basu taba dadewa irin ta yau ba, gashi ta kasa ce masa zata tafi dan ya tsare ko ina motsi kad'an zai ce ta duba masa abu kaza wanda kuma ko ta duba daga baya sai ya sake dubawa dan ba wai tasan kan aikin bane dukka, musamman harka ta kudi da lissafi yana da rikitarwa sosai. Ta idar da sallar kenan tana zaune tana tunanin ko ta gudu sai tunanin kiran da Hajiya Zeenat take mata ya shigo mata, ta manta shaf tace zata kirata idan zata zo gashi bata fadawa Kamal din ba ma bare ya gaya mata abinda zatayi. Wayar ta, ta dauka tayi masa text message ta ajiye tana jiran reply dinsa akan zuwan.
"Call her kice zaki taho yanzu."
Yayi mata reply a take, tana duba message din ta kira number Hajiya Zeenat din, tace mata zata zo yanzu, toh tace mata duk da bata gidan amma ta lissafa zata iya zuwa kafin ta karasa ta jirata ko ma suyi daidai dan bata so damar yau din ta kufce mata.
Tashi tayi daga wajen sallar ta gyara mayafin ta sannan ta komo office din ta ganshi ya dora akan aikin ba ko hutawa, sau daya tak ya kalle ta sanda ta shigo ya cigaba da abinda yake yi, daga in da take ta tsaya tace masa zata tafi. Banza yayi Mata kamar ba dashi take magana ba, wanda a zahiri ya ji ta sarai sai dai haka kawai yaji maganar ta, ta dan bata mishi rai haka kawai kuma. Sai da ta kara maimaitawa sannan yace
"Go."
A bacin rai duk da be dago ba amma taji yanayin yadda yayi sounding, juyawa tayi kawai tayi ficewarta ya bi bayan ta, da kallo nan take sai yaji aikin ya fice daga kansa. Lunch din da yayi musu order dukkan su ma'aikatan ya kalla, kowa ya dau nasa sai nata kawai da nashi a wajen a ajiye. Ajiye pen din hannun sa yayi ya ji ba zai iya cigaba da rubutun ba, ya rufe komai ya tashi ya hau tattare kayan sa.
Tana tafe suna waya da Kamal yana gaya mata abinda yake so tayi masa a cikin gidan, har ta karaso gate ta dagawa masu gadin hannu dan har sun saba sannan ta fita. A daidai lokacin shima Aryan ya fito Habeeb dake zaune karkashin wata bishiya yayi saurin sanarwa Kamal fitowar Aryan din dan sun san dole idan ya ganta zai iya cewa su rage mata hanya kuma hakan zai bata musu shirin su. Da sauri Kamal yace mata ta samu wani wajen ta dan labe ta jira wucewar motar Aryan din. Da sauri ta shige wani dan lungu ta labe. Daga ganin yadda ya fito neman ta yake yi, yadda yake rarraba idanun sa a tsakanin wajen ya tabbatar musu da hakan, wajen sa Habeeb ya karaso bayan ya jawo motar
"Baka ga wata yanzu ta fita ba?"
"Ai da yake yallabai bacci ne ya dan dauke ni naji sanyin kasan bishiya, inaga ta fita ban lura ba sam."
"Ok, muje."
Ya bud'e masa motar ya shiga. Ta na nan a labe suka zo suka wuce sannan ta fito ta karasa titi ta samu abun hawa ta fada masa in da zai kaita.
Tun kafin ta karasa Hajiya Zeenat tayi waya tace a barta ta shiga, dan haka kai tsaye ta wuce in da tasan zata same ta. Falon tsit babu motsin kowa, dan zama tayi kad'an tana sake karewa falon kallo, sai ga kiran Kamal.
"Kinga kafar bene?"
"Eh." Tace tana kallon stairs din
"Yawwa, tashi ki hau karki kashe wayar."
Tashi tayi a tsorace ta kama matattakalar ta fara hawa cike da tsoro, babu abinda kirjinta yake sai dukan uku-uku. Shi yake directing dinta har taje kofar, tasa hannu ta murd'a da nufin budewa amma sai ta jita a rufe
"A rufe take da key."
"Gosh!" Ya hau kama goshin sa yana murzawa
"Kinsan me zaki? Saka bakin ki a jikin kofar ki kira sunan Daddy."
"Ok." Tace, ta dan makala kanta a hankali tace
"Daddy."
Shiru babu wani motsi, ta sake maimaitawa a karo na biyu, sai taji kamar motsi kamar gurnani, sake fadan sunan tayi, sosai taji sautin numfashin babban mutum me cike da wahalarwa.
"Akwai mutum a ciki Sir, wallahi akwai mutum." Ta fada a rude tana yin baya
"Calm down Raihana, don't panic please, maza ki koma falon kaza ki jirata, suna daf da shigowa gidan kiyi sauri."
"Ok."
Tace da sauri ta yi hanyar sauka daga saman, ta dinga hadawa da bibiyu ta sauka ta zauna tana dafe kirjin ta
"Daddyn Aryan ne kenan a ciki?"
Wani hawaye ne ya biyo mata ya sauko tayi saurin share shi jin alamun ana shigowa, tayi matukar kokari wajen daidai ta kanta sanda Hajiya Zeenat ta karaso ciki fuskar ta a sake da fara'ah
"Yau ga yata da ta gujeni."
Zamewa tayi daga kujerar ta zauna akan carpet sannan ta hau gaishe ta
"Tashi ki hau kujera mana, tashi tashi sai kace wata bakuwa Raihana?"
"Nan ma yayi Anty."
"Toh ai shikenan, ya gida ya mutanen gidan?"
"Duk lafiya lou."
"Masha Allah , ya labarin Abban ki kuwa? Kin sake zuwa kin duba shi?"
"Ai ya fito ma."
"Kai haba? Ah Masha Allah, yaushe? Shine amma baki fada min ba."
"Last week ne Anty, sannan bani da lafiya."
"Ok haka ne, toh sai na shirya ai naje na gaishe shi ko?"
"Ai baya nan Anty,baya kasar."
"Ah lafiya dai ko?"
"Da sauki toh."
"Ayya toh Allah ya bashi lafiya, yana dawowa ki sanar dani zanje na duba shi nayi masa barka da arziki."
"Ok tam in sha Allah."
Wayar tace tayi kara, message ne daga Kamal
_"maza ki fice Aryan yana hanyar zuwa."_
Yunkurawa tayi da sauri
"Hajiya zan tafi, Addah tana kirana."
"Toh, toh shikenan sai munyi waya ko? Wajen aikin naki ba dai wata matsala ko?"
"Babu komai Anty, nagode."
Sauri ta dinga yi tana waige har ta fita daga unguwar baki daya, har ta samu napep ta shige. Bayan wajen mintuna ashirin da tafiyar ta sannan Aryan ya iso. Da k'yar ya iya bari Habeeb yayi parking a harabar gidan ya balle murfin motar ya shiga ciki a sukwane. Yanayin yadda ya shigo gidan ya saka Hajiya Zeenat mikewa tsaye,
"Lafiya?"
Ta tare shi tana tambayar sa, wuce ta yayi ya fara hayewa saman da sauri da sauri. Bin bayan sa tayi da sauri tana kiran sunan sa. Kai tsaye dakin daddy ya nufa, yana zuwa ya tura kofar da karfi. Babu kowa a ciki sai dakin da yake a gyare ko ina.
"Menene wai Aryan?"
"Ina Daddy?" Yace yana zare mata ido cikin matukar bacin Rai.
"Mtsw! Taja tsaki,
"Dalilin da zaka shigo gidan a haka? Baka san yayi tafiya bane ko me? Me kake nufi kenan da abinda kayi yanzu?"
"Ina kika kaishi? Yana ina?"
"Ban sani ba, tunda baka yarda ba ai gidan ba bakon ka bane ba, ka shiga ka bincika. Mtsw!"
Ta juya ta barshi a tsaye a wajen. Dafe kansa yayi da hannu biyu da yake masa wani irin bugawa ya shiga bi dakunan daya bayan daya yana dubawa har da lekawa kasan gado. Text message din da aka tura masa ya sake dubawa yana son sake tabbatar da abinda yake kunshe a sakon
_"Kayi sauri kaje mahaifin ka yana rufe a dakinsa, suna kokarin chanja masa dakin dan haka sai kayi sauri."_
Abinda ya taso shi kenan afujajan duk da be san waye yayi amsa message din ba, waye yake kokarin wasa da hankalin sa? Ya tambayi kansa. Kiran Ya Nabeela a karo na kusan biyar ya shigo, dagawa yayi yana yarfe hannun sa ya zauna a gefen gadon Daddyn ya dafe kansa sannan ya daga
"Ya ake ciki Aryan?"
"Bata ciki ya Nabeela."
"Na shiga uku, yanzu ya zamuyi?"
Idon sa ne ya sauka akan yar karamar wayar Daddyn da ta kusa shigewa kasa gado, hannu yasa ya dauka ya ganta a kashe alamun charging ya kare
"Na ga karamar wayar sa Ya Nabeela."
Ya mike da sauri yana rike da wayar,
"Sake duba dakin sosai Aryan, babu wani abu kuma?"
Duddubawa ya hau yi amma be ga komai ba, fitowa yayi ya fice da wayar daga gidan.
Asalin office dinsa ya nufa ya kira Kamal yace su hadu a can, yana zuwa Kamal din ma na zuwa kamar wanda yake a kusa, abinda yake faruwa da tunanin da Ya Nabila tayi har zuwa text message din da aka tura masa ya nuna ma Kamal din, shiru yayi kamar me nazari wajen mintuna biyar kafin yace
"It's time da ya kamata muje muga Barrister Matawalle!"
"Yaushe?"
"Zan yi kokarin nema mana ganin shi ta wajen wanda ya sanar min da labarin fitowar sa, ina ganin kar mu wuce kwana biyu bamu neme shi ba, sannan maganar Daddy ka bar komai a wajena."
"I trust you with my life Kamal, ka sani kai kadai na yarda dashi."
"Ba zaka taba dana sanin taraiya dani ba Aryan, I promise you that."
"Shikenan. Allah yasa."
"Amin, muje mu kwantar wa Ya Nabeela hankali, in sha Allah ba abinda zai faru."
"Ok Allah yasa."
"Amin."
***Washegari ya tashi da wani irin ciwon kai sosai, dan dama tun dare yake jin alamar sa, haka ya daure ya shirya ya fito office. Kamal yau ya riga shi zuwa saboda rashin shigowar da be yi ba jiya, wanda aikin Aryan din ne gaba daya ya hana shi shigowa, a yanzu haka yasan komai akan daddy har in da suke kaishi, kuma shine da kanshi yayi wa Aryan din text message bayan ya aikawa Hajiya Zeenat nata akan tayi gaggawar dauke Daddyn daga gidan. Dan hatta gidan da ta maida shi suna kallon ta, tabbas karshen ta ne yazo dan haka cikin kankanin lokaci zasu kammala komai su damke ta, bayan sun samu dukkan hujjoji akanta.
"Ya labarin zuwa gidan Alhaji Nasir din?" Aryan yace bayan ya shigo office din nasu sun gaisa
"Gobe in sha Allahu zamu je mu ganshi."
"Ya amince?"
"Ko be amince ba, zuwa zamuyi dan idan ya ganmu ma dole ya amince, disk din wajensa shine kawai abinda muke jira dan shine yake dauke da komai da ya faru ranar, babban dalilin da ya kaishi prison Kenan, amma duk da haka be yarda ya bada shi ba tsawon lokacin."
"Ina fatan komai zai zo karshe Kamal, na gaji wallahi, inaso nayi rayuwa kamar kowa, amma na kasa, idan ba gani nayi an daure Hajiya Zeenat ba hankali na ba zai taba dawowa jiki na ba."
"Lokacin yazo ai."
"Allah yasa."
"In sha Allah, Amin."
"Bari na je naga Ya Nabeela, kamar bata jin dadi tun ranar ."
"Allah sarki, ka duba ta please, aiki ne dani da munje."
"A ah yi aikin ka, jiya nima haka nayi nawa."
"Na sani kam,sai ka dawo."
Kofar ya ja masa ya fita, ko office dinsa be shiga ba ya sauko kasa. A reception din k'asa suka hadu da ita ta shigo, dauke kai yayi kamar be ganta ba, yana ji tana gaishe shi yyi biris kamar be ji ba, ya wuce kawai kansa tsaye. Tabe bakin ta, tayi kawai yau abin ya motsa, kaamar me aljanu jiya yana ta kula ta amma yau yayi kamar be san ta ba.
Sarai ya ji sanda ta gaishe shi, haka kawai yaji yana fushi da ita tun jiya da ta matsa ana aikin nan sai ta tafi, shiyasa yayi kamar be ganta ba yay wucewar sa, sai dai kasan zuciyar sa na karanta masa rashin kyautawar sa.
Adam na tsaye tun bayan da ta shige be bar wajen ba, magana yayi mata ta masa banza hakan ya kona masa rai, ganin Aryan yasa shi tunawa da abinda yayi niyya. Tarar shi yayi yana shirin shiga motar sa yace
"Na raina wayon ka Malam, kana ganin kamar kana da wayo,amma ina, kana tare da mutanen mu amma baka sani ba, lallai na raina wayon ka."
Yana rike da hannun motar be shiga ba yana jin shi amma be tanka ba, sai da ya kai karshe sannan yace
"Kune baku da aikin yi da har kuke bibiya ta, dan haka wahala ce bata ishe ku ba."
Ya shige ya zauna ya banko kofar, gaban motar Adam ya bud'e da sauri ya zauna yana dariyar shakiyanci
"Da kana da wayo da sai ka tambaya su waye hakan? Ba wai ka share maganar ba, bayan nasan waye kai, hankalin ka ba zai taba kwanciya ba har sai ka gano waye."
"Malam ka fitar min daga mota kafin na kira securities."
"Please ka fita." Habeeb yace
"Shut up, ba da kai nake ba, da ubangidan ka nake yaro, ka bari mu yi dashi. Kai kuma...". Ya juyo kan Aryan
"Check your WHATSAPP!" Yana fadan haka ya fice daga motar gami da banko masa kofar.