Rumbun Qaya page 23

Rumbun Qaya page 23

 

Rumbun Qaya page 23

RQ


   23


*TUNA BAYA*




****Gidaje guda biyu a jere da juna iri daya sak, hatta fentin jikin gidan da na gate din iri daya ne komai da komai. Daga cikin gidajen biyu akwai wata kofa da tayi linking gidajen biyu wanda baka da bukatar fitowa ainahin gate din idan zaka shiga daga wannan gidan zuwa wannan. Fiye rabin rayuwar su a tare suke yin ta shiyasa zaka samesu a kowanne lokaci a taren idan basa gidan wannan toh suna dayan anan suke komai.

   Nasir da Ibrahim Aminan juna ne tun daga zamanin kuruciya har kawo girman su har kawo yanzu da sukayi aure har suka samu zuria suna yadda suke babu wani abu da ya taba shiga tsakanin su. Asalin mahaifin su Nasir dan Zamfara ne sai aiki ya kawo shi kano in da suka hadu da mahaifin Ibrahim suka zama abokai ta in da abokantar yaran ta samo asali kenan. Tun daga primary suke tare sai da aka zo university sannan suka rabu in da Nasir ya karanci bangaren law shi kuma Ibrahim ya karanci mass communication. A university din suka hadu da matan su, kawaye ne su uku suma duk da banbancin jahohin da suka fito amma sun zama kawaye sosai. Khadija, Aisha da Zeenatu. Khadija itace yar kano sai Aisha daga Adamawa sai Zeenatu da ta kasance yar kogi state. Duk weekend a gidan su Khadija suke zama sun yi mugun sabon da babu wadda take boye wa wani sirri saboda shakuwa. A haka suka kammala karatun su lokacin har su Ibrahim sun fara business ba tare da sun jira aikin gwamnati ba dan sun kusan shekara uku da gama karatun kafin su Khadija su gama, Nasir dai yana dan zuwa chamber shima ba kowanne lokaci ba, saboda haka basu wani damu da dole sai sun samu aiki ba, suka fara business dinsu cikin ikon Allah komai ya soma bunkasa. Kiwon kifi suka fara Allah ya saka musu albarka a hankali sai suka yi expanding dinsa zuwa babban gidan gona cikin shekara daya komai ya kankama dan ba karamin samu suke da harkar ba, daga nan ne suka fara shawarar aure, tunda already suna da yan matan nasu a hannu. Ibrahim ya auri Khadija shi kuma Nasir ya auri Aisha wanda aka daura auren a Yola Adamawa tunda ita chan ne garin su. Duk shagalin bikin nan da Zeenatu akayi shi musamman da ta kasance babbar kawa kuma aminiya ga amaren dan haka ne ma ya kasance kusan itace akan komai har aka kai amaren gidajen su da suke a manne da juna.

   Rayuwa ta cigaba da garawa a hankali lokaci zuwa lokaci Zeenat ta kan kawo musu ziyara musamman idan ta shigo Kano wanda take sakewa tamkar a gidan ta ne saboda babu wani shamaki a tsakanin su saboda yadda suka yarda da junan su, duk sanda tazo suna jin dadi sosai dan ba karamin kirki ne da ita ba haka kuma ta saba sosai da nasir da Ibrahim dama tun a school. Aisha ce ta fara haihuwa ta haifi Namiji wanda nan take Nasir yayi masa huduba da sunan Ibrahim wanda suke ce masa Lamido. Bayan lokaci kadan itama Khadija ta haihu amma sai ta haifi mace ita, aka saka mata Nabeela. Rayuwar su gwanin sha'awa suka cigaba da rainon yaran su har shekara biyu sannan suka sake samun wani cikin a kusan lokaci daya amma wannan karon Khadija ta riga Aisha.


   

*Mafarin Matsalar su*


   Watarana da azumi bayan sun yi sahur nakuda ta tasar wa Khadija, nan da nan suka dunguma zuwa asibiti aka bar Aisha da yaran a gida. Wajen azahar ta haihu ta haifi dan ta namiji, Zeenat a lokacin tana gari dan ta dawo Kano saboda ta fara masters a lokacin dan haka tana jin suna asibiti ta shirya ta tafi tana chan akayi haihuwar itace ma ta fara kira ta fadawa Aisha, nan da nan sai gata nan ta taho ita da Lamido da Nabeela. Daga nan aka sallamo su suka yo gida. A tsakanin gidajen biyu Zeenatu take zama, daga wannan gidan ta koma wannan har ranar suna in da sukayi anko su uku hadda ita, akayi suna gagarumi saboda ko a lokacin business dinsu ya sake bunkasa sosai har sun fara harkar man fetur. Bayan an gama suna mutane sun watse Khadija ta shiga wanka, ta bar Zeenat da Aisha a dakin. Ta dade a ciki sosai tana fitowa ta tarar basa nan dukkansu, ta dauka suna falo sai kawai ta hau shiryawa ta gama sannan ta fito falon. Basa falon babu kuma jaririn sai ta dauki waya ta kira Aisha.


"Ashe kun shiga ciki."


"Eh wallahi, ai kina shiga wanka na dawo na dan gyara gidan, na bar Zeenat dai ko itama bata nan?"


"Eh bata nan."


"Ok kira ta."


"Gata ma ta shigo." Khadija tace idonta akan hannun Zeenat din ganin ita kadai ba jariri


"Kin fito sister?"


"Eh, na zata kuna falo sai naga bakwa nan, waye ya dau Ahmad?"


"Ahmad? Baya dakin?" Tace tana kallon ta. Wani irin faduwa gaban Khadija yayi, ta juya da sauri zuwa dakin Zeenat ta mara mata baya.

 

   Abun daukar sa ne kawai a gadon babu komai, jikinta ne ya hau rawa cikin tsananin tashin hankali suka shiga dubawa, lungu da sako har da leka kasan gado amma babu jinjiri babu dalilin sa. Kanwar Khadija Habiba ce ta shigo daga waje dan suna chan dakin dake compound din basu san me ake ba.


"Habiba kun dau Ahmad ne?" 


"A ah." Tace, hannu Khadija ta dora aka ta fara kuka, 


"Na shiga uku." Da sauri suka yo waje suka shiga gidan Aisha, tana gyarawa Nabila riga kenan bayan tayi musu wanka ita da Lamido suka shigo a birkice wai basu ga Ahmad ba, nan fa hankalin ta ya tashi itama suka yo waje gaba daya cikin tsananin tashin hankali. Wasa wasa ya tabbata an sace jaririn!


   Duk irin binciken da za'a yi an yi, babu jariri babu dalilin sa kuma babu wanda yasan sanda aka fita dashi daga gidan. Iyakar tashin hankali iyalan biyu sun shiga, an kai report din police station amma babu wani labari, haka suka zauna jigum-jigum yadda suka ga rana haka suka ga dare babu wanda ya runtsa. 

   Tsawon lokaci ana saka ran zaa samu wani abu game da batan Ahmad Amma shiru har suka fitar da rai, Zeenat ko wanne lokaci tana tare da Khadija tana kwantar mata da hankali har Aisha ta haihu babu wani taron suna ko wani abu da akayi dan duk basa cikin nutsuwar su, ta sake haifar danta Namiji aka saka masa Abubakar Sadeeq.

   Rayuwar iyalan biyu ta sauya sosai tun bayan batan Ahmad, wanda har lokacin Khadija ta kasa hakura kullum cikin kuka take sosai dan ma Zeenat da Aisha suna kwantar mata da hankali sosai Amma duk da haka abun ya riga ya bar mata gibi me girma a rayuwar ta wanda zata dade bata cike shi ba. 

   A hankali rayuwa ta cigaba da turawa yaran suna dada wayo sosai kuma suna kara shakuwa da juna, dan ko yaushe suna tare da juna a gida daya. Bayan wani lokaci suka sake samun wani cikin, tsoron Mommy (Khadija) ya dadu sosai tun bayan da ta gane tana da ciki, dole ta matsawa Daddy (Ibrahim)suka saka CCTV a kowanne sako da lungu na gidan sannan aka kawo megadi dan har lokacin bata amince cewa babu saka hannun na gida a dauke mata d'a ba, dan dai bata san wa zata ce ba dan dukka mutanen da suka yi ragowa a gidan a lokacin na jikinta ne makusanta. Ita ta fara haihuwa wannan karon ma, ta haifo dan ta namiji kyakkyawan gaske, ta rungume shi tana hawaye sosai tana tuno Ahmad, babu wanda yazo asibitin daga ita sai Ammy (Aisha). yaran suna gida tare da me aikin su da kanwar Mommy Habiba. Babu wanda ya san da labarin haihuwar sai yan gidan su har sai da aka kwana sannan ta kira Zeenat ta fada mata, ta nuna rashin jin dadin ta da ba'a fada mata tun jiya ba. Muhammad Aryan shine sunan jaririn, wanda baki daya dawainiyar sa Zeenat ta dauke saboda yadda take tsananin son shi. Yaro ne me shiga rai sosai da abun sha'awa, ada Sadeeq ne nata amma ana haifo Aryan ta tattara ta watsa Sadeeq a dustbin tayi sabo, suka dinga tsokanar ta tana dariya. Ko da Ammy ta haifi Hydar still dai Aryan din shine nata, dan duk wani kudi da zata samu toh Aryan ne, duk wani abu da yake so shi take masa, duk wani abu da ta gani nasa ne. 

  Watarana suna zaune su uku suna hira sai Ammy tace mata yaushe zatayi aure wai? Lokaci yana tafiya gasu duk da yaran su ya kamata ta yi aure saboda shekarun sun fara tafiya. Murmushi kawai tayi tace ta kusa lokaci kawai take jira suka barta a haka da addu'ar Allah ya kawo lokacin kawai. Tun daga lokacin ta dauke kafarta daga gidan nasu, sai dai a waya kawai suke magana sai rana daya ta kirasu wai an daura mata aure a garin su. Dukkan su basu ji dadi ba ace har tayi aure sai bayan an daura zata sanar dasu amma sai ta nuna musu itama baa son ranta bane ba, dole sukayi mata uzuri amma a kasan zuciyar Mummy sam sai taji bata gamsu ba.



 *DAWOWA LABARI*


    Da sauri ya dawo cikin building din yana hawowa suka hadu da Kamal kunnen sa sakale da waya yana magana, rike hannun sa yayi yanayin Aryan din yasa shi katse wayar yana duban sa


"Na kwafsa Kamal."


"Da kayi me?" Yace yana duban sa


"It's a long story, kasan gidan su Raihana please?"


"Raihana kuma? Gidan su? Me ya faru?"


"Ka sani? No wait ka sani Kamal, ranar nace kayi dropping dinta, please take me, inaso naga Hydar."


"Wai me ya faru? Ka fada min naji tukunna."


"Muje zan fada maka a hanya." Ya shiga jansa,binsa yayi yana cewa


"An yanka ta tashi, Barrister yace mu dakata da zuwa."


"Mu dakata? Akan me? Ba zai gan mu ba Kenan?"


"Be dai ce ba, amma yace a dakata dai."


"Zanje kuwa, kuma zai ganni. Na gaji da wannan jeka ka dawo din, dole ma ya ganni."


"Toh yanzu fada min, menene ya faru? Me ya hada ka da Raihanan."


"Shiga mota please."


Ya bud'e masa kofar gaba da kansa, shi kuma ya shiga baya Habeeb ya tada motar


"Kasan Raihana yar gidan Barrister Matawalle ce Kamal?"


Juyowa yayi bayan


"Na sani."


"What? Ka sani Kamal? Baka fada min ba amma."


"Ban dade da sani ba nima, kamar yadda ka sani yanzu, kuma ina shirin fada maka dama."


"Shit!" Ya daki kujerar da Kamal din yake kai ta baya


"Ouch, Aryan karya min baya zakayi ne?"


"Ban sani ba, Adam yayi fooling dina, he sent me some audios da pictures da suke nuna Raihana tana ma Hajiya Zeenat aiki ne."


"Yes? Sai kayi me?"


"Na kore ta."


"Kaji matsalar ka, kaji matsalar ka. Habeeb please drop me here, ba dani zaa ji ba gaskiya, me yasa zaka yarda da maganar Adam without proper investigation, me yasa ba zaka bata damar kare kanta ba? Me yasa kowa ba zai dinga wasa da hankalin ka ba, abu kad'an zai bata maka rai ka yanke hukunci, me yasa zaka damu yanzu? Ka yarda bata aikata bane shine zaka je ka ganta ko kuma dan ka gane yar gidan Barrister Matawalle ce shine zaka je? Wanne a ciki.?"


"I don't know, I just want to see her, sannan naji her own side of the story."


"Ba zata saurare ka, ko zata saurara sai na hanata, kuma nasan komai da ya faru, Raihana saved your life sau ba adadi, duk abinda tayi saboda taimakon ka tayi, kasan wace Hajiya Zeenat, kasan wayon ta, tayi amfani da innocent mind din yarinyar ta sata abu da niyyar wai taimakon ka zatayi, duk abinda tayi saboda kai tayi, idan zaka tuna ranar da tazo tana kuka, a ranar ta gane Hajiya Zeenat amfani take da ita, sannan ta gano tasa anyi poisoning tea din ka, hakan yasata cikin tashin hankali har sai da ta kwanta ciwo, she saved you a ranar har ta zubar da tea din ba tare da kasha ba, nasan duk wannan saboda ta fada min tun a ranar, tsoron yadda zaka yi reacting yasa naki sanar da kai."


"Habeeb sauke ni anan." Kamal yace ransa a bace. Parking Habeeb yayi da sauri Kamal ya bud'e kofar ya fita shima Aryan ya fita ya tare shi


"Nayi laifi, na ji kuma ban kyauta ba I'm very sorry."


"Ni bani kayi ma laifi ba, fisabillillah tunda yarinyar nan tazo Aryan kake mata abubuwa, menene laifin ta?"


"I'm sorry."


"Ita zaka bawa hakuri bani ba, gashi kila dalilin da yasa Barrister yace ba zai ganmu ba, kasan yadda Raihana take a wajen yan uwanta? Ka sani? Suna sonta fiye da yadda suke son kansu."


"Na fisu son ta wallahi." Ya fada kansa tsaye, wani kallon Kamal yayi masa kamar be ji me yace ba, ya girgiza kunnen sa yana sake duban sa


"Me kace?"


"Yes, I love her Kamal, tun bata san kanta ba."


Kafadar Aryan din Kamal ya daka ya bud'e masa kofar motar yace


"Let's go, idan muka je bata saurare ka ba, ba ruwana dan muna zuwa zan juyo, kasan yadda zaka yi."


"Just take me, zan ga Hydar, I need to talk to him kafin Raihanan."


"Wai corper?" Kamal yace yana dariya, bugo shi Aryan yayi daga bayan yayi murmushi kawai





ZAFAFA BIYAR.....× 2023

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥💥💥💥🔥🔥🔥🔥💥🔥💥🔥🔥💥🔥🔥💥💥💥💥💥🔥💥🔥🔥🔥🔥


INA MAABOTA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR WRITERS? WANNAN KARON MA MUN SAKE DAWO MUKU DA ZAFAFAN LITATTAFAN MU, MASU DAUKE DA ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A ZUCIYA


KU GARZAYO. ZAFAFAN NA KU SUN SAKE TAHOWA DA WASU ZAFAFAN LITTATTAFAN MASU DIMBIN DARUSSA NA MATAKAN ILMANTARWA RAYUWAR MU TA YAU DA KULLUM...


SAFIYYAH HUGUMA

A RUBUCE TAKE (KADDARATA)♥️


HAFSAT RANO

(RUMBUN QAYA)🥰


MAMUH GEE

(IDON NERA)🤩


NANA HAFSATU

KI KULA NI (MALLAKIN ZUCIYA)😘


BILLYN ABDULL

DAUDAR GORA (CIKI KA SHATA)💗


DUKA DUKA WADANNAN LITTATTAFAN ZASU ZO MUKU NE CIKIN FARA SHI MAI RAHUSA KAMAR KO DA YAUSHE. 


DUKA BIYAR DIN AKAN NERA DUBU DAYA DA DARI BIYU 1200


GUDA HUDU AKAN NAIRA DUBU DAYA 1k


GUDA UKU AKAN 800


GUDA BIYU AKAN 600


GUDA DAYA AKAN 400


DADIN DADAWA, MUNA TALLATA HAJOJIN KU AKAN FARASHI ME SAUKIN GASKE! SANNAN GA BIYAN BUKATA


HANYOYIN DA ZAKU IYA TUNTUBAR MU DOMIN ZAMA CIKIN SAHUN FARKO NA WANNAN SABUWAR TAFIYAR SABUWAR SHEKARAR SUNE;



MASU BIYA TA BANKI ZAKU BIYA A WANNAN ACCOUNT DIN 


BANK: ACCESS BANK 


ACCOUNT NAME: MARYAM SANI


ACCOUNT NUMBER; 0022419171


SAI A TURA EVIDENCE OF PAYMENT HADE DA ACCOUNT NAME TA WHATSAPP TA WANNAN NUMBER;  


09033181070


IDAN KUMA KATIN WAYA NE NA MTN SEKU TURO KATIN VTU/SHARE AND SELL KO NUMBER KATIN HADE DA SHEDAR SA TA WHATSAPP ZUWA: 09166221261


FARASHIN LITTTAFAN ZAFAFA BIYAR NA CHANJAWA DA ZARAR AN KAMMALA SU. SAI KU YI SAURI KU GARZAYA DOMIN A DAMA DAKU A WANNAN SABUWAR TAFIYAR SABUWAR SHEKARAR 2023🔥🔥🔥🔥🔥🔥💥


KU GARZAYO A SAKE DAMAWA DA KU A WANNAN SABUBAR TAFIYAR MAI DAUKE DA SALO NA BAN MAMAKI. KAR KU BARI AYI BABU KU.


DOMIN ZAFAFA BIYAR NA KU NE. 😘🤩

[05/01, 21:53] Billyn Abdul 2: 🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR MAZAUNA K'ASAR NIJER?*🤏🏾


*TO KU MARMATSO KUSA TA SAMU!!*🇳🇪🇳🇪


*MUN SAURARI KOKENKU MUN KUMA AMSA*


*Zafafa biyar dinku sun samo muku hanyar biyan naku kudin karanta litattafan zafafa har guda biyar din*


*ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE*


+22799643131


*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*


*DAUDAR GORA Billyn abdul*


*KI KULANI hafsat xoxo*


*A RUBUCE TAKE Huguma*


*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*


*IDON NERA Mamuh ghee*


*KUDIN LITATTAFAN ZAI KAMA KAMAR HAKA*


Books biyar  1250CFA

Books hudu  1050CFA

Books uku  850CFA

Books biyu  650CFA

Bookk daya  450CFA


*MUNA GODIYA DA SOYAYYARKU GAREMU AL'UMMAR NIJER,MUNA MUKU FATAN ALKHAIRI TARE DA GODIYA BISA ZABIN ZAFAFA BIYAR*🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post