Rumbun Qaya page 24

Rumbun Qaya page 24

 

Rumbun Qaya page 24

RQ

   24




****Kamal ne yake yiwa Habeeb kwatance har suka karaso kofar gidan Adda maimuna, Kamal ya juyo yace


“Munzo, amma ban ga alamar suna nan ba.”


“Call her please.” Aryan yace yana langwabe kai


“I can’t gaskia, ai da kunya wallahi.”


“Please please, ka taimaka.”


“Sai kace please oga Kamal.” 


“Please Oga Kamal.” Ya fada da sauri


“Ok let me call her, ba dan halin ka ba.” 


Ya Ciro waya yayi dialing number raihana, lokacin suna zaune a wani park ta gama bawa hydar labarin komai, fada yake mata sosai bayan da Ya gama jin komai din, be san zata iya saka kanta a irin wannan abun haka ba da tun farko basu barta tazo kanon ba. Abinda ya kawo shi kanon kenan a ranar dan Abby ya samu labarin in da take aiki da kuma labarin taraiyar su da hajiya zeenat har prison da ta rakata ganjn shi shiyasa yace lallai hydar yazo Ya dawo masa da ita, sannan kuma yace ya fasa ganin su Aryan din domin Abby yayi matukar fushi da daddyn su Aryan, baya jin zai iya yafe masa ballantana har wani abu ya sake hadasu, ba zai so taraiyar Aryan da raihanar sa ba, dan ba zai iya taba daukar yarsa Ya bawa dan gidan Mukaddas ba. Ba zai taba ba!


“Gobe zamu wuce tare, kin daina zuwa sai karshen wata ni zan dinga kawo ki da kaina Kina clearance.” 


Bata ce komai ba, wayarta ta dauki kara 


“Waye?” Yace yana mika mata hannu, bashi wayar tayi Ya daga ya sakata handfree


“Raihana gamu a kofar gidan ku.” Kamal yace shima wayar a handfree din take


“Ba ita bace ba, yayanta ne.”


“Ok Oga Barka da rana ya gida’?”


“Lafiya lou, please dama zan wuce da raihana gida, idan yaso zata dinga zuwa karshen wata tana clearance.”


Da sauri Aryan ya karbi wayar


“Hydar please kuna Ina? Inason ganin ka dan Allah.”


“Na riga na wuce.”


“Please nasan baka wuce ba, nasan kana nan ka fada min inda kuke, zanzo Yanzu muyi magana dan Allah.”


Kallon raihana yayi da itama shi take kallo sannan yace


“Skypark.”


“Gamu nan toh.” Yace yana katse wayar


“Me yasa baya so ku hadu?” Kamal yace 


“Saboda fushin abinda ya faru tsakanin Daddy da Alhaji Nasir ya shafe mu.”


“Me yasa kake son ganin shi toh?bayan ya nuna baya so.”


“Muje dai please, kar mu bata lokaci ya gaji su tafi .”


“Ok, muje Habeeb.”


“Ok.” Ya tada motar 


   A cikin sabon wajen sukayi parking, Kamal ya kara kiran raihana sannan ya bawa aryan bayan an daga yace wa hydar sun shigo wajen, in da zasu same su ya kwatanta musu.


“Kaje kai kadai Aryan, zamu jiraka anan.”


“Ba zakayi mata magana ba?”


“Wa, nace mata me? Kai zaka gyara mess din ka da kanka.”


“Ni? Ni fa Hydar nake son gani ma, not her.” 


Yace yana yatsine fuska 


“Haka kace?”


“Yes, ni ba abinda zan ce mata, salon ta raina ni. Noo I can’t.”


“Ikon Allah, Yanzu yanzu fa ka gama cewa you love her, ko ka manta?”


“Yea I love her, tun tana yar babyn ta nake nufi ba fa Yanzu ba.”


“Ok, a kyale ta.” Kamal yace yana gyara zama a motar Ya dauke kansa


“A kyale.” Shima aryan din yace yayi gaba. Murmushin mugunta Kamal yayi, dole sai ya kure Aryan a wannan lokacin yaga karshe miskilanci. Text ya shiga ya rubutawa raihana


“Karki kula aryan kanwata, ina parking lot come and meet me.”


“Ok.” Tayi masa reply ya sake yin murnushi kawai dan ya riga ya san halin Aryan.



   Daga chan nesa ya hango su, raihana na facing din ta side din da yake hydar kuma ya bashi baya, sai da yazo daf dasu sannan ya lura sosai da yadda idanun raihanan suka dan tashi alamun taci kuka, kallon ta yake yana tuna shekarun baya tana yar karama suyi ta goya ta shi da hydar har suna fada akan wanda ya riga, tafi son Aryan dan haka ne ma kusan kowanne lokaci tana manne dashi yana fama da ita. Murmushi ne ya subce masa, a duk memory din rayuwar su ta baya wannan sune memory masu dadi a gare shi, kafin komai yazo ya tarwatse ya zama babu wani sauran haske a rayuwar sa sai bakin duhu da ya mamaye ko ina. Dagowa tayi da niyyar kallon wasu saurayi da budurwa dake gefen su sai ta ganshi a tsaye daga kusa dasu yana kallon ta. Saurin dauke idon ta tayi zuwa wani wajen tasa hannu a idon tana jin kamar wani abu ne ya fada mata a idon bayan tuno irin ihun da ya gama yi mata dazu dazun nan. Mikewa tayi tsaye hydar ya kalle ta da alamar tambaya


“Zan je toilet ne Hamma, ga bakon naka nan yazo.” Sai ta bar wajen ba tare da ta ko kalli bangaren da Aryan din yake ba


_“Get out of my life, bana son sakè ganin ki.”_


Kalaman da ya gama jifanta dasu suka shiga dawo masa a kansa. Kenan abinda take nufi da bako tana nufin ta fita daga rayuwar tasa har ma ta shafe babin sa kenan ko me? 


“Bismillah.” Hydar yace yana nuna masa wajen zaman da raihana ta tashi. Zuwa yayi ya zauna kamar wanda kwai ya fashe wa a ciki saboda rashin kuzari. Kwarjini sosai yaji hydar din yayi masa musamman bayan abinda ya faru ya kuma tabbatar raihana ta sanar masa da komai. Hannun sa ya zaro daga aljihun rigar sa da ya zube su ciki ya mikawa hydar din suka gaisa.


“Hope kana lafiya, ko da yake from all indications kana lafiya din, well menene maganar da zamuyi saboda ina sauri ne, yau nake son barin kano ko mai dare.” Ya kalli agogon dake daure a tsintsiyar hannun sa yana maganar 


“I want to know Dama yadda kuke, ya bayan rabuwa!”


“We moved on Aryan, tun bayan abinda ya faru muka dauki kaddara muka cigaba da rayuwa, duk kuwa da Daddy yaso rayuwar mu ta katse mu ta gayyara, sai dai bamu mutu ba, mun yi rayuwa me inganci duk kuwa da wahalar da muka sha din.”


“Menene banbancin mu Hydar? Karka manta a gaban idona aka raba mahaifiyata da ranta, a gaban ido na aka tarwatsa ma wadanda suka fi kowa kusanci dani rayuwa, ka dauka nayi wata rayuwar jin dadi ne bayan haka? Ko ka dauka na manta daku? Allah ne shaida ta, rana bata taba fitowa ta fadi ban tunaku ba, ban kuma yi missing dinku ba.”


“Kasan rayuwar da mukayi kuwa aryan? Ka sani? Kasan rayuwa babu uba babu uwa, ku zakuyi wa kanku komai, Atleast ka tsira da mahaifi Aryan, mu fa? Kayi karatu me kyau cikin rayuwa me kyau baka rasa komai ba, mu fa? Kasan da ya akayi muka zo har nan? Mu muka dauki nauyin kanmu da kanmu.”


“Bani da banbanci da rayuwar da kukayi Hydar, duk abinda Ya faru ni ne na dauki consequences din.”


“Hmm, ya wuce Aryan, ina ganin dawo da abinda Ya faru ba zai wani amfani ba, mu bar shi kawai.”


Sai Ya mike tsaye


“Raihana yarinya ce karama wadda bata san komai ba, bata komai akn abinda ya faru ba, dan haka nake rokon ka, stay out of her life dan Allah Aryan, ka rubuta mata clearance letter din ta complete har na last month, ka fada min nawa ne zan biya, ba sai ta sakè zuwa Office din ku ba.”


Wani irin kallo Aryan yake masa, shi zai biya kudi? Shi? Akan raihana?


“Kudi Hydar?”


“Yes, nawa zan biya?” 


Hannun sa ya dunkule ya runtse idon sa ba tare da yace komai ba saboda tsananin bacin ran da yaji ya taso masa. Gid'a kai Hydar yayi


"Well,idan sai kayi tunani ne toh, ga complementary card dina nan, just call me sai muyi magana.”


Yana fadan haka ya soma tafiya yana barin wajen, ya bar Aryan cikin yanayin da ya kasa tantance a wacce duniya yake, tabbas yasan an cutar dasu cuta mafi girma, amma be dauka hakan zata shafe shi ba, shi menene nashi? Laifi na Daddy ne taya hakan zai shafi dangantakarsu. Kamar wanda aka dasa a wajen haka ya cigaba da tsaiwa har sai da Kamal ya gaji da jiransa dan a gabansa hydar din ya fito suka tafi da raihana sannan ya bishi ciki ya same shi cikin wani irin yanayi. 



***TUBA BAYA*


   Zeenat ta dade tun daga lokacin bata ziyarce su ba, sun kuma yi kokarin zuwa su ganta amma sai ta dinga yi musu hanya hanya har suka hakura suka kyale ta kawai. Kwatsam sai mahaifin Mummy ya rasu, wanda ya tilasta mata zuwa yiwa mummyn gaisuwa, anan ne suka dinga yi mata fada akan share su da tayi tunda tayi aure ta dai basu hakuri kuma tace sun rabu da mijin, talaka ne gashi dan giya ne idan yasha sai yazo ya kamata da duka haka dai Allah ya taimake ta ya saketa. Sun mata murna sosai sun kuma tausaya mata rayuwar da ta shiga, ko da tazo zata koma garin su sai suka ce ta zauna ta dan kwana biyu ta sake hutawa sosai, ba musu kuwa tayi zaman ta dan dama chan hanya take nema. A lokacin arziki ya kara bunkasa sun gyara gidajen an dora bene komai an chanja shi kamar ba gidajen nasu ba na da. Duk abinda suke yi idanun Zeenat yana kai wani abun kusan ma tare da ita ake yi dan wata yar uwar mummy ta taba yi mata complain akan yadda suka sakar wa Zeenat din musamman ita mummy tunda ita Ammy bata da hayaniya sosai shiyasa Zeenat tafi shigewa Mummy sosai dan tafi fuska tafi kuma sakewa sosai da ita.

   Zaman ta a gidan ya kara mata kusanci sosai da Aryan dan ba karamin son ta yake ba, komai ita take yi masa ko yaushe yana wajenta tana dawainiya dashi haka yasa ita kuma mommy ta sake sakankancewa da ita dan dama an ce me d’a wawa, dan tunda ta rasa ahmad ta dauki son duniya ta dorawa Aryan din. 

   Tafiyar ta ta karshe ita ta fara bawa Mummy shakkun akan zeenat, daidai lokacin da aka raba musu gadonsu tazo tana fada mata washegari ta shirya tace ta tafi okene zata kwana biyu kafin ta leko su, da farko bata kawo komai ba sai bayan tafiyar zeenat din da ta shiga dakin da take kwana sai taga wata takarda akan bedside drawer, hankalin ta ne Ya kai wajen ta sa hannu ta dauka ta warware sai taga takardar chèque ce a tsakiyar dayar takardar wadda ta fito daga hannun Daddy.


“Kudi?” Tace tana sakè son tabbatarwa


“Me zai hada Daddy da bawa zeenat kudi, kudi masu yawan gaske kuma be sanar da ita ba?" Ta tambayi kanta, rike takardar tayi a hannu ya fito a lokacin Daddy yana sama yana kallo ta same shi tare da Aryan da yake jingine dashi suna Kallon tare ta mika masa takardar tana kallon yanayin fuskar sa.


"Ta mecece?" Yace yana warware ta


"Duba ka gani." 

 

 Dagowa yayi bayan ya gama dubawa ya mika mata yana maida hankalin sa kan TV cikin halin ko in kula yace


"Me ya faru da wannan din?"


"Me ya faru Daddy? Kudi ne naga ka turawa Zeenat har haka, kuma babu sani na at least ko wani abu ne ya faru ya kamata na sani."


"Ke da kawarki? Menene dan na taimaka mata tana cikin halin neman taimako?"


"Babu komai, amma a kalla na sani ba wai sai dai na gani ba."


"Kishi dai irin naku na mata, ni ban ga abinda nayi ba." Ya mike yana daga Aryan


"Let's go my boy, mummy tana bukatar hutawa ."


Ya janye dansa suka fice suka barta a tsaye tsananin mamaki na neman kashe ta. Yau Ibrahim ne yake bata irin wannan amsar? Lallai akwai matsala. 

 Mayafin ta, ta dauka ta sauko ta shiga gidan su Lamido, ta samu Ammy da yaran tana koya musu homework, yanayin mummyn da ta gani tasa tace su shiga ciki.


"Menene ya faru sister?" 


"Akwai babbar matsala sister, nayi kuskure me girma."


"Na me fa? Wai me ya faru fada min dan Allah duk hankali na ya tashi."


"Kalli." Ta mika mata cheque din tana yin tagumi. Zaro ido Ammy tayi


"Ban gane ba."


"Zeenat ce ta karbi kudi a wajen Ibrahim, babu wanda ya sanar dani a cikin su, ni ba yawan kudin ne damuwa ta ba, yadda za'a boye min bayan duk cikin su babu wanda nake boyewa komai na."


"Tabbas biri yayi kama da mutum, dazu da asubah Nasir yake ce min zamuyi magana akan Zeenat dani dake dashi idan ya dawo, tabbas akwai abinda ya faru, amma yanzu da abinda Zeenat zata saka mana kenan?"


"Kin gani, mutum! Shiyasa aka ce karka taba yarda da mutum."


"Gaskiya bata kyauta ba, da sai ta fada miki ma idan ni ba zata sanar dani ba."


"Ni duk jikina yayi sanyi wallahi, tun farko laifi na ne, da na sakar mata gida na bayan duk fadan da akayi min, ke ai kinga kin fini hankali."


"Ba haka bane ba, akwai yarda me karfi tsakaninmu uku, kema kin sani yanayi na ne kawai da naki ba daya ba, amma nima in dai Zeenat ce bana jin dar ko wani tunani akanta wallahi. Kawai dai ta zabe ki ne akai na."


"Still duk da haka Aisha munyi shirme, a zamanin nan da yarda tayi karanci ka bar mutum babba baligi a cikin gidan ka bayan babu wata alaka ta jini a tsakani, wanda a yanzu ko yar uwarka ce ciki daya wallahi shaidan zai iya tasiri a wajen bare kawa, nayi kuskure sosai kuma na sabawa dokokin Allah."


"Kuskure ne dukka mun tiga mun yi, yanzu kiranta za'a yi muji dalilin ta kila ko nauyin fada miki take kar kiga ta tambaye shi."


"Babu yar wannan a tsakanin mu ai, bansan kuma yaushe ta fara ba."


"Kirata muji." 


Kiran Zeenat din tayi amma har ta gama ringing bata daga ba, ta sake kira a karo na biyu amma still no answer daga karshe ba sai ta kashe wayar baki daya. Abinda ya daure kan su kenan har jikinsu ya sake sanyi.

   Bayan kwana biyu da abun babu wani shiri tsakanin Daddy da Mummy dan fushi take sosai dashi amma sai taga kamar ma be damu ba, sabgar gabansa kawai yake daga shi sai yayansa, hakan ya kara saka mata tsoro sosai a zuciyar ta, ta rasa in da zata saka kanta taji dadi. 

   Zuwa tayi ta samu Abby a gida ta kai masa karar Daddyn yace su je gidan su sameshi dan shima kwana biyu basa wani zama sosai kamar akwai abinda ya dauke masa hankali. Yana ganin su tare yasan abinda ya kawo su, lokacin ma waya yake yana ta shewar sa, sai ya katse bayan yace mata zan sake kiranki. Sannan yace


"Aboki bamu zauna ba kwana biyu, ga abu ya taso mana bakatatan gobe zaka rakani kogi state."


"Kogi?" Yace zargin sa na tabbatuwa kafin yace


"Magana nazo muyi ni."


"Nasan maganar da zakayi, ai na ganku tare nasan kara ta aka kai, toh bari na saukaka muku maganar, Maman Nabila gobe in Allah ya yarda zaa daura min aure da Zeenat!"

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post