RQ
25
Ji da ganin Mummy ne ya dauke na wasu mintuna, sai taji kamar mafarki take tana fatan ta farka daga mummunan mafarkin. Jiri na ya kusan dibar ta, tayi saurin kama hannun kujera ta rike kam, shi kuwa Abby ya rasa me zai ce saboda tsabar takaici da bacin rai. Duk maganar da yayi masa akan yadda suke rayuwa da Zeenat be dauka ba ashe, shine har da aure?
"Aure kuma aboki? Ban fuskance ka ba."
"Aure dai da ka sani, kasan komai kaga ya faru Allah ya riga ya kaddara zai faru, a kalla ita amaryar ma ai ba bare bace, itama yar uwa ce kaga shikenan sai a zauna lafiya."
Kukan bakin cikin Mummy ta fashe da, ta juya ta fice da sauri. Zama Abby yayi yana duban daddy
"Menene matsalar? Yanzu ace ta haka zaka sanar da matarka zakayi mata kishiya? Anya Ibrahim? Anya ka dauko hanya me kyau kuwa a shaanin auren nan?"
"Toh ai kamawa tayi, dama yau nake shirin fada mata tunda sai a karshen satin nan fa muka yanke shawarar auren ma"
"Amma yanzu kun kyauta Kenan? Ana barin halak dan kunya fa."
"Toh ai ba laifi mukayi ba, kai fa da kanka kace soyayyar da muke bata dace ba, shine mukayi deciding muyi aure kawai ba shikenan ba?"
"Still dai baka kyauta ba, sai ka sameta ka rarrasheta ka bata hakuri, dan ba'a kyauta mata ba."
"Haba dai, a wannan gabar ai ba zan nuna mata lako lako ba bare ta botsare, ka bari sai an daura gobe yawwa, sai na dawo nayi rarrashi."
"Baka kyauta ba gaskiya."
"Toh ya za'a yi ne wai Barrister? Haka Allah ya tsara ya kaddara, bawa ai baya taba gujewa KADDARAR sa, kuma da sauki ba fa wata ce chan ta daban ba, Zeenat ce kasan dai yadda alakar su take, kuma ni ban ma ga abin damuwa ba in dai da gaske ake kawancen."
"Me ta baka kasha wai? Maganganun ka sunyi kama da na wadda akayi brainwashing, maganar Khadija fa mukeyi fa, Khadijan ka ba wata ba, why are you trying to make it looks like kamar bakayi laifi ba."
"Ai banyi bane ba Abokina, babu laifi a raya sunnar ma'aiki."
"Shikenan, ni dai babu wani kogi state da zanje gaskiya, dan nasan na sake na bika wallahi Nima fushin sai ya shafe ni."
"Wa zai rakani toh? Dole ango ai sai ya tafi da wani, kasan al'adarsu ba irin tamu bace ba."
"Ba in da zani, ka kira zanna ya rakaka dan shima irin wannan tunanin ne dashi."
"Alaka ta da Zanna daban taka daban, please ka shirya dan na riga na siya mana tikiti, sai tafiya kawai hatta kayan da zamu saka na dinka mana yana cikin closet dina."
"Allah ba in da zani, har sai ka bawa Maman Aryan hakuri sannan idan sun amince sai muje."
"A wannan kurarren lokacin yaushe ma har ta sauko ta hakura ta amince? "
"Sai a d'aga har sai ta amince din."
"Tab! Haba wa, ai idan kaga an daga goben nan ko? Toh mutuwa daya a cikin mu yayi. Kasan yadda ire iren matan nan nasu suka iya caring kuwa? Wai wai wai, soyayya alaji, wallahi kamar zasu kwanta maka saboda tsabar love da biyayya."
"Allah ya kyauta, bari na je." Ya mike ya fice ya bar daddyn akan bakansa.
Tun Mummy tana kuka da hawaye har ya koma ya kafe sai ajiyar zuciya da take saukewa, ita kanta Ammy tayi kukan ba dan kad'an ba dan duk abinda ya shafi daya daga cikin su toh dukkan su ne, musamman irin wannan auren cin amanar, bayan babu irin hidimar da mummyn batayi dasu ba tun ma a zamanin makaranta da kuma bayan auren, komai ta samu nasu ne su uku ta yarda dasu fiye da yadda ta yarda da yan uwanta na jini ma, sai gashi irin sakayyyar da Zeenat din zata saka mata kenan. Abby ne yake ta kokarin basu baki da kwantar musu da hankali dan yasan ba'a kyauta musu ba, duk kuwa da shi namiji ne amma a kalla yasan abinda ya kamata da wannan be dace ba. Ita Ammy har shi take fushi da tunda dai ai ance Abokin barawo barawo ne, kuma ba zai yiwu ace tun farkon alakar Daddyn da Zeenat ace be san komai ba, amma yayi shiru har sai da abu ya riga ya kwabe kafin yace zai yi magana dasu ashe ma already su sun riga sun gama yanke hukuncin abinda zasuyi. Babu irin kiran da batayi wa Zeenat din ba amma bata shiga da alamu ma ta sakasu a black list ta yadda ko sun kira ba zata shiga ba, ta riga ta shirya musu ko ma menene wato babu gudu babu ja da baya.
Da daddare daddy na gaban mirror a dan corridor din dake gaban toilet yana shaving fuskar sa Mummy ta shigo wajen, ta jikin mirror ya kalle ta sai ya cigaba da abinda yake yana yana dan jujjuya kansa cike da nishadi kamar be san ta shigo ba. Wasu kaya ta zuba a cikin watching machine ta juya ba tare da tayi masa magana ba. Dakatar da ita yayi ya tako gabanta taki kallon fuskar sa
"Na manta dazu ban fada miki ba, idan an daura auren daga chan zamu wuce honeymoon na wata daya, idan mun dawo zata zauna a k'asa sai ke kiyi amfani da sama. Please sai a kwashe komai zan turo masu gyara da interior designers suzo su hada mata kasan, naso kowa ta zauna ita kadai amma tace tafi so ku zauna tare, kinsan abunku da na kawaye."
Kad'a kanta tayi kawai tayi gaba ba tare da tace masa uffan ba, dan ta lura so yake zuciyar ta, tayi bindiga ta fashe ta mutu bashi da asara. Daki ta koma tayi kuka, tayi kuka kamar ranta zai fita, sannan taje ta wanko fuskar ta, ta kuduri aniyar ko me zai yi ba zata taba tanka masa ba, zata zauna ta rungumi yayanta ta kula dasu amma ita dashi shikenan, yaje ta barshi da Allah idan ya cutar da ita.
Sati uku da daura auren suka tattaro suka dawo, sati ukun nan ya zamar wa ahalin gidan tamkar wasu shekaru, babu wata walwala a gidajen biyu dan dukkansu abun ya taba su hatta yaran Aryan da Hydar ne kawai suke shaanin su amma kowa baya cikin walwala. Nabila da Lamido sun fi shiga yanayin sosai saboda sun riga sun girma sun san damuwar iyayen su. Ranar da zasu taho Kanon suka fara biyawa ta Kaduna ta dauko Adam, dan dama ta riga ta fada masa zata dauko Adam daga hannun kanwar ta, be musa ba dan a yanzu kaf duniya babu wadda yake so sama da Zeenat din dan shi ji yake kamar sai yanzu ne ma yayi aure dan wani irin kulawa da take bashi kamar zata maida shi ciki uwa uba ga soyayyar da take nuna masa a fili babu wata kunya ko noke-noke.
Kamar babu kowa a gidan da suka shigo dan Mummy tana sama a dakin ta yaran kuma suna wajen Ammy sai ya zama gidan yayi tsit. A falo suka baje manne da juna bayan sun ajiye kayan su. Adam na zaune a gefe yana buga game a sabuwar tablet dinsa da Daddyn ya siya masa. Sakkowa mummy tayi ta gansu kawai dan ko sanin ranar zasu dawo ma batayi ba. Tun daga ranar komai ya sake chanjawa!
*Dawowa LABARI*
****Tunda suka dau hanya babu wanda yayi magana da dan uwansa, har suka iso office din. Balle murfin motar Aryan yayi Ya fita da sauri Kamal ya mara masa baya. Kai tsaye office dinsa Ya nufa duk da sauri yake komai ya bude ya shiga, Ya jawo drawer da yake ajiye takardun ya fito dasu daga tsayen da yake duk ya bisu da stamp da signing ya bar wajen date da sunan ta blank ya tattare su ya zuba a envelope sannan ya fito. Kamal ne ya tsaida shi ganin zai sakè fita
“Wai me ya faru? Baka fada min komai ba.”
“Ni hydar zai duba yace zai biya kudi kamal? Ni zai biya kudi akan raihana? Ni?”
“Comman, na tabbatar ba abinda ya fada yake nufi ba har zuciyar sa, bacin rai ne kawai. Beside ko waye dole yayi abinda hydar yayi.”
“Na tafi takanas na ganshi, thinking shine zai fi kowa fahimta ta, but me yayi? Yana fada min na kyale masa kanwarsa. Did I say I’m keeping her? Ba maganar tace ta kaini ba ni, Amma yana nuna kamar ni din mugu ne, ko ina nufin kanwar sa da sharri. Problems din dake kai na sun ishe ni, ba zan karawa kai na wasu ba kuma. Tunda sun zabi hakan fine, tunda ban mutu da ba, Yanzu ma ba zan mutu ba.”
“Calm down, ka bari zan neme shi muyi magana, shima barrister Nasir na sake aika masa da sako, hopefully zai amince ya bamu goyon bayan da muke nema."
"Don't please, ka kyale su kawai."
Ya juya ya soma sauka daga stairs din, girgiza kai Kamal yayi kawai, yana ganin lokaci yayi kawai da zasu aiwatar da abinda suka tsara, sai ya ciro wayarsa ya yi kira, suka danyi magana kad'an sannan ya katse yana sauka shima.
Gidan sa ya wuce yana shiga ya jefar da envelope din a saman kujera ya shiga ciki, ya fara watsa ruwa sannan ya sauya kayansa zuwa kanana marasa nauyi, fuskar sa a hade take babu walwala ko kad'an domin a chunkushe yake jin sa amma dole sai ya aiwatar da abinda yayi niyya dan yafi karfin abinda Hydar yake jefan shi dashi. Fitowa yayi rike da wayar sa hannu daya rike da envelope din ya dan kalli time yaga biyar ta wuce ya tabbatar yanzu ta koma gida. Tun a office suka rabu da Habeeb shiyasa yanzu ya kasance shi zai tuka kansa. Sai da ya fara biyawa ta wani waje har magriba sannan ya dauki hanyar gidan nasu da suka je dazu. Lokacin masallacin unguwar suke sallah dan haka ya zamto babu mutane a waje duk suna ciki, a kofar gidan yayi parking ya zaro wayar sa ya kalli lokaci sannan ya dan jingina jikin motar yana karewa layin kallo. Muhammad ne ya dawo daga masallaci ya ganshi a tsaye a kofar gidan su. Sallama yayi masa ya amsa ya mika masa hannu suka gaisa kafin yace
"Please wajen Raihana nazo."
"Ok, ina zuwa." Ya shiga ciki ya barshi. Hannun sa ya zube a aljihu yana kallon kofar gidan fuskar sa a hade tsaf. Mintuna kad'an Muhammad ya dawo
"Oga ko zaka kirata a waya? Tace bata expecting kowa."
"Sorry bani da number ta ne, amma please kace mata Aryan ne."
"Ok." Ya sake juyawa ciki. Jujjuyawa ya dinga yi a tsakanin wajen tsawon lokaci muhammad din be dawo ba, ita kuma bata fito ba. Ransa ne ya dan sosu, ya sake kallon agogon da yake daure a tsintsiyar hannun sa yaga a kalla ya kusan shafe mintuna ashirin a tsaye a wajen. Sallama akayi masa ya waigo da sauri, ganin babban mutum yasa ya dan russuna ya gaishe shi.
"Sai dai ban shaida ka ba." Baban su Amina yace yana kallon sa
"Eh dama ogan Raihana ne a wajen aiki, na kawo mata wasu papers ne."
"Ah toh bismillah, shigo ciki mana ka tsaya a waje? Shigo shigo." Yayi masa jagoranci zuwa ciki, ya bud'e kofar falon sa da yake ajiye bakin sa yace ya shiga shi kuma ya shiga ciki.
Be zauna ba, ya tsaya daga farkon falon yana jiran shigowar ta, hankalin sa na kan kofar dan idan be aiwatar da abinda yayi niyya a yau ba toh tabbas sai ya kasa runtsawa. Yana tsayen yaji ana bud'e kofa, kafin sallamar ta, ta biyo baya amma a chan ciki. Amsawa yyi shima ciki cikin ta karasa shigowa sanye da dogon Hijab har k'asa kanta na kallon kasa sosai ta shige ciki ta tsaya itama daga dan nesa sosai dashi.
Envelope din ya bud'e ya ciro takardun ya ajiye a saman kujerar da take tsaye gefenta,
"Babu bukatar sake dawowa duk wata kina karbar clearance saboda bani da wannan lokaci. Wajen suna da date blank yake dan haka sai ki cike da kanki."
Wani abu ne ya sake taba ta, a tunanin ta Aryan yazo ya bata hakuri ne, yazo ya janye kalaman da ya faffada mata dazu, sannan ya kaskantar da kansa ya nemi afuwarta kuma yaji ta bakin ta, sai dai tsananin mamakin sa ya hanata cewa komai, ta dinga kokarin hadiye wani kukan bakin ciki da yake taso mata, tun da ta dawo ta kasa hada kayanta, ta kasa yin komai saboda yadda zuciyar ta, take a chunkushe. Akwai tarin bakin ciki a zarge ga da cin amana bayan kasan ba hakan ka aikata kai tsaye ba, sannan a hanaka kare kanka ballantana a samu yi maka uzuri, sannan ayi maka kora irin ta Wanda bashi da wani amfani. Duk wannan be isheshi ba, shine sai ya biyo ta har gida ya dora a in da ya tsaya? Lallai.
Gefen Hijab dinta ta kama ta rufe fuskar ta dashi kawai tayi hanyar barin dakin dan idan ta cigaba da zama kukan bakin cikin da take ta dannewa sai ya fito. Da wani irin sauri ya riko ta, Hijab dinta yayi niyyar rikewa Amma sai ya samu kansa da damko hannun ta, wanda yaji tamkar an jona masa shocking sabida yadda yaji. Tsayawa tayi chak ta kasa yin gaba, shi kuma ya kasa sakin hannun ta, saboda wani irin bugawa da kirjin sa ya shiga yi tamkar zai hudo. Kusan minti daya yana rike da hannun ta, yaki saki sai sheshekar kukan ce take tashi. Kokarin kwace hannun ta hau yi,sai a lokacin ya tuna yayi saurin cikata yana kallon nasa hannun.
"Subhanallah." Ya furta a a hankali ya dafe kansa.
"I'm sorry."
Ya samu kansa da furtawa sai dai kamar iya saman leban sa maganar ta tsaya dan ko motsawa batayi daga wajen da take tsaye ba, bare yayi tunanin taji abinda yace
"Kiyi hakuri."
Ya sake furtawa wannan karon da dan karfi. Kamar mashi haka taji maganar tasa ta shige ta, kukan da take ta soma ragewa a hankali tana jan ajiyar zuciya.
Zuciyar sa ce ta dinga kokarin ingiza shi, ya dinga jin tamkar yaje ya rungume ta, tayi kukan a kirjinsa akan zafin da yake ji duk lokacin da sautin kukan nata ya shiga zuciyar sa. Gwara ya tafi, kar yaje ya karawa kansa zunubi bayan na rik'e mata hannun da yayi.
Gefen ta ya rabo yazo daidai saitin ta, a hankali yace
"Na tafi." Sai ya bud'e kofar ya fice ya barta a tsaye a wajen cikin wani irin yanayi.
***Ya dade a kofar gidan be tada motar ba, har sai da bugun zuciyar sa ya daidaita, sannan ya kunna motar ya bar unguwar cike da wasu irin tunani da suka cika masa kwanyarsa har yake jin kamar zasu fito waje. Gida ya wuce cike da son dauke hankalin sa daga kan abinda ya faru ya maye su da tunanin halin da Daddy yake ciki duk kuwa da Kamal yace zai duba, ya kamata suyi abinda ya kamata dan a yanzu ya kara samun tabbacin akwai babban al'amarin da yake faruwa da Daddyn.
Hajiya Zeenat bata nan, tana chan gidan da suka kai Daddy ta samu wani nurse ta sakashi duba Daddyn dan tana so ya dan yi regaining energy dinsa saboda ta samu damar da zai karasa mata abinda ya fara. Suna zaune a falo yana cigaba da aikin da yake mata sai sako ya shigo wayar ta, budewa tayi ba tare da ta bada dukkan attention dinta ba, sai dai abinda yake kunshe a sakon ya sakata mikewa tsaye ta dafe kirjin ta
"Na shiga uku."
Tace tana kokarin yadda wayar, video dinta ne da akansa ta salwantar da rayuwar mutane biyu, ta tura daya gidan yari, video da ta tabbatar sai da ya bata bat a doran k'asar nan amma kuma ta yaya? Waye yake dashi da har zai turo mata shi a irin wannan lokacin, babu abinda yafi tsorata ta, irin abinda yake rubuce a karshen sakon, abinda ya kara saka ta a matukar rudani, waye? Waye wannan? Wayar ya dauka da ta yar ya bud'e sakon sannn yayi kokarin daukar number ya hau duba ta, sai dai babu wani bayani da ya samu akan number din duk da ya riga dama yasan ba lallai a samu komai akan sako irin wannan ba.
"Me nake dauke dashi? Me na samo a wajen Aryan kenan?" Tace a birkice. Gida ta nufa a matukar rikice, taje ta bud'e in da ta ajiye takardun nan ta fito da komai sannan ta sake fitowa ta dawo in da yake. Ta bashi ya karba ya hau dubawa sannan yasa cd din a cikin computer
"Babu komai a ciki Hajjaju. Empty disk ne."
"Na shiga uku."
"Sannan..." Sai ta durkusa a wajen
"Baki daya takardun nan fake ne, ba sune originals din ba, sannan takardun properties din Alhaji ma duk fake din ne."
"Shikenan, na gama, na gama." Ta zare dankwalin kanta ta dora hannu aka ta fara ihu, sai kuma ta tuno da wani abu, tayi wajen da daddy yake kwance da sauri ta kama jijjigashi
"Ashe tsawon lokacin da muka dauka yaudara ta kake? Cuta ta kake ban sani ba? Wallahi sai na ga bayanka, sai na karar da duk dangin ka, ba zan je kasa ni kadai ba, idan ma mutuwa ce sai dai mu mutu tare, bakin azzalumi."
Wayar ta, ta fara kashewa d sauri sannan ta saka shi ya kira gardawan nan suka zo suka dauke mata Daddy, suka saka shi a mota suka dau hanyar barin garin.