Rumbun Qaya page 27

Rumbun Qaya page 27

Rumbun Qaya page 27

*RQ*

  

      27


****Murza gefen goshin sa yayi ya juya kawai ya koma ciki dan yana so ya tabbatar da lafiyar Daddyn. Ya Nabeela ce ta karaso da maigidan ta, ta tarar da Daddyn ana kan yi masa gwaje-gwaje domin gano ainahin matsalar sa, domin akwai wasu allurai da Hajiya Zeenat tasa aka dinga yi masa a spinal cord dinsa wanda zai yi wuya idan basu yi effecting dinsa ba. Hankalin ta yayi matukar tashi da taga halin da Daddyn yake ciki, ta dinga kuka suna rarrashin ta dole ta dawo reception ta zauna saboda ta kasa yin shiru kwata-kwata. Babu kowa a ciki da ya rage sai Kamal wanda yake tsaye a kofar cikin jin zafin abinda Hajiya Zeenat ta aikata. Waje  ya fito bayan kiran Lamido ya shigo wayar sa, ya daga daga chan kofa sukayi magana sannan ya koma ciki suka cigaba da tsaiwa da jiran tsammani. 

   Driving Aryan yake amma ya kasa controlling fushin sa, sosai ya zama baya ganin gaban sa saboda yadda yake ji tamkar zuciyar sa zata yi bindiga, me yasa kowa sai ya dinga boye masa komai akan me? Zai iya rantsewa a yanzu be san waye Kamal ba, be kuma san komai a kanshi ba duk kuwa da tsawon lokacin da suka dauka a tare suna tare da juna. A dan lokacin da be gaza kwana uku ba ya zama heartbroke, daga wajen mutane masu matukar muhimmaci a wajen sa, duk kuwa da ya gano komai da sukayi sun yi shi saboda farin cikin sa amma me yasa sai an boye masa? Me yasa yake zama na karshe da zai san komai akan abinda ya shafe shi? Gefe ya samu yayi parking ya dora kansa a saman steering motar kawai dan ya tabbatar idan ya cigaba da tukin zai iya yi wa kansa mummunar illah. Ya dade a haka har sai da wani me wucewa ya zo ya kwankwasa masa glass din motar, ya dago ya kalle shi sai ya tuno a in da yake wanda shaf ya manta ma. Kunna motar yayi kawai ya bar wajen ya juya zuwa asibitin dan be wani yi nisa da chan din ba. A reception ya hadu da su Ya Nabeela taci kuka ta koshi kawai sai ya zauna a gefen ta ya rike hannun ta a cikin nasa ya sunkuyar da kansa. A gefen sa Kamal ya zauna ya dora hannun sa a saman kafadar Aryan din, dagowa yayi suka had'a ido sai ya juyar da kansa ba tare da yace komai ba. Shima Kamal din be masa magana ba dan ya san ba zai saurare shi ba. Cigaba da zama sukayi har zuwa sanda Dr ya fito suka tashi gaaba daya suka isa wajen sa, bayani yayi musu akan zasu maidashi ICU sannan ya wuce su kuma duk jikin su ya kara sanyi sosai.

   Gida suka fara lallaba Ya Nabeela ta tafi saboda dare yayi sosai ya zama sai Kamal din da Aryan kadai har aka gama duk processing komai Kamal ya biya Bill din duk Aryan na kallon sa amma yaki masa magana shima kuma ya share shi kansa tsaye yake abubuwan sa dan ya riga yasan waye Aryan duk abinda zai kallon sa kawai zai, ya kuma san abun da ya tsana a shareshi idan ya nuna yayi fushi ka nuna sam baka san yanayi ba yafi saurin sakkowa. Wasu allurai likitan yace a siyo a pharmacy Kamal yasa hannu zai karba Aryan ya karbe yana bata fuska


"Zan iya kula dashi."


Dariya ce ta kwacewa Kamal ya fizge takardar sannan yace


"I can do it too, kai I'm already doing it ma."


"Ya isa hakan toh, I will take over."


"Waya saka?"


"Ni na saka kaina."


"Kana magana da hukuma ne please, so ka gyara maganar ka kaga yaran chan jiran umarni suke kawai."


Tsaki Aryan yaja kawai ya barshi a wajen yana masa dariya. Daya daga cikin yaran ya bawa takardar ya samo allurar a pharmacy ya kawo sannan ya kaiwa likitan. Sosai Aryan ya cika fam da abinda Kamal din yake masa, amma ya kyale shi dan ya lura so yake ya tike shi kamar yadda Adam yake masa a ko da yaushe.


     Tare suka jera suka tafi masallaci da asubah dan a zaune suka kwana, sukayi sallar suka sake jerowa suka dawo sai a lokacin Kamal yace


"Zanje gida na dawo, sannan inaso ka san Hajiya Zeenat ta shiga hannu, sai ka shirya shari'ah da ita."


   Da sauri Aryan ya kalle shi,amma sai yayi tafiyar sa ya barshi a tsaye cike da mamakin Kamal din. Bin sa yayi da sauri ya sha gabansa yana kallon sa


"Yaushe? Me ya faru? Ya akayi duk hakan ta kasance?"


"Sai naje naga Madam naga yadda ta kwana tukunna, kasan me iyali gashi na barta ita kadai kuma ba wani Jin dadi take ba, mayi magana dai yanzu sauri nake."


"Please kamal, tell me everything dan Allah."


"Ka daina fushin kenan?"


"Dan Allah!"


"Labari ne me tsawo, amma from abinda ka gani a jikina zaka gane cewa duk plan ne, kuma a karshe munyi nasara, yanzu sai kayi taking over daga nan, da mun tura ta kotu aiki ya koma hannun ka. Sannan, barrister Matawalle yana tare da mu, duk da yana yi ne ba dan mu din ba shima saboda tasu matsalar amma a kalla mun samu strong evidence na videon ta da yake wajen sa wanda shine mafarin komai, kuma shine zai yi linking duk wani abun da ta aikata tare da me taimaka mata."


"Huhh!" Ya sauke ajiyar zuciya cikin wani irin yanayi ya rungume Kamal din kwalla na taruwa a idon sa. Kwallar shima Kamal ya goge a boye sannan ya bubbuga bayan Aryan din yace


"Over to you Barrister ARYAN!"


Bud'e masa kofar Aryan yayi ya shiga motar ya zauna sannan ya rankwafo jikin window yace


"I owe you Kamal. Bansan yadda zan saka maka duk abinda kayi min ba, you are more than a friend Kamal, bayan abinda ya faru da su Mummy na daina trusting duk wani friendships, na daina yarda da kowa da komai saboda ban taba ganin irin amintar su ba. Sannan abinda ya faru tsakanin Daddy da Barrister Matawalle ya kara tabbatar min da babu abokan gaskiya a duniyar nan. Amma banda irin ka Kamal, kai na daban ne."


"Kana mantawa baka saka sir a farkon sunan, ko kana so ka kwana a guard room ne?"


"Sorry Sir.' ya matsa baya ya sara masa sukayi dariya a tare


"Kaje ciki, zanje an dawo, we have alot to talk about akan case din, kafin na yi maka handing over na dukkan evidence din plus wanda na karba a wajen ka."


"Ok Sir, duk yadda kace haka za'a yi."


"Duk abinda nace? Kayi alkawari?"


"Eh nayi, anything."


"Ok, ka kira Raihana a waya."


"Me? Noo I can't me yasa Zan kirata?"


"Yanzu kace anything, so dole kayi."


"Please banda wannan, zanyi komai amma banda wannan."


"Hadda shi, call her and apologies again."


"Not now gaskiya, I'm sorry."


"Ok! Bari naje, ka koma ciki."


"Ok." Ya matsa daga jikin motar suka ja yana kallo har suka fita daga gate din sannan ya juya ciki yana jin sa wani irin sakayau kamar wanda kaya ta makalewa a makogwaro ya samu nasarar zare ta.


   


****Da farko Hajiya Zeenat ta dauki abun wasa dan tayi tunanin normal yan sanda ne suka kamota sai data ganta a office din DSS sannan jikinta ya soma rawa tasan tabbas ba wasa a lamarin su. Bata taba hasaso wannan ranar ba, bata kuma taba tunanin duniya zata juya mata baya haka ba, komai da take yi a cikin tsari da plan take yin sa abinda ya saka take nasara a duk abinda tasa a gaba, sai dai wannan karon ta gama tabbatarwa karyar ta kare bata da kowa dan hatta wadanda take tunanin suna tare da ita ashe duk karya ne. Sun yi outsmarting dinta sunyi wasa da brain dinta kamar dai yadda ta dinga yi da tasu a baya. Laifukan ta masu girma ne idan har zasu taru akanta toh tabbas tasan hukuncin da ya dace da ita shine na kisa, mutum daya ne take da yakinin be juya mata baya ba har zuwa karshe sai dai ta tabbatar daga zarar ya samu labarin kamata shikenan zai cikawa wandon sa iska. SAN Mandawari wanda duk wata nasarar ta da taimakon sa ne dan hatta shari'ar abby shine ya tsaya mata har sukayi nasarar tura shi gidan yari.

   Tana durkushe a k'asan dakin da aka ajiye ta ita kadai. Babu haske ko kad'an gashi an karbe komai nata an saka wayarta ana monitoring duk wata wayar da zata shigo daga daren zuwa wayewar garin yau. Budo kofar da aka yi ne ya bawa haske damar shigowa cikin dakin ta yinkura da sauri daidai lokacin da suka shigo su uku, Kamal ne a gaba sai Lamido sannan Abby a karshe, a gaban ta ya tsaya kamar jiya ta daga kan ta da k'yar ta kalle shi shima ita yake kallo, yana ganin lokacin da ta sauya masa rayuwa a saman fuskar ta, lokacin da suka kala masa sharrin kisa. 


***Karar motar Yan sanda ce ta fara isowa kafin su hauro saman su shigo dakin su zagaye shi, kalmar da ogan cikin ya furta a lokacin da yake ce masa "you are under arrest." Ita tafi komai tsaya masa a lokacin ya kasa tantancewa abinda suke nufi da kalmar sai da yaga wani yazo ya damki hannun sa ya zura masa ankwa sannan abun ya shiga dawo masa a kansa.

   Sakkowa sukayi dashi bayan sun dan gama dudduba dakin suka bar wasu cikin yan sandan a dakin hade da likitan da ya karaso a lokacin. Zeenat na zaune a falon ta hada kai da guiwa tana ta rusa kuka tamkar ranta zai fita, Nabeela na daga jikin kujera itama tana kuka sai Aryan da yake kiran mummyn sa a rikice yake gaba daya. Ammy ce ta shigo jin hayaniya a gidan ta tarar da mummunan tashin hankali a take ta yanke jiki ta fadi kasa sumammiya amma Abby yana kallo haka suka fice dashi suka saka shi a mota. Cikin kankanin lokaci labari ya soma zagaye gari anacewa aminin miji yaci amanar mijin bayan yayi tafiya, ya haike wa matar sa bayan nan kuma ya kashe ta har lahira. 

    Runtse idon sa yayi yana jin kamar a lokacin komai yake faruwa, yana jin da zai iya komar da hannun agogo baya da sai ya goge sanin da yayi wa Daddy iyakar rayuwar sa, amma duk da haka ba zai manta abinda yayi masa ba, ba kuma zai taba yafe masa ba har duniya ta nade. 

  Da niyyar yi mata magana Abby ya shigo amma sai ya fasa saboda baya ko son ganin fuskar ta, juyawa yayi ya bar Kamal da Lamido a dakin daga baya Lamido ya fita jim kadan wasu mata kedaru suka shigo, suka gaishe da Kamal din sannan ya basu umarnin su dan sassamata yayi ficewar sa. Jibgarta suka fara yi sukayi mata likis dan sai da suka farfasa mata jikinta sosai fatar nan me laushi da sheki tayi dud'um nan da nan ta sauya fasali da halitta ta koma kamar ba ita bace Hajiya Zeenat yar gayu me aji da tarin kudi.


***Adam na kwance a gida yana baccin asara bayan ya tabbatar da ya gama hada Aryan da Raihana ya kuma tabbatar zuwa lokacin Aryan ya yi mata korar kare shikenan hankalin sa ya kwanta ya samu damar shekar baccin sa hankali kwance duk da kuwa yana son yarinyar amma haka zai hakura bashi da asara tunda Aryan dai be same mu. Wayar sa ce ta farkar dashi ya daga yana jan tsakin katse masa baccin da yake yi amma abinda yaji a cikin wayar sa sashi wartsakewa nan da nan ya diro dga gadon ya hau neman dogon wandon sa da ya jefar tun a hanya da daddare. Da k'yar ya zura ya fito hankalin sa tashe da mummunan labarin da ya samu na zuwan DSS companyn su suka kuma yi awon gaba da wasu daga cikin securities din dake zaune a gate sannan suka hada da Abdulhakeem da wani abdullahi da yake a office din Adam din. A hanya kafin ya karasa office din ya sake samun labarin da ya sake rikita shi ya sashi chanja alakar motar tasa daga zuwa office din zuwa nearest police station dan tuni labari ya warwatsu a social media an kama Hajiya Zeenat Mukaddas bisa zargin yinkurin kashe mijinta, Alhaji Ibrahim Mukaddas,salwantar da rayukan wasu mutane da kuma wasu manyan laifukan da ta aikata wanda take da daurin gindi daga chan sama. Duk in da Adam yake tunanin zai sameta yaje amma sai ya tarar bata nan, haka ya wuni cur yana zagaye karshe ya hakura da ya gano tabbas daga saman ne aka kama dan be kawo DSS bane ba, kuma ko da ace ya sani bashi da hanyar tunkarar wajen domin bakin rijiya ba wajen wasan yaro bane ba.


    ****Matsawa Daddyn ya dan soma yi ya dan daga dan yatsan sa kafin ya bud'e idanun sa a hankali, da sauri likitocin suka rufa a kanshi dan dama suna cikin dakin harda Dr Mahfouz da ya iso da safe, sun yi kokari sosai wajen samun daidaituwar numfashin shi saboda irin shak'ar da Zeenat tayi masa bayan ya riga ya gama zama so weak saboda ajiye shi da tayi babu ruwa babu abinci, sun yi kokari sosai wajen samun daidatun amma kuma ya sake komawa wani baccin me matukar nauyi wanda suke tunanin zai yi wahalar gaske ya farka a nan kusa duk kuwa da yana numfashi amma idan har ya kai wasu hours be farka ba, toh tabbas ya shiga coma sai dai wani ikon Allah kuma. 

   Dr Mahfouz ne ya samu karfin guiwar yi musu bayani nan da nan Ya Nabeela ta rushe da kuka Aryan kuwa shiru yayi kawai ba tare da yace uffan ba, sai Kamal da yayi kokarin samun karin bayani daga bakin Dr Mahfouz din sannan ya yi kokarin kwantar musu da hankali.


"Zan iya ganin shi?" Aryan yace yana kallon Dr Mahfouz


"Zaka iya, muje." Bin bayan sa yayi suka shiga dakin dake cike da wasu irin na'urori manya manya, daga kofa ya hangi Daddyn a kwance sambal tamkar bashi ba, dan har wani irin dashewa fatar jikin sa tayi kasancewar babu riga a jikin sa an kakkafa masa wasu irin na'urori da suke nuna duk abinda yake fafuwa a jikin nasa.


"Zai tashi Dr?" 


"Muna fatan hakan Aryan, amma... Yana bukatar addu'ar ku."


"Ok, Allah ya bashi lafiya."


"Amin ya Allah, in sha Allah komai zai wuce, abinda ya faru shine ta dade tana cutar da shi baa sani ba, akwai wata kwaya da take bashi a ruwa ko lemo da take kashe jikin mutum slowly, shi ta dinga bashi tsawon lokaci sai yanzu damage din ya nuna, so amma muna iya kar kokarin mu akai sannan ko ma sai kun hada da addu'a sosai, we are monitoring his kidneys yanzu haka and we are hoping ya zama babu abinda ya faru dasu."


"Allah yasa." 


"Amin Amin."


Shiru sukayi na dan wasu sakanni, sannan Aryan din ya juya ya fita cikin karyewar zuciya. 
🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*_SAK'ON ZAFAFA BIYAR GA AL'UMMAR K'ASAR NIJER_*🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪


_ASSALAMU ALAIKUM MASOYA MAKARANTA LITATTAFAN ZAFAFA BIYAR JAMA'AR NIJER_


_DIMBIN GAISUWA DA FATAN ALKHAIRI A GAREKU_


_MUN FIDDA TALLA MUN BADA NUMBER DA ZAKU TUNTUBA,TO AMMA WANCAN NUMBER DA ZAKU TUNTUBA BA'A SAMUNTA,A HALIN YANZU GA SABUWAR NUMBER DA ZAKU TUNTUBA DON TURA KATI KU SAMU DAMAR SHIGA GROUP NA ZAFAFANKU BIYAR_


+227 90 16 59 91


*Yan jamhuriyyarmu nigeria kuma😂🇳🇬🇳🇬,zaku ci gaba da pyment ne ta account dinmu na*


Maryam sani

0022419171

ACCESS bank


Ku tura shaidar biya ga


+234 903 318 1070


*Katin waya ko VTU zaku tura ta wannan number*


09166221261Litattafan dai sune kamar haka


RUMBUN KAYA Hafsat rano


A RUBUCE TAKE Huguma


IDON NERA Mamuhghee


KI KULANI Hafsat xoxo


DAUD'AR GORA Billynabdul*Muna godiya da zabin zafafa biyar*🤝🤝🤝🔥🔥🔥🔥

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post