Rumbun Qaya page 28

Rumbun Qaya page 28

Rumbun Qaya page 28

 *RQ*


     28


****Kwana daya tak da faruwar abun Daddy ya dawo a hargitsa, tuni Hajiya Zeenat ta riga ta juya masa labarin abinda ya faru wanda ya samu komai a baibai. Yadda yake jin tsanar Abby da abinda ya aikata masa me girma ne, musamman video da Hajiya Zeenat din ta aika masa tun a chan din. Be taba tunanin zai ci amanar sa haka ba, dan a duniya ya yarda dashi fiye da yadda ya yarda kansa. Labarin da Hajiya Zeenat ta shirya shine dai yake cigaba da yawo a gare hakan ya kara tunzura daddy yaci alwashin sai ya ga bayan Abby ko da kuwa zai karar da duk abinda ya mallaka.

    Barrister Mandawari shine ya shiga shari'ar a lokacin kuma yana da sama sosai dan haka shine ya sauya komai na abinda ya faru ya maida shi kan Abby din wanda dama ya dade yana envying nasa da duk nasarar sa. 

   Babu wata hanya da suka barwa Abby da zai kare kansa, haka yana ji yana gani suka tura shi prison ba tare da ya aikata komai ba.
***Zaune Ammy take ta hada kanta da guiwa tana kuka sosai, tun bayan da aka karkare shari'ar kuma aka tisa keyar shi zuwa prison ta saddakar da rayuwar ta da ta yaranta ta shiga cikin babbar matsala. Zagaye suke da ita dukkan su, Lamido na tsaye daga saman kanta kasancewar shine babba, Sadiq na durkushe a gabanta sai Haidar da yake rike da hannun karamar kanwar su Raihanawadda take kuka itama ganinAmmyn na kuka ba tare da tasan abinda yake faruwa ba.

  Banko gate din gidan aka yi da mugun karfi, duk suka mike a firgice, kafin su farga har sun shigo ciki, suka shiga watsi da kayansu suna watso musu su waje, dukkan su kukan suka saka da kyar suka kyale su, suka dauki abinda zasu dauka suka fito daga gidan, su kuma suka saka padlock suke datse suka tafi bayan sun watso musu da ragowar kayan nasu waje. A daidai lokacin motar da Hajiya Zeenat ke ciki ya shigo layin, tayi murmushi ganin su a kofar gidan tsaye cirko-cirko, dan dama sun yi magana da Daddy tasan kuma zai aikata komai a yadda yake jin tsana da kiyayyar su a lokacin. Lamido ne ya durkusa ya dauki Raihana da hannun days, dayan hannun nasa ya rike jakar yan kayan su da suka samu suka dauka. Sauran abubuwan na hannun Sadiq da Haidar da ya rike hannun Ammyn suka soma takawa cikin yinkurin barin layin ba tare da sun lura da ita ba ma. Tana hangen su, har suka fice gaba daya daga layin dake dauke da tsirarun mutane suna kai kawo. 


"Wannan shine sakamakon duk wanda yace zai ja da Zeenatu!" Tace tana murmushi. Yanzu rayuwar zata dawo sabuwa taci karen ta babu babbaka tayi rayuwa me inganci.  Gate din gidan aka bud'e driver ya saka motar ciki ya samu gefe daya yayi parking sannan ya fito da sauri ya bud'e mata kofar, ta fito a hankali ta shiga takawa zuwa balcony din da zai sadaka da cikin gidan.

  

   Kuka Aryan yake sosai yana kiran mummyn sa, Nabila na rik'e dashi tana rarrashin sa amma sam yaki yin shiru, yau kwana wajen arba'in kenan da rasuwar Mummyn, amma  ya kasa hakura, babu irin lallashin da ba'a yi masa ba amma kullum sai yayi kuka saboda shakuwar da suka yi da mahaifiyar sa.

    Da kallo Zeenat ta bisu cikin zuciyar ta,ta ayyana sune kadai suka rage mata a yanzu, sune kadai matsalar ta. Siririn tsaki taja a ciki -ciki, dole zata bi komai a sannu kafin tayi maganin su. Karasowa tayi da nufin rike hannun aryan din ya fizge da sauri yana matsawa baya.


"Don't touch me!" 


Ya fada da karfi yana sake yin baya da sauri


"Aryan nice fa? Aunt Zeenat come here my boy."


Tace tana sake matsowa, cigaba da matsawa yayi yana mata kallon tsana kafin ya juya da gudu ya haye sama. Kallon Nabila tayi wadda itama ita take kallo tace


"Ina Adam?" Ta zame jakar hannun ta tana jan tsaki


"Yana falon Mummy yana kallon cartoon."


"Ok." Tace tana zama a cikin jerin manya manyan kujerun dake zagaye a falon.


"Jeki kawo min ruwa." 


Juyawa tayi zuwa kitchen ta dauko ruwa da cup ta kawo mata, ta ajiye,.


"Kije ki dubo yaron nan, dan wannan bakar zuciyar tasa zata iya sakashi aikata komai,yaro karami da shegiyar zuciya kamar fir'auna, sai kace akan sa aka fara mutuwa. Mtsw!" 


Taja tsaki tana balle murfin ruwan


Bata ce koma ba, dan ita dama ba me yawan magana bace ba, ta juya tana kokarin kama staircase din sai ta dakatar da ita 


"Ki turo min Adam."


"Toh." Tace ta cigaba da hawa a hankali zuciyar ta na mata zafi.


   A bedroom din Mummy ta same shi, ya kwanta lamo a saman gadon ta yana kuka k'asa -kasa, da sauri ta karasa ta dagoshi ta rungume shi suka sake fashewa da kukan a tare, Sun dade a haka kafin ta cika shi ta shiga share masa hawayen dake bin fuskar sa


"Ka daina kuka kaji? Idan kana kuka kanka zai yi ciwo."


"Ni Mummy!" 


"Zata dawo ne, very soon kaji? Amma sai ka daina kuka ka daina yiwa Anty Zeenat rashin kunya."


"Bana son ta, I hate her. Muguwa ce sosai ita ta dauke min mummy ta."


"Shsshh!" Ta rufe masa baki da sauri tana kallon kofar da ta bari a bud'e,tashi tayi da sauri ta rufo ta sannan tace


"Don't say that again kaji? Ka daina fada kar Daddy yaji."


"Na daina." Yace yana kwanciya a jikin ta. 


"Good boy."


Tace tana share kwallar da ta zubo mata. Tunowa tayi da sakon Kiran Adam ta mike da sauri ta fita, taje ta same shi yayi kacha-kacha da falon ya zubar da ledojin munch-it da caprison ko ina.


"Anty Zeenat na kiran ka."


"Ta dawo?" Yace yana tashi daga riginginen da yayi yana kallo


"Tana falon k'asa." 


Fita yayi ta jawo karamin dustbin ta kwashe komai da ya zubar sannan ta share wajen tas ta goge. Muryar Daddyn su taji a falon sa na sama, tayi saurin komawa bedroom din Mummy ta rike hannun Aryan ta dawo dashi dakin sa, sannan ta rufe dakin Mummy din ta sauko kasa. 

   Fada Daddyn ya hau ta dashi ta in da yake shiga ba tanan yake fita ba, bata san takamaimai laifin da tayi masa ba,sai da ya gama banbamin tana durkushe sannan ya hau kwala wa Aryan kira, kin sakkowa yayi yasa key a kofar dakin nasa yana jin Daddyn yayi ta kiransa har ya hakura ya kyale shi.
***Gida Aryan ya koma da safe bayan Ya Nabeela tazo asibitin da nufin ya shirya. Dakin sa ya shiga da ya watsa ruwa ya sauya kayan sa ya fito ya tarar da Adam yana jiransa a falo. 


"Me yake faruwa?" Ya tambaya yana kallon Aryan din da yanayin sa


"Baka sani ba?"


"Eh ban sani ba, nake so ka sanar dani."


"Da yake ka ajiye ni ne ko? Toh ban sani ba."


"Please Aryan, ba fada nake so ba, just tell me, me yake faruwa ina Mom dita?"


"Ban sani ba, dan bani da lokacin batawa, kawai dai mu hadu a kotu, koma me yake faruwa idan kaje chan zakaji."


Wucewa yayi da nufin sauka Adam din ya riko shi da sauri


"Aryan dan ALLAH! Help me."


"Me kake so nace maka Adam?"


"Me ya faru?"


"Kamar yadda ka samu labari haka ne,kuma DSS ne sukayi kamen bayan hakan bansan komai akai ba, ina tare da daddy a asibiti."


"Bashi da lafiya?" Ya fada cike da tashin hankali 


"Eh." Kawai yace cike da kosawa,ya karasa sauka. Da sauri Adam din yabi shi suka sauka a tare yana shiga mota shima ya shiga tasa yabi bayan Aryan din.***Raihana na zaune tare da Daadah tana gyara mata kanta, suna yar hirar su, hankalin ta baki daya yana kan hirar da suke yi bata ji ringing din da wayarta take yi ba har sai da Hydar da ya shigo lokacin yace


"Ba wayarki bace ba?"


Sai lokacin ta ankara ta tashi da sauri ta dauki wayar sai dai sunan da ta gani akan screen din wayar ya saka ta jin kamar an sare mata kafarta, tayi sakale da wayar a hannu ta saci wajen da Hydar yake tsaye yana kallon ta


"Aryan ne?" Yace yana kafe da ido


Daga masa kai tayi alamar eh


"Share shi please, me zai ce miki?"


"A ah Aliyu, barta ta daga, ki daga mana kiji mai zai ce." 


Daadah tace 


"Daadah me zai ce mata? Mutumin da ya yi mata kora irin ta kare, kinji tsawar da yake mata ne? Idan tana da hankali ai ba zata dauki wayar sa ba."


"Duk naji wannan, a kalla dai taji me zai ce mata ko?"


"Ko me zai ce ma dai, muna nan akan bakan mu gaskiya, babu wata alaka da zata sake hada mu dasu, babu."


"Toh wai Hydar duk hakilon nan da kake, shi Aryan din yace yana son Raihana ne?"


"Ke Raihana yace yana son ki ne?"


Girgiza kai tayi tace


" A ah."


"A ah toh, ba abinda kake tunani bane ba, maza kirashi kiji dalilin kiran nasa."


Juyawa kawai Hydar yayi ya fice be sake cewa komai ba.


"Kinsan zuciya irin ta Hydar."


"Daadah wai dama Hamma Hydar yasan Aryan ne?"


"Hmm.. ya sanshi Raihana."


"Ok,wai menene yake faruwa? Naji tun ranar yana ta jaddada babu alaka a tsakaninmu dashi, kuma naji suna maganar da Abby ma har naji ya dau zafi sosai akai."


"Labarin na da tsawo Raihata, amma je kira shi kiji me yake faruwa sai ki dawo na baki labarin komai, be kamata a bar ki a duhu ma musamman tunda yanzu kema kin shiga cikin abun."


"Bari muga ko zai sake kira Daadah, ko mistake yayi dama ba kiran zai ba."


"Wa yace miki? Kira shi dan Allah wallahi tausayi yake bani."


"Kai Daadah, kamar kin sanshi?"


"Jeki dai ki kirashi kizo."


"Ok." Tace ta wuce dakin ta. Ta samu gefen gado ta zauna sannan ta shiga kan number Aryan din kirjinta na bugawa kamar zai fito, wani abu me kama da tsoro take ji musamman sanda wayar ta fara ringing sai taji kamar da bugun zuciyar ta yake tafiya.


"Hello." Yace cikin husky voice dinsa wanda yasa ta yin tsam


"Helloooooooo Raihanaaa?"


Yace yana tashi daga wajen da yake zaune, har cikin kwanyar kanta taji yadda ya kira sunan nata, karo na farko kenan da ya taba fadan sunan ta amma sai taji sunan yayi sounding wani iri kamar ba nata ba 


"Helloooo." Ya sake maimaitawa


"Hello." Tace a gajarce


"Kina jina?"


"Umm."


"Ok, kina lafiya?"


"Lafiya Lou."


"Ok, sai anjima."


"Sai anjima?" Tace a ranta cike da mamakin sa, 


"Ok." Tace a sanyaye


"I'm sorry, bye."


Ya kashe wayar, hankalin sa gaba daya yana wajen Dr da ya fito daga dakin Daddy shiyasa ya amsa wayar a gajarce, ya kirata ne ya sake bata hakuri kamar yadda Kamal yace kuma zuciyar sa ta amince da kiran dan haka kawai ya samu kansa da son ji daga gare ta, sai dai kuma bata daga wayar ba har ta katse lokacin kuma ya shiga wata sabgar sanda kuma ta kira yayi busy. Wayar ya tura a aljihun dogon wandon sa ya koma ciki yana shafa sumar gashin kansa Adam na tsaye ya dafe kansa tun bayan da ya ga halin da Daddy yake ciki jikin sa yayi sanyi sosai.


   ***Da daddare Kamal ya shigo asibitin, dan gaba daya be shigo ba ranar yana kan case din Hajiya Zeenat din in da suka gama tattare dukka bayanin wajenta da fari bata yarda ba amma daga baya da ta ji uwar bari sannan ta bud'e baki wasu abubuwan ma babu dadin ji dan ba karamin basu mamaki tayi ba dan wasu abubuwan ma basu san ta aikata su ba sai da tasha matsa sannan ta bud'e baki. Abu daya ne Abby ya dage ta fada musu in da Ahmad yake ko in da ta kaishi amma ta kafe akan bata san komai akai ba,dan tun bayan lokacin bata sake samun labarin sa ba, bata kuma sake ganin mutumin da ta ajiywa shi ba a lokacin da ta dauke shi, burin ta kawai a lokacin ta salwantar dashi kawai yadda zata fi samun saukin mallake daddy da duk dukiyar sa idan ya zama bashi da d'a namiji a matsayin magaji.

   Hannun Aryan ya kama bayan ya fito daga dakin Daddyn suka fito waje, suka samu gefen bishiya suka tsaya ya kwashe masa duk yadda akayi ya sanar dashi sannan yace 


“Zaka ji ni shiru na kwana biyu, ina da yakinin zakayi abinda Ya dace wajen ganin mun yi nasara.”


“Karka ce min tafiya zakayi ka barni?”


“Kamar dai haka ne, ba zan dawo ba kuma har sai ka nemo ni.”


“Ban gane ba!?”


“Zaka gane idan aikin ya biyo ta kaina.”


“Kamal please waye kai? Kana sani tunani wallahi.”


“Na lawyer bane ba kai? Find out please. And please be fast about it dan zan zauna zaman jiran ka ne.”


“Ba zaka fada min ba?”


“Yes! Na riga na gama part dina.”


“Ok. I will find out.”


“Please do, cox I’m eager.”


“Ok, stay safe please. Ko ina zaka make sure to stay healthy. I will look for you kamar yadda kace in sha Allah.”


“That’s my friend. Allah ya bawa Daddy lafiya Ya kuma baka nasara.”


“In sha Allah Captain!” Ya tsara masa Sannan ya kame suka kwashe da dariya


“Did you call her? Ka kirata?”


“Wa? Ban kira ba bani ma da wannan lokacin ni.”


“Ok let me find out.” Ya zaro wayar sa. Da sauri Aryan ya warce yana hararar sa


“Me kake shirin yi?” 


“Kiran kanwata zan yi naji ko ka kira ka sakè bata hakuri.”


“Akan me wai? Ka damu da ita sosai ni da ko tuno sunan ta ma banayi.”


“Ikon Allah. Waye ya gama mana wakar I love her ranar?”


“Ni ne, amma ai ba love na love nake nufi ba, na addinin muslunci.”


“Hard guy.”


Ya dake shi a chest sannan yace 


“please ka dan bude zuciyar nan taka haka nan mana, Atleast we are one step toward victory.”


“We still have alot Kamal, kama hajiya zeenat kamar dai eye opener ne, we have to find out ina Ammy take? Ina Ahmad?”


“Sannan sulhu sakanin daddy da Alhaji Matawalle.”


Kamal yace


“Anya? Haka zai yiwu?”


“Gashi nan dai. Muyi addua sosai akai. Dan inaso mu kulla alaka me karfi bayan wannan ma, ko da yake kamar fa an ce min raihana tana da saurayi ko? Shaf na manta nake ta wannan abun.”


Ya dan bubbugi kansa alamar yayi kuskure. Yanayin fuskar Aryan din ce ta sauya nan da nan, ya yi kicin da fuska ya hade rai kmar bashi ne yanzu suke magana normal ba.


“Kasan ashe wai akwai wani guy da yake ciki, ta fada min sam na manta amma dai babu wani official magana akai gaskia.”


“Toh ni menene nawa da zaka din ga fada min? Ina ruwana?”


“Oh na manta ba ruwan ka, bari na wuce gobe da safe zan zo na dauke ka mu je Office dina.”


“Ba zan je ba.”


“Me yayi zafi ?” Ya fada yana kokarin hana kansa dariya


“Ba komai , kaje bari na koma ciki sai anjima.”


“Ok sai anjima. Ma yi waya.”


“Oho.” Aryan yace yana juyawa Ya bar Kamal a wajen dariya na neman kashe shi

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post