Rumbun Qaya page 32

Rumbun Qaya page 32

 

Rumbun Qaya page 32 Hausa novel by Hafsat Rano

*RQ*


    32


***A kwance ta sameta tana kuka,ta zauna gefen ta


"Kina so kanki yayi ciwo ne? Toh ki daina kukan nan haka, babu ne takura miki a gidan nan, idan ma soyayya kuke ai ba haramun bane ba."


"Ni ba soyayya muke ba Dadah, ni bana son shi ya fiye masifa da fada."


"Toh ba shikenan ba? Tunda kinsan haka sai daina kukan haka nan, suma duk neman rigima ce tasu, ai ba haramun bane ba, kuma kowa ba da KADDARAR sa ba ?"


"Duk yasa kowa yana mun fada, Abby na ma be taba min fada ba sai yau, ga Hamma na Hydar shima tun a kano yake ta min fada, nima duk abinda basa so bana son shi."


"Toh ai shikenan, sai ki tashi kije ki wanko fuskar nan, kizo mu fita yau chan gida zamu,sai dare zamu dawo naga me dafa musu abinci kuma."


"Dadah fushi kikayi dasu?"


"Eh mana, akan me zasu takura miki akan abinda ke ba shine ma a ranki ba? Bar su munyi fushi sai sun zo biko."


"Waye zai kaimu toh?"


"Ba zamu hau motar kowa ba, gwara ma Sadeeq idan yana nan,shi babu ruwan sa da wannan fi'ilin nasu, kira shi ma idan yana kusa yazo ya kaimu yau chan zamu wuni ki shiga cikin yan uwanki kuyi hirar zumunci ba ko da yaushe kina kunshe a daka ba daga ke sai basawan yayyan ki wanda basa son gaskiya, ko wa zai ganki yace yana so suna kaf kaf dake? Yadda suke manyan tuzurai haka suke so ki zauna kema saboda rashin gaskiya"


"Kai Daadah,yau su Hamma sun tsokanawa kansu."


"Dama fa a wuya nake dasu Allah, dole fa sai kin fita wani zai gani ya kyasa, ko a dangi ko a gari, amma duk inda zaki suna biye dake wannan ai kamar ma kashe kasuwa ne."


Dariya ta fashe da, Dadah tayi tsut da fuska dan ita har zuciyar ta da gaske take, dole a sake sabon zama lokaci yana tafiya su bar yarinya ta sarara.


"Bafa wasa nake ba kike dariya, da gaske nake kuma wannan karon dole a sake lissafi, ni da zai yiwu duk a hade ku dasu a sha biki wallahi."


"Ashe kin gaji da gani na Daadah na?"


"Yo ko na gaji dake ko ban gaji dake ba Raihanatu ke fa 'ya mace ce, gidan wani zaki kuma dole."


"Ai shikenan tunda neman head kike dani, dama kin daina so na kwata-kwata."


"Soyayyar ce ta jawo ai, dan haka ki tsaida hankalin ki waje daya kina jina? Ki bawa masu son ki dama ku daidaita, babu wanda lokaci yake jira su bar ganin kina da wannan jar kalar namiji da kin wuce lokacin ki zai daina ta taki."


"Wannan maganar dai a barta sai next time Dadah, bari na wanko fuskar mu tafi."


"Kyaji dashi, yi sauri kafin azahar tayi su shigo neman abinci, sun ga tsiya yau. Shima Abban naku aure ya dace dashi,sai na koma nima cikin yan uwana."


"Ai ko aure Abby zai ba in da zaki Dadah, nan ne gidan ki,."


"Sai dai ki tafi dani naki gidan idan an miki auren ke, amma ba zan zauna ba."


"Ni ai muna jone Dadah, kafata kafarki ba wani da zai raba mu."


"Karya, irin ku ne da an kaiku sai aji luf an samu gidan miji anyi shiru, wata tara a ishemu da kukan jinjiri."


"Bari na dai wanko fuskar tawa Dadah." Tace da sauri ta shige toilet din dan ta lura yau Daadan a sama take neman rikici take da kowa. Fita tayi ta ja mata kofar tana sababi.***Adam na tsaye a jikin stairs yana jiran fitowar Aryan sai gashi ya fito da dan saurin sa.


"Lafiya?"


"Yes, naji kana waya yau za'a kai mom kotu, so nake naji gaskiyar maganar."


"Eh yanzu haka ma chan zani, kotun dake Normansland."


"Why are you doing this?"


"Wai tambaya ta kake?"


"Yes, menene yasa kake son ganin bayana."


"Bayan ka? Ina bayan? Kasan me kake cewa kuwa? Who are you by the way ma?"


"Ba ta kai nake ba dan Allah Adam, kazo kotu sai kaji duk charges din da yake kanta, sai kasan irin maganar da zakayi."


"Ba zaka taba succeeding ba in sha Allahu, heartless human being."


Murmushi kawai Aryan yayi ya wuce ya bar shi a wajen, yasan ba a hayyacin sa yake ba, shiyasa ma ba zai biye masa ba, dan yana da abun yi, daga kotun wani kauye zai wuce wanda ya samu labarin Hajiya Zeenat din ta taba kai wa wani mutum ziyara garin. Shi zai je ya gani dan yana da yakinin akwai wani abu da ya sani game da ita. 


***Sune tsaye a gaban kotun aka shigo da ita, tayi masifar sauyawa tamkar ba ita ba, hayaniya ce ta kaure a cikin kotun kowa yana kokarin tofa albarkacin bakin sa, masu daukar hoto na dauka a boye. Alkaliyar da zata saurari karar ce tayi calling attention din mutane aka samu wajen yayi shiru, sannan aka soma sauraran karar ta bakin lauyan gwamnati tare da Aryan. Bayan an karanto mata dukkan laifukan ta, ta kuma musanta, sai justice Fatima ta bada umarnin aike wa da ita gidan dan kande sannan an d'age sauraran karar zuwa sati biyu masu zuwa in da za'a dawo a fara gabatar da shaidu.

   Da sauri Adam ya mike daga in da yake tsaye yayi wajen ta, akayi saurin tare shi ya hau ihu yana zagin Aryan aka samu aka fitar dashi daga kotun sannan itama aka fice da ita ta kofar baya.

  

   Aryan na tsaye tare da wasu manyan barrister message ne ya shigo wayar, tun kafin ya bude yasan waye ya turo message din dan tun jiya ya fara aike masa da sakon akan shari'ar yana kuma kokarin kara masa kwarin guiwa akan abinda yake gaban shi, dan shine ma ya tura masa address din mutumin da kauyan da yake zaune kuma zai je ya ganshi dan so suke a sati biyun nan su karasa tattara duk shaidar da suke bukata 


"I'm proud of you.KM."


Murmushi yayi kawai ya kashe wayar ya maida ita aljihu, sannan sukayi sallama ya fito daga cikin kotun. Habeeb ya hanga tsaye jikin motar sa, ya karasa yana duban shi da mamaki


"Barka da rana Sir."


"Ina ka shiga wai Habeeb?"


"Na danyi tafiya ne. Amma na dawo yanzu zamu cigaba in sha Allah."


"Ya akayi kasan ina nan?" Ya tambaye shi da mamaki sosai


"Oga Kamal ne ya sanar dani."


"Kaima cikin su kake ko?"


"Na'am?"


"I know, dama tun farko ban yarda ba, nasan akwai wani abu dole, baka yi mun kama da driver ba, lallai Kamal, akwai tarin abubuwa game dashi da ban sani ba."


"Haka aikin yake sir, mu cigaba da tafiya a yadda muka faro, dan Hajiya Zeenat ba ita kadai bace a wannan tafiyar ba, tana da support kuma suna kokarin duk yadda zasuyi su dakile ka, muna cigaba da bincike a kansu amma dai for now kana bukatar tsaro."


"Allah ya kyauta, muje toh." Ya mika masa key din, ya bud'e masa kofar ya zauna sannan ya zagaya shima ya zauna a mazaunin driver sannan ya kunna motar.


  ***A rana irin ta yau tarihi ya maimaita kansa, kamar yadda a irin wannan ranar Hajiya Zeenat take cike da murnar tura Abby prison sai gashi a yau an nufi gate din da ita. Hankalin ta ne ya tashi ta shiga tuno makamanciyar ranar. Goron dutse prison aka kai ta ita, ana zuwa aka tura ta prison 1 (welcoming prison) In da ake ajiye duk wanda ya shigo prison din a ranar kafin gobe a rarraba kowa prison din da ya dace da shi.

   Abby na zaune yana kallon komai da yake faruwa ta cikin wayar sa, duk da akwai sauran zama a shari'ar amma ko a yanzu hakan burin sa ya cika, idan komai ya dawo normal zai yi kokarin sake nesanta kansa da wani abu da zai iya hada su da Alhaji Mukaddas, baya ko bukatar ganin sa shiyasa ma ko zuwa be yi ya duba shi ba, haka ranar da aka kama Hajiya Zeenat din be ko bi ta kansa ba bare ya nemi ganin sa duk kuwa da ya samu labarin yana cikin matukar wahala.

  Lamido ne ya shigo ya zaune a gefen sa, ya kalle shi sannan ya ajiye wayar


"Kaga komai Abby?" 


"Na gani, ko a yanzu buri na ya gama cika, matsala daya ce nake tsoron ta, Aliyu ya bani labarin alakar kanwarku da Aryan, ni kuma gaskiya ba zan amince ba, ba zan yadda ba, babu wata sauran alaka tsakaninmu da mutanen nan,."


"Hydar din ya fada min nima, kuma in sha Allah babu abinda zai faru, Raihana yarinya ce me biyayya ba zata taba son abinda bama so ba."


"In sha Allahu, ya isa hakan alakar da akayi a baya ta rashin sani ta wadatar,."


"In sha Allah."


"Yaushe zaka tafi wajen aikin ne?"


"Karshen satin nan zan tafi, ina dan karasa hada abubuwan da zan bukata a chan ne."


"Ok Allah ya taimaka ya bada sa'a, dama case din nan da kuke kai ya hana ayi muku transfer din tuntuni."


"Eh shine yasa."


"Ok, Allah yayi riko da hannayen ku, ya taimaka muku ya tsare ku a duk in da kuke."


"Amin Abby."


"Sai a fara maganar saka rana, zaman ya isa haka nan, ni ba mace kuma babu, dan haka dole ayi abinda ya dace."


Sosa kansa yayi


"In sha Allah."


"Madallah. Bari na dan shiga ciki na kishingida ko zan dan samu bacci kafin la'asar, idan Sadeeq ya dawo kace inason ganin shi."


"Ok a huta lafiya."


"Allah yasa."***

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post