Rumbun Qaya page 33

Rumbun Qaya page 33

Rumbun Qaya page 33 Hausa novel by Hafsat Rano

 *RQ*


   Page 33


©Hafsat Rano


  



***Tafiya kilometres hamsin da hudu ta kaisu garin na Rano, karon farko da Aryan ya taba zuwa garin duk da yana samun labarin cigaban da suka samu sosai ta fannoni daban daban musamman bangaren ilimin zamani da kuma kasuwanci da yan garin suka rike na man petrol, gas da kerosene. Sun kafu sosai akan harkar kuma suna samun arziki sosai dan tun daga kofar garin zaka tabbatar da hakan ganin tsarin gine-gine masu matukar kyau da suka zagaye garin ga wasu manyan duwatsu da suke karawa garin kyau da tsari. Akwai abokan Daddy sosai da suke harkar m ai a garin wasu suna haduwa idan an tashi taro ko kuma wani abun ya hada. Rage gudun motar Habeeb yayi sanda suka karaso kofar asibitin garin yayi parking bisa umarnin Aryan din sannan. Da kansa ya fito ya samu wasu mutane a zaune ya gaishe su sannan ya tambaye su in da zasu bi su je layin gidan sarki. Kwatance sukayi masa yadda zai gane yayi musu godiya ya koma mota ya nunawa Habeeb in da zasuyi, suka daga musu hannu suka wuce. Kasancewar karamin gari kowa ya san kowa basu wani sha wahalar gano gidan ba, maimaita sunan mutumin Aryan yayi, yayi daidai da sunan mahaifin Kamal, amma duk da haka be kawo komai ba, ya dauka kawai coincidence ne sunan yazo daya. A kofar gidan sukayi parking ya kalli layin me dan fadi ya hango wani dattijo a zaune a kan wata tabarma gaban wani dan karamin masallaci tare da wasu a zaune a gaban sa kamar suna daukar karatu, bayan su babu kowa a layin sai yan wasu yara suna wasan taya suma daga wani gefen. 


"Mu karasa wajen mutanen chan Habeeb."


"Ok." Yace ya kashe motar suka fito suka nufi masallacin. Zuwan su wajen ya saka dattijon katse karatun da yake na littafin sunanin nabiy da yake karantar da manyan unguwar duk bayan sallar la'asar har zuwa magriba sannan suyi karatun alkurani me girma bayan magriba din zuwa Isha, daga nan sai su hadu suci tuwon dare har zuwa karfe taran dare sai kowa ya shige gida sai kuma asubah idan da rai da lafiya. Durkusawa sukayi har k'asa suka gaishe su dukka, suka amsa a sake sannan ya tambaye su daga ina dan be gane su ba.


"Daga kano muke, munzo wajen Malam Hassan sarki ne, daga chan titi aka kwatanto mana wanchan gidan."


"Ni ne nan Hassan sarki, sannun ku da zuwa."


Kallon juna sukayi shi da Habeeb sai Aryan yayi murmushi ya kara gaishe shi sannan yace magana ce take tafe dasu. Tashi yayi bayan ya nemi afuwar wanda suke tare yace su taso su biyo shi, suka nufi gidan da suka yi parking. A jikin motar Habeeb ya tsaya shi kuma Aryan yabi bayansa zuwa cikin zauren gidan, me dauke da wani dan madaidacin daki.


"Bismillah shigo." 


Yace masa bayan ya shiga ya zauna, shiga Aryan yayi ya zauna a ladafce sannan ya shiga yi masa bayanin dalilin zuwansa, 


"Yanzu haka an soma shari'ar tata, kuma ana bukatar samun hujjojin da zasu bada damar yanke mata hukunci."


Ya karkare yana duban Malam Hassan din


"Tabbas lokaci yayi da azzulumar matar nan zata girbi duk abinda ta shuka, naji dadi matuka kuma zan bada gudunmawa ta dari bisa dari, zan zo har kotun na bada shaidar duk abinda ya faru ranar, amma kafin nan inaso na sanar da kai yadda komai ya kasance. Gyara zama Aryan yayi cikin zakuwar son jin labarin duk da kuwa baya duniya a sanda abun ya faru amma ya samu labari daga baya, kuma yasan yana daga cikin abin da har Mummy ta koma ga Allah be bar zuciyar ta ba, ta kan tuna tayi kuka sosai dan ba karamin tashin hankali bane a raba ka da dan ka tun yana jinjiri.


_"Kana jina yaro? Watarana bayan Magriba daf da ishai na fito daga gida ina kokarin karasawa masallaci a lokacin ni ne ladanin masallacin ni ke kiran sallah, a daidai wata kwalbati dake da dan tazara da masallacin na ji kamar kukan jinjiri, matsawa nayi domin tabbatarwa cikin tsananin mamaki na ga jariri babu ko riga a jikin sa sai pampers ya cure waje daya yana kuka sosai, waigawa nayi da tunanin zan ga wani amma babu kowa kasancewar layin babu mutane ba kuma kasafai aka fiya bin sa ba idan dare saboda masu kwacen waya da yan iska. Ni kaina a lokacin saurin da nake yasa ni yankewa nabi ta lungun saboda yafi kusa da masallacin akan ta chan titi. Jaririn ne ya cigaba da kuka na juya da nufin tafiya ta amma sai naji chak na tsaya, ba zan iya ba, rashin tausayi na be kai haka ba, dawowa nayi na duka nasa hannu na dauko shi ya kara chanyarewa da kuka, hawaye ne suka biyo gefen kunci na, na share ina rike shi kam kam kar ya sullube dan ba iya daukar jarirai nayi ba ko haihuwa akayi a gidana bana iya dauka har sai sunyi kwari. Lungun na sake bi da nufin na shiga cikin mutane sosai sannan na nemi taimakon su mu mika jaririn gidan mai gari ina shigowa wani dan lungu sai na hadu da wasu maza su biyu suna tsaye a dan wani lungu. Ina zuwa daidai in da suke tsaye dan da fari ban ma lura dasu ba, sai da na matso daf naji kuma sun min magana sannan na ankare."Malam Hassan barka da wannan lokaci." Gudan yace min yana kallon na. Amsawa nayi ina kallon yanayin suturar da take jikin su ta rashin d'a da wata uwar suma da suka tara akan nasu babu kyawun gani. Kallon hannu na sukayi nayi saurin cewa "jariri ne aka yar dashi a cikin kwata, ko su waye suka yar dashi basuyi adalci ba, basu kyauta ba kuma basu da imani, gidan me gari zan mika shi nasan in sha Allah za'a iya samun iyayen sa in da anan kusa suke." Babu wanda ya ce uffan a cikin su, sai cigaba da kallon na da sukayi , ganin haka kawai yasa nA juya da nufin yin tafiyar ta,sai ji nayi an fisgoni kamar wani karamin yaro, nayi baya kamar zan fadi suka shataloni sannan suka shaka min wani abu me warin gaske, Allah ne ya kiyaye ban yada jinjirin hannu na ba. Tun daga nan na rasa hankali na, bansan ina nake ba. Tsawon awoyi na dauka a hakan kafin na farfado na ganni a wani daki me duhun gaske. Kukan karamin jariri ne ya karade dakin a hankali sai haske ya maye gurbin duhun da ya mamaye dakin. Matata Rabi na hango a zaune a kuryar dakin rike da jaririn sai lokacin na tuna abinda ya faru, na yinkura da sauri zan mike naji an daure min kafa ta da hannu na. Rabi? na kira sunan ta, kanta a kasa tana kuka bata san na farfado ba sai da nayi magana ta dago a zabura. "malam." Tace cikin muryar kuka, "me muke anan Rabi?" Na tambaye ta ina kallon jaririn hannun nata da har lokacin kuka yake. "Wasu maza ne suka je har gida suka dauko mu ni, suka kawo ni nan sannan suka ce wai kashe mu zasuyi." Subhanallah, me mukayi musu." Ban sani ba, amma koma menene Malam akan jaririn nan ne, naji suna maganar kashe shi zasuyi ma, wallahi Malam inason shi, lokaci daya son shi ya shiga zuciya ta, dan Allah kar mu bari su kashe shi, ina son shi." Menene alakar su da jaririn toh? Tabbas shine dalilin da yasa su kawo mu nan, kuma ina kyautata zaton akwai wani abu da suke boyewa." Jin ana taba kofar ya saka mu yin shiru, samarin nan ne tare da wata mace wadda sai daga baya na gane wacece, itace Hajiya Zeenatu Mukaddas, itace kuma ta sace jaririn ta sa aka jefar dashi, mu kuma muka tsince shi, bamu taba haihuwa ba tsawon lokacin nan, dalilin da yace muka gudu da jaririn kenan muka raine shi, bayan mun gudun da safe a hanyar barin garin muka samu labarin batan dan gidan Alhaji Ibrahim Mukaddas, tabbas a lokacin mun so juyawa mu maida musu dansu, amma bamu samu dama ba saboda biyo mu da sukayi suka kuma yi yinkurin sake kwace shi, mun riga mun san idan har muka barsu suka tafi dashi kashe shi zasuyi, shine muka roke su, su bar mana shi da alkawarin ba zamu bari ya san su waye iyayen sa ba, zamuyi nisa da garin kano ba zamu sake waiwayowa ba. Kaji abinda ya faru a lokacin muka bar gari muka tafi chan Kaduna muka soma sabuwar rayuwa, muka raini jariri har ya kai munzalin saurayi daga nan muka tattaro muka dawo Kano mahaifar mu, daga nan ne kuma muka sanar dashi komai game da rayuwar sa, sannan muka bashi damar neman iyayen sa da kansa saboda a lokacin ya kai matakin da babu wanda zai iya takashi. Yanzu haka a cikin Kanon yake zaune da matar sa tunda da ma daga bayan dawowar mu nan gidan dan uwana ya koma da zama a chan kanon saboda makaranta."_


Hannu Aryan yasa ya goge hawayen da suka biyo gefen kuncin sa, ya dago kansa ya kalli mutumin yayi masa murmushi


"Yanzu yana ina?"


"Ya tafi umrah shi da mai dakin shi, amma a cikin satin nan muke saka ran zasu dawo in sha Allah."


"Allah ya dawo dasu lafiya, ba zan iya fasalta yanayin farin cikin da na tsinci kai na a ciki ba, Baba."


"Allah sarki, wasu mutanen ne basu da imani sam, mutane irin su Zeenatu zasu iya komai akan cikar burin su, dan ko da muka yi alkawarin yin nisa bata daina bibiyar mu ba, ta dinga tsoratar damu tana jaddada mana in dai muka karya alkawari sai taga bayan mu, na kuma tabbatar da zata aikata duk abinda tace."


"Karshen ta yazo Baba, in sha Allah da duk masu taimaka mata, fatan dai zaka daure ka shigo ranar domin bada shaidar ka, sannan ina fatan zaku zo tare da dan uwana,."


"In sha Allah, nayi maka wannan alkawarin."


"Shikenan Baba, nagode sosai Allah ya kara girma."


"Amin ya Allah."


"Toh zamu koma Baba."


"Har zaku koma?"


"Eh in sha allah."


"Toh madallah, ga number waya ta idan yaso sai ka bani taka, ma yi magana kafin ranar idan akwai bukatar hakan."


"Yawwa Baba, hakan yayi nagode."


Exchanging number sukayi, Aryan ya ciro kudi a envelope ya ajiye masa, da fari kin karba yayi yace ba zai karba ba, sai da ya matsa masa sosai sannan ya karba yayi godiya duk da yanayin sa be nuna yana da bukatar wani abu ba, tsaf yake kana gani kasan yana cikin rayuwa me kyau da hutu.


  A mota ya samu Habeeb ya kwantar da kujerar ya kwanta idon sa a rufe. Sallama yayi masa ya tashi dan dama idon sa biyu, ya zauna daidai sannan ya kunna motar, Malam Hassan na tsaye yana kallon su har suka bar layin. A garin karfi magriba ta riske su, suka tsaya suka yi sallar sannan suka cigaba da tafiya. Asibiti suka wuce direct Aryan yace masa yaje kawai idan ya gama zai tafi, watakila kuma ya kwana ma. Sallama sukayi ya bashi key din ya shiga ciki. Daddy na zaune an dan saka masa pillow daga bayan sa, sai wuyan sa dake makale da neck pillow ya jingina yana kallon kowa na dakin, abinci ya gama ci wani dan uwanshi da yazo ya bashi Ya Nabeela ta tashi ta shiga toilet din cikin dakin ta wanko cup tazo ta hada masa tea tana gama bashi Aryan ya turo kofar ya shigo. Mamakin ganin Daddyn a zaune ya saka shi karasowa ciki da hanzari. 


"Daddy?" Ya zauna a kujerar dake gaban gadon yana masa kallon tausayi. Be amsa ba sai motsi da yayi da idon sa a hankali yayi masa murmushi. Waigawa yayi wajen da Ya Nabeela take zaune yace 


*Yaushe ya tashi?"


"Yau da safe."


"Baki fada min ba amma?"


"Nasan ka shiga busy, bana so nayi distracting dinka,gashi yanzu kazo ka gani, sai dai maganar ce har yanzu bata dawo ba, da tafiya amma doctor yace a hankali zai dawo normal tunda har yana cin abinci ma."


"Alhamdulillah." Ya furta yana maida kallon sa kan Daddyn


"Ya jikin? Allah ya kara sauki."


"Ya maganar da mukayi ranar Aryan?"


"Eh yanzu ne right time din, sai a fita dashi dama Dr Mahfouz yace a tsaya a ga progress din, kuma alhamdulillah akwai, amma idan aka je chan din za'a samu karin kulawa in sha Allah."


"Ok, hakan yayi, sai a tafi da Baba Rabi'u da Uncle Mamman."


"Eh, in sha Allah. Amma ke zaki kira su kuyi maganar."


"Ai Baba Rabi'un yana nan yau masallaci ya tafi, idan ya shigo yanzu sai muyi maganar."


"Ok good, wannan abun da ya faru kinga ya dawo musu da closeness dinsu da daddy."


"Sosai, da mu ma kanmu."


Shiru yayi yana tunanin ya fada musu ko ya bari tukunna, yadda zuciyar sa ta cika da son sanar musu baya jin zai iya rikewa.


" Ahmad yana raye." Ya fada yana kallon bangaren Daddyn da yake kallon sa shima


"Da gaske?* Ya Nabeela tace tana mikewa tsaye


"Kwarai da gaske, a binciken da mukayi mun gano yana raye, kuma yau na je har in da yake wajen mutumin da ya rike shi, na kuma roke shi akan su bayyana a kotun."


"Allah sarki Mummy." Ya Nabeela tace ta fashe da kuka, ta tuno masifa da tashin hankalin da mahaifiyar su ta shiga a lokacin akan batan Ahmad din. Kukan daddy yake shima ya motsa bakin sa a hankali yace


"Yana ina yanzu, ka kaini wajen sa?"


Da sauri suka kalle shi a tare, duk da maganar bata fito sosai ba amma tabbas magana yayi, girgiza kansa yayi hawayen na cigaba da sakkowa daga idon sa, yayi nadamar rusa gidan sa, da farin cikin sa da farin cikin matar sa me tsananin so da kaunar sa, yaci amanar aminin sa sannan ya ci amanar yayan sa. Kukan da yake na dauke da manufofi masu yawan gaske, yana sane yaki magana saboda bashi da karfin zuciyar da zai iya bud'e baki yayi musu magana, yace musu me toh? Kuyi hakuri ko me? 


"Daddy me kace? Magana kayi daddy?" Suka rufa akansa suna tambayar sa


"Eh, magana nayi."


"Alhamdulillah!" Suka hada baki wajen fada.


"Kira doctor Aryan." Ya Nabeela tace tana murmushi hade da dariyar farin ciki.


"Baki fushi dani ba Nabeela?" Ya tambaya bayan Aryan din ya fita duk da yasan dama ko a da din bata taba ketare maganar sa ba, bata kuma taba nuna masa ba daidai yake yi ba, hasalima a kullum nuna masa take yayi daidai saboda tsananin biyayyar ta. Da sauri ta hau girgiza kanta tana share hawayen fuskar ta


"Babu abinda kayi min daddy, da zan yi fushi dakai."


"Allah yayi muku albark." 


"Amin Daddy."


Shigowar Dr da Aryan yasa ta matsawa baya ta basu waje, ta dauki wayarta ta fita waje dan kiran Mijinta ta sanar dashi daddy ya dawo daidai. 

  Kallon Aryan Daddyn yake tayi yana so yasa idanun sa a cikin nasa amma sam Aryan din yaki kallon sa, har Dr ya gama abinda zai ya fita Aryan din yabi bayan sa jim kadan ya dawo ciki ya tsaya daga saitin kafafun Daddyn yace


"Yau aka fara shari'ar Hajiya Zeenat, an dage sauraron karar zuwa sati biyu, ina fatan ban yi laifi ba, ina kuma fatan zaka saka min albarka sannan kayi min fatan nasara."


"Allah ya taimaka ya baka sa'a, ina jiran bincike yazo kaina, domin nima me laifi ne Aryan, nayi muku laifi ku da mahaifiyar ku."


Kin kallon sa Aryan yayi dan yadda zuciyar sa ta karye da maganganun Daddyn zai iya fashewa da kuka, amma baya so ko kad'an yaji d'ar wajen tabbatar da gaskiya,duk da deep down baya fatan wani abu ya shafi Daddyn amma kuma ya zai yi? Idan har kotu ta kama shi da laifi dole ta hukuntashi daidai da laifin da ya aikata.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post