Rumbun Qaya page 36


Health College

Rumbun Qaya page 36

Rumbun Qaya page 36 Hausa novel by Hafsat Rano

Rumbun Qaya

     Page 36

****A hankali mutanen da ke cikin kotun suka dinga ficewa har ya rage saura Aryan, Ya Nabeela Kamal, Daddy da Malam Hassan. Takowa Kamal yayi a hankali zuwa gaban Aryan, ya kashe masa ido daya yana murmushi.


"Chill broh." Yace ganin Aryan din ya kasa ko da kwakkwaran motsi. Bin sa yake da ido kawai ya karasa gaban Daddy ya durkusa akan kafafunsa idanun sa na taruwa da kwalla kamar yadda na Daddyn suke cike da kwalla amma ta farin ciki.


"K...a..mal?" Ya Kira sunan sa, sai kuma ya hau girgiza kai


"Ahmad, Ahmad sunan ka."


Hannun Daddyn Kamal ya rike yana durkushen ya girgiza masa kai


"Karka takura kanka Daddy, kaga baka da lafiya."


"Alhamdulillah!" Ya furta yana goge hawayen da ke bin fuskar sa, sannan ya daga kai ya kalli Malam Hassan da yake tsaye yana kallon su yayi masa nuni da hannu alamar ya matso, matsowa yayi sai Kamal ya mike ya karasa wajen Ya Nabeela. Da sauri kamar me jiran zuwan sa ta rungume shi tana fashewa da kukan da take ta rikewa,kukan farin cikin samun Kamal din a matsayin dan uwan su. Ashe shiyasa be taba barin su ba, ya tsaya sosai a rayuwar su musamman Aryan yayi masa duk gatan da wa ya kamata yayi wa kanin sa. ya shanye bacin ran halin Aryan din duk dan ya cimma wannan burin nasa. Tun farkon ganin sa taji ya shiga zuciyar ta, har ta kan jishi tamkar aryan din a gareta. Sakin sa tayi ta kai masa duka a bayan sa ya goce yana dariya sosai.


"All this while ka sani Kamal? Amma Ka boye mana.?"


Tace tana kuka me hade da dariyar farin ciki


"Ayi min afuwa big sis, ina ta jiran right time ne, gashi kuma yazo yanzu." 


Ya hade hannayen sa waje daya alamar tayi masa afuwa.


"Shikenan, dole na na hakura ma ai,farin cikin da nake ci, amma dai akwai sauran aiki, ga kanin ka chan yayi poster go and check on him please, dan kai kadai kasan kansa."


"Troublesome guy kenan, nasan yadda zan yi handling nasa, bari kiga" 


Yace yana barin wajen ya nufi wajen Aryan din dake tsaye yana kallon su kamar ma baya gane abinda yake faruwa a wajen. Taping bayan sa Kamal yayi yana karasawa ya ratayo kafadarsa sannan yace


"Won't you say anything Oga Aryan?"


"Are you for real?" Ya nuna shi da hannun sa


"Ofcouse, or did you need a DNA test to prove it?"


"Noo." Ya girgiza kai da sauri


"Ok... Tell me ya kake ji?"


"Me yasa kayi min haka?"


"Me nayi? Mr complainer." 


Ya ture shi yana hararar sa 


"Me yasa ba zaka fada min ba,all this while ashe kai ne, tsawon lokacin nan Ka sani ka boye min, I was so shocked Kamal, bansan wane irin abu ke min yawo akai ba."


"Baka murna ne Aryan?"


"Ina yi, sosai fiye da yadda kake tunani, like bansan wanne irin abu nake ji ba kawai, kamar mafarki nake, Kamal a matsayin Yaya na? Uwa daya uba daya? Nooo."


"Yes, ba mafarki bane ba, same thing naji sanda na fara haduwa da kai, daddy, ya Nabeela. But bani da option than to hide it, idan nazo claiming zama Ahmad Hajiya Zeenat will never allow me to be close to you, zata san yadda zatayi ta bata ni wajen Daddy, wasu kuma zasu ce saboda dukiyar Daddy ne ba gaskiya nake ba, sai tasa ayi mun korar kare, so dole nayi hakuri, and watched you  tsawon lokacin nan feeling like ku din responsibility dina ne, I have to guard and protect you. Shiyasa nayi dedicating dukka komai na, just to be close to you and achieve this, gashi kuma nayi."


"Oh Ya Allah! Ka shammace ni wallahi, Alhamdulillah. Alhamdulillah."


"Won't you give me a hug?" Ya matso da hannun sa da ya bud'e. Ture shi Aryan yayi sukayi dariya a tare


"Kana da matsala, deep down nasan yadda kake ji, amma you can't show it, haka zaka yi winning heart din Raihanan?"


"Oh Ya Allah, ka dawo fa, shikenan na shiga uku."


"Na dawo amma ba a Kamal ba, a matsayin Ahmad na dawo, kuma dole ne kabi duk umarni na, I'm your boss ka sani."


"Na sani sir, kai ne ogan dama, shiyasa nake tuna maka office dinka yana jiran ka, lil bro need a break."


"Baka isa ba, nayi yaya da aiki na?'


"Please please, I'm tired wallahi."


"Then tafiya Adamawa ta kama ka, kaje ka dawo da ita." 


"Wa?"


"Babyn ka mana, a kalla zata rage ma loneliness din, sannan ta taya Ka aikin."


"Daddy yana magana." Yace yayi gaba da sauri, dariya Kamal yayi yabi bayan sa, suka karasa wajen su Daddyn, Kamal ya rike saman Wchair din ya shiga tura Daddyn a hankali suka fito daga cikin kotun. A harabar suka hadu da Abby da Lamido jikin wata mota tsaye suna magana da wani lawyer, Lamido ne ya taho wajen su ya mikawa Kamal hannu suka gaisa sannan ya bawa Aryan hannu ya gaida Daddyn da Baba Rabi'u.


"Congratulations Lt Kamal, I'm so happy for you." 


"Thank you sir, nagode for all your support."


"Karka damu."


"Aryan kula da Daddyn bari mu gaisa da Barrister."


"Kuje tare, zan kula dashi." Baba Rabi'u yace


"Ok." Suka bi Lamidon zuwa wajen da Abbyn yake tsaye. Har k'asa suka russuna suka gaishe shi ya amsa kadaran kadahan sannan yayi wa Kamal din murna, ya shige mota be kalli wajen da Aryan yake ba balle kuma su Daddy dake gefe suna kallon su. 


"Nasir yayi fushi da yawa." Baba Rabi'u yace


"Ya chanchanci yayi fushi Rabi'u, baa kyauta masa ba, kuma an cutar dashi da yaran sa."


"Kaima Yaya ai hakan ne, iya cuta kai ma an maka."


"Still dai, amma shi be yi min ba, amma nifa, ban masa uzuri ba, na yarda da abinda aka fada min akansa bayan nafi kowa sanin waye Nasir, shi ko irin kule-kulen yan mata be yi ba, amma duk na manta na rufe ido na, na bi rudin shedaniyar mace ta kaini ta baro ni, ta raba ni da matata, ta raba ni da d'ana sannan ta raba ni da Yan uwana."


"Allah ya kyauta, ka bar damun kanka kaga condition dinka, idan ka kara samun sauki sai kaje ka bashi hakuri har gida, Allah ma muna masa laifi ya yafe."


"Haka ne kam, Allah ya yafe mana baki daya."


"Amin ya Allah."


"Malam Hassan dan Allah muje gida, a chan sai mu karasa maganar da zamuyi, dan Allah."


"Ba damuwa Alhaji, amma me zai hana mu bari ka kara samun sauki, da an fadawa Kamalu zai kawo ni har gidan."


"Um um, muyi dai yanzun, bamu san me zai faru gobe ba, dan Allah ka amince."


"Ban ki ba dama Alhaji, dama na duba yanayin jikin naka ne, amma ba damuwa muje."


"Yawwa Nagode kwarai."


"Babu komai Alhaji, yanzu ai mun riga mun zama daya."


"Haka ne."


Mota suka shiga suka bar su Aryan din zasu biyo bayan su. Motar Kamal ya Nabeela ta shiga shi kuma Aryan ya shiga tasa yabi bayan su daga karshe. Gida suka wuce direct gidan yana nan a gyare tunda dama akwai masu aiki dake kaiwa da komowa a gidan. A falon k'asa suka zauna saboda daddy aka sake sabuwar gaisuwa tsakanin Daddy da Alhaji Hassan sannan aka dora akan maganar.  Har la'asar suna tare anan aka jere musu abinci suka ci sukayi sallah sannan Malam Hassan yace zai tafi amma daddy yace sam ba in da zashi sai gobe saboda yamma yayi, yayi yayi ya bar shi ya tafi amma yaki fafur dole ba yadda yaso ya hakura.


  A gidan baki daya suka kwana, har Ya Nabeela ma da yaran ta, suna zaune ana cin abincin dare Adam ya shigo fuskar nan tasa babu walwala, ya shige su ya haye sama ba tare da yacewa kowa komai ba. Girgiza kai Ya Nabeela tayi Aryan ya kalle ta yace


"Ehen?"


"I feel bad for him."


"Kai Ya Nabeela , tausayin ki yayi yawa wallahi."


"No da gaske, be yi sa'ar mahaifiya ba."


"Ni dai I don't feel anything for him, bana jin komai kuma ba zan taba ji ba."


"Kai dashi dama baa shiri."


"Babyna tana Kira." Kamal yace yana mikewa daga table din, tsaki Aryan yaja a hankali ya harare shi


"Yaushe zata zo?"


"Kinsan kwana biyu kenan da dawowar mu, so na barta a gidan su ne ta kwana biyu, amma bari muga ko gobe sai naje na dauka ta, dan nima na fara missing dinta."


"Gaskiya ne, shiyasa kake burge ni, kamata yayi mu hada kanmu a waje daya gaba dayan mu wallahi, saboda mu rufe gaf din da muka rasa a childhood."


"Wallahi Ya nabee, dama zaa yi hakan."


"Dr ne matsalar kawai, ba zai yarda ba."


"Eh gaskiya, but zamu iya samun area daya mu gina gida, nasan zai iya yarda da hakan."


"Yes zan gwada convincing dinsa."


"Kinga idan bana nan my wife ba zatayi zaman kadaita ba, ga kanin ta nan ta aike shi sannan ga big sis incase of emergency."


"Wai ba zaka ajiye aikin ba? Ka dawo gida?"


"Ba yanzu ba, akwai abubuwan da nake son nayi achieving."


"Ok, best of luck kanina, Allah ya baka sa'a."


"Amin, kinga ta kara kira, bari na daga kar nayi laifi."


"Oya, Mr Romeo."


Tunda suka fara maganar Aryan be saka musu baki ba, abincin sa yake ci hankali kwance kamar ma baya wajen. Sai da yaji sun kai karshe sannan ya ture plate din da yake gabansa, ya dauki tissue ya goge bakin sa ya mike rike da toothpick a hannun sa ya kalli Ya Nabeelan


"Zan hau sama."


"Ok, zaka watsa ruwa ne?"


"No akwai abinda zan yi, zan sakko idan na gama."


"Ok, bari naje na duba su Amna, nasa su suyi bacci."


"Ok a shafa min kansu."


"In sha Allah."


Staircase din ya kama ya haye ya wuce bedroom dinsa yana shiga ya saka key dan baya so Kamal ya biyo shi bare yaga abinda zai. Kwanciya yayi rigingine ya jawo wayar sa dake jikin socket ya kunna ta ya shiga wajen contact dinsa yayi dialing number ta, gaba daya tsawon kwanakin nan tunanin ta yake sosai, komai yake sai ta dinga fado masa, kin kiranta yayi ko chat din yaga iyakar yadda zai iya daurewa. Abinda ya faru yanzu a dining yasa shi jin ba zai iya cigaba da pretending ba, dole ya kirata yaji lafiyar ta, sannan yaji yadda za'a yi ta dawo kawai domin hankalin sa ba zai taba dawowa daidai ba idan ba dawowa tayi ba. Ringing wayar tayi tayi har ta gama ta katse ba'a daga ba, sake kira yayi a karo na biyu duk da missed calls daya kawai yake yiwa mutum idan be daga ba shikenan amma sai gashi ya samu kansa da kira a karo na biyu hoping ta daga yaji zazzakar muryar ta me taushi da dadin sauraro. 

   Wayar Daadah ta jawo daga cikin blanket din da ta rufa mata bayan baccin ya dauke ta, wunin ranar a kwance tayi shi dauke da zazzabi me zafin gaske, wanda take yin shi dama lokaci zuwa lokaci. Tun yarintar ta dama haka take zazzabin ta me zafi sosai gashi har yanzu bata daina ba. Kamar baby haka take narke musu a duk sanda bata da lafiya suyi ta fama da ita dukkan su tarewa suka akanta suna bata duk kulawar da take bukata. Fitar Babbo Sadeeq kenan bayan bacci ya dauke ta saboda allurar da yayi mata Daadah na gyara mata kwanciyar kiran farko ya shigo, bata daga ba har ta katse da aka sake kira ne tace bari ta dauka taji waye.


"Salamu Alaykum."


Tayi sallama bayan ta daga, zaro wayar yayi daga kunnen sa da sauri ya duba number sosai ya tabbatar ita ya kira sannan ya maida wayar kunnen sa ya amsa sallama a hankali


"Bata jin dadi ne yau da zazzabi ta wuni sai yanzu ta samu bacci, sai dai ka kira anjima idan ta tashi."


"Ina wuni?" Ya gaishe ta dan bata bari sun gaisa ba ta hau yi masa bayani


"Lafiya Lou, wa za'a ce mata ya kira?"


"Aryan za'a ce mata Mama."


"Toh toh, na gane. Shikenan zan fada mata."


"Nagode Mama, Allah ya kara sauki."


"Amin an gode." Ta ajiye wayar


   Akan kirjin sa ya dora wayar bayan ta kashe, duk sai yaji hankalin sa ya tashi da aka ce masa bata da lafiya. Knocking aka yi a kofar, ya kalli kofar jiki a sanyaye ya mike, yasan ma waye yake knocking din yana budewa yayi baya ya matsa masa ya shigo.


"Me ya faru?" Kamal ya fada yana kallon yanayin sa


"Na gaji ne kawai, kai na kamar zai bursting."


"Kana shan maganin ka kuwa? When last kaga Dr Mahfouz."


"Umm... Kusan month kenan."


"Drugs din naka sun ma kare kenan."


"Abubuwa ne suka sha min kai wallahi, ba time kwata -kwata."


"Amma lafiyar ka comes first, don't joke with it."


"Tam, zanje da safe."


"Good." Ya zauna a gefen gadon Aryan din yana karewa dakin kallo


"Me kake nema?" 


Ware hannu Kamal yayi ya fada saman gadon yana kallon sama


"Hoton mummy zaka bani please kanina."


"A nawa?"


"Ko nawa, zan siya saboda na mallake shi."


Ya fada sounding so down idanun sa ma sun nuna yanayin da ya shiga. Takowa Aryan yayi ya zauna a gefen sa sai Kamal din ya mike yana kallonsa


"Kayi hakuri, kowanne bawa da tasa KADDARAR. Imanin mumini baya taba cika har sai ya yarda da kaddara me kyau ko mara kyau."


"Haka ne, thank you."


"Bari na dauko maka album din, har na ranar sunanka akwai, mummy ta ajiye komai, tana sonka so me yawa."


"Allah sarki, how i wish? Amma alhamdulillah hakan ma nagode Allah coz Ya bani iyaye masu matukar so da kaunata, masu riko da addini da amfani dashi, masu son duk wani farin ciki na a saman nasu.  Dole nayi Wa Allah godiya dan da Yaso sai ya barni a hannun baragurbin iyaye wanda zasu watsa min tarbiyya ta."


"Alhamdulillah. Alhamdulillah."


"Kasan me?" Aryan yace yana mikewa tsaye, 


"A ah."


"You are my role model."


"Wow! Da gaske?"


"Da gaske, duk abinda nake kai nake kallo, you are just like a father figure to me."


"Masha Allah, amma kake min rashin kunya."


"Ahh, sanda ina boss dinka ne fa, amma na daina yanzu."


"Yaro yaji tsoron hukuma, kaga tsaf zan saka a rufe min kai sai bayan Raihana tayi aure an kaita dakin ta."


Fasa daukar album din yayi ya dago yana kallonsa 


"Why? So kake lallai sai ka kure ni ko?"


"Yes, so nake kayi zuciya coz ina tabbatar maka idan Ka tsaya kallon ruwa kwado sai yayi maka kafa, which ba zan so hakan ta faru ba, please Aryan kayi abinda ya dace, kai ne yanzu kawai zaka iya dawo da rayuwar baya me cike da farin ciki."


"Ta yaya zan fara? Bayan kana gani irin tarbar da na samu a wajen Barr. Nasir."


"Ka kama zuciyar su mana, Raihana itace zuciyar ahalin nan, build your relationship with her, hakan dole zai saka su hakura coz farin cikin ta yana saman komai a wajen su."


"Zan iya Kana gani?"


"Why not? Don't you love her ne?"


Shiru Aryan yayi yana jin yadda heart beat dinsa ya sauya lokaci daya


"Please kayi abinda ya dace, dan Allah don't make a mistake da zai saka ka rasata."


"But already kace tana da saurayi, no na ganshi ma da ido na ya kawo ta office ranar,har ta kirashi da Honey." Ya karashe muryar sa na nuna bacin ransa. Dariya sosai Kamal ya kwashe da, ya dinga tafa hannun sa yana dariya kafin ya tsagaita


"Kaga ni ko?"


"Menene na dariyar toh."


"Baka ji yadda kayi sounding bane ba, man Ka tsaya watsa wallahi, ba ruwana."


"Na kirata ma yanzu, sai wata babbar mata ta dauka tace min tana bacci bata da lafiya."


"Ayya, shisa na shigo na ganka so down kenan?"


"Ban sani ba." Ya ajiye masa album din a gabansa yana bata rai


"Kasan me za'a yi, tafiya zamuyi kawai muje Yolan nan, zama ba namu bane ba, baa bori da sanyin jiki kar muje honey yayi mana shigar sauri."


"Kana da matsala wallahi, shiyasa bana son fada maka abu sai kayi ta mocking dina."


"Sorry oga Aryan, wasa nake maka amma dai zan siya mana ticket mu je , muyi dubiya sannan mu yada jam'iyar mu, yadda ka hadun nan da wuri zata fola amma sai ka aje girman head ka bud'e baki."


"Ya Allah!"


"Nan kuka gudo kuka bar ni?" 


Ya Nabeela da ta turo kofar ta shigo tace


"Yanzu nake shirin zuwa wajen ki." Aryan yace


"Nima hakan."


"Album zamu kalla?" Ta karaso tana kallon hannun Kamal, gid'a mata kai yayi ya matsa mata gefen sa ta zauna Aryan ya zagayo ya zauna a dayan side din suka sakata a tsakiya suka shiga kallon album din a tare.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post