Rumbun Qaya page 35

Rumbun Qaya page 35

Rumbun Qaya page 35 Hausa novel by Hafsat Rano

Rumbun Qaya

       Page 35


®️®️ Rano 


***Tsawon sati biyun nan Aryan be zauna ba, shine daga nan yayi chan har ya samu ya kammala processing tafiyar Daddyn sannan ya tabbatar duk evidence din da zasu gabatar a kotu yana hannu. Sau daya sukayi waya da Malam Hassan ya kara rokar sa ya kuma amsa masa da zasu zo in sha Allah. 

    Yana tsaye a gaban table dinsa bayan ya gama tattare hannun rigar sa zuwa sama yana jiran shigowar Zainab kafin ya shiga ya dauro alwala ganin lokacin sallah yayi. Knocking ta fara yi ya bata izinin shigowa ta shigo ta gaishe shi sannan ta ajiye takardun a saman table din ta saci kallon sa ta gefe tana jin wani shaukin soyayyar sa na sake kamata.


"Komai ya cika? Babu wata matsala?"


"Eh sir, babu."


"Ok good, sannu da kokari."


"Thank you sir, akwai abinda kake bukata ne sir."


"No babu, sallah zan na fita akwai in da zanje, zaki iya tafiya thank you."


"Ok, Allah ya bada sa'a."


"Amin." Yace ya shige toilet din bayan ya tabbatar ta fita ta rufe masa kofar. Alwala yayi ya fito ya samu dan karamin towel ya goge ruwan hannun sa da fuskar sa, sannan ya maida hannun ya saka links din ya kashe komai ya fito rike da wayar sa. A reception din ya tsaya ya dan duba abinda zai duba sannan ya leka office din su Abdulhakeem ya tarar dasu suna aiki ya kalli empty desk dinta ya kad'a kansa ya fito ya fice gaba daya daga cikin building din.


****Adam na zaune a office din shima ya hango fitowar Aryan din, waya ya dauka ya yi kira ya sanar dasu ya fito yanzu sannan ya kashe, tunda ya daure damarar ganin bayan sa toh shima zai yi nasa kokarin wajen ganin bayan Aryan din ya kuma taimaki mahaifiyar sa, a da ya kasa tunanin abinda ya kamata yayi ya taimaka mata sai da ya samu kira jiya akan maganar sannan ya zaburo,ya kuma kuduri aniyar sai ya hana shi aiwatar da komai.

  Driving yake hankalin sa na kan titin gaba daya zuciyar sa ta lula zuwa kundin tunani har be san ana bin sa ba. Wayar sa dake a silent sanda yana aiki ya maida ita shaf ya manta be cire ba tana ta faman ringing a gefen sa amma be ji ba, he was so focused akan abinda yake yi har ya kusa karasawa asibitin, sai ya tuna wata allura da ya kamata ya siya ya manta gashi an ce masa sai yaje wellcare sannan zai samu. Yana daidai wani U-turn ya tuna sai kawai ya juya motar ya koma. Juyawar sukayi suka cigaba da bin sa cikin dabara. Sai da ya isa wellcare din sannan ya dauki wayar ganin tarin missed calls din Habeeb yasa shi shan jinin jikin sa, ya waiga bayan sa da sauri amma be ga kowa ba. Da sauri ya shige cikin wellcare din sannan ya danna kiran Habeeb din.


"Kana jina? Ka jira mu a cikin wellcare din karka fito please, suna following dinka tun daga company luckily baka shiga wata hanya da babu mutane ba."


"Su waye su?"


"Idan nazo zamuyi magana, oga Kamal yace please karka fita, zai mana wuya mu iya tracing naka yanzu ma dan ka dauki wayar ne har muka ga location dinka."


"Ok, sai kinzo." Ya katse wayar ya shiga ciki ya nufi bangaren magunguna yana dubawa. Biyo shi ciki sukayi, biyu suka zauna a mota. Kamar masu siyan abu haka sukayi pretending suna dubawa har suka kawo saitin da yake suna kallon sa suna monitoring din sa. Sarai ya lura da yadda suke bibiyar sa a cikin wajen. Glass din da ya ciro a aljihun sa ya saka me dauke da camera da Kamal ya bashi yayi amfani wajen capturing abinda yake faruwa duk da ba komai ba amma yayi sa'ar samun hoton fuskar daya daga ciki. 

   Cikin casual dress Habeeb suka shigo su ma wajen su uku, kunnen sa dake makale da Bluetooth ya taba yace


"Kana ina?"


"Wajen pharmacy, ina tunanin sun shigo ciki, 


"Ok, ka shiga wani dan corridor haka muga"


"Okh." Yace ya juya ya hangi wani dogon corridor ya nufi wajen ya shiga, suna ganin ya shiga wajen suka rufa masa baya a daidai lokacin su Habeeb suma sun shigo. Su biyu suka yi wajen da Aryan din yake daya kuma ya tafi wajen receptionist din ya nemi office din manager ya nuna masa. Suna shiga lungun su Habeeb suka dirar musu, suka yi arresting dinsu a take.

  Tare wanda ya shiga wajen manager suka fito bayan yayi masa bayanin abinda ya kawo su wajen, godiya manager yayi musu suka fito har wajen da motar su take, suka tura su a ciki sannan Habeeb ya mikawa Aryan wata yar karamar na'ura ya shige motar.

  Tsaye kawai Aryan yayi cike da mamakin abinda ya faru just now, wato akwai mutanen da zasu iya goyan bayan duk zaluncin da hajiya Zeenat tayi kenan, har suyi kokarin taimaka mata da karfi da aljihun su. mutum daya ya rage DSS su kama shine SAN Mandawari shi kuma tun kama Hajiya Zeenat ya bi dare ya fice daga k'asar amma suna dakon dawowar sa wanda tabbas akwai saka hannun sa a harin nan da aka kaiwa Aryan din kuma shine mutumin da yake taimakawa Hajiya Zeenat din wanda suke da alaka me karfi tun da. Shine yayi shari'ar Abby kuma shine ya tabbatar da an tura shi prison.***Kotun ta cika makil fiye da zaman farko, Adam na gaba dan da wuri ya iso kotun dan tun kafin a bud'e ma ya iso ya zauna a mota duk abin duniya yayi masa zafi. Tun da aka kama yaran nan da suka tura su tare Aryan yake cikin zulumi duk da kamasu ba bashi da direct alaka dashi sai na wanda suka tura shi, amma kuma idan har suka shiga hannu toh fa shima bincike zai iya zuwa ta kansa. Duk da ba lallai nasa yayi wani tasiri ba saboda su din manyan masu aikata laifi ne a k'asar kuma suna da daurin kafa shiyasa a sau da yawan lokuta Hajiya Zeenat din take having way din ta, wannan karon ne dai aka mamaye ta bayan ta gama sakankancewa itace da nasara domin ta samu duk wata hujja tasu a hannu not knowing that sunyi outsmarting dinta a matsayin su na yara matasa masu ji da zarra.

  Shigowar judge din ya saka wurin ya dau shiru daidai lokacin aka shigo da Hajiya zeenat ta saka gefen mayafin ta, ta rufe fiye da rabin fuskar ta. Aryan na zaune tsakankanin manyan lawyers tare da Barrister Awais da yake leading din su.

  Shi ya fara mikewa ya gabatar da kansa ga kotu sannan lawyer da yake kare Hajiya Zeenat din ya mike shima yayi introducing kansa sannan su Aryan da Barrister Hakim da Barrister Fatima suma suka gabatar da kansu. Cikin shari'ar aka shiga kai tsaye ba tare da bata lokaci ba, Judge din ta sake karanto tarin laifukan da ake tuhumar Hajiya Zeenat din dasu wanda suka hada da zargin salwantar da rayuwar Hajiya Khadija Mukaddas, Hajiya Aysha Matawalle, satar yaro jinjiri Ahmad tun yana zanin goyo sannan tayi yinkurin kashe mijinta Alhaji Mukaddas wanda yake kwance a asibiti yanzu haka da kuma sauran laifukan. Barrister Awais ne ya sake mikewa a isa gaban wajen da take tsaye saboda yana da bukatar ta amsa masa wasu tambayoyi.


"Sannu Hajiya Zeenatu, akwai wasu yan tambayoyi ba masu yawa ba, da nake so ki amsa min." 


Idon ta akan Aryan da yake zaune daidai saitin ta yana facing dinta dan shi kadai kawai take gani a wajen.


"Kina jina? Da farko dai kotu zata so sanin alakar ki da wadannan mutanen, Aisha da kuma Hajiya Khadija."


"Kawaye na ne da muke tare tun makaranta."


"Wani abu na rashin jituwa ya taba faruwa tsakaninku? Ko sun yi miki wani abu da ya bata miki rai har kika ji bari ki salwantar da rayuwar su?"


"Objection My lord." Barrister Sule yace yana mikewa


"Me kamata Barrister Awais ya dinga jinginawa mata kalmar kisa kai tsaye ba, tunda har yanzu zargi ne ba'a tabbatar da gaskiyar ba."


"Barrister Awais ya kiyaye."


"Ok, my lord."


Komawa Barrister Sule yayi ya zauna ya yi folding hannun sa.


"Muna son sanin me ya faru ranar bakwai ga watan October, da daddare wajen asubah, a lokacin da aka samu gawar Hajiya Khadija a kwance cikin jini."


"Bansan komai akai ba, kamar yadda aka samu gawar ta haka nima na ganta,."


"Hmm."


"Abinda ya faru a ranar 7 ga watan October da misalin karfe biyar na asubah an samu gawar Hajiya Khadija a kwance a cikin jini, wanda barrister nasir Matawalle ya samu gawar tata bayan ta tura masa wani sako da misalin karfe biyun dare, in da be tashi samun sakon ba sai da asubah saboda ko a lokacin da ta tura masa sakon dare yayi, ga abinda sakon ya kunsa ya mai girma me shari'a."


  Ya mikawa daya daga cikin na zaune gaban wajen sannan shi kuma ya mika mata, ta karba ta gani sannan ta ajiye a gefe


"Kotu na sauraran ka Barrister Awais."


"Bayan Hajiya Khadija ta kama Hajiya Zeenat da abokin aikin nata sai tayi yinkurin daukar hoto a lokacin ne suka lura da ita, sannan suka biyo ta har cikin daki suka kashe ta."


"Objection My lord, ya za'a yi barrister Awais ya dinga jingina mata laifin kisa kai tsaye? Hakan yayi muni sosai, ina rokon da ya janye kalaman sa ya kuma tausasa lafuzan sa."


"Ko kana da shaidar abinda ka fada barrister?" Tace tana kallon sa


"Kwarai da gaske, ina da shaidu guda biyu, na farko shine d'an marigayiya Hajiya Khadija wanda duk da karancin shekarun sa a lokacin yana iya tuna abinda ya faru akansa, na biyu shine shaidar da aka samu a cikin CCTV camera din dake hanyar shiga dakin marigayiyar wanda ya dauki hoton hajiya Zeenat da abokin harkar ta wanda bamu iya ganin fuskar sa ba a lokacin da suke shiga cikin dakin."


"Kotu tana bukatar ganin shaidun a gabanta."


Aryan ne ya mike ya isa gaban wajen ya sake yin gaisuwa sannan ya gabatar da kansa a matsayin shaida duk kuwa da ba lallai shaidar tasa tayi tasiri ba sosai duba da karancin shekarun da yake dashi a lokacin da kuma kasancewar sa cikin lawyers masu kara. Yana maganar kirjin sa yana harbawa sosai saboda yadda a duk lokacin da ya tuna memory din yake shiga matukar tashin hankali, da kyar ya karasa maganar ya koma wajen zaman sa ya zauna dafe da kirjin sa. Ruwa Barrister Hakim ya bashi Yasha sannan ya dan samu daidatuwa. Shiru ne na dan sakannni ya bayan komawa wajen zaman Aryan din, sannan aka cigaba da sauraron karar. Sosai barrister Awais yayi kokari wajen bada hujjoji kwarara kafin ya gangaro laifi na biyu wanda yake akan batan ahmad ne. Hankalin Aryan gaba daya yana ga kofar yana lokaci zuwa lokaci yana kallon agogon dake daure a tsintsiyar hannun sa, fatan sa shine Allah yasa su karaso a daidai lokacin da ake bukatar su. 

  Ta kofar dake chan gefe Barrister Nasir matawalle suka shigo tare da Lamido sun samu delay na flight dinsu ne abinda yasa suka makara. Waje suka samu suka zauna a nutse aka cigaba da shariar.


   ***Tun da suka tashi Daddy yake faman rokon su akan su barshi yaje kotun amma suka ki, Har nurse din da ke duty yayi ma magana da ta shigo amma tace yayi hakuri Dr yazo. Hankalin sa baki daya yana wajen yana son sanin yadda zata kasance sannan yana so yaji komai game da hajiya zeenat duk da ya gano Wasu abubuwa masu yawa game da ita wanda sai lately ya gano dalilin da yasa shi shiga ya tsaya tsayin daka ya samu aka fitar da Abby, shine ya bada evidence din da ya wanke Abbyn sannan ya tsaya tsayin daka har aka fitar dashi da taimakon Kamal. Duk da ya san babu wani abu da zai fada masa ya yafe masa laifukan sa gare shi, amma duk da haka yana ganin yayi abun da ya dace, ko da ba zai yafe masa ba. Baba Rabi'u ne yazo gaban sa ya tsaya sannan yace


"Nayi magana da Dr sun yi discharging dinka, yanzu sai muje chan kotun saboda nasan hankalin ka Yana wajen."


"Nagode sosai Rabi'u, nagode." Yace cike da jin dadi. Sabuwar wheelchair din da Aryan ya siyo jiya ya jawo ya taimakawa Daddyn ya zauna akai tinda har lokacin baya tsayawa sosai akan kafarsa, dalilin da zasu fitar dashi kenan ma saboda ta wajen spine dinsa ne yake ciwo sosai. Tura shi yayi suka fito a hankali har zuwa wajen motar sa in da driver yake jiran su. Tare suka taimaka masa suka saka shi a motar sannan suka bar asibitin.

   Abby suna zama shima Daddy aka shigo dashi ta same kofar da Abbyn suka shigo, karon farko suka hadu da juna bayan lokaci me tsawo, kallon sa Abby yayi kallo me cike da tsana da ki sannan ya dauke kansa da sauri ba tare da yaji ko dar din tausayin halin da yake ciki ba, dan shima sanda ya shiga matsala be tausaya masa ba, hasalima shi ya kara kokarin kara masa matsalar sannan ya kori iyalin sa ya kwace duk wata dukiya da suka mallaka a tare ya maida ita tasa. Jikin Daddyn ne yayi sanyi ganin abbin da kuma yanayin da ya ganshi yasan ko mutuwa yake yana farfadowa saboda tsananin azaba ba zai kula Shi ba. A bayan su Baba Rabi'u ya ajiye Daddyn sannan ya zauna a gefen sa suka cigaba da sauraron shari'ar duk da kusan rabin hankalin Daddyn baya tare dashi musamman ganin Hajiya Zeenat da abubuwan da ake faduwa a kanta wanda be taba tunani ko hasashen zata aikata ba.

  Kara kallon lokaci Aryan yayi, Barrister Awais ya matso wajensa ya rada masa magana ya gid'a masa kai kawai zuciyar sa fal tsoro da zulumi. Daga waje me tsaron kofar ya shigo ya sanar wa da judge din karasowar shaidar da ake jira. Hakan yasa gaban Aryan yayi mummunar faduwa cike da tsoro yake kallon kofar haka ma daddy da Ya Nabeela da take dayan bangaren a zaune ita da Dr Farouk mijinta. Kofar ce ta bud'e, Malam Hassan sarki ne a gaba cikin shigar babbar riga shadda fara da kula jaddara wanda ya kasance shigar sa a kowanne lokaci. Wanda yake take masa baya ne yasa Aryan mikewa tsaye daga wajen zaman sa yana kallon Kamal din wanda shi kuma ko kad'an be kalli wajen da yake ba, hankalin sa yana kan Hajiya Zeenat fuskar sa a dinke tsaf babu alamun fara'a ko dariya. He looks very serious dan Aryan be taba ganin sa a irin wannan yanayin ba. Ganin Malam Hassan yasa Hajiya Zeenat tayi suman tsaye, taji kamar numfashin ta zai dauke ya bar gangar jikinta dan ko kad'an fuskar sa bata bace mata ba, duk da babu irin neman da batayi masa ba wasu shekaru baya amma bata same shi be. 


"Ya mai girma me shari'a, wannan shine mutumin da Zeenatu ta dauki jinjiri ta bashi bayan ta raba shi da mahaifiyar sa tun yana tsumma."


"Kotu zata so taji abinda ya faru daga bakin ka."


"Sunana Malam Hassan sarki, dan asalin garin Rano dake jihar Kano, ni ne mutumin da na tsinci jariri a cikin kwalabati a unguwar Tudun yola."


"Kotu na sauraran ka." Justice Fatima tace tana rubutu


"Abinda ya faru shine..."


Ya shiga bada labarin abinda ya faru tun daga farko har karshe, sannan ya dora da


"Wannan shine yaron da na tsinta a cikin ramin an yar dashi, shine kuma na raineshi har ya kai wannan munzalin." Ya nuna Kamal da yayi wani irin murmushi me ciwo ya rissinar da kansa alamar girmamawa ga me shari'ar. Ba Aryan kadai ba, Hatta Daddy, Ya Nabeela , Hajiya Zeenat , Abby, Lamido da sauran mutanen kotun sai da suka shiga mutukar mamaki.


"Kamal?" Aryan ya furta yana kallonss


_"You have to fiind me, look for me daga nan zaka waye ni."_. Abinda yake nufi kenan da yace ya neme shi dama? Kenan all this while, duk tsawon lokacin nan yana tare da brother dinsa ne, one and only brother din da yake dashi kaf duniya. Tunda yake da Kamal be taba yin abinda yasan zai bata mishi ba, be taba yin wani abu da zai cutar dashi ba, duk abinda zai yi yana yi ne saboda yayi protecting dinsa, ya kula dashi da rayuwar sa dan yafi kowa Zama dashi da karfafa masa guiwa. Hannu Kamal din ya d'aga masa ganin yadda yake kallon sa babu ko kifatawa.


"An dage sauraron karar zuwa sha biyu ga watan maris me zuwa, kotu na bada umarnin a cigaba da tsare wadda ake tuhuma har zuwa ranar da za'a dawo kotu."


Abinda kawai Aryan yaji kenan dan gaba daya hankalin sa baya kan shari'ar ya lula zuwa duniyar tunanin rayuwar su da Kamal tsawon lokaci.*_ZAFAFA BIYAR COMPLETE DOCUMENTS_**ZAFAFA BIYAR BACTH A*1.. _WUTSIYAR RAƘUMI_ 350

 *(Bilyn Abdul)*2.. _KAI MIN HALACCI_ 350

*(Miss xoxo)*3.. _BURI DAYA_ 350

 *(Mamu gee)*


4... _DAURIN BOYE_ 350

*(Huguma)*


5... _SAUYIN KADDARA_ 350

*(Hafsat Rano)*


_Duka biyar 1500_


*___________________________*

    


*_ZAFAFA BIYAR BATCH B_*1... _DAURIN GORO_ 350

*(Hafsat Rano)*


2... _ALKAWARIN ALLAH_ 350

*(Huguma)*


3... _QAUNAR MU_ 350

*(Mamu gee)*


4... _IGIYAR ZATO_ 350 

*(Miss xoxo)*


5... _GUDU DA WAIWAYE_ 350

*(Bilyn Abdull)*_Duk biyar 1500_


*_____________________________*


*_ZAFAFA BIYAR BATCH C_*


1... _MIN QALB_ 350

*(Mamu gee)*


2... _SARAN ƁOYE_ 350

*(Bilyn Abdull)*


3... _KIBIYAR AJALI_. 350

*(Miss xoxo)*


4... _ABINDA KE CIKIN ZUCIYA_ 350

*(Hafsat Rano)*


5... _SIRADIN RAYUWAR BILKISU_ 350

*(Huguma)*


_Duk biyar 1500_


*____________________________**_ZAFAFA BIYAR BACTH D_*


1... _ALKIBLA_ 350

*(Huguma)*


2... _DALAAL_  350

*(Miss xoxo)*


3... _UBAYD MALEEK_ 350

*(Mamu gee)*


4... _MABUDIN ZUCIYA_ 350

*(Hafsat Rano)*


5... _MAKAUNIYAR KADDARA_ 350

*(Bilyn Abdull)*_Duk biyar 1500_


*____________________________*


*_ZAFAFA BIYAR BATCH E_*


1... _SO DA ZUCIYA_ 350

*(Mss xoxo)*


2... _TAKUN SAAKA_ 350

*(Bilyn Abdull)*


3... _HALIN GIRMA_ 350

*(Hafsat Rano)*


4... _DAB'IZAR ZUCIYA_ 350

*(Huguma)*


5... _DEEN MARSHALL_ 350

*(Mamu gee)*_Duk biyar 1500_


*______________________________**_ZAFAFA BIYAR BACTH F_*


1... _BAKAR INUWA_ 350

   *(Bilyn Abdull)*


2... _RAYUWAR MACE_ 350

    *(Hafsat Rano)*


3... _NOOR ALB_ 350

     *(Mamu gee)* 


4... _MASARAUTA_ 350

    *(Mss xoxo)*


5... _KUFAN WUTA_ 350

    *(Huguma)*


_Duk biyar 1500_


*_____________________________*


*_ZAFAFA BIYAR BATCH G (COMPLETED)_*


1... _FARHATAL QALB_

*(mss xoxo)* 400


2... _GURBIN IDO_

*(Huguma)* 400


3... _SANADIN LABARINA_

*(Hafsat Rano)* 400


4... _INAYAH_

*(Mamu gee)* 400


5... _BABU SO_

*(Bilyn Abdull)* 400


_Kuɗinsu a yanzu 2K duk biyar_

*_ZAFAFA BIYAR 2023_*🔥🔥🔥

_*Sabuwar shekara sabon salo sabon taku,*_

_*Makaranta littafan hausa kuma masoya marubutan zafafa kuzo ga sabuwar tafiya zazzafa tazo karku bari ayi babuku *_


_*Zafafan alkaluman haziqan maruban zafafa biyar kowa yasan na daban ne,wannan karon ma sunzo da sababbin salo me kama zuciya.*_

_*ZAFAFAN MARUBUTAN SUNZO DA SABABBIN LITATTAFANSU NA 2023 Kamar haka,*_


1  _*IDON NERA*_

    Mamuhgee


2  _*DAUDAR GORA*_ ciki ka shata 

    Billyn Abdul


3  _*RUMBUN QAYA*_

     Hafsat Rano


4  _*KI KULANI*_ mallakin zuciyata

    Hafsat Miss Xoxo


5   _*A RUBUCE TAKE*_ qaddarata

    Safiya Huguma_DUKA GUDA BIYAR DIN ZAKA SAMESU A FARASHIN 1200_


Guda 5 1200

Guda 4 1000

Guda 3 800

Guda 2 600

Guda 1 400


_*zaku saka kudin a wannan account din👇*_


_*0022419171 Access Bank Maryam sani*_


Saiku tura shedar ta👇


_*09033181070*_


Idan kuma katin Waya ne zaku tura katin MTN ta wannan layin👇


09166221261
TEAM ZAFAFA BIYAR🔥🔥

MUNGODE🙏🙏❤️

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post